Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 7/1 pp. 10-13
  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 7/1 pp. 10-13

Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane

ME YA sa wani manomin taba ya canja sana’arsa da kuma addininsa da ya riƙe hannu biyu-biyu a dā? Ta yaya wata mashayiya ta samu ƙarfin canja salon rayuwarta? Ka karanta abin da waɗannan mutanen suka ce.

“Na yi murnar kasancewa cikin wannan babban iyali.”​—DINO ALI

SHEKARAR HAIHUWA: 1949

ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: OSTARELIYA

TARIHI: MANOMIN TABA SIGARI

RAYUWATA A DĀ: A shekarar 1939, iyayena sun ƙaura daga Albaniya zuwa Mareeba wani ƙaramin gari a Queensland, a ƙasar Ostareliya. Mutane da yawa daga ƙasashe dabam-dabam kamar Italiya, Sarbiya, Bosniya da Girka sun ƙaura zuwa wannan garin, kuma sun zo da tarbiyyarsu da kuma al’adunsu. Mareeba gari ne da ake noma taba, hakan ya sa iyayena suka fara noma taba.

Ba da daɗewa ba, aka haifi yayata, sai yayyena maza biyu kafin ni. Abin baƙin ciki, ciwon zuciya ya yi sanadiyyar mutuwar babanmu sa’ad da nake ɗan shekara ɗaya. Mahaifiyarmu ta sake yin aure kuma ta haifi ’ya’ya huɗu. Mu duka mun girma ne a cikin gidan gonar taban mijin mahaifiyata.

Na bar gida sa’ad da nake matashi. Na auri matata Saime, a lokacin da na kai ɗan shekara 23, da yake mu Musulmai ne, an ɗaura auren ne a masallacin da ke unguwarmu. Dukan dangina Musulmai ne. Na sauke karatun Alƙur’ani da kuma Hadisi. A wannan lokacin kuma, ina karanta wani ƙaramin Littafi Mai Tsarki. Alƙur’ani na ɗauke da labaran annabawan da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki, kuma karanta Littafi Mai Tsarki da na yi ya sa na san lokacin da suka wanzu.

Shaidun Jehobah suna zuwa gidana kuma suna ba ni mujallu da littattafai, ni da matata Saime mun ji daɗin karanta su. Na tuna mukan yi mahawara a kan batutuwa dabam-dabam game da addini. A kowane tattaunawar da muka yi, maimakon su faɗi ra’ayinsu, Shaidun sun amsa tambayoyina daga Littafi Mai Tsarki. Hakan ya burge ni sosai.

Shaidun sun sha ƙoƙartawa su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni kuma sun gayyace ni zuwa taronsu, amma na ƙi. Abin da kawai na sa gaba shi ne samun gonar kaina da kuma iyali mai yawa. Ko da yake ban mallaki gonar kaina ba, amma na haifi ’ya’ya biyar waɗanda nake ƙauna sosai.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: Sai da na yi shekara tara da sanin Shaidun Jehobah, amma ban canja addinina ba. Amma ina karɓar dukan littattafansu kuma ina jin daɗin karanta su. Ni da matata Saime mukan keɓe lokaci don mu karanta littattafan nan a kowace ranar Lahadi. Mun ajiye dukan littattafan da muka yi shekaru muna karɓa. Waɗannan littattafan sun taimaka mini sosai sa’ad da na fuskanci gwaji daga mutane saboda wannan sabuwar imanina.

Alal misali, na haɗu da wani fasto da ya yi ƙoƙarin tilasta mini in karɓi addininsa. Ya riga ya rinjayi ƙanin matata da kuma ɗan mahaifiyata su bi addininsa. Ba da daɗewa ba, abokai daga addinai dabam-dabam suka yi ta ƙoƙarin shawo kaina in bi addininsu. Wasu kuma sun ba ni littattafan da ke sūkar Shaidun Jehobah. Na gaya wa masu sūkar su nuna mini abin da suke koyarwa daga Littafi Mai Tsarki, amma sun kasa amsa tambayoyin da na yi musu.

Wannan hamayyar ta sa na ƙara bincika Littafi Mai Tsarki da littattafan da na karɓa daga Shaidun Jehobah. Daga ƙarshe, na fahimci cewa lokaci ya yi da ya kamata in yi amfani da abin da nake koya daga Littafi Mai Tsarki.

Ban yi nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah kafin na fara halartar taronsu ba. Da farko, gabana yana ta faɗuwa kuma kunya yana kama ni, amma mutanen da na haɗu da su a waɗannan taron suna da fara’a, kuma na ji daɗin abin da na koya. Na yanke shawara cewa zan zama Mashaidin Jehobah, kuma na yi hakan sa’ad da na yi baftisma a shekara ta 1981.

Matata ba ta tsananta mini a kan wannan shawarar da na yanke ba, ko da yake a wasu lokatai tana ganin cewa an yaudare ni ne. Duk da haka, ta halarci baftismata. Na ci gaba da bayyana mata gaskiyar da nake koya daga Littafi Mai Tsarki. Kusan shekara ɗaya da na yi baftisma, wata rana muna kan hanyarmu ta komawa gida daga hutu a cikin motarmu, sai matata Saime ta gaya mini cewa tana so ta zama Mashaidiya. Sai na ji kamar in zuba ruwa a ƙasa in sha, saboda murna! Ta yi baftisma a shekara ta 1982.

Yin canje-canje da ake bukata bai zo mana da sauƙi ba. Na daina noman taba domin yin hakan ya saɓa wa abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. (2 Korintiyawa 7:1; Yaƙub 2:8) Mun daɗe kafin mu samu aikin da ya dace wanda ke ba mu isashen kuɗin biyan bukatunmu. Kuma, shekaru da dama bayan hakan danginmu sun ƙi su ziyarce mu. Mun ƙoƙarta mun nuna musu ƙauna kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce. Da sannu-sannu, danginmu na kusa suka daina ƙaurace mana.

YADDA NA AMFANA: Jarrabar da na fuskanta waɗanda suka haɗa da daina faɗuwar gaba, fama da rashin abin biyan bukata, tare da jure hamayya daga dangi, duk sun nuna mini yadda Jehobah Allah yake taimaka mini in magance matsalolina. Alal misali, yanzu ni dattijo ne a cikin ikilisiya kuma ina bukatar in riƙa koyar da Littafi Mai Tsarki daga kan dakali a cikin ikilisiya. Hakan bai da sauƙi, domin faɗuwar gaba tana sa ni i’ina sa’ad da nake magana. Amma da taimakon Jehobah da kuma addu’a a kullum, na samu damar cika wannan gatan da aka ba ni.

Dangantakata da matata ta inganta sosai. Mun yi kuskure sa’ad da muke renon yaranmu amma mun yi iya ƙoƙarinmu mu koya musu gaskiyar da muka koya daga Littafi Mai Tsarki. (Kubawar Shari’a 6:6-9) Abin farin ciki, ɗana na fari da matarsa suna aikin wa’azi a ƙasashen waje.

Na tuna wata rana, jim kaɗan bayan iyalita ta soma halartan taron Shaidun Jehobah. Bayan na ajiye mota sai na kalli mutanen da ke cikin majami’a. Na tambayi iyalita, “Me kuka gani?” A cikin majami’ar, akwai mutanen da suka fito daga ƙasashe da kuma al’adu dabam-dabam, wato, mutanen Ostareliya, Albaniya, Croatia, duk da haka, suna cuɗanya da juna cikin farin ciki. Na yi murnar kasancewa cikin wannan babban iyali na ’yan’uwa masu bi, iyalin da ke faɗin duniya ba Ostareliya kaɗai ba.—1 Bitrus 5:9.

“Yayata ba ta taɓa fid da rai a kaina ba.”​—YELENA VLADIMIROVNA SYOMINA

SHEKARAR HAIHUWA: 1952

ƘASAR HAIHUWA: RASHA

TARIHI: MASHAYIYA, KUMA TA TAƁA YUNƘURIN KASHE KANTA

RAYUWATA A DĀ: An haife ni ne a Krosnogorsk, wani ƙaramin birnin da ake da kwanciyar hankali a kusa da Moscow. Iyayena malaman makaranta ne. Ni ɗaliba ce mai ilimi kuma na je makaranta na koyi yin waƙa da kiɗa. Na yi tunanin cewa zan yi nasara a rayuwata.

Sa’ad da na yi aure, ni da maigidana mun ƙaura zuwa yankin da ake yawan yin ashar da maye da kuma shan taba. Ko da yake ban sani ba a lokacin, wurin da muka zauna ya sa na koyi abubuwa marar kyau. Da farko, ina zuwa fati don yin waƙa da kuma kaɗa jita kawai. Da zarar na isa wurin, mutane za su ce in zo mu sha taba sigari tare da giya. Ba da daɗewa ba, na fara jarabar shan giya.

Wannan halin ya soma ɓata rayuwata. Hakan ya jefa ni cikin wani yanayi na baƙin ciki sosai, har na kasa cin abinci. Na gwammace mutuwa, kuma na yi yunƙurin kashe kaina amma ban yi nasara ba. Idan na tuna dā, ina godiya cewa ban yi nasarar kashe kaina ba.

Yayata ta ziyarce ni a kai a kai sa’ad da nake cikin wannan mawuyacin hali. Ta riga ta zama Mashaidiyar Jehobah, kuma ta yi ƙoƙarin bayyana mini yadda Littafi Mai Tsarki zai taimaka mini. Ba na sha’awar tattauna Littafi Mai Tsarki a lokacin, saboda haka na yi ƙoƙarin hana yayata ziyara ta. Amma yayata ba ta taɓa fid da rai a kaina ba. Ta bi da ni cikin haƙuri da ƙauna sosai kuma hakan ya sa na amince in yi nazarin Littafi Mai Tsarki.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: Bayan na fara nazarin Littafi Mai Tsarki, sai na ƙuduri aniyar daina shan giya. A wannan lokacin ne wani maƙwabcinmu da ya sha giya ya bugu ya yi mini dukan tsiya. Ya ji mini rauni sosai har aka kwantar da ni a asibiti. Ya karya mini haƙarƙari guda huɗu kuma ya fasa mini ido. Duk da haka, kasancewa a asibiti ya taimaka mini in daina shan giya.

A wannan lokacin, na yi ta yin addu’a a kullum. Nassin Littafi Mai Tsarki da ya ƙarfafa ni shi ne Makoki 3:55, 56, wadda ta ce: “Daga cikin zurfin ɗakin duhu na kira sunanka, ya Ubangiji. Kā ji muryata; kada ka toshe kunnenka daga jin lumfashina, da jin kukata kuma.”

Na tabbata cewa Jehobah ya amsa addu’o’ina ƙwarai. Ya ba ni ƙarfin ƙin komawa ga yin abubuwa marar kyau da nake yi a dā. Akwai lokatan da nakan yi sha’awar sake soma shan giya. Ina farin ciki cewa ban koma ga wannan jarrabar ba.

Sa’ad da na ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki, na koyi cewa ina bukatar in riƙa ba da haɗin kai ga mijina a matsayinsa na maigida. (1 Bitrus 3:1, 2) Hakan bai zo mini da sauƙi ba domin na saba yi wa mijina mulki. Na yi addu’a ga Jehobah don ya taimaka mini. Na ɗauki lokaci kafin in yi wannan canjin, amma da sannu-sannu na soma ba maigidana haɗin kai.

Canjin da na yi ya ba mijina mamaki sosai. A lokacin, ba ya son tattaunawa game da Littafi Mai Tsarki. Amma sa’ad da na yanke shawarar daina shan taba, sai ya ce: “Idan kika daina shan taba, ni kuma zan soma nazarin Littafi Mai Tsarki!” Mu biyun mun daina shan taba a rana guda.

YADDA NA AMFANA: Maigidana ya cika alkawarinsa kuma ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Da shigewar lokaci, muka yi baftisma a matsayin Shaidun Jehobah. Yanzu, muna karanta Littafi Mai Tsarki a kullum tare, kuma muna fita wa’azi gida-gida a kai a kai don mu koya wa mutane Littafi Mai Tsarki.

Ba zan iya kwatanta yadda rayuwarmu a matsayin iyali ta inganta ba, da kuma yadda ni da kaina na amfana. Ina godiya ga Jehobah domin jawo ni da ya yi zuwa ƙungiyarsa. (Yohanna 6:44) Ina godiya cewa yayata ba ta taɓa fid da rai a kaina ba. A sakamakon haka, na shaida cewa Littafi Mai Tsarki yana gyara rayuwar mutane da gaske.

[Bayanin da ke shafi na 11]

Na fahimci cewa lokaci ya yi da ya kamata in yi amfani da abin da nake koya daga Littafi Mai Tsarki

[Bayanin da ke shafi na 13]

Yayata ta bi da ni cikin haƙuri da ƙauna sosai kuma hakan ya sa na amince in yi nazarin Littafi Mai Tsarki

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba