Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 4/1 pp. 24-27
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • “Na Daina Zalunci”
    Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 4/1 pp. 24-27

Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka

TA YAYA wata mai sayar da giya a mashaya, wadda take da ɗanyen baki, ga mugun shan giya, kuma tana amfani da ƙwayoyi masu sa maye ta canja salon rayuwarta? Me ya sa wani ɗan siyasa a dā wanda ya tsane addini ya zama mai hidima na addini? Waɗanne ƙalubale ne wani mai horar da ’yan sandan kwantar da tarzoma a ƙasar Rasha ya sha kansu don ya zama ɗaya daga cikin Shaidun Jehobah? Ka karanta abin da waɗannan mutanen suka ce.

“Ni da mahaifiyata mun sake zama abokai na kud da kud.”—NATALIE HAM

SHEKARAR DA AKA HAIFE TA: 1965

ƘASAR DA AKA HAIFE TA: OSTARELIYA

TARIHI: NA SHA ƘWAYOYI MASU SA MAYE

RAYUWATA A DĀ: Na girma ne a wani ɗan ƙaramin gari mai suna Robe inda ake kamun kifi, a ƙasar Ostareliya ta Kudu. A irin waɗannan yankunan, mutane suna zuwa su shaƙata ne a hotal ɗin da ke yankin. Iyaye suna zama sosai a hotal, saboda haka, yaransu suna girma ne a inda ake yin shaye-shaye, maganganun banza, da kuma shan taba.

Na soma shan taba sa’ad da na kai ’yar shekara 12, ina da ɗanyen baki, kuma ba na shiri da mahaifiyata. Sa’ad da na kai ’yar shekara 15, iyayena suka rabu, kuma bayan watanni 18, na bar gidanmu. Na zama mashayiya, ina amfani da ƙwayoyi masu sa maye, kuma na zama ’yar iska. Na cika na batse kuma na rikice. Amma da yake na yi shekaru biyar ina koyon wasan dambe da kāre kai, na ji cewa zan iya kula da kaina. Duk da haka, a duk lokacin da nake tunani cikin natsuwa, baƙin ciki ya kan sha kaina kuma in yi addu’a ga Allah, ina roƙonsa ya taimake ni. Na kan gaya masa, “Kada dai ka ce in tafi coci.”

A bayan wani lokaci, wani abokina wanda ya ɗauki kansa a matsayin mabiyi amma ba shi da wani coci na musamman da yake halarta ya ba ni Littafi Mai Tsarki. Kamar sauran abokanmu, yana shan ƙwayoyi masu sa maye. Duk da haka, yana da’awar ba da gaskiya ga Allah kuma ya shawo kaina in yi baftisma. Ya kai ni wani tafki a yankin kuma ya yi mini baftisma. Tun daga lokacin, na soma jin cewa ina da dangantaka na musamman da Allah. Amma, ban taɓa neman lokacin karanta Littafi Mai Tsarki ba.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: A shekara ta 1988, Shaidu guda biyu suka ƙwanƙwasa ƙofata. Ɗaya daga cikinsu ya tambaye ni, “Kin san sunan Allah?” Mashaidin ya karanta Zabura 83:18 daga nasa Littafi Mai Tsarki, wanda ya ce: “Domin su sani kai, wanda sunanka Jehobah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.” Hakan ya ba ni mamaki sosai! Bayan sun tafi, na yi tafiyar mil 35 (kilomita 56) da motata zuwa shagon da ake sayar da littattafan Kirista don in bincika sunan a wasu fassarar Littafi Mai Tsarki kuma na duba sunan a ƙamus. Bayan na tabbatar wa kaina cewa sunan Allah shi ne Jehobah, sai na soma mamakin sauran abubuwan da suka rage da ban sani ba.

Mahaifiyata ta riga ta gaya mini cewa Shaidun Jehobah wasu irin mutane ne. Daga ɗan abin da sani game da su, na ɗauka cewa su masu ra’ayin riƙau ne waɗanda ba sa son canji kuma ba sa yin nishaɗi. Na yanke shawarar cewa zan yi kamar ba na gida idan suka ziyarce ni. Amma na canja ra’ayina sa’ad da suka ziyarce ni. Na marabce su, kuma nan take muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki.

Bayan kowane nazari, ina gaya wa saurayina, Craig, abin da na koya. Daga bisani ya yi fushi sosai har ya ƙwace littafin da muke amfani da shi daga hannuna kuma ya soma karanta shi. Cikin makonni uku, ya kammala cewa ya samu gaskiya game da Allah. Daga baya ni da Craig muka daina shan giya da ƙwayoyi masu sa maye, kuma na daina aikin da nake yi a matsayin mai sayar da giya a mashaya. Don rayuwarmu ta jitu da mizanan Littafi Mai Tsarki, mun yanke shawarar yin aure.

YADDA NA AMFANA: A lokacin da muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki tare da Shaidun Jehobah, ni da Craig muna gab da rabuwa. A yau, Craig mijin da ke nuna kula ne sosai, kuma muna da ’ya’ya biyu masu kyau. Muna da abokan arziki da suke da imani ɗaya da mu.

Da farko, mahaifiyata ta yi fushi sa’ad da ta ji cewa ina tarayya da Shaidun Jehobah. Amma, ta damu ne saboda rashin fahimta. A yanzu ni da mahaifiyata mun sake zama abokai na kud da kud. Na daina tunanin cewa ba ni da wani amfani. Maimakon haka, rayuwata tana da ma’ana da manufa, kuma na biya bukatar da nake da ita na kasancewa da dangantaka da Allah.—Matta 5:3.

“Na koyi abubuwa masu ban mamaki da yawa daga Littafi Mai Tsarki.”—ISAKALA PAENIU

SHEKARAR DA AKA HAIFE SHI: 1939

ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: TUVALU

TARIHI: ƊAN SIYASA

RAYUWATA A DĀ: An haife ni a garin Nukulaelae, a wani kyakkyawan tsibirin Pacific, wanda a yanzu ya zama sashen Tuvalu. Rayuwa a tsibirin tana ƙarƙashin ja-gorancin fastoci waɗanda suke samun koyarwarsu ta addini a wata kwaleji a Samoa. Mutanen da ke zaune a tsibirin ne suke da hakkin ciyar da fastocin da iyalansu a kullum, kuma su ba su masauki, su ne za su yi tanadin dukan abubuwa mafi kyau da suke bukata. Ko da mazauna tsibirin ba su da isasshen abincin da za su ciyar da iyalansu, dole ne su yi wa fastocin tanadin abin da suke bukata.

Faston da ke tsibirinmu ne yake kula da makarantar da ke ƙauyen kuma yana koyar da ilimin addini, lissafi, da labarin ƙasa. Na tuna lokacin da na ga faston yana yi wa ɗalibai dukan kawo wuƙa, jikinsu cike da jini. Amma, babu wanda ya isa ya ce komi, har da iyayen. An ɗauki faston kamar Allah.

Sa’ad da na kai ɗan shekara goma, na bar gida domin in halarci makarantar gwamnati wadda ita kaɗai ce ke yankin, a wani tsibiri dabam. Sa’ad da na kammala karatu, na shiga aikin gwamnati. A lokacin, tsibiran yankuna ne na Tsibirin Gilbert da Ellice waɗanda mallakar Ingila ne. Na yi aiki a ma’aikatu dabam-dabam kafin na zama editan jaridar gwamnati na mako-mako. Kome yana tafiya daidai har sai da na buga wata wasiƙa daga wani mai karanta jaridarmu, wanda ya yi sūka a kan kuɗin da aka kashe wajen shirya ziyarar Yariman ƙasar Wales. Marubucin wasiƙar ya yi amfani da sunan ƙarya, kuma shugabana ya nace sai ya san ainihin sunan mutumin. Na ƙi gaya masa, kuma wannan jayayyar ta zama sananniya a dukan yankin.

Ba da daɗewa ba bayan wannan aukuwar, na bar aikin gwamnati kuma na shiga siyasa. Na ci zaɓe a Nukulaelae kuma an naɗa ni Ministan Kasuwanci da Arzikin Ƙasa. Bayan haka, sa’ad da mutanen tsibirin Kiribati (Gilbert a dā) da tsibirin Tuvalu (Ellice a dā) suke shirin samun ’yancin kai daga Ƙasar Ingila, gwamnan ya yi mani tayin zama shugaban hukumar Tuvalu. Amma, ba na son wani abu ya haɗa ni da mulkin mallaka. Na ƙi tayin da aka yi mini kuma ba tare da neman goyon bayansa ba na shiga takarar neman zaɓen zama minista a gwamnatin. Ban ci zaɓen ba. Bayan haka, na koma ƙauyenmu da ke kan tsibiri tare da matata kuma na yanke shawarar yin rayuwar ƙauye.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: Ranar Lahadi ce ake yin Assabaci a tsibiran, kuma dukan mutanen ban da ni, suna ɗaukan ranar da tsarki. Ranar da nake zuwa tuƙa jirgin ruwa da kamun kifi ke nan. Ba na son a haɗa ni da duk wani addini. Mahaifina ya gaya mini yadda halaye na suka ɓata wa shi da sauran mutane rai. Amma na ƙudurta cewa ba zan yarda coci ya yi tasiri a kaina ba.

A wata tafiyar da na yi zuwa tsibirin Funafuti, wato, babban birnin Tuvalu, ƙanina ya gayyace ni in bi shi zuwa taron Shaidun Jehobah. Daga baya, wani Mashaidi mai wa’azi a ƙasashen waje ya ba ni tarin mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! in karanta. Ya kuma ba ni wani littafin da ya fallasa tushen koyarwar arna waɗanda ake koyarwa a coci da dama da suke da’awar cewa su Kiristoci ne. Na karanta littafin sau da yawa. Na koyi abubuwa masu ban mamaki da yawa daga Littafi Mai Tsarki, har da gaskiyar cewa ba tilas ba ne Kiristoci su kiyaye Assabaci na kowane mako ba.a Na gaya wa matata waɗannan abubuwa, kuma nan take ta daina zuwa coci.

Na riga na ɗauki alkawari cewa babu ruwana da addini. Ko da yake an yi wajen shekara biyu, na kasa mance abubuwan da na koya. Daga bisani, na rubuta wasiƙa zuwa ga mai wa’azi a ƙasashen waje da ke tsibirin Funafuti, na gaya masa cewa na shirya na yi canji. Ya shiga kwalekwale mai zuwa tsibirinmu nan take kuma ya zo ya taimaka mini in ƙara fahimtar Littafi Mai Tsarki. Mahaifina ya yi fushi sosai sa’ad da ya ji cewa ina son in zama ɗaya daga cikin Shaidun Jehobah. Amma na gaya masa cewa na riga na koyi abubuwa da yawa game da Littafi Mai Tsarki daga Shaidun kuma na riga na yanke shawarata.

YADDA NA AMFANA: Na yi baftisma a shekara ta 1986, a matsayin ɗaya daga cikin Shaidun Jehobah, kuma matata ta yi baftisma bayan shekara ɗaya. ’Ya’yanmu biyu mata su ma sun koyi abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa kuma suka yanke shawarar zama Shaidun Jehobah.

Ina farin cikin kasancewa cikin rukunin addinin da, kamar Kiristoci na ƙarni na farko, ba sa nuna bambancin da ke tsakanin limami da mabiyan da ke ƙarƙashinsu. (Matta 23:8-12) Suna bin misalin Yesu cikin tawali’u kuma suna yin wa’azi ga mutane game da Mulkin Allah. (Matta 4:17) Ina godiya ga Jehobah Allah da ya sa na koyi gaskiya game da shi da mutanensa!

“Shaidu ba su tilasta mini in gaskata da abin da suka ce ba.”—ALEXANDER SOSKOV

SHEKARAR DA AKA HAIFA SHI: 1971

ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: RASHA

TARIHI: MAI KOYAR DA DAMBE

RAYUWATA A DĀ: An haife ni ne a birnin Moscow, wadda a lokacin ita ce birnin tarayyar Rasha ta dā. Iyalina sun zauna ne a wani babban gida, kuma maƙwabtanmu da yawa suna aiki tare a wani kamfani. Na tuna gunagunin da suka yi cewa ba na zama wuri ɗaya kuma suka ce idan ban mutu da wuri ba zan samu kaina a ofishin ’yan sanda. Hakika, sa’ad da na kai ɗan shekara goma, na riga na samu matsala da ’yan sanda.

Sa’ad da na kai ɗan shekara 18, an tilasta mini shiga aikin soja kuma na yi aiki a matsayin mai tsaron iyakar ƙasa. Na dawo gida bayan shekara biyu kuma na yi aiki a wani kamfani, amma aikin ya gundure ni. Saboda haka, na shiga aikin ’yan sandan kwantar da tarzoma a Moscow kuma na zama mai koyar da dambe. Na taimaka wajen kama masu aikata laifi a Moscow kuma na je wurare dabam-dabam da ake tarzoma a faɗin ƙasar. Kaina yana yawan ɗaukan zafi. Idan na dawo gida, a wasu lokatai ba na kwana a kan gado guda da matata, domin ina tsoron cewa zan iya raunata ta sa’ad da nake barci.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWANA: Sa’ad na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah, na fahimci cewa rayuwar nuna ƙarfi da nake yi ba ta jitu da mizanan Littafi Mai Tsarki ba. Na kuma gane cewa ina bukatar daina shan taba da kuma daidaita yawan giyar da nake sha. Amma, na yi tunanin cewa ba zan iya canja aikin da nake yi ba, tun da yake ba ni da wata ƙwarewar da za ta sa in samu wani aikin da nake bukata don in ciyar da iyalina. Na kuma yi tunanin cewa ba zan iya yin wa’azi ba, kamar yadda Shaidu suke yi.

Daga baya, na amince cewa labarin Littafi Mai Tsarki gaskiya ne. Kuma na samu ƙarfafawa daga labarin da ke Ezekiyel 18:21, 22. Waɗannan ayoyin sun ce: “Amma idan mugu ya juya ga barin dukan zunubansa da ya aikata, . . .  ba za a riƙe laifinsa da ya yi ko ɗaya a kansa ba.”

Na so yadda Shaidu ba su tilasta mini in gaskata da abin da suka ce ba amma sun taimaka mini in yi tunani a kan abin da nake koya. Na ɗauki mujallunsu guda 40 ko fiye da haka kuma na karance su cikin makonni uku. Abin da na koya ya sa na amince cewa na samu addinin gaskiya.

YADDA NA AMFANA: Kafin in soma nazarin Littafi Mai Tsarki, ni da matata muna gab da kashe aurenmu. Yanzu mun kyautata aurenmu. Matata ta yarda ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki sa’ad da na soma, kuma muka yanke shawarar bauta wa Jehobah tare. A yanzu, dangantakarmu ta ƙara yin daɗi. Na kuma samu aikin da bai saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba.

Sa’ad da na soma wa’azi daga ƙofa-ƙofa, kaina yana ɗaukan zafi, kamar yadda nake ji a dā idan ina gab da kai hari. Yanzu ina da gaba gaɗin cewa zan iya riƙe kaina, ko da wani ya ba ni haushi. Da shigewar lokaci, na koyi yin haƙuri da mutane. Ina nadamar cewa na ɓata rayuwata sosai a dā, amma yanzu rayuwana tana da ma’ana sosai. Ina jin daɗin yin amfani da ƙarfina wajen bauta wa Jehobah Allah da kuma taimaka wa mutane.

[Hasiya]

a Don ƙarin bayani, ka duba talifin nan “Should You Keep The Weekly Sabbath?” da aka wallafa a Hasumiyar Tsaro, na 1 ga Fabrairu, 2010, shafofi na 11 zuwa 15, na Turanci.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba