Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
ME YA sa wata mata mai shekaru sittin da wani abu ta daina bauta wa gumaka? Mene ne ya motsa wani firist na addinin Shinto ya daina hidimarsa a inda suke bauta kuma ya zama Kirista mai hidima? Ta yaya wata matar da aka ɗauke ta riƙo tun daga haihuwa ta jimre da tunanin watsarwa? Ka yi la’akari da abin da waɗannan mutanen suka ce.
“Na daina bauta wa gumaka.”—ABA DANSOU
SHEKARAR DA AKA HAIFE TA: 1938
ƘASAR DA AKA HAIFE TA: BENIN
TARIHI: MAI BAUTA WA GUMAKA
RAYUWATA A DĀ: Na girma ne a ƙauyen So-Tchahoué, wadda fadama ce kusa da wani tafki. Mazauna ƙauyen masunta ne kuma suna kiwon shanu da awaki da tumaki da aladu da tsuntsaye. Babu hanyoyi a ƙauyen, mutane suna amfani ne da jiragen ruwa da kwalekwale don zuwa wurare dabam-dabam. Wasu suna gina gidajensu da itatuwa da kuma ciyayi, amma wasu suna gini ne da bulo. Yawancin mutanen ƙauyen talakawa ne. Duk da haka, ba a yawan aikata laifi kamar yadda ake yi a birane.
Sa’ad da nake ƙarama, mahaifina ya tura ni da yayata zuwa inda matsafa suke yin ibada, a nan ne aka koya mana al’adar su ta gargajiya. Sa’ad da na girma, na yanke shawarar bauta wa Dudua (Oduduwa) wanda alla ne a ƙasar Yarabawa. Na gina wa allan nan ɗakin yin bauta kuma a kai a kai ina yin hadayu da doya da man ja da dodon koɗi da kaji da kurciyoyi da kuma wasu dabbobi iri-iri. Waɗannan hadayun suna da tsada, sau da yawa suna cin dukan kuɗin da nake da shi.
YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: Sa’ad da na fara nazarin Littafi Mai Tsarki, na koyi cewa Jehobah ne kaɗai Allah na gaskiya. Na kuma koyi cewa bai amince da yin amfani da gumaka a bauta ba. (Fitowa 20:4, 5; 1 Korintiyawa 10:14) Na gane abin da ya kamata na yi. Saboda haka, na zubar da dukan gumakana kuma na fid da duk wani abin da ke da alaƙa da bautar gumaka daga gidana. Na daina zuwa wurin masu dūba kuma na daina yin bukukuwan al’ada da na jana’iza.
Yin waɗannan canje-canje bai kasance mini da sauƙi ba, a matsayi na na mace mai shekara 60 da wani abu. Abokaina da dangogi da maƙwabta sun ƙi su ba ni goyon baya kuma suka yi ta yi mini dariya. Amma na yi addu’a ga Jehobah don ya ba ni ƙarfin yin abin da dace. Na samu ƙarfafawa daga kalmomin Misalai 18:10, wadda ta ce: “Sunan Ubangiji kagara ne mai-ƙarfi: mai-adalci ya kan gudu ya shiga ciki, shi sami lafiya.”
Wani abin da kuma ya taimaka mini shi ne halartar taron Shaidun Jehobah. A nan ne na shaida ƙauna ta Kirista, kuma hakan ya burge ni domin mutanen nan suna ƙoƙartawa wajen yin rayuwar da ta jitu da mizanan Littafi Mai Tsarki a kan ɗabi’a. Abin da na gani ya gamsar da ni cewa Shaidun Jehobah ne suke bin addini na gaskiya.
YADDA NA AMFANA: Yin amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki ya taimaka mini in kyautata dangantakata da ’ya’yana. Na kuma ji cewa wani irin nauyi ya sauka daga kaina. A dā, nakan kashe dukan kuɗina a kan gumakan da ba sa amfana ta sam. A yanzu, ina bauta wa Jehobah wanda yake tanadar da magani na dindindin ga dukan matsalolinmu. (Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Ina farin ciki sosai cewa na daina bauta wa gumaka, a maimakon haka, ina bauta wa Jehobah! A wurinsa ne na samu kwanciyar rai ta ƙwarai da kuma kāriya.
“Na soma biɗar Allah tun ina yaro.”—SHINJI SATO
SHEKARAR DA AKA HAIFE SHI: 1951
ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: JAPAN
TARIHI: FIRIST NA ADDININ SHINTO
RAYUWATA A DĀ: Na girma ne a wani gari a Fukuoka Prefecture. Iyayena ba sa wasa da addininsu; sun koya mini na bauta wa allolin Shinto tun ina yaro. Sa’ad da nake yaro, sau da yawa nakan yi tunanin yadda zan samu ceto kuma ina da muradi mai ƙarfi na taimaka wa mutanen da suke cikin matsala. Na tuna lokacin da nake firamare, sa’ad da malaminmu ya tambayi ’yan ajinmu abin da za mu so mu zama sa’ad da muka girma. ’Yan ajinmu suna da takamaiman muradi, kamar na zama masana kimiyya. Na ce muradina shi ne in bauta wa Allah. Sai kowa ya fashe da dariya.
Bayan da na kammala sakandare, na shiga makarantar horar da malaman addini. A lokacin wannan horon, na sadu da wani firist na Shinto, wanda yakan yi amfani da lokacinsa na hutu don ya karanta wani littafi mai baƙin bango. Wata rana ya tambaye ni, “Sato, ka san ko wane littafi ne wannan?” Na riga na lura da bangon littafin, sai na ce, “Littafi Mai Tsarki.” Ya ce, “Ya kamata duk wanda yake so ya zama firist na addinin Shinto ya karanta wannan littafin.”
Nan take na fita na je na sayi Littafi Mai Tsarki. Na saka Littafi Mai Tsarki ɗin a inda kowa zai gani a kan kabat ɗina na littattafai kuma na kula da shi sosai. Amma ban nemi lokacin karanta shi ba, saboda na shagala sosai da ayyukan makaranta. Sa’ad da na gama makaranta, na fara aiki a matsayin firist na addinin Shinto a wurin da ake yin bauta. Na cim ma burin da nake da shi tun ina yaro.
Amma, ba da daɗewa ba na gane cewa kasancewa firist na addinin Shinto bai kasance yadda nake zato ba. Yawancin firistoci ba sa nuna ƙauna da kula ga mutane. Kuma da yawa ba su da bangaskiya. Ɗaya daga cikin shugabannina ya gaya mini: “Idan kana so ka yi nasara a nan, dole ne ka riƙa tattaunawa game da batutuwan da suka shafi falsafa kawai. An haramta yin magana game da imani.”
Irin waɗannan maganganu sun sa na yi ƙasa a gwiwa game da addinin Shinto. Ko da yake na ci gaba da aiki a gidan bautar, na soma bincika wasu addinai. Amma, ban ga wani bambanci tsakanin addinan ba. Na ci gaba da yin ƙasa a gwiwa yayin da na ci gaba da bincika addinai dabam-dabam. Na yi tunanin cewa babu addinin gaskiya.
YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: A shekara ta 1988, na haɗu da wani mabiyin addinin Buddhism da ya ƙarfafa ni in karanta Littafi Mai Tsarki. Na tuna da firist ɗin addinin Shinto wanda a shekarun baya ya ƙarfafa ni na yi hakan. Na bi shawarar da ya ba ni. Sa’ad da na fara karanta Littafi Mai Tsarki, nan da nan na duƙufa wajen yin hakan. A wasu lokatai nakan yi karatu tun daga dare har wayewar gari.
Abin da na karanta ya motsa ni na yi addu’a ga Allahn da aka ambata cikin Littafi Mai Tsarki. Na fara da addu’ar misali da ke Matta 6:9-13. Ina maimaita wannan addu’ar bayan kowace awa biyu, har da lokacin da nake hidima a wurin bautar Shinto.
Ina da tambayoyi da yawa game da abin da nake karantawa. A wannan lokacin, na riga na yi aure, kuma na san cewa Shaidun Jehobah suna koya wa mutane Littafi Mai Tsarki domin sun taɓa ziyartar matata. Na sami wata Mashaidiya kuma na yi ma ta tambayoyi da dama. Yadda ta yi amfani da Littafi Mai Tsarki wajen amsa kowace tambaya ya burge ni. Ta gaya wa wani Mashaidi ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni.
Jim kaɗan bayan haka, na fara halartar taron Shaidun Jehobah. Ko da yake ban farga ba a lokacin, a cikin Shaidun da ke zuwa taron akwai waɗanda na yi wa rashin kunya sosai a dā. Duk da haka, sun gai da ni sosai kuma sun yi min kyakkyawar maraba.
A waɗannan taron, na koyi cewa Allah ya bukaci maza su nuna ƙauna da daraja ga waɗanda ke cikin iyalinsu. Zuwa wannan lokacin, na fi mai da hankali ne sosai ga aikina na firist kuma na yi watsi da matata da ’ya’yanmu biyu. Na gane cewa ina kasa kunne sosai ga abin da waɗanda suke zuwa bauta suke cewa, amma ban taɓa damuwa da abin da matata take cewa ba.
Yayin da nake samun ci gaba a nazari na, na koyi abubuwa da yawa game da Jehobah da suka jawo ni kusa da shi. Ɗaya daga cikin ayoyin Littafin Mai Tsarki da suka ratsa zuciyata ita ce Romawa 10:13, wadda ta ce: “Dukan wanda za ya kira bisa sunan Ubangiji za ya tsira.” Na soma biɗar Allah tun ina yaro, kuma na same shi!
Na fara jin cewa bai kamata na riƙa zuwa ɗakin da ake bautar ba. Da farko, na damu da abin da mutane za su ce idan na bar addinin Shinto. Amma na sha gaya wa kaina cewa idan na sami Allah na gaskiya a wani addini dabam, zan bar addinin Shinto. Saboda haka, a bazarar shekara ta 1989, na yanke shawarar bin lamirina. Na bar wurin bautar kuma na miƙa kaina ga Jehobah.
Barin wurin bautar bai zo da sauƙi ba. Shugabannina sun tsauta mini kuma sun yi ƙoƙarin hana ni barin aikin. Abin da ya fi wuya shi ne gaya wa iyayena labarin. Sa’ad da nake kan hanyata ta zuwa gidansu, gabana ya riƙa faɗuwa har ƙirjina ya soma mini ciwo kuma ƙafafuna suka soma rawa! Sau da yawa na tsaya a hanya domin in yi addu’a ga Jehobah don ya ba ni ƙarfi.
Da na isa gidan iyayena, da farko tsoro bai bar ni na ta da zancen ba. Awoyi suka wuce. A ƙarshe, bayan na yi addu’a sosai, na bayyana kome ga mahaifina. Na gaya masa cewa na samu Allah na gaskiya kuma zan bar addinin Shinto domin in bauta masa. Mahaifina ya gigice kuma ya yi baƙin ciki. Sauran dangogina sun zo gidan kuma suka yi ƙoƙarin sa ni na canja ra’ayina. Ba na son na ɓata wa iyalina rai, amma na san cewa bauta wa Jehobah shi ne abin da ya dace. Da shigewar lokaci, iyalina suka amince da matakin da na ɗauka.
Ko da yake na daina zuwa wajen bautar, ina bukatar na daidaita tunanina. Rayuwar firist ta riga ta zama jinina. Na yi ƙoƙarin mance irin wannan rayuwar, amma duk inda na juya, ina ganin abubuwan da suke tuna mini irin rayuwar da na yi a dā.
Abubuwa guda biyu ne suka taimaka mini in shawo kan waɗannan tasiri. Da farko, na dudduba cikin gidana kuma na tattara dukan abubuwan da ke da alaƙa da addinina na dā. Sai na ƙona su gaba ɗaya, littattafai da hotuna har ma da abubuwa masu tsada da suka shafi bautar gumaka. Na biyu, na yi amfani da duk zarafin da na samu don in yi tarayya da Shaidu. Abutarsu da kuma goyon bayan da suka ba ni ya taimaka mini sosai. A kwana a tashi, na mance irin rayuwar da nake yi a dā.
YADDA NA AMFANA: A dā, nakan yi watsi da matata da yarana kuma hakan yana sa su jin kaɗaici sosai. Amma sa’ad da na fara kasancewa tare da su, kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya koya wa magidanta su yi, sai muka ƙara kusantar juna. Da shigewar lokaci, matata ta soma bauta wa Jehobah. A yanzu, ni da matata, ɗanmu, ɗiyarmu da mijinta muna bauta wa Allah na gaskiya tare.
Sa’ad da na yi tunanin burin da nake da shi tun ina yaro, na bauta wa Allah da kuma taimaka wa mutane, na ga cewa na samu duk abin da nake nema, har da ƙari. Ina matuƙar godiya ga Jehobah.
“Na san cewa akwai abin da na rasa.”—LYNETTE HOUGHTING
SHEKARAR DA AKA HAIFE TA: 1958
ƘASAR DA HAIFE TA: AFIRKA TA KUDU
TARIHI: YIN TUNANIN CEWA AN WATSAR DA ITA
RAYUWATA A DĀ: An haife ni ne a Germiston, wani gari mai ɗan arziki inda ba a yawan aikata laifi. Domin suna tunanin cewa ba za su iya kula da ni ba, sai iyayena suka yanke shawarar bayar da ni riƙo. Sa’ad da nake ’yar kwana 14, wasu ma’aurata masu ƙauna suka ɗauke ni riƙo kuma na ɗauke su a matsayin mama da babana. Duk da haka, bayan da na ji tarihina, na yi fama da tunanin watsarwa. Na soma jin cewa bai kamata in zauna da iyayen da suka ɗauke ni riƙo ba, kuma cewa ba su fahimce ni ba.
Sa’ad da nake ’yar wajen shekara 16, na soma zuwa mashaya, inda ni da abokaina muke yin rawa kuma mu saurari mawaƙa. Na soma shan taba sigari sa’ad da na kai ’yar shekara 17. Ina so in zama siririya kamar ’yan matan da ake nunawa a tallar taba sigari. Sa’ad da na kai ’yar shekara 19, na soma aiki a birnin Johannesburg, nan da nan na fara abuta da mutanen banza. Ba da daɗewa ba na soma yin muguwar magana, ina mugun shan taba sigari kuma ina shaye-shaye sosai a ƙarshen mako.
Duk da haka, ina da ƙarfin jiki sosai. Ina zuwa motsa jiki da kuma buga ƙwallon mata da dai sauran wasanni a kai a kai. Na nuna ƙwazo sosai a wajen aiki na, kuma na yi suna a masana’antar kwamfuta. A sakamakon hakan, ina da abin hannu kuma mutane da yawa suna mini kallon mai kuɗi. Amma gaskiyar ita ce, ina cike da baƙin ciki , kuma na rikice sosai. A cikin zuciyata, na san cewa akwai abin da na rasa.
YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: Sa’ad da na soma nazarin Littafi Mai Tsarki, na koyi cewa Jehobah Allah ne mai ƙauna. Na kuma koyi cewa ya nuna wannan ƙaunar ta wajen ba mu Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Kamar ya rubuto mana wasiƙa ce da kansa domin ta yi mana ja-gora. (Ishaya 48:17, 18) Na fahimci cewa idan ina son in amfana daga ja-gorar da Jehobah yake ba da wa cikin ƙauna, dole ne in yi canje-canje sosai a rayuwata.
Ɗaya daga cikin canjin da nake bukatar yi shi ne canja waɗanda nake abota da su. Na yi tunani sosai a kan kalmomin Misalai 13:20, wadda ta ce: “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima: Amma abokin tafiyar wawaye za ya cutu dominsa.” Wannan mizanin ya motsa ni na daina tarayya da abokaina na dā kuma na yi sabon abokai a tsakanin Shaidun Jehobah.
Ƙalubale mafi girma da na fuskanta shi ne daina shan taba sigari; na kamu da jarabar shan taba sosai. Yayin da na shawo kan wannan ƙalubalen, na fuskanci wani ƙalubalen kuma. Barin taba ya sa na ƙara jiki da nauyin kilo 13.6! Hakan ya shafi darajata sosai, kuma sai da na yi wajen shekara goma kafin jikina ya koma yadda yake a dā. Duk da haka, na san cewa matakin da na ɗauka na daina shan taba yana da kyau sosai. Na ci gaba da yin addu’a ga Jehobah, kuma ya ba ni ƙarfin yin nasara.
YADDA NA AMFANA: A yanzu, lafiyar jikina ta ƙaru. Ina da wadar zuci, na daina biɗar farin cikin da aka ce mutum zai iya samu ta wajen yin aiki, samun matsayi da kuma dukiya, domin hakan tamkar allura ce cikin ruwa. A maimakon haka, ina samun farin ciki daga tattauna gaskiyar Littafi Mai Tsarki da mutane. A sakamakon haka, uku daga cikin abokan aikina na dā tare da ni da maigidana muna bauta wa Jehobah tare. Kafin iyayen da suka ɗauke ni riƙo su mutu, na tattauna da kowannensu game da alkawarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki na tashin matattu zuwa aljanna a duniya.
Kusantar Jehobah da na yi ya taimake ni in jure tunanin watsarwa da nake ji. Ya nuna mini cewa ina da daraja ta wajen kawo ni cikin iyalin ’yan’uwa masu bi a dukan duniya. A cikinsu, ina da uwaye, ubanni, ’yan’uwa maza da mata da yawa.—Markus 10:29, 30.
[Hoto a shafi na 12]
A tsakanin Shaidun Jehobah ne na shaida ƙauna ta Kirista
[Hoto a shafi na 13]
Gidan addinin Shinto inda na taɓa bauta