Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 3/15 pp. 15-19
  • Ka Riƙa Tuna Cewa Ƙarshe Ya Yi Kusa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Riƙa Tuna Cewa Ƙarshe Ya Yi Kusa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ME YA SA WA’AZIN DA MUKE YI YAKE DA GAGGAWA?
  • MENE NE YIN WA’AZI DA GAGGAWA YAKE NUFI?
  • KADA KA MANTA CEWA ƘARSHE YA KUSA
  • MUNA RAYUWA A LOKACI MAI MUHIMMANCI SOSAI
  • TUNA CEWA ƘARSHE YA KUSA YA SA SUN YI ƘWAZO
  • Yadda Za Mu Koyi Yin Wa’azi da Gaggawa
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • “Babbar Ranar Ubangiji Ta Kusa”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ka Kasance Da Himma Don Bauta Ta Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ka Taimaki Mutane Su “Farka Daga Barci”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 3/15 pp. 15-19

Ka Riƙa Tuna Cewa Ƙarshe Ya Yi Kusa

Ka yi wa’azin kalma; ka yi naciya. —2 TIM. 4:2.

ZA KA IYA BAYYANAWA?

Me ya sa Kiristoci na ƙarni na farko suka yi wa’azi a gaggawa?

Ta yaya za mu ci gaba da kasancewa da azancin gaggawa?

Me ya sa aikin wa’azi na Mulki ya fi gaggawa yanzu?

1, 2. Waɗanne tambayoyi ne za a amsa game da yin wa’azi da gaggawa?

JAMA’A suna yawan taimaka wa mutum da gaggawa idan yana cikin haɗari. Alal misali, idan mutum ya faɗa cikin kogi kuma yana shan ruwa, ana bukatar a ciro shi ba tare da ɓata lokaci ba don kada ya mutu.

2 A matsayinmu na Shaidun Jehobah, muna ɗokin taimaka wa mutane su tsira. Saboda haka, muna ɗaukan aikinmu na yin wa’azin bishara ta Mulki da muhimmanci. Ko da yake aikinmu yana da gaggawa, amma ba ma ɗaukan mataki nan da nan ba tare da yin tunani ba. Mene ne manzo Bulus yake nufi sa’ad da ya ba da gargaɗin nan cewa: “Ka yi wa’azin kalma; ka yi naciya?” (2 Tim. 4:2) Ta yaya za mu yi wa’azi da gaggawa? Kuma me ya sa aikinmu yake da gaggawa sosai?

ME YA SA WA’AZIN DA MUKE YI YAKE DA GAGGAWA?

3. Mene ne zai iya faruwa idan mutane suka saurari ko kuma ƙi da saƙon Mulki?

3 Idan muka yi tunani a kan yadda aikinmu na wa’azi zai ceci rayukan mutane hakan zai sa mu ga cewa muna bukatar mu yi wa wa’azi da gaggawa. (Rom. 10:13, 14) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan na ce ma mugu, Hakika mutuwa za ka yi; idan ya juya ga barin zunubinsa, ya yi abin da ke halal da daidai kuma, . . . lallai rai za ya yi, ba za ya mutu ba. Zunubansa da ya yi, ko ɗaya ba za a riƙe su a kansa ba.” (Ezek. 33:14-16) Hakika, Littafi Mai Tsarki ya gaya wa masu wa’azin Mulki cewa: ‘Za ku ceci kanku duk da masu-jinku.’—1 Tim. 4:16; Ezek. 3:17-21.

4. Me ya sa ake bukatar yin wa’azi da gaggawa don ’yan ridda?

4 Don mu fahimci abin da ya sa Bulus ya gargaɗi Timotawus ya yi wa’azi da gaggawa, muna bukatar mu yi la’akari da wasu abubuwa da ke cikin nassin da aka ɗauko jigon daga ciki. Wajen ya ce: “Ka yi wa’azin kalma; ka yi naciya ko da dama, ko ba dama; ka tsautar, ka kwaɓa, ka gargaɗar, da iyakacin jimrewa da koyarwa. Gama kwanaki za su zo inda ba za su daure da koyarwa mai-lafiya ba; amma bisa ga ƙaiƙayin kunnuwa za su tattara wa kansu masu-koyarwa bisa ga sha’awoyinsu; za su kawarda kunnuwansu ga barin gaskiya.” (2 Tim. 4:2-4) Yesu ya annabta cewa za a samu ’yan ridda. (Mat. 13:24, 25, 38) Tun da hakan zai faru ba da daɗewa ba, Timotawus yana bukatar ya yi wa’azi domin kada ’yan ridda su rinjaye Kiristoci da koyarwar ƙarya. Kiristoci suna cikin haɗari a lokacin. Shin hakan ma ya shafe mu a yau?

5, 6. Wane ra’ayi ne ya zama gama gari da mutanen da muke wa wa’azi suke da shi?

5 A yau, ’yan ridda suna ko’ina. (2 Tas. 2:3, 8) Wace koyarwar ƙarya ce mutane suke bi a yau? A wurare da yawa, ana koyar da ra’ayin bayyanau daidai yadda ake yi da addini. Ko da yake ana yin amfani da kimiyya don bayyana ra’ayin bayyanau, amma kamar dai ra’ayin bayyanau ya zama addinin, da babu Allahn da ake bauta wa. Kuma hakan yana shafar yadda mutane suke ji game da Allah da kuma mutane. Wata koyarwa kuma ita ce cewa, Allah ba ya ƙaunarmu kuma bai kamata mu ƙaunace shi ba. Me ya sa mutane da yawa suke sauraron waɗannan koyarwar da suke hana su bauta wa Jehobah? Waɗannan koyarwa guda biyu sun sa mutane su gaskata cewa za su iya yin duk abin da suke so domin babu Allahn da zai tambaye su abin da suka yi. Abin da mutane suke son su ji su kuma gaskata ke nan.—Karanta Zabura 10:4.

6 Amma akwai wasu koyarwa da mutane suka amince da ita. Wasu mutane da har ila suna zuwa coci suna moran jin cewa ko da mene ne suka yi, Allah yana ƙaunarsu. Wasu kuma suna son firistoci da fastoci su gaya musu cewa bukukuwa da mass da gumaka za su taimaka musu su taki sa’a. Amma waɗannan mutanen ba su fahimci cewa suna cikin haɗari ba. (Zab. 115:4-8) Amma, za su iya amfana daga Mulkin Allah idan sun farfaɗo daga barcin da suke yi a bautarsu ga Allah, kuma muka taimaka musu su fahimci gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

MENE NE YIN WA’AZI DA GAGGAWA YAKE NUFI?

7. Ta yaya za mu nuna cewa muna da azancin gaggawa?

7 A wasu lokatai, hanya mafi kyau da za mu nuna cewa muna da azancin gaggawa ita ce ta wajen mai da hankali ga abin da muke yi. Alal misali, sa’ad da likita yake wa wani fiɗa, dole ne ya mai da hankali sosai ga aikin da yake yi don kada mutumin ya rasu. Za mu iya nuna azancin gaggawa a hidimarmu ta wajen mai da hankali ga wa’azin da muke yi. Muna iya yin hakan ta wajen yin tunani sosai game da batun da za mu tattauna da mai-gida da tambayoyin da za mu yi ko kuma abin da mutane za su so su saurara. Kasancewa da azancin gaggawa zai kuma iya taimaka mana mu tsara lokacinmu don mu ziyarci mutane a lokacin da za su saurare saƙonmu.—Rom. 1:15, 16; 1 Tim. 4:16.

8. Mene ne yake nufi a kasance da azancin gaggawa?

8 Kasancewa da azancin gaggawa yana kuma nufin cewa za mu fara yin abubuwan da suka fi muhimmanci. (Karanta Farawa 19:15.) Alal misali, a ce ka je yin gwaji a asibiti, sai likitan ya kira ka cikin ofishinsa ya ce maka: “Kana bukatar ɗaukan mataki nan da nan, domin nan da wata ɗaya ciwonka zai yi tsanani sosai.” Shin za ka fito daga cikin ofishinsa a guje? Da kyar. Amma babu shakka, za ka fara saurara don ka ji abin da likitan zai gaya maka da ya kamata ka yi. Bayan haka, sai ka je gida ka yi la’akari sosai.

9. Me ya sa za mu iya cewa Bulus ya yi wa’azi da gaggawa sa’ad da yake birnin Afisa?

9 Za mu iya koyan darasi daga yadda Bulus ya kasance da azancin gaggawa, ta wajen karanta abin da ya gaya wa dattawan da ke Afisa game da wa’azin da ya yi a lardin Asiya. (Karanta Ayyukan Manzanni 20:18-21.) Wataƙila, ya soma yi wa mutane wa’azi daga gida zuwa gida a rana ta farko da ya isa lardin. Ƙari ga hakan, “kowacce rana yana kawo hujjoji cikin makarantar Tirannus.” (A. M. 19:1, 8-10) Babu shakka, azancin gaggawar Bulus ya shafi ayyukansa. Shawarar da aka ba mu cewa mu yi wa’azi da gaggawa, ba don mu ji cewa aikin wa’azin da muke yi yana da wuya ainun. Amma, ya kamata hakan ya sa mu wa’azin Mulki ya zama abu na farko a rayuwarmu.

10. Me ya sa ya kamata mu yi farin ciki don Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun soma wa’azi da gaggawa?

10 Kafin shekara ta 1914, wani ƙaramin rukunin masu nazarin Littafi Mai Tsarki sun soma wa’azin da za a yi a dukan duniya. Misalinsu ya nuna mana abin da kasancewa da azancin gaggawa yake nufi. Ko da yake ba su da yawa a wannan lokacin, sun san cewa suna rayuwa a lokaci na gaggawa sosai, kuma suka soma yin wa’azi game da Mulkin Allah da ƙwazo. Sun wallafa jawabai a cikin jaridu da yawa kuma sun nuna wa mutane hotuna da fim mai suna, “Photo-Drama of Creation.” Hakan ya sa sun yi wa miliyoyin mutane wa’azi. Da a ce Jehobah bai sa su kasance da azancin gaggawa ba, mu da yawancinmu ba za mu samu zarafin jin saƙon Mulkin ba?—Karanta Zabura 119:60.

KADA KA MANTA CEWA ƘARSHE YA KUSA

11. Me ya sa wasu suka daina kasancewa da azancin gaggawa?

11 Abubuwan da ke janye hankali suna iya hana mutum yin tunani game da muhimmancin aikin wa’azi. Shaiɗan yana yin amfani da zamaninsa don ya janye hankalinmu daga hidimar Jehobah. Kuma yana sa mu fi mai da hankali ga biɗe-biɗen kanmu. (1 Bit. 5:8; 1 Yoh. 2:15-17) Wasu da a dā suke ɗaukan hidimar Jehobah da muhimmanci sun daina yin hakan. Alal misali, Demas wani Kirista ne da ya yi hidima tare da manzo Bulus, amma daga baya, abubuwan duniya suka janye hankalinsa. Maimakon ya fi mai da hankali ga ƙarfafa Bulus a lokacin wahala, Demas ya gudu ya bar shi.—Fil. 23, 24; 2 Tim. 4:10.

12. Wane zarafi ne muke da shi yanzu, kuma wane zarafi ne za mu samu a nan gaba?

12 Idan muna son mu ci gaba da kasancewa da azancin gaggawa, muna bukatar mu guji yin abubuwan da suke janye hankalinmu daga yin wa’azin. Muna bukatar mu yi ƙoƙari don mu “ruski rai wanda ya ke hakikanin rai.” (1 Tim. 6:18, 19) Babu shakka, ka amince cewa rayuwa za ta yi daɗi sosai, sa’ad da Mulkin Allah ta soma sarauta bisa duniya. Kuma a wannan lokacin, za mu more rai na har abada. Amma, ba za mu sake samun wannan zarafi na yi wa mutane wa’azi don su tsira daga Armageddon kuma ba.

13. Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da kasancewa da azancin gaggawa?

13 Mutane da yawa da ke yankinmu ba su san Jehobah ba. Saboda haka, mene ne za mu yi don mu taimaka musu? Ya kamata mu tuna cewa akwai lokacin da mu ma ba mu san Allah ba, kuma ba mu da begen yin rayuwa a nan gaba. Amma mun koyi gaskiya game da Jehobah da kuma Yesu Kristi. Kuma yanzu muna da zarafin koya wa wasu wannan gaskiyar. (Karanta Afisawa 5:14.) Bulus ya ce: ‘Ku duba fa a hankali yadda kuke yin tafiya, ba kamar marasa-hikima ba, amma kamar masu-hikima; kuna rifta zarafi, tun da ya ke miyagun kwanaki ne.’ (Afis. 5:15, 16) Tun da muna rayuwa a miyagun kwanaki, zai dace mu “rifta zarafi” don yin ayyukan da za su ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah.

MUNA RAYUWA A LOKACI MAI MUHIMMANCI SOSAI

14-16. Me ya sa wa’azin Mulkin ya fi gaggawa sosai a yau?

14 Ko da yake ya daɗe da ake aikin wa’azi da gaggawa, amma yanzu ne ya fi kasance da gaggawa sosai. Tun shekara ta 1914, abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya annabta suna faruwa sarai. (Mat. 24:3-51) Ana wa rayukan mutane barazana. Ko da yake ƙasashe mafi iko na duniya sun amince cewa za su zauna cikin salama, amma duk da haka, suna da makaman nukiliya kusan dubu biyu da za su iya jefo zuwa kowanne ɓangare na duniya. Hukuma ta ba da rahoto sau da yawa cewa wasu kayakin nukiliya sun ɓace. Shin ’yan ta’adda suna da wasu cikin waɗannan kayayyakin? Wasu sun ce idan ’yan ta’adda suka soma yaƙi, za su iya kashe kowa a duniya. Amma, ba yaƙi kaɗai ba ne yake wa rayuwar ’yan Adam barazana.

15 An faɗa a University College London da kuma mujallar nan The Lancet cewa: “Canjin yanayin duniya ne ya fi yi wa lafiyar ’yan Adam barazana.” Sakamakon canjin yanayi zai shafi lafiyar yawancin mutane kuma zai sa rayukan miliyoyi cikin haɗari. Kuma aman ruwa a teku da fari da ambaliyar ruwa da cututtuka da guguwa da yaƙe-yaƙe saboda ƙarancin abinci da kuma sauransu. Babu shakka, yaƙe-yaƙe da bala’i suna wa rayuwar ’yan Adam barazana.

16 Wasu suna iya yin zato cewa yaƙin nukiliya zai iya sa annabcin Yesu game da kwanaki na ƙarshe ya cika. Amma, yawancin mutane ba su fahimci ainihin ma’anar annabcin nan na Yesu ba. Abubuwan da suke faruwa a cikin shekaru da yawa yanzu sun nuna cewa Yesu ya soma sarauta. Kuma nan ba da daɗewa ba, za a kawo ƙarshe ga wannan zamanin. (Mat. 24:3) Yanzu ne aka fi ganin cikar annabcin Yesu. Yanzu ne ainihin lokacin da ya kamata ’yan Adam su kasance da dangantaka mai kyau da Allah. Wa’azin da muke yi zai iya taimaka musu.

17, 18. (a) Ta yaya kasancewa a kwanaki na ƙarshe yake shafarmu? (b) Me zai iya sa wasu su soma saurarar saƙon Mulkin Allah?

17 Lokacin da ya rage kaɗan ne da za mu nuna ƙaunarmu ga Jehobah da kuma kammala aikin wa’azi da ya ce mu yi a waɗannan kwanaki na ƙarshe. Abin da Bulus ya ce ga Kiristocin da ke ƙasar Roma ya fi muhimmanci a yau: “An san wokacin nan, sa’a ta yi sarai da za ku farka daga barci: gama yanzu ceto ya fi kusa da mu bisa ga lokacin da muka fara bada gaskiya.”—Rom. 13:11.

18 Abubuwan da aka annabta cewa za su faru a kwanaki na ƙarshe za su iya taimaka mana mu san cewa ya kamata mu kasance da dangantaka da Jehobah. Yadda gwamnatin ’yan Adam ta kasa kawo ƙarshe ga wahalar mutane, ya sa wasu sun soma son saƙon Mulkin Allah. Mulkin ’yan Adam ba ta iya kawo ƙarshe ga taɓarɓarewar tattalin arziki da barazanar halaka duniya da nukiliya da nuna ƙarfi da gurɓatar da duniya. Kuma wasu sun soma son saƙon Mulkin Allah saboda matsalolin da ke faruwa a cikin iyalinsu, kamar su, rashin lafiya ko kashe aure ko rashin wani da suke ƙauna. Za mu iya taimaka wa irin waɗannan mutanen, sa’ad da muke yin wa’azi.

TUNA CEWA ƘARSHE YA KUSA YA SA SUN YI ƘWAZO

19, 20. Ta yaya kasancewa da azancin gaggawa ya taimaki wasu ’yan’uwa su canja salon rayuwarsu?

19 Kasancewa da azancin gaggawa ya motsa Kiristoci da yawa su daɗa saka hannu sosai a aikin wa’azi. Alal misali, wasu ma’aurata a ƙasar Ecuador sun sauƙaƙa salon rayuwarsu bayan sun halarci taro na musamman na shekara ta 2006, mai jigo: “Bari Idonka Ya Kasance Sosai.” Sun rubuta abubuwan da ba sa bukata, kuma cikin watanni uku, suka ƙaura daga babban gidan da suke zama zuwa ciki da falo. Suka sayar da wasu kayayyakinsu kuma suka biya basussukan da suka ci. Ba da daɗewa ba, suka soma hidimar majagaba na ɗan lokaci kuma suka bi shawarar da mai kula da da’ira ya ba su cewa su ƙaura zuwa inda ake da bukatar masu wa’azi sosai.

20 Wani ɗan’uwa a Amirka ya rubuta: “Ni da matata mun yi shekara 30 da yin baftisma sa’ad da muka halarci wani taro a shekara ta 2006. Sa’ad da muke dawowa gida daga taron, ni da matata mun tattauna yadda za mu yi amfani da abin da aka faɗa a taron cewa, mu sauƙaƙa salon rayuwarmu.” (Mat. 6:19-22) A lokacin, muna da gidaje uku da filaye da motoci masu tsada da kwalekwale mai inji da kuma mota mai kayan ɗaki a ciki. Da yake muna jin cewa mun ɓata lokacinmu da kuma kuzarinmu ta wajen tara kayan duniya, sai muka tsai da shawara cewa za mu soma hidima ta cikakken lokaci. A shekara ta 2008, muka soma hidimar majagaba kamar ’yarmu. Muna matuƙar farin ciki don yin hidima tare da ’yan’uwanmu. Mun samu gatan yin hidima a inda akwai bukatar masu shela sosai. Kuma, saka hannu sosai a hidima ya sa mu kusaci Jehobah sosai. Muna kuma farin ciki sosai, don taimaka wa mutane su ji da kuma fahimci gaskiyar Littafi Mai Tsarki.”

21. Sanin mene ne ya sa muke yin wa’azi da gaggawa?

21 Mun san cewa nan ba da daɗewa ba, “ranar shari’a da halakar mutane masu-fajirci” zai kawo ƙarshe ga miyagun mutane. (2 Bit. 3:7) Domin mun san Kalmar Allah sosai, muna yin wa’azi da ƙwazo game da ƙunci-mai-girma da zai faru da kuma sabuwar duniya. Muna ci gaba da kasancewa da azancin gaggawa ta wajen gaya wa mutane game da bege na ainihi da muke da shi a nan gaba. Ta wajen saka hannu sosai a wannan aiki na gaggawa, muna nuna cewa muna ƙaunar Allah da kuma mutane sosai.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba