Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 10/1 pp. 29-31
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Makamantan Littattafai
  • “A Dā Ina Haka Kabarina”
    Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • “Ni Mai Zafin Rai Ne a Dā”
    Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 10/1 pp. 29-31

Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka

Ta yaya mutumin da ya soma shan wi-wi da taba sigari sa’ad da yake matashi ya samu ƙarfin daina wannan halin? Menene ya taimaki wani ɗan daba ya kame kansa kuma ya daina nuna ƙiyayya don launin fata? Ka yi la’akari da abin da kowannensu ya faɗa.

TARIHI

SUNA: HEINRICH MAAR

SHEKARU: 38

ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: KAZAKHSTAN

LABARI: MAI BALA’IN SHAN WI-WI DA TABA SIGARI

TARIHI NA NA DĀ: An haife ni ne a kudancin Kazakhstan, kusan mil saba’in daga birnin Tashkent. Da rani, wurin yakan bushe kuma yakan yi zafi sosai, kuma a lokacin ɗari, wurin yana yin sanyi sosai, yanayin da ya dace don shuka inabi da wi-wi.

Iyaye na ’yan Jamus ne. Su biyun ’yan Cocin evengelical ne amma ba sa bin addininsu. Amma, sun koya mini in haddace addu’ar Ubanmu. Sa’ad da nake ɗan shekara sha huɗu, mamata da yaya ta sun yi nazarin Littafi Mai Tsarki tare da Shaidun Jehobah na ɗan lokaci. Na taɓa jin Shaidun biyu da suke nazari da mamata suna nuna mata sunan Allah, Jehobah, a cikin nata Littafi Mai Tsarki. Hakan ya burge ni. Mama ta daina nazarin, kuma ban ɗauki mataki ba don na koya game da Allah. Duk da haka, sa’ad da nake makaranta, malamarmu ta maimaita duk ƙaryan da ake yi game da Shaidun Jehobah. Tun da yake na taɓa halartar wasu tarurruka na Shaidun Jehobah tare da ’yar’uwata, na gaya wa malamarmu cewa abubuwan da take faɗi ba gaskiya ba ne.

Sa’ad da na kai ɗan shekara sha biyar, an tura ni Leningrad, wadda yanzu ake kira St. Petersburg, a ƙasar Rasha, don na koyi sana’a. Na gaya wa abokan ɗaki na game da abubuwan da na ɗan koya game da Jehobah. Amma, sai na soma shan taba sigari. Sa’ad da na ziyarce gida a Kazakhstan, sayen taba wi-wi yana da sauƙi, ko da yake doka ta hana hakan. Ina yawan shan vodka wadda giya ce mai ƙarfi da kuma giyar gargajiya.

Na kammala makarantar koyan sana’a kuma na zama sojan Soviet har tsawon shekara biyu. Duk da haka, wasu abubuwan da na koya daga Littafi Mai Tsarki sa’ad da nake matashi suna cikin zuciya ta. Sa’ad da na samu zarafi, na gaya wa sojojin da muke aiki tare game da Jehobah kuma na kāre Shaidu sa’ad da aka faɗi ƙarya game da su.

Bayan da na kammala hidima ta na soja, sai na koma ƙasar Jamus. Sa’ad da nake sansanin baƙi, na karɓi ɗan ƙaramin littafin nazarin Littafi Mai Tsarki wanda Shaidu suka wallafa. Na karanta shi da ƙwazo kuma na kammala cewa abin da ke ciki gaskiya ne. Amma dai, ban samu damar daina shan taba sigari da wi-wi ba. Bayan wani ɗan lokaci na koma birnin Karlsruhe. A nan ne na sadu da wani Mashaidin Jehobah, kuma ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWANA: Tun da daɗewa, na ke tunanin cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ne. Kuma bayan da na karanta littafin nazarin Littafi Mai Tsarki da aka ba ni, sai na amince cewa Littafi Mai Tsarki ya amsa dukan tambayoyi masu muhimmanci a rayuwa. Duk da haka, na ɗauki lokaci mai tsawo kafin na canja halaye na. Daga baya, na ɗauki shawarar da ke Littafi Mai Tsarki a 2 Korintiyawa 7:1 kuma na yanke shawarar tsarkake kaina daga “dukan ƙazamtar jiki da ta ruhu,” wanda yake nufin daina shan wi-wi da taba sigari.

Na daina shan wi-wi nan da nan. Amma ya ɗauke ni watanni shida kafin na daina shan taba sigari. Wata rana Mashaidin da ke nazari da ni ya tambaye ni, “Menene ma’anar rayuwarka?” Hakan ya sa na yi tunani sosai game da mugun shan taba sigari da nake yi. Sau da yawa na yi ƙoƙarin daina shan taba. A yanzu dai, na yanke shawarar yin addu’a kafin na ɗauki taba maimakon na nemi gafara daga Allah bayan na yi hakan. A shekara ta 1993, na kafa ranar da zan daina. Da taimakon Jehobah, ban sake taɓa taba sigari ba tun lokacin.

YADDA NA AMFANA: Yanzu da na daina shan wi-wi da taba sigari, lafiyar jikina ya ƙaru. A yau, na samu gatan yin hidima a ofishin reshe na Shaidun Jehobah da ke Jamus. Ina farin ciki sosai cewa na koyi yin amfani da shawarar Littafi Mai Tsarki a rayuwana! Sanin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa ya sa rayuwata ta kasance mai ma’ana.

TARIHI

SUNA: TITUS SHANGHADI

SHEKARU: 43

ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: NAMIBIYA

LABARI: MUGUN ƊAN DABA

RAYUWA NA NA DĀ: Na girma ne a karkaran Ohangwena a arewancin Namibiya. An bugi mutanen ƙauyenmu kuma an kashe su sa’ad da aka yi yaƙi a wannan yankin a cikin shekaru na 1980. A ƙauyenmu, ana ɗaukan yaro a matsayin namiji ne idan ya iya faɗa sosai kuma zai iya dukan wasu yara. Don haka na koyi yin faɗa sosai!

Sa’ad da na gama makaranta, na soma zama da kawu na a birnin Swakopmund da ke yammanci ƙasar. Ban daɗe da kai wa wurin ba, sai na soma tarayya da wasu matasa ’yan daba. Za mu je wurare a cikin gari inda baƙaƙen fata ba sa shiga, kamar masauki da mashaya don mu tayar da rigima. Sau da yawa, mun yi faɗa da masu gaɗi da kuma ’yan sanda. A kowane dare ina riƙe doguwar wuka mai kaifi ko kuma adda, don na sari duk wanda ya tsokane ni.

Akwai wani daren da muke yin faɗa da wasu ’yan daba, kaɗan ya rage da an kashe ni. Wani cikin ’yan daba da muke hamayya da su ya taho daga baya da niyar ya fille kaina, amma wani daga cikin ’yan dabarmu ya sumar da shi. Duk da cewa na kusan mutuwa, na ci gaba da yin mugunta. Idan na soma gardama da wani, mace ko namiji, ni ne ke soma kai bugu.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWANA: Sa’ad da na sadu da ɗaya daga cikin Shaidun Jehobah, matar ta karanta mini Zabura 37 kuma ta gaya mini cewa Littafi Mai Tsarki a Ru’ya ta Yohanna yana ɗauke da wasu alkawura masu ban al’ajabi game da nan gaba. Amma tun da ba ta faɗi wurin da aka yi wannan alkawuran ba, na sayi Littafi Mai Tsarki kuma na karance littafin Ru’ya ta Yohanna gaba ɗaya a wannan daren. Na so alkawarin da na karanta a Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4 cewa “mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba.” Sa’ad da Mashaidiyar ta sake dawowa, na aminci da nazarin Littafi Mai Tsarki.

Canja tunanina da rayuwana ya yi mini wuya sosai. Amma na koya daga littafin Ayyukan Manzanni 10:34, 35 cewa “Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda ya ke tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gareshi.” Na kuma yi ƙoƙarin yin amfani da Romawa 12:18: “Idan ya yiwu, ku zama lafiya da dukan mutane, gwargwadon iyawarku.”

Ƙari ga koyan yadda zan rage yin fushi, ina kuma bukatan na daina shan taba. Sau dayawa, da hawaye a idanu na, nakan yi addu’a ga Jehobah don ya taimake ni. Amma da fari na yi abubuwa yadda bai dace ba, sai na ce wannan shi ne taba sigari na “ƙarshe” da zan sha kuma bayan hakan sai na yi addu’a. Mashaidiyar da take yin nazarin Littafi Mai Tsarki da ni ta taimaka mini na ga muhimmancin yin addu’a kafin na ɗauki taba. Ina kuma bukatan na guji yin tarayya da masu shan taba. Ƙari ga hakan, na bi shawarar gaya wa abokan aikina cewa shan taba ba shi da kyau. Hakan ya taimake ni sosai domin abokan aikina sun daina yi mini kyautar taba.

Daga baya, na daina shan taba kuma na watsar da halaye na na dā. Bayan watanni shida na nazari da kuma yin amfani da ƙa’idodin da ke cikin Littafi Mai Tsarki, an yi mini baftisma a matsayin ɗaya daga cikin Shaidun Jehobah.

YADDA NA AMFANA: Na amince cewa Shaidun Jehobah ne suke bin addini na gaskiya sa’ad da na ga alamar ƙauna da ke tsakanin su, duk da cewa sun fito ne daga ƙabilu dabam-dabam. Kafin ma na yi baftisma a matsayin Mashaidi, wani bature a ikilisiyar ya gayyace ni zuwa gidansa don mu ci abinci tare. Ya kasance kamar mafarki. Ban taɓa zama tare da bature ciki salama ba, ballantana ma mu ci abinci tare. A yanzu na zama sashen tabbatacciyar ’yan’uwanci na dukan duniya.

A dā, masu gadi da ’yan sanda sun so su tilasta mini na canja tunanina da rayuwana, amma ba su yi nasara ba. Littafi Mai Tsarki ne kawai ya taimaka mini na canja rayuwana kuma na zama mai farin ciki.

[Bayanin da ke shafi na 31]

“Sau dayawa, da hawaye a idanu na, nakan yi addu’a ga Jehobah don ya taimake ni”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba