Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 7/1 pp. 18-22
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 7/1 pp. 18-22

Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka

MENE ne ya motsa wani mawaƙi ɗan tawaye da ba ya hulɗa da mutane ya soma ƙaunar mutane har ya kai ga taimaka musu? Me ya sa wani mutum a ƙasar Meziko ya daina iskanci? Me ya sa wani shahararren ɗan gasar keke a ƙasar Japan ya daina gasar don ya cim ma burinsa na bauta wa Allah? Ka ji abin da waɗannan mutanen za su ce.

“A dā ni mai taurin kai ne da girman kai, kuma ina cin zalin mutane.”​—DENNIS O’BEIRNE

SHEKARAR DA AKA HAIFE SHI: 1958

ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: INGILA

TARIHI: MAWAƘI ƊAN TAWAYE

RAYUWATA A DĀ: A ɓangaren babana, iyalinmu mutanen Irish ne, kuma na girma ne a matsayin ɗan Katolikan Irish. Ina zuwa coci da kaina, ko da yake ba na son zuwa. Duk da haka, ina sha’awar abubuwa na ruhaniya. Ina maimaita Addu’ar Ubangiji a kai a kai, kuma na tuna cewa nakan yi tunanin ma’anarsa yayin da nake kwance a kan gado da daddare. Nakan rarraba shi don in gane ma’anar kowane sashe.

Sa’ad da nake matashi, na shiga ƙungiyar Rastafariya. Na kuma yi harka da ƙungiyar siyasa irin su Masu Hamayya da Nazi. Amma na yi nisa sosai wajen bin halin tawaye na rukunin mawaƙan punk rock. Na sha mugayen ƙwayoyi, musamman taba wi-wi, wadda nake sha kusan kowace rana. Saboda halin “ko-in-kula” da nake da shi, ina mugun shan giya, na sha yin kasada da raina kuma ban damu da mutane ba. Ba na hulɗa da mutane balle in yi magana da su, sai idan na ga cewa yin hakan yana da muhimmanci. Kai, ba na ma bari a ɗauki hotona. Idan na tuna dā, ina ganin yadda na nuna taurin kai, da girman kai, kuma na ci zalin mutane. Ina nuna alheri da karimci ne kawai ga wanda ya kusace ni.

Sa’ad da nake ɗan wajen shekara 20, na soma marmarin sanin Littafi Mai Tsarki. Wani abokina mai sayar da mugayen ƙwayoyi ya soma karanta Littafi Mai Tsarki sa’ad da yake kurkuku, kuma muka tattauna sosai game da addini, Coci, da matsayin Shaiɗan a duniya. Na sayi Littafi Mai Tsarki kuma na soma nazarinsa da kaina. Ni da abokina mukan karanta wani sashen Littafi Mai Tsarki, kuma bayan haka mu haɗu don mu tattauna abin da muka koya, kuma mu yanke shawarwari a kai. Mun yi watanni muna yin haka.

Ga wasu daga cikin abubuwan da muka kammala daga karatun da muka yi: muna zaune ne a kwanakin ƙarshe na wannan duniya; ya kamata Kiristoci su yi wa’azin bisharar Mulkin Allah; ya kamata su kasance ba na duniya ba, har da siyasarta; kuma Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da shawara mai kyau a kan tarbiyya. Mun gano cewa abubuwan da ke cikin Littafi Mai Tsarki gaskiya ne kuma ya wajaba a ce akwai addini na gaskiya guda ɗaya tak. Amma wanne ne? Mun yi tunanin manyan coci-coci masu fahariya da kuma son yin bukukuwa da kuma shiga siyasa, kuma muka gan cewa Yesu bai yi irin wannan rayuwar ba. Mun san cewa Allah ba ya amfani da su, sai muka yanke shawarar bincika sauran addinan da ba a san da zaman su ba sosai don mu ji koyarwarsu.

Muna haɗuwa da mabiyan addinan nan kuma mu yi musu tambayoyi. Mun san abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da kowace tambaya, saboda haka muna sanin sa’ad da amsarsu ba ta jitu da Kalmar Allah ba. A ƙarshen irin waɗannan taron, ina yawan yin addu’a ga Allah, ‘Idan mutanen nan suna cikin addinin gaskiya, ina roƙon ka motsa ni in yi sha’awar sake saduwa da su.’ Amma bayan mun yi watanni muna irin waɗannan taron, na kasa samun rukunin da ya amsa tambayoyin da muka yi daga Littafi Mai Tsarki; kuma ban yi sha’awar sake haɗuwa da su ba.

A ƙarshe, ni da abokina muka sadu da Shaidun Jehobah. Mun yi musu tambayoyin da muka saba yi, kuma suka ba da amsoshin daga Littafi Mai Tsarki. Amsoshinsu sun yi daidai da abubuwan da muka riga muka koya. Saboda haka, mun yi musu tambayoyin da ba mu samu amsoshinsu daga Littafi Mai Tsarki ba tukuna, alal misali, game da ra’ayin Allah a kan shan taba da mugayen ƙwayoyi. Sai kuma suka sake ba da amsar daga Kalmar Allah. Muka yanke shawarar halartar taro a Majami’ar Mulki.

Halartar taro ya yi mini wuya. Na ƙi jinin yin hulɗa da mutane har ya kai ga ba na son saduwa da waɗannan mutane masu adō mai kyau da suke cike da fara’a. Na gaya wa kaina cewa wasu daga cikin su suna da mummunar muradi, saboda haka, na ce ba zan sake halartar wani taro ba. Amma kamar yadda nake yi kullum, na yi addu’a ga Allah cewa ya ba ni sha’awar sake saduwa da mutanen nan idan addininsu ne na gaskiya, kuma na ji sha’awa mai ƙarfi na yin nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: Na san cewa ya kamata in daina shan mugayen ƙwayoyi, kuma yin hakan bai yi mini wuya ba. Mai wuyar ita ce taba sigari. Sau da yawa, na yi ƙoƙarin daina shan taba amma na kasa. Sa’ad da na ji labarin waɗanda suka yar da sigarin da ke hannunsu kuma ba su sake sha ba, na yi addu’a ga Jehobah ya taimaka mini in yi hakan. Bayan haka, da taimakon Jehobah, na daina shan taba. Na koyi amfanin yin magana da Jehobah cikin gaskiya kuma daga zuci.

Wani babban canjin kuma da na yi shi ne irin tufafi da adōn da nake yi. Sa’ad da na halarci taro na farko a Majami’ar Mulki, ina ɗauke ne da wani irin suma mai tsini da ruwan shuɗi a tsakiyar kai, daga gaban goshi zuwa baya. Daga baya, na mayar da shi ruwan lemu. Na saka wandon jin da rigar fata da aka yi rubuce-rubuce a jikinta. Ban ga bukatar canjawa ba, duk da cewa Shaidun sun tattauna da ni cikin sanin ya kamata a kan wannan batun. Amma a ƙarshe, na yi tunani a kan 1 Yohanna 2:15-17: “Kada ku yi ƙaunar duniya, ko abubuwan da ke cikin duniya. Idan kowa ya yi ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa.” Na kammala cewa ina nuna ƙaunar duniya ta hanyar adon da nake yi, kuma dole ne in canja idan zan nuna cewa ina ƙaunar Allah. Abin da na yi ke nan.

Da shigewar lokaci, na fahimci cewa ba Shaidun Jehobah ne kaɗai suke son in halarci taron Kirista ba. Littafin Ibraniyawa 10:24, 25 sun nuna mini cewa Allah ma yana son in yi hakan. Bayan na fara halartar taro da kuma sanin mutanen, na yanke shawarar keɓe rayuwata ga Jehobah ta hanyar yin baftisma.

YADDA NA AMFANA: Yadda Jehobah yake ba mu zarafin yin dangantaka na kud da kud da shi ya taɓa ni sosai. Juyayi da kula da yake nunawa sun motsa ni na yi koyi da shi kuma na bi sawun Ɗansa, Yesu Kristi, a matsayin wanda nake bin gurbinsa. (1 Bitrus 2:21) Na koyi cewa yayin da nake ƙoƙarin yafa halin Kirista, zan iya kasancewa da kamannin da Allah ya halicce ni da shi. Na ƙoƙarta in gina halin ƙauna da kula. Ina ƙoƙarin nuna irin halin Kristi a yadda nake bi da matata da ɗana. Kuma ina kula sosai da ’yan’uwana maza da mata da suke cikin gaskiya. Bin Kristi ya sa na kasance da mutunci da daraja, kuma ya motsa ni na nuna ƙauna ga mutane.

“Sun daraja ni.”​—GUADALUPE VILLARREAL

SHEKARAR DA AKA HAIFE SHI: 1964

ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: MEZIKO

TARIHI: YIN ISKANCI

RAYUWATA A DĀ: Mu bakwai ne iyayena suka haifa, kuma na girma ne a birnin Hermosillo, a Sonora, a ƙasar Meziko, yankin da talauci ya addaba sosai. Mahaifina ya rasu sa’ad da nake ɗan ƙarami, saboda haka, mahaifiyata ce take zuwa ta yi aiki don ta kula da mu. Sau da yawa ina takawa babu takalmi domin ba mu da kuɗin sayen takalma. Tun ina yaro, na soma aiki domin in tallafa wa iyalinmu. Kamar iyalai da yawa, muna cunkushe ne a ɗaki.

Mahaifiyarmu ba ta cika zama a gida da rana domin ta kāremu. Sa’ad da nake ɗan shekara 6, wani ɗan shekara 15 ya soma luwaɗi da ni. Wannan lalatar ta ci gaba da faruwa har wani lokaci mai tsawo. Ɗaya daga cikin sakamakon wannan shi ne ra’ayi na game da jima’i ya rikice. Na ɗauka daidai ne yin sha’awar maza. Sa’ad da na nemi shawara daga likitoci da limamai, sun tabbatar da ni cewa ban da wata matsala kuma daidai ne sha’awar da nake ji.

Sa’ad da nake ɗan shekara 14, na yanke shawarar bayyana kaina a fili a matsayin ɗan luɗu. Na yi irin wannan rayuwar har tsawon shekara 11, kuma na yi zama da mazaje dabam-dabam da dama a lokacin. Daga baya, na koyi gyaran gashi kuma na buɗe shagon kaina. Amma, ba na farin ciki. Sau da yawa nakan sha wahala sosai kuma an sha cin amana ta. Jikina ya ba ni cewa abin da nake yi bai da kyau. Sai na soma tambayar kaina, ‘Akwai mutane masu kirki da mutunci kuwa?’

Sai na tuna da yayata. Ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah kuma daga baya ta yi baftisma. Takan gaya mini abubuwan da take koyo, amma na ƙi mai da hankali. Duk da haka, zaman aurenta da rayuwarta suna burge ni. Na ga cewa ita da mijinta suna ƙauna da kuma daraja juna sosai. Suna bi da juna cikin sanin ya kamata. Bayan wani lokaci, wata Mashaidiyar Jehobah ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Da farko, na ƙi mai da hankali ga nazarin sosai. Amma al’amarin ya canja daga baya.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: Shaidun sun gayyace ni zuwa wani taronsu, kuma na je. Na ga abin da ban taɓa gani ba. Shaidun ba su yi mini dariya ba kamar yadda sauran mutane suke yi. Sun gaida ni cikin mutunci, kuma sun daraja ni. Hakan ya ratsa zuciyata.

Darajar da nake ba Shaidun ta ƙaru sosai sa’ad da na halarci wani babban taronsu. Na ga cewa ko a cikin jama’a ma, mutanen nan masu zuciyar kirki ne, kamar ’yar’uwata. Na tambayi kaina ko wannan ne rukunin mutane masu kirki da mutunci da nake nema tuntuni. Ƙauna da haɗin kai da ke tsakaninsu ya ba ni mamaki sosai, har da yadda suke amfani da Littafi Mai Tsarki wajen amsa duk wata tambaya. Na gane cewa Littafi Mai Tsarki ne ke yi wa rayuwarsu ja-gora. Na kuma ga cewa dole ne in yi canje-canje da dama domin in zama ɗaya daga cikinsu.

Hakika, ina bukatar canji gabaki ɗaya, domin ina rayuwa irin na mata. Ina bukatar in canja furuci na, halayena, tufafina, adon gashina, da kuma abokaina. Abokaina na dā suka soma yi mini ba’a, suna cewa: “Me ya sa kake yin wannan? Yadda kake yana da kyau. Kada ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Kana da dukan abubuwan da kake bukata.” Abubuwan da suka fi mini wuyar canjawa su ne halayena na lalata.

Amma, na san cewa zai yiwu in yi waɗannan canje-canje masu girma, gama kalmomin Littafi Mai Tsarki a 1 Korintiyawa 6:9-11 sun taɓa zuciyata: “Ko kuwa ba ku sani ba marasa-adalci ba za su gaji mulkin Allah ba? Kada ku yaudaru; da masu-fasikanci, da masu-bautan gumaka, da mazinata, da baran mata, da masu-kwana da maza . . . ba za su gāji mulkin Allah ba. Waɗansu ma a cikinku dā haka ku ke: amma aka wanke ku.” Jehobah ya taimaki mutane a dā su yi canji, ni ma ya taimake ni. Ja-gora da kuma ƙauna da Shaidun suka nuna mini sun taimake ni sosai, ko da yake na yi shekaru da dama ina gwagwarmaya sosai kafin na canja.

YADDA NA AMFANA: A yau, ina rayuwar da ta cancanta. Ina da aure, kuma ni da matata muna koya wa ɗanmu ya yi rayuwar da ta jitu da mizanan Littafi Mai Tsarki. Na mance da rayuwata ta dā, kuma ina more amfani da gata na ruhaniya da yawa. Ina yin hidima a matsayin dattijo a cikin ikilisiya, kuma na taimaka ma wasu su koyi gaskiyar da ke cikin Kalmar Allah. Canje-canjen da na yi a rayuwata sun faranta zuciyar mahaifiyata sosai har ya sa ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ta zama Kirista da ta yi baftisma. Wata ƙanwata da take yin lalata a dā ta zama Mashaidiyar Jehobah.

Wasu daga cikin mutanen da suka ƙarfafa ni in ci gaba da irin rayuwata ta dā su ma sun gane cewa na yi canji mai kyau. Na san abin da ya taimake ni yin waɗannan canje-canjen. A dā na nemi taimako daga wajen masana amma sai mummunar shawara kawai na samu. Amma, Jehobah ya taimake ni da gaske. Ko da yake na ji ban cancanta ba, ya lura da ni kuma ya bi da ni cikin ƙauna da haƙuri. Na canja rayuwata ne domin na san cewa Allah mai basira da ƙauna zai kula da ni kuma yana son in more rayuwa mai kyau.

“Na shaida rashin gamsuwa, kaɗaici, da kuma rashin manufa a rayuwa.”​—KAZUHIRO KUNIMOCHI

SHEKARAR DA AKA HAIFE SHI: 1951

ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: JAPAN

TARIHI: MAI YIN TSERE DA KEKE

RAYUWATA A DĀ: Na girma ne a wani garin da ke da tashar jirgin ruwa a Shizuoka Prefecture a Japan, inda iyalinmu mu takwas muke zaune a wani ƙaramin gida. Mahaifina yana da shagon da ake gyara da kuma sayar da keke. Tun lokacin da nake ɗan ƙarami, yakan kai ni inda ake yin tsere da keke kuma hakan ya sa ni sha’awar wasan. Sai mahaifina ya fara shirya ni don in zama gogaggen mai yin tsere da keke. Sa’ad da nake sakandare, ya soma horar da ni da ƙwazo. A shekaru uku na ƙarshe kafin in kammala sakandare, na ci kofi sau uku a jere a gasar wasanni na ƙasa da ake yi kowace shekara. An ba ni damar shiga jami’a, amma na yanke shawarar shiga makarantar koyan yin tsere da keke. Sa’ad da nake ɗan shekara 19, na zama ƙwararren mai yin tsere da keke.

A lokacin, makasudi na a rayuwa shi ne in zama na farko a tseren keke a ƙasar Japan. Burina shi ne in yi kuɗi sosai domin iyalina ta kasance da kwanciyar hankali da farin ciki. Na duƙufa sosai a horon da ake yi mini. Duk lokacin da na yi sanyin gwiwa saboda tsananin horon ko kuma sa’ad da tseren ya yi wuya, nakan gaya wa kaina cewa an haife ni ne domin yin tseren keke kuma dole in ci gaba! Kuma abin da ya faru ke nan. Sai na soma cin moriyar ƙwazona. A shekara ta ta farko na zo na farko a cikin sababbin ’yan tsere. A shekara ta ta biyu, na cancanci shiga tseren sanin wanda zai zama na ɗaya a tseren keke a ƙasar Japan. Sau shida a lokatai dabam-dabam, na zo na biyu a wannan tseren.

Yayin da nake cikin ƙwararrun ’yan gasa masu cin kofi, mutane a ko’ina suna kira na ƙaƙƙarfan ƙafafun Tokai, wani yanki a ƙasar Japan. Nakan yi gasa sosai. Da sannu-sannu mutane suka soma jin tsoro na saboda zafin halin da nake nunawa a wasanni. Kuɗin da nake samu sun ƙaru kuma zan iya sayan duk abin da nake sha’awa. Na sayi gida da ke da ɗakin motsa jiki mai na’urori mafi kyau a ciki. Na sayi motar ƙasashen waje mai tsadar da ta kusan kai kuɗin da na sayi gidan. Domin samun kāriya na soma sayen kadara da kuma hannun jari.

Duk da haka, na kasance da rashin gamsuwa, kaɗaici, da kuma rashin manufa a rayuwa. A lokacin, na riga na yi aure kuma ina da yara, amma sau da yawa ba na bi da iyalina cikin haƙuri. Ina saurin fushi da matata da yarana a kan abin da bai taka kara ya karya ba. Sai suka soma kallon fuskata domin su gane ko raina a ɓace yake.

Bayan wani lokaci, sai matata ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Wannan ya kai ga canje-canje masu yawa. Ta ce za ta so ta halarci taron Shaidun, saboda haka sai na yanke shawara cewa za mu je ne a matsayin iyali. Na tuna daren da wani dattijo ya kawo ziyara gidana kuma ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Abin da na koya ya burge ni sosai.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: Ba zan taɓa manta yadda karanta Afisawa 5:5 ta ratsa zuciyata ba. Ayar ta ce: “Mai-fasikanci, da mutum mai-ƙazanta, [“ko mutum mai kwaɗayi wanda shi da mai bautar gumaka duk ɗaya ne,” Littafi Mai Tsarki] duk ba su da gādon kome cikin mulkin Kristi da na Allah.” Na gane cewa yin tsere da keke yana da alaƙa da yin caca kuma irin wannan wasan yana ɗaukaka kwaɗayi. Sai lamirina ya soma damu na. Na gane cewa idan ina son in faranta wa Jehobah Allah rai, ina bukatar daina yin tsere da keke. Amma yin hakan ya yi mini wuya sosai.

Ban daɗe da kammala shekarar da na fi samun ci gaba ba, kuma ina marmarin samun wasu ƙarin shekarun. Amma, na gan cewa yin nazarin Littafi Mai Tsarki ya ba ni kwanciyar hankali, akasin halin da nake bukata don in ci wasa! Na yi tseren ne sau uku kawai bayan da na soma nazari, amma ban fid da zuciyata daga yin tsere ba. Na kuma rasa yadda zan kula da iyalina. Ji nake kamar na kafe, na kasa yin gaba ko baya, kuma dangina suka soma tsananta mini domin sabon addinina. Ran mahaifina ya ɓace sosai. Na damu sosai har na kamu da gyambon ciki.

Abin da ya taimake ni a wannan mawuyacin lokaci shi ne cewa na ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki ina kuma halartar taron Shaidun Jehobah. Da sannu-sannu, bangaskiyata ta yi ƙarfi. Na roƙi Jehobah ya amsa addu’o’ina kuma ya taimake ni in ga cewa ya yi hakan. Matata ta daɗa kwantar mini da hankali sa’ad da ta tabbatar da ni cewa ba ta bukatar zama a babban gida kafin ta kasance mai farin ciki ba. Da sannu-sannu, na samu ci gaba a ruhaniya.

YADDA NA AMFANA: Na ga cewa kalmomin Yesu da aka rubuta a Matta 6:33 gaskiya ne ƙwarai. Ya ce: “Ku fara biɗan mulkinsa, da adalcinsa; waɗannan abubuwa duka fa za a ƙara maku su.” Ba mu taɓa rasa “waɗannan abubuwa” da Yesu yake nufi ba, wato, ainihin bukatun rayuwa. Ko da yake albashina na yanzu kashi ɗaya ne cikin 30 na wanda nake karɓa sa’ad da nake yin tsere, ni da iyalina ba mu taɓa rasa kome ba tun shekaru 20 da suka shige.

Fiye da haka ma, sa’ad da na yi aiki ko ibada da ’yan’uwana masu bi, ina samun farin ciki da gamsuwa da ban taɓa samu ba. Kwanaki suna wucewa da sauri domin ina shagala a hidimar Jehobah. Rayuwar iyalina ta kyautata sosai. ’Ya’yana uku maza da matansu sun zama bayin Jehobah masu aminci.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba