Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 12/15 pp. 7-11
  • Ka Kasance Da Himma Don Bauta Ta Gaskiya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kasance Da Himma Don Bauta Ta Gaskiya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi La’akari da Yesu Wanda Muke Bin Misalinsa
  • An Kamanta Gaggawa da Himma
  • Ka Kasance da Himma don Bauta ta Gaskiya
  • Ka Riƙa Tuna Cewa Ƙarshe Ya Yi Kusa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Kana Bin Kristi Sosai Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ka Yi Waꞌazi da Ƙwazo Kamar Yesu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Kana Da ‘Himman Yin Nagargarun Ayyuka’?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 12/15 pp. 7-11

Ka Kasance Da Himma Don Bauta Ta Gaskiya

“Girbi hakika yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne.”—MATT. 9:37.

1. Ta yaya za ka kwatanta gaggawa?

KANA tafiya don ka sadu da wani game da wani batu mai muhimmanci, amma lokaci ya ƙure. Mene ne za ka yi? Za ka yi tafiya da sauri.” Hakika, idan kana yin aikin da ya wajaba ka yi kuma lokaci ya ƙure, za ka ji gabanka yana faɗiwa. Wasu ƙwayoyi da suke jikinka za su soma gaggautawa, kuma za ka soma yin aiki da gaggawa da kuma sosai. Wannan yanayi na gaggawa ne!

2. Wane aiki ne ya fi muhimmanci ga Kiristoci na gaskiya a yau?

2 Ga Kiristoci na gaskiya a yau, babu aikin da ya fi gaggawa da yin wa’azi game da Mulkin da kuma almajirantar da dukan al’ummai. (Mat. 24:14; 28:19, 20) Da yake ƙaulin Yesu, almajiri Markus ya rubuta cewa dole ne a “fara” yin wannan aikin, wato kafin ƙarshen ya zo. (Mar. 13:10, Littafi Mai Tsarki) Hakika, ya dace a yi hakan kafin ƙarshen ya zo. Yesu ya ce: “Girbi hakika yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne.” Aikin girbin ba zai jira ba; sai an yi girbi kafin kaka ta wuce.—Mat. 9:37.

3. Mene ne mutane da yawa suka yi don su amsa bukata na gaggawa na aikin wa’azi?

3 Domin aikin wa’azin yana da muhimmanci sosai a gare mu, muna bukatar mu ba da lokacinmu, kuzarinmu, da kuma hankalinmu yadda ya yiwu. Abin yabawa ne, ’yan’uwa maza da mata da yawa suna yin hakan. Wasu sun sauƙaƙa ayyukansu don su soma hidima ta cikakken lokaci a matsayin majagaba, ko masu-wa’azi na ƙasashen waje, ko kuma yin hidima a gidajen Bethel a dukan duniya. Sun shagala sosai. Mai yiwuwa sun yi sadaukarwa da yawa, kuma suna da ƙalubale da yawa da suke fuskanta. Duk da haka, Jehobah ya albarkace su sosai. Muna farin ciki da su. (Karanta Luka 18:28-30.) Ko da yake wasu ba su iya zama masu shela na cikakken lokaci ba, suna ba da lokaci sosai yadda ya yiwu ga wannan aikin ceton rai, wanda ya ƙunshi taimakon yaranmu su tsira.—K. Sha 6:6, 7.

4. Me ya sa wasu za su yi rashin azancin gaggawa?

4 Kamar yadda muka gani, azanci na gaggawa yana da iyaka da kuma ƙarshe. Muna rayuwa a lokaci na ƙarshe, kuma muna da tabbaci mai yawa na Nassi da na tarihi da suka nuna hakan. (Mat. 24:3, 33; 2 Tim. 3:1-5) Har ila, babu wanda ya san ainihin lokaci da ƙarshen zai zo. Sa’ad da yake bayyana dalla-dalla game da “alamar” da ke nuna “cikar zamani,” Yesu ya faɗa cewa: “Zancen ranan nan da sa’an nan ba wanda ya sani ba, ko mala’iku na sama, ko Ɗa, sai Uba kaɗai.” (Mat. 24:36) Da hakan, zai yi wa wasu wuya su kasance da azanci na gaggawa kowace shekara, musamman idan suna yin hakan da daɗewa. (Mis. 13:12) Kana jin hakan wani lokaci? Mene ne zai taimaka mana mu kasance da azancin gaggawa ga aikin da Jehobah Allah da Yesu Kristi suke son mu yi a yau?

Ka Yi La’akari da Yesu Wanda Muke Bin Misalinsa

5. A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya nuna yana da azancin gaggawa game da hidima?

5 A cikin dukan waɗanda suka nuna azancin gaggawa a hidimarsu ga Allah, Yesu Kristi ne ya nuna misali mafi kyau. Dalili ɗaya da ya sa ya kasance da azancin gaggawa shi ne domin yana da abubuwa da yawa da zai yi cikin shekara uku da rabi kawai. Duk da haka, Yesu ya cim ma abubuwa da yawa game da bauta ta gaskiya fiye da kowa. Ya sanar da sunan Ubansa da nufinsa, ya yi wa’azin bishara na Mulkin, ya fallasa munafunci da koyarwa na ƙarya na shugabannin addinai kuma ya ɗaukaka ikon mallakar Jehobah har mutuwa. Yesu ya ba da kansa ta wajen koyarwa, ba da taimako da kuma warkar da mutane a duk inda ya tafi. (Mat. 9:35) Babu wanda ya taɓa cim ma abubuwa da Yesu ya yi a wannan ƙanƙanin lokaci. Yesu ya yi aiki tuƙuru yadda ya yiwu.—Yoh. 18:37.

6. Mene ne Yesu ya mai da wa hankali a rayuwarsa?

6 Mene ne ya motsa Yesu ya yi aiki sosai a duk lokacin da yake hidima? Daga annabcin Daniyel, Yesu ya san yawan lokaci da yake da shi don ya cim ma aikinsa bisa ma’ajin lokaci na Jehobah. (Dan. 9:27) Saboda haka, kamar yadda aka ambata, hidimarsa a duniya za ta zo ƙarshenta a “tsakiyar bakwaiɗin,” ko kuma bayan shekara uku da rabi. Ba da daɗewa ba bayan ya shiga cikin Urushalima a matsayin wanda ya yi nasara a ranin shekara ta 33 A.Z., Yesu ya ce: “Sa’a ta zo da za a ɗaukaka Ɗan mutum.” (Yoh. 12:23) Ko da Yesu ya san cewa mutuwarsa ta kusa, bai ƙyale wannan ya zama inda ya mai da hankali a rayuwarsa ba, ko ainihin dalilin da ya sa yake aiki tuƙuru. Maimakon hakan, ya mai da hankali ga yin amfani da kowane zarafi da yake da shi don ya yi nufin Ubansa kuma ya nuna ƙauna ga ’yan’uwansa ’yan Adam. Wannan ƙauna ta motsa shi ya samu almajirai kuma ya koyar da su, yana tura su zuwa kamfen na wa’azi. Ya yi hakan don su ci gaba da aikin da ya soma kuma za su yi ayyuka mafi girma.—Karanta Yohanna 14:12.

7, 8. Yaya almajiran Yesu suka aikata ga yadda ya tsarkake haikalin, kuma me ya sa Yesu ya aikata hakan?

7 Wani abu da ya faru a rayuwar Yesu ya ba da tabbaci sosai cewa yana da himma. Ya faru a farkon hidimarsa, a lokacin Idin Ƙetarewa na shekara ta 30 A.Z. Yesu da almajiransa sun zo Urushalima kuma suka ga a cikin haikali “waɗanda suke sayarda shanu da tumaki da kurciyoyi, kuma da masu-musanyan kuɗi, suna zaune.” Mene ne Yesu ya yi, kuma yaya hakan ya shafi almajiransa?—Karanta Yohanna 2:13-17.

8 Abin da Yesu ya yi kuma ya faɗa a wannan lokacin ya tuna wa almajiran Yesu kalaman annabci na zabura da Dauda ya rera: “Himma domin gidanka ya cinye ni.” (Zab. 69:9) Me ya sa suka tuna waɗannan kalaman? Domin sai mutumin da yake da irin wannan himmar ne zai yi wani abu da ya ƙunshi irin wannan kasada da haɗari mai girma. Ballantana ma, masu iko a haikalin, wato, firistoci, marubuta, da sauransu ne suka goyi bayan kasuwanci na mugun riba da ake yi a wajen. Ta wajen fallasa da kuma kawar da ƙullinsu, Yesu ya mai da kansa magabcin shugabannin addinai na wannan zamanin. Yayin da almajiran suka yi la’akari da yanayin yadda ya dace, hakan ya nuna ‘himma domin gidan Allah’ ko kuma himma don bauta ta gaskiya. To, mene ne himma? Dabam yake ne da gaggawa?

An Kamanta Gaggawa da Himma

9. Ta yaya za a kwatanta himma?

9 Wani ƙamus ya ce “himma” tana nufin “ɗoki da kuma son biɗan wani abu,” kuma tana nufin sha’awa da kuma ƙwazo. Hakika Yesu ya nuna dukan waɗannan a hidimarsa. Saboda haka, juyin Today’s English Version ya fassara wannan ayar cewa: “Ibadata ga gidanka, Ya Allah, ya cinye ni kamar wuta.” Abin farin ciki, a wasu harsuna na gabas, wannan kalmar “himma” ta ƙunshi sashe biyu da a zahiri tana nufin “zafin zuciya,” kamar dai zuciyar tana cin wuta. Ba abin mamaki ba ne cewa almajiran sun tuna da kalaman Dauda sa’ad da suka ga abin da Yesu ya yi a haikalin. Me ya sa a alamance zuciyar Yesu take cin wuta, kuma ta motsa shi ya aikata hakan?

10. Mene ne “himma” take nufi kamar yadda aka yi amfani da ita a cikin Littafi Mai Tsarki?

10 An samo kalmar nan “himma” da ke cikin zaburar da Dauda ya rubuta daga kalmar Helenanci da sau da yawa aka fassara “kishi” a sauran wurare a cikin Littafi Mai Tsarki. A wani lokaci juyin New World Translation ya fassara shi, “bauta wa Allah kaɗai.” (Fitowa 20:5; 34:14; Joshua 24:19.) Wani ƙamus na Littafi Mai Tsarki ya ce game da wannan kalmar: “Ana yawan yin amfani da ita a batun aure . . . kamar yadda mata ko miji take son mijin ya so ta ita kaɗai, hakan nan ma yake da Allah, yana son bayinsa su bauta masa shi kaɗai.” Saboda haka, himma kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta ta ba biɗin wani abu da ƙwazo ba ce, kamar yadda wasu masu kallon wasanni suke goyon bayan rukunin da suke so. Hakan nan ma, himma da Dauda ya yi daidai ne, domin bai amince da ɓata sunan Jehobah ba, amma yana da marmarin kāre sunan ko kuma ya daidaita wani laifi da aka yi wa Jehobah.

11. Mene ne ya motsa Yesu ya ƙoƙarta da himma?

11 Almajiran Yesu ba su yi kuskure ba wajen haɗa kalmomin Dauda da abin da suka ga Yesu ya yi a haikalin. Ƙoƙartawar da Yesu ya yi ba don yana da daidai lokacin da aka ba shi ba amma don yana da himma ko kishi don sunan Ubansa da kuma bauta ta gaskiya. Sa’ad da ya ga zagi da saɓo da ake yi wa sunan Allah, sai ya nuna himma ko kishi kuma ya aikata daidai ga yanayin. Sa’ad da Yesu ya ga cewa shugabannan addinai suna wulakanta da kuma cutan talakawa, himmarsa ta motsa shi ya taimaki mutane, ya kuma furta kaito ga shugabannin addinai masu wulakanci.—Mat. 9:36; 23:2, 4, 27, 28, 33.

Ka Kasance da Himma don Bauta ta Gaskiya

12, 13. Mene ne shugabannin addinan Kiristendam a yau suka yi game da (a) sunan Allah? (b) mulkin Allah?

12 Halaye da kuma ayyukan mutane da suke da’awa suna bauta wa Allah a yau ya yi daidai da na zamanin Yesu in bai fi ta ba ma. Alal misali, ka tuna cewa abin da Yesu ya fara koya wa mabiyansa su yi addu’a game da shi ya shafi sunan Allah ne: “A tsarkake sunanka.” (Mat. 6:9) Shin shugabannin addinai, musamman limaman Kiristendom, suna koya wa mutane su san sunan Allah kuma su tsarkake ko su ɗaukaka wannan sunan kuwa? Akasin haka, suna ƙarya game da Allah da irin waɗannan koyarwa kamar su Allah Uku Cikin Ɗaya, kurwa marar mutuwa da kuma wutar jahannama, suna sa Allah ya kasance gaibi, da wuyar fahimta, marar-tausayi, har ma azzalumi. Sun kuma ɓata sunan Allah ta wurin ayyukan ban kunya da munafuncinsu. (Karanta Romawa 2:21-24.) Bugu da ƙari, sun yi iyakar ƙoƙarinsu don su ɓoye sunan Allah, har ma sun cire sunan daga fassarar Littafin Mai Tsarkinsu. Da haka sun hana mutane kusantar Allah da kuma ƙulla dangantaka da shi.—Yaƙ. 4:7, 8.

13 Yesu ya kuma koyar da mabiyansa su yi addu’a don Mulkin Allah: “Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” (Matt. 6:10) Ko da yake shugabannin addinai na Kiristendam sun maimaita wannan addu’a sau da yawa, sun aririce mutane su goyi bayan siyasa da wasu ƙungiyoyi na ’yan Adam. Ƙari ga haka, sun raina waɗanda suke ƙoƙari su yi wa’azi kuma su ba da shaida ga wannan Mulkin. Saboda haka, mutane da yawa da suke da’awa su Kiristoci ne ba sa tattauna game da Mulkin Allah, kuma ba su ba da gaskiya a gare shi ba.

14. Ta yaya limaman Kiristendam suka rage muhimmanci Kalmar Allah?

14 Sa’ad da yake addu’a ga Allah, Yesu ya faɗa dalla-dalla: “Maganarka ita ce gaskiya.” (Yoh. 17:17) Kafin ya koma sama, Yesu ya nuna cewa zai naɗa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” don ya yi tanadin abinci na ruhaniya ga mutanensa. (Matt. 24:45) Ko da sun yi saurin da’awa cewa suna koyar da Kalmar Allah, shin limaman Kiristendam sun yi aikin da Ubangijin ya ba su da aminci ne? A’a. Sukan faɗa cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa almara ce ko kuma ƙage. Maimako su ciyar da mutanensu da abinci na ruhaniya, da hakan su ƙarfafa da kuma wartsake su, limaman suna ƙaiƙaya kunnuwan masu bi da falsafa na ’yan Adam. Ƙari ga haka, sun bijire daga mizanan Allah na ɗabi’a don su koyar da abin da suke kira wai sabuwar tarbiyya.—2 Tim. 4:3, 4.

15. Yaya kake ji game da dukan abubuwa da limamai suka yi cikin sunan Allah?

15 Domin dukan abubuwa da aka yi wai cikin sunan Allah da cikin sunan Littafi Mai Tsarki, mutane da yawa masu zuciyar kirki sun fid da rai ko kuma sun yi rashin bangaskiyarsu gabaki ɗaya ga Allah da kuma Littafi Mai Tsarki. Sun faɗa cikin tarkon Shaiɗan da mugun zamaninsa. Yaya kake ji sa’ad da ka ga da kuma ji game da irin waɗannan abubuwa da suke faruwa a kowace rana? A matsayin bawan Jehobah, sa’ad da ka ga zargi da saɓo da ake ɗora wa sunan Allah, hakan ba ya motsa ka ka yi iyakar ƙoƙarinka don ka daidaita al’amuran? Sa’ad da kuka ga ana ruɗin da kuma cutar sahihiyar mutane da masu zuciyar kirki, ba ku yin marmarin kawo sauƙi ga waɗanda ake zalunta ne? Sa’ad da Yesu ya ga mutane a zamaninsa “suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi,” bai ji tausayinsu kawai ba. Ya “fara koya masu abu dayawa.” (Mat. 9:36; Mar. 6:34) Muna da dalili mai kyau na kasancewa da himma don bauta ta gaskiya, kamar yadda Yesu ya yi.

16, 17. (a) Mene ne ya kamata ya motsa mu mu yi ƙoƙari sosai a cikin hidima? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

16 Sa’ad da muka ɗauki hidimarmu hakan, kalaman Bulus da ke cikin 1 Timotawus 2:3, 4 za su kasance da ma’ana na musamman a gare mu. (Karanta.) Muna aiki tuƙuru a hidima ba don kawai mun san muna zama a kwanaki na ƙarshe ba, amma domin mun fahimci cewa nufin Allah ne. Yana son mutane su san gaskiya domin su ma su koya su bauta masa da yi masa hidima kuma ya albarkace su. Muna ƙoƙartawa a cikin hidima ba don lokaci yana ƙurewa ba amma domin muna son mu ɗaukaka sunan Allah kuma mu taimaka wa mutane su san nufinsa. Muna da himma don bauta ta gaskiya.—1 Tim. 4:16.

17 A matsayin mutanen Jehobah, an albarkace mu da sanin gaskiya game da nufin Allah don ’yan Adam da kuma duniya. Muna da hanyar taimaka wa mutane su yi farin ciki kuma su samu tabbataccen bege don nan gaba. Muna iya nuna musu yadda za su samu kāriya sa’ad da za a halaka zamanin Shaiɗan. (2 Tas. 1:7-9) Maimakon mu yi sanyin gwiwa domin muna gani kamar zuwan ranar Jehobah yana jinkiri, ya kamata mu yi farin ciki cewa har ila muna da lokacin kasancewa da himma don bauta ta gaskiya. (Mi. 7:7; Hab. 2:3) Ta yaya za mu kasance da irin wannan himma? Za mu tattauna wannan a talifi na gaba.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Mene ne ya motsa Yesu ya yi aiki tuƙuru a lokacin hidimarsa a duniya?

• Mene ne kalmar nan ‘himma’ take nufi a cikin Littafi Mai Tsarki?

• Mene ne muke gani ya kamata ya motsa mu a yau mu kasance da himma don bauta ta gaskiya?

[Hoton da ke shafi na 8]

Yesu ya mai da hankali ga yin nufin Ubansa da kuma nuna ƙauna ga ’yan’uwa masu bi

[Hoton da ke shafi na 10]

Muna da dalili mai kyau na kasancewa da himma don bauta ta gaskiya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba