Ka Taimaki Mutane Su “Farka Daga Barci”
“An san wokacin nan, sa’a ta yi sarai da za ku farka daga barci.”—ROM. 13:11.
ZA KA IYA BAYYANAWA?
․․․․․
Me ya sa yake da muhimmanci Kiristoci su kasance a faɗake a bautarsu ga Jehobah?
․․․․․
Me ya sa ya kamata mu riƙa lura da kuma saurara sa’ad da muke wa’azi?
․․․․․
Me ya sa kirki da kuma sauƙin hali yake da muhimmanci a hidimarmu?
1, 2. A wacce hanya ce mutane da yawa suke bukatar su farka daga barci?
AKOWACCE shekara, dubban mutane suna samun hatsari kuma su rasa rayukansu sanadiyyar yin barci sa’ad da suke tuƙa mota. Wasu kuma suna rasa aikinsu domin ba sa tashi daga barci da sauri don su je aiki ko kuma suna barci a wurin aiki. Amma, yin barci a dangantakarmu da Jehobah ya fi kawo mugun sakamako. Littafi Mai Tsarki yana mana gargaɗi a kan irin wannan barci, ya ce: “Mai-albarka ne shi wanda ya ke tsaro.”—R. Yoh. 16:14-16.
2 Yayin da ranar Jehobah take kusatowa, mutane gabaki ɗaya suna barci a bautarsu ga Jehobah. Har ma wasu limaman Kiristendam sun ce mabiyansu suna yin barci. Ta yaya mutum zai iya yin barci a bautarsa ga Jehobah? Me ya sa yake da muhimmanci Kiristoci na gaskiya su kasance a faɗake? Ta yaya za mu iya taimaka wa mutane su farka daga barci?
TA YAYA MUTUM ZAI IYA YIN BARCI A BAUTARSA GA JEHOBAH?
3. Yaya za ka kwatanta mutumin da yake barci a bautarsa ga Jehobah?
3 Mutum ba ya aikace-aikace sa’ad da yake yin barci. Akasin haka, waɗanda suke barci a bautarsu ga Jehobah suna iya shagala sosai da aikace-aikace. Amma waɗannan ba aikace-aikacen da za su kyautata dangatakarsu da Jehobah ba ne. Suna iya mai da hankali ga ayyuka na yau da kullum, kamar su, biɗan annashuwa da wadata da kuma kuɗi. Domin suna shagalawa da waɗannan ayyukan sosai ba sa nuna ƙwazo a bautarsu ga Jehobah. Amma waɗanda suke a farke a bautarsu ga Jehobah sun sani sarai cewa muna rayuwa a “kwanaki na ƙarshe,” kuma suna iya ƙoƙarinsu a yin nufin Allah.—2 Bit. 3:3, 4; Luk 21:34-36.
4. Mene ne muhimmancin gargaɗin nan: “Kada fa mu yi barci, kamar sauran mutane”?
4 Karanta 1 Tasalonikawa 5:4-8. A cikin waɗannan ayoyin Bulus ya gargaɗi ’yan’uwansa kada su yi “barci kamar sauran mutane.” Mene ne yake nufi? Hanya ɗaya da za mu iya yin “barci” ita ce ta wajen ƙin bin mizanan Jehobah game da ɗabi’a. Wata hanya kuma da za mu iya yin “barci” ita ce ta yin watsi da gargaɗi cewa lokacin da Jehobah zai halaka miyagun mutane yana kusatowa. Ya kamata mu mai da hankali don kada irin waɗannan miyagun mutane su rinjaye mu mu riƙa yin tunani da kuma yin abubuwa kamar su.
5. Wane ra’ayi marar kyau ne mutane da yawa suke da shi?
5 Wasu mutane suna zato cewa babu Allahn da zai hukunta su don ayyukansu. (Zab. 53:1) Wasu kuma suna tunani cewa Allah ba ya ƙaunar ’yan Adam, kuma bai kamata mu ma mu ƙaunace shi ba. Wasu ma suna jin cewa zuwa coci zai sa su zama aminan Allah. Dukan irin waɗannan mutanen suna barci a bautarsu ga Jehobah. Suna bukatar su farka. Ta yaya za mu iya taimaka musu?
WAJIBI NE MU KASANCE A FAƊAKE
6. Me ya sa ya wajaba Kiristoci su kasance a faɗake?
6 Don mu iya ta da mutane daga barci, dole ne mu ma mu kasance a farke. Mene ne yin hakan ya ƙunsa? Littafi Mai Tsarki ya ce waɗanda suke barci a dangatakarsu da Jehobah suna aikata “ayyukan duhu.” Waɗannan ayyukan sun haɗa da yin liyafa ana ihu da yin maye da lalata da fajirci da jayayya da kuma kishi. (Karanta Romawa 13:11-14.) Guje wa irin waɗannan ayyuka yana da wuya. Dole ne mu kasance a faɗake. Wajibi ne direban mota ya tuna cewa idan ya yi barci sa’ad da yake tuƙi, zai iya hatsari kuma ya mutu. Yana da muhimmanci sosai Kiristoci su san cewa yin barci a bautarsu ga Jehobah zai iya sa su rasa ransu.
7. Ta yaya samun ra’ayi marar kyau game da mutanen da ke yankinmu zai iya shafarmu?
7 Alal misali, Kirista zai iya soma tunani cewa waɗanda suke yankinsu ba za su taɓa sauraran wa’azinmu ba. (Mis. 6:10, 11) Za mu iya yin tunani cewa, “idan babu mutumin da zai saurare mu, mene ne amfanin sa ƙwazo don taimaka musu?” Gaskiya ce cewa mutane da yawa suna barci a bautarsu ga Jehobah, amma yanayinsu da halayensu suna iya canjawa. Wasu suna iya farkawa kuma su soma bauta wa Jehobah. Za mu iya taimaka musu idan mun kasance a faɗake, muna yin amfani da sababbin hanyoyi don gabatar da wa’azin Mulki. Mu ma za mu kasance a farke, idan mun tuna cewa wa’azinmu yana da muhimmanci.
ME YA SA HIDIMARMU TAKE DA MUHIMMANCI SOSAI?
8. Me ya sa wa’azin da muke yi yake da muhimmanci sosai?
8 Ka tuna cewa ko da mutane ba su saurari abin da muka ce musu ba, wa’azin da muke yi yana ɗaukaka Jehobah. Kuma yana amfani da aikin wa’azi don ya cika nufinsa. Nan ba da daɗewa ba, za a hukunta waɗanda ba su canja salon rayuwarsu ba. Kuma za a halaka waɗanda ba su aikata bisa ga wa’azin da muka yi musu ba. (2 Tas. 1:8, 9) Bugu da ƙari, bai kamata mu yi tunani cewa ba ma bukatar sa ƙwazo sosai a wa’azi domin za a “yi tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.” (A. M. 24:15) Kalmar Allah ta nuna cewa za a halaka waɗanda “awaki” ne. Wa’azin da muke yi yana nuna yadda Allah yake mana jin ƙai, kuma hakan yana sa mutane su yi canje-canje a rayuwarsu kuma su samu rai na har abada. (Mat. 25:32, 41, 46; Rom. 10:13-15) Idan ba mu yi wa’azi ba, ta yaya mutane za su samu zarafin sauraron saƙon da zai ceci rayukansu?
9. Ta yaya yin wa’azin bishara zai amfane ka da kuma wasu?
9 Muna kuma amfana don yin wa’azin bishara. (Karanta 1 Timotawus 4:16.) Shin ba ka ga cewa yin magana game da Jehobah da kuma Mulkinsa yana ƙarfafa bangaskiyarka kuma da ƙaunar da kake wa Allah ba? Shin hakan bai sa ka kasance da halaye na Kirista ba? Shin ba ka daɗa farin ciki sa’ad da ka nuna cewa kana ƙaunar Allah ya wajen yin wa’azi ba? Mutane da yawa da suka samu gatar koya wa wasu gaskiya sun yi farin ciki yayin da suka ga yadda ruhun Allah ya taimaka wa waɗannan su yi canje-canje a rayuwarsu.
KA RIƘA LURA
10, 11. (a) Ta yaya Yesu da Bulus suka lura da bukatun mutane? (b) Ka kwatanta yadda yin lura zai iya kyautata hidimarmu.
10 Akwai hanyoyi dabam dabam da za mu iya sa mutane su so sauraron wa’azi. Saboda haka, wajibi ne mu zama masu lura. Yesu ne muke bin misalinsa. Domin shi kamili ne, ya san cewa wani Bafarisi ya yi fushi, ko da bai furta haka ba. Ya kuma san cewa wata mata da mai zunubi ce sosai ta tuba kuma wata gwauruwa ta ba da gudummawar dukan kuɗin da take da shi. (Luk 7:37-50; 21:1-4) Yesu yana iya taimaka wa mutane domin ya san bukatunsu. Amma dai, bawan Allah ba ya bukatar ya zama kamili kafin ya lura da bukatun mutane. Manzo Bulus ya kwatanta hakan. Ya yi wa’azi a hanyoyi dabam dabam, domin ya taimaki dukan mutane.—A. M. 17:22, 23, 34; 1 Kor. 9:19-23.
11 Idan muna lura kuma mun san bukatun mutane kamar yadda Yesu da kuma Bulus suka yi, za mu san yadda za mu taimaka musu. Alal misali, sa’ad da ka je wa mutane wa’azi, ka duba ko za ka ga abubuwan da za su sa ka san al’adarsu da abubuwan da suke so da kuma ko suna da aure ko a’a ko kuma suna da yara. Ka kuma lura da abin da suke yi kuma ka yi magana a kan wannan sa’ad da ka soma tattaunawa da su.
12. Me ya sa ya kamata mu mai da hankali da hirar da muke yi sa’ad da muke wa’azi?
12 Idan muna yin lura a hidima, ba za mu ƙyale kome ya janye hankalinmu sa’ad da muke wa’azi ba. Muna iya yin hira da wanda muke wa’azi tare da shi. Amma duk da haka, ya kamata mu tuna cewa dalilin da ya sa muke hidima shi ne don mu yi wa mutane wa’azi. (M. Wa. 3:1, 7) Saboda haka, ya kamata mu yi hankali don kada hirar da muke yi ta janye hankalinmu daga hidima. Yin hira a kan abin da za mu tattauna da mai-gida hanya ce mai kyau na mai da hankali a hidimarmu. Kuma, ko da yake wayar selula tana iya taimaka mana a hidima, amma ya kamata mu mai da hankali don kada ta janye hankalinmu sa’ad da muke tattaunawa da mai-gida.
KA SAURARA KUMA KA NUNA KANA DARAJA MUTANE
13, 14. (a) Mene ne zai taimaka mana mu san ra’ayin mai gidan? (b) A wace hanya ce za mu iya soma tattaunawa da mutane a hidima?
13 Mai wa’azin da ke lura sosai yana saurarawa sa’ad da waɗanda yake wa wa’azi suke magana. Waɗanne tambayoyi ne za ka iya yi don ka sa wani a yankinku ya faɗi ra’ayinsa? Shin ya damu da yawan addinai da ke duniya da muguntan da ke faruwa a ko’ina da kuma yadda gwamnati ta kasa biyan bukatun mutane? Za ka iya sa mutane su san Allah ta wajen yin magana game da abubuwa masu ban al’ajabi da Allah ya halitta ko kuma yadda shawarar Littafi Mai Tsarki take taimaka mana? Mutane da yawa daga al’adu dabam dabam suna son yin addu’a, har da waɗanda ba su gaskata cewa Allah ya wanzu ba. Mutane da yawa suna mamaki ko akwai wanda yake jin addu’armu. Mutane da yawa suna iya son sanin amsa ga tambayar nan: Shin Allah yana amsa dukan addu’o’i? Idan ba ya amsa dukan addu’o’i, mene ne za mu iya yi don ya ji addu’o’inmu?
14 Za mu iya koya yadda ake soma tattaunawa da mutane ta wajen yin koyi da ’yan’uwan da suka ƙware a hidima. Ka lura da yadda suke yin tambaya, ba tare da kunyatar da mutumin ba. Ka lura da yadda muryarsu da kuma fuskarsu ya nuna cewa suna son su fahimci ra’ayin mai gidan.—Mis. 15:13.
KA KASANCE DA KIRKI KUMA KA TAIMAKA WA MUTANE DA BASIRA
15. Me ya sa ya kamata mu kasance da kirki sa’ad da muke wa’azi?
15 Kana farin ciki idan wani ya tashe ka sa’ad da kake barci mai daɗi sosai? Mutane da yawa ba sa farin ciki idan an tashe su daga barci farat ɗaya. Yawanci sun fi so a tashe su a hankali. Hakan ma yake idan muna son mu sa mutane su soma bauta wa Jehobah. Alal misali, mene ne ya kamata ka yi idan wani ya yi fushi don kana son ka yi masa wa’azi? Ka kasance mai kirki, kuma ka nuna cewa kana daraja ra’ayinsa. Sai ka masa godiya don ya furta yadda yake ji, kuma ka tafi. (Mis. 15:1; 17:14; 2 Tim. 2:24) Yadda ka nuna masa kirki zai iya sa ya saurara, sa’ad da wani Mashaidi ya ziyarce shi.
16, 17. Ta yaya za mu iya yin amfani da basira a hidimarmu?
16 A wani lokaci kuma, kana iya ci gaba da tattauna da mutum ko da ba ya son saƙonmu. Wani yana iya cewa, “A’a ka je wani wuri. Mun riga mun karɓi Yesu. Ko kuma muna da namu addini. Yana iya ce hakan domin kada a tattauna da shi. Amma idan ka kasance da kirki da kuma basira, za ka iya yin tambaya da za ta taimaka wa mai gidan ya so saƙon Littafi Mai Tsarki.—Karanta Kolosiyawa 4:6.
17 A wasu lokatai, idan mun haɗu mutanen da suka ce suna aiki kuma ba za su iya saurarawa ba, zai fi kyau mu amince da hakan kuma mu tafi. Alal misali, wasu suna iya tattauna da masu gida a kasa da minti ɗaya. Suna karanta aya a cikin nassi kuma su yi tambaya da za su amsa sa’ad da suka koma ziyara. A wasu lokatai, irin wannan tattaunawar tana sa mai gidan ya amince a ci gaba da tattaunawa da shi. Idan ka samu irin wannan zarafin wata rana, ka gwada ka ga sakamakon?
18. Mene ne za mu iya yi don mu iya yin wa’azi sa’ad da muka samu zarafin yin hakan?
18 Idan muna a shirye mu tattauna da mutane sa’ad da muka samu zarafin yin hakan, za mu iya taimaka wa mutanen da muke haɗu wa da su kowace rana su soma ƙaunar Allah. ’Yan’uwa da yawa suna saka ƙasidu a aljihunsu ko kuma jakarsu. Wasu suna a shirye su karanta aya guda na nassi idan sun samu zarafi. Kana iya gaya wa dattijon da ke kula da hidima a ikilisiyarku ko kuma majagaba su nuna maka yadda ake wa’azi sa’ad da aka samu zarafi.
KA KASANCE DA KIRKI SA’AD DA KAKE TAIMAKA WA DANGINKA
19. Me ya sa bai kamata mu yi watsi da danginmu ba?
19 Dukanmu za mu so mu taimaka wa danginmu su soma bauta wa Jehobah. (Josh. 2:13; A. M. 10:24, 48; 16:31, 32) Idan suka ƙi saƙonmu lokaci na farko da muka musu wa’azi, hakan zai iya sa mu sanyin gwiwa. Za mu iya tunani cewa babu abin da za mu ce don su canja salon rayuwarsu. Amma wataƙila wasu abubuwa suna iya faruwa da za su sa danginku su canja salon rayuwarsu. Ko kuma wataƙila ka ƙware sosai a yadda kake bayyana Littafi Mai Tsarki.
20. Me ya sa ya kamata mu daraja danginmu sa’ad da muke musu wa’azi?
20 Ya dace mu riƙa daraja danginmu. (Rom. 2:4) Ya kamata mu yi magana da su da daraja kamar yadda muke bi da waɗanda muke wa wa’azi. Kada ka yi musu baƙar magana, amma ka daraja su. Ba tare da cika su da maganganu ba, ka nuna musu yadda bishara ta shafi rayuwarka. (Afis. 4:23, 24) Ka bayyana yadda Jehobah ya albarkace ka, yana “koya maka zuwa amfaninka.” (Isha. 48:17) Ka nuna wa danginka ta halinka yadda ya kamata Kiristoci su yi rayuwa.
21, 22. Ka faɗi labarin da ya nuna amfanin ci gaba da yin ƙoƙari don taimaka wa danginmu su san Jehobah.
21 Wata ’yar’uwa ta rubuto kwana kwanan nan: “Ina ƙoƙari don na yi wa ’yan’uwana maza da mata guda goma sha uku wa’azi ta kalamina da kuma halina. Ina rubuta musu wasiƙa kowacce shekara. Kuma cikin shekara 30 da ta gabata, ni kaɗai ce Mashaidiya a cikin iyalinmu.”
22 ’Yar’uwar ta ci gaba da cewa: “Akwai wata ranar da na yi wa yata da take zama a wuri mai nisa sosai waya. Sai ta gaya mini cewa ta faɗa wa limaminsu ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita, amma ya ƙi. Sa’ad da na gaya mata cewa zan so na yi nazarin da ita, sai ta ce: ‘Babu laifi, amma ki san cewa, ba zan taɓa zama Mashaidiyar Jehobah ba.’ Ina kiranta a kai akai, bayan da na aika mata littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Amma ta ƙi karanta littafin. Bayan haka, na ce ta buɗe littafin ta, kuma mun yi amfani da minti 15 ta waya don karanta da kuma tattauna nassosin da aka yi ƙaulinsu a ciki. Bayan ɗan lokaci, sai ta yarda na riƙa nazarin da ita fiye da minti 15. Kuma ta soma kira ta don na yi nazari da ita, a wasu lokatai tana kira ta kafin na tashi daga barci da safe, a wani zubi kuma tana kira na sau biyu a rana. Sai ta yi baftisma a shekara ta gaba, kuma shekara ɗaya bayan ta yi baftisma, ta soma hidimar majagaba.”
23. Me ya sa za mu ci gaba da taimaka wa mutane su soma bauta wa Jehobah?
23 Muna bukatar ƙwarewa sosai don mu ci gaba da taimaka wa mutane su soma bauta wa Jehobah. Kuma mutane da yawa suna sauraron wa’azin da muke musu. Aƙalla, fiye da mutane 20,000 ne suke yin baftisma a matsayin Shaidun Jehobah a kowacce shekara. Saboda haka, ya kamata mu yi la’akari da gargaɗin da Bulus ya ba Arkibbus a ƙarni na farko: “Ka yi lura da hidima wadda ka karɓa cikin Ubangiji, domin ka cika ta.” (Kol. 4:17) Talifi na gaba zai taimaka mana mu fahimci ma’anar yin wa’azi da azancin gaggawa.
[Akwati a shafi na 13]
YADDA ZA KA KASANCE A FAƊAKE
▪ Ka lizima a yin nufin Allah
▪ Ka guje yin miyagun ayyuka
▪ Ka tuna cewa yin barci a bautarmu ga Jehobah yana da haɗari
▪ Ka riƙa tunani mai kyau game da mutanen da ke yankinku
▪ Ka gwada sababbin hanyoyi na yin wa’azi
▪ Ka tuna cewa hidimarka tana da muhimmanci