Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 10/1 pp. 18-21
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 10/1 pp. 18-21

Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka

TA YAYA wata uwa wadda ba ta da miji a ƙasar Rasha wadda take bala’in shan ƙwaya ta daina hakan kuma ta kyautata dangantakarta da yaranta? Ta yaya wani mutum wanda ba shi da wurin kwana da ke birnin Kyoto, a ƙasar Japan, ya samu ƙarfi da gaba gaɗin shawo kan matsalar da ta sa ya talauce? Mene ne ya sa wani kaboyi ɗan Ostareliya ya daina maye? Ka yi la’akari da abin da waɗannan mutanen suka ce.

“Na koya cewa ina da hakkin tallafa wa kaina.”—NELLY BAYMATOVA

SHEKARU: 45

ƘASAR DA AKA HAIFE TA: RASHA

TARIHI: MAI BALA’IN SHAN ƘWAYA

RAYUWATA TA DĀ: Na yi girma a Vladikavkaz, birnin tarayyar Jamhuriyar Ossetia ta Arewa (yanzu Alania). Iyalita suna da wadata da ɗan dama. Amma duk da dukiyar da muke da ita, rayuwata cike take da baƙin ciki. Sa’ad da nake ’yar shekara 34, na riga na fita daga gidan miji har sau biyu. Na yi shekaru goma ina shan ƙwaya, a sakamakon hakan, an kwantar da ni sau biyu a asibiti. Ko da ina da yara biyu, ba na ƙaunarsu a lokacin, kuma ba ni da dangataka mai kyau da abokaina ko kuma iyalita.

Mahaifiyata ta riga ta zama Mashaidiyar Jehobah, kuma sau da yawa ina jin tana kuka tana yin addu’a ga Jehobah cewa ya taimake ni. Na yi tunani: ‘Kai mahaifiyata ba ta waye ba! Ta yaya Jehobah zai taimake ni?’ Na yi ƙoƙarin daina shan ƙwaya. Amma ba ni da ƙarfin dainawa da kaina. Akwai sa’ad da na yi kwana biyu ban sha ƙwaya ba. Sai na yanke shawarar fita daga gida, kuma na tsallake tagar gidan. Abin baƙin ciki, ina kan hawan bene na biyu. Tsallen da na yi ya sa na ƙarya hannuna da ƙafata kuma na ji rauni a baya na. Sai da na yi fiye da wata ɗaya ina kwance.

Sa’ad da nake warkewa, mahaifiyata ta kula da ni sosai kuma ba ta yi mini ba’a ba. Ta fahimci cewa ina da matsalar motsin rai da tunani. Amma, ta ajiye wasu mujallun Awake!a kusa da gado na. Na karanta ɗaya bayan ɗaya kuma na ga cewa suna ɗauke da saƙo masu amfani sosai. Sai na yanke shawarar yin nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidu.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: Wani abin da Littafi Mai Tsarki ya koya mini shi ne ɗaukan hakki. Maimakon in sa rai cewa mahaifiyata za ta tallafa mini, na koyi cewa ina da hakkin tallafa wa kaina da kuma yarana a batun kuɗi. Bayan na yi shekaru ina yin abin da na ga dama, sabawa da yin aiki ya yi mani wuya.

Shawarar da ke Kubawar Shari’a 6:5-7, wadda ta ce iyaye su koyar da yaransu game da Allah ta taimake ni sosai. Na fahimci cewa zan ba Allah lissafin yadda na yi renon ’ya’yana biyu. Sanin hakan ya motsa ni in soma kasancewa tare da su kuma na soma nuna musu ƙauna.

Na yi farin ciki matuƙa cewa Jehobah ya ba ni zarafin koyon gaskiya game da shi. Saboda haka, na keɓe masa rayuwata kuma na yi baftisma a matsayin Mashaidiyar Jehobah.

YADDA NA AMFANA: Domin na koyi yadda zan kame mugun fushin da nake yi, hakan ya kyautata dangantakata da mahaifiyata. Dangantakata da yarana ta ƙara kyau.

Tun da yake ina ƙyamar ayyuka marasa kyau, matsaloli da yawa da salon rayuwata ta dā take jawowa duk sun ɓace. Yanzu na samu farin cikin taimaka wa wasu su koyi gaskiya game da Allah mai ƙauna, Jehobah.

“Ina ganin cewa an ceci raina.”—MINORU TAKEDA

SHEKARU: 54

ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: JAPAN

TARIHI: INA KWANA A KAN TITI

RAYUWATA TA DĀ: Na yi girma a birnin Yamaguchi tare da babana da mahaifiyarsa. Ban taɓa sanin mahaifiyata ba. Kakata ta mutu sa’ad da nake ɗan shekara 19, sai na ci gaba da zama da babana. Ina aikin dafa abinci, babana ma haka. Lokacin aikinmu ya bambanta, saboda haka ba ma yawan ganin juna. Na faɗa cikin halin yin aiki na sa’o’i da yawa da kuma shaye-shaye da abokaina.

A kwana a tashi, sai na soma gajiya da aikina. Na yi cacar baki da shugaban aikina kuma na soma maye sosai. Sa’ad da na kusan kai ɗan shekara 30, sai na yanke shawarar barin gida. Sa’ad da kuɗina ya ƙare, sai na soma aiki a gidan caca. Na sadu da wata yarinya, sai muka yi aure. Amma auren ya mutu bayan shekara biyu da rabi.

Na yi baƙin ciki matuƙa kuma na ci bashin kuɗi sosai daga hannun masu ba da rancen kuɗi. Na gudu daga wurin waɗanda suka ara mani kuɗi kuma na soma zama tare da babana, amma ina yawan yi masa ƙarya kuma hakan ya ɓata dangantakarmu. Na saci kuɗi daga wurinsa kuma na ci gaba da yin caca na ɗan lokaci. Daga baya, na talauce kuma na soma kwana a tashar jirgin ƙasa na ɗan lokaci. Na koma birnin Hakata, daga nan kuma na je birnin Himeji, bayan hakan na koma birnin Kyoto. Na yi ’yan shekaru ina kwana a kan titi.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: A shekara ta 1999, sa’ad da nake a wata mashaƙata kusa da Kogin Kamagawa a birnin Kyoto sai wasu mata biyu suka zo wurina. Sai ɗaya daga cikinsu ta tambaye ni, “Za ka so ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki?” Sai na amince da hakan. Kiristoci da suka manyanta a ikilisiyar Shaidun Jehobah da ke yankin suka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni kuma suka taimaka mini in ga muhimmancin yin amfanin da ƙa’idodinsa. Suka shawarce ni in nemi aiki da kuma gidan da zan riƙa kwana. Don na faranta musu rai, na je na yi wasu intabiyu na neman aiki, amma da farko ban nemi aikin da ƙwazo ba. Daga baya, na soma yin addu’ar samun taimako kuma na ƙoƙarta sosai wajen neman aiki, kuma daga baya na samu aiki.

Addu’a kuma ta taimaka mini a mawuyacin lokatai. Waɗanda na ari kuɗaɗe daga wurinsu suka kama ni kuma suka ce sai na biya su. Na damu sosai. A karatun Littafi Mai Tsarki da nake yi kullum, na ga kalaman da ke Ishaya 41:10. A wannan ayar, Allah ya yi wa bayinsa amintattu alkawari cewa zai “taimake[su].” Wannan alkawarin ya ba ni ƙarfi da gaba gaɗi. Na yi aiki tuƙuru kuma na magance matsalolin kuɗi da nake da su. A shekara ta 2000, na cancanci yin baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah.

YADDA NA AMFANA: Abin da na koya daga Littafi Mai Tsarki ya motsa ni na yi ƙoƙarin daidaita dangantakata da babana, kuma ya gafarta mini halayena na dā. Ya yi farin ciki sosai cewa na koyi yin rayuwar da ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Ina ganin cewa an ceci rayuwata domin na soma yin rayuwar da ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.

Ƙari ga hakan, ina iya yin aiki don na tallafa wa kaina. (Afisawa 4:28; 2 Tasalunikawa 3:12) Na kuma samu abokan kirki a cikin ikilisiyar Kirista. (Markus 10:29, 30) Ina godiya sosai domin abubuwan da Jehobah ya koya mani.

“Yin canje-canjen da nake bukata bai zo mini da sauƙi ba.”—DAVID HUDSON

SHEKARU: 72

ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: OSTARELIYA

TARIHI: MUGUN MASHAYI

RAYUWATA TA DĀ: Ni ne ɗa na 11 da iyaye na, Willie da Lucy suka haifa. Iyalita suna zama a yankin Aurukun a Ostareliya, a can arewancin Queensland. An gina Aurukun a bakin Kogin Archer kuma yana kusa da teku. Iyayena sun koya mana mu riƙa fita farauta da kamun kifi don samun abinci. A wannan lokacin, sa’ad da Turawa suka zo, gwamnatin ƙasar ta hana mu ainihin ƙabilun da ke zaune a ƙasar wato mu mutanen Aboriginal, yin amfani da kuɗi kuma ta ce mu zauna a wani keɓaɓɓen wuri.

Iyayena sun yi iya ƙoƙarinsu don su koya mini halaye masu kyau kuma sun koya wa dukan yaransu su riƙa girmama manya a yankin kuma mu riƙa raba duk abin da muke da shi da wasu. A sakamakon haka, mun ɗauki dukan manyan mutane a matsayin babanmu da mamarmu da gwaggonmu da kuma kawunanmu.

Babana ya mutu sa’ad da nake da ɗan shekara bakwai, sai muka koma wani keɓaɓɓen yanki na Aboriginal a Mapoon, wanda ke da nisan mil casa’in a arewacin Aurukun. Sa’ad da na kai ɗan shekara 12, na soma koyon yadda ake kula da dawaki da kuma shanu, kuma har sa’ad da na kusan kai shekaru 50 na ci gaba da aikin Kaboyi a wurare dabam dabam. Salon rayuwata ba ta da kyau. Ina yawan yin shaye-shaye. Hakan ya jawo mini matsaloli da kuma wahaloli da yawa.

A wata fitan shan giya da na yi, na fito daga hotal ina tangaɗi sai na faɗa gaban wata motar da ke kan gudu. Bayan hakan na yi shekaru biyu ina jinya, kuma na daina aikin kiwon dabbobi da nake yi.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: A lokacin da nake jinya, wata abokiyata ta kawo mini wasu mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! don na karanta. Amma, da yake ban je makaranta ba sosai, na kasa karatun sosai. Wata rana, wani dattijo ɗan shekara 83 ya zo wurina da rana tsaka. Na ce ya shigo ya sha ruwan sanyi. Sai ya ba ni wasu littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki kuma ya tambaye ni ko zai iya sake dawowa don ya bayyana mini abin da ke cikin littattafan. Bayan hakan, muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai. Na soma ganin cewa ina bukatar yin canji a halaye na da kuma salon rayuwata idan ina son in faranta wa Allah rai.

Yin canje-canjen bai yi mini sauƙi ba. Amma, saboda abubuwan da mamata ta koya mini, ina girmama dattijon da ke nazarin Littafi Mai Tsarki da ni sosai da kuma fahimi na ruhaniya da yake koyarwa. Duk da haka, na yi jinkirin keɓe rayuwata ga Allah. Na yi tunanin cewa ya kamata na san duk wani abin da ke rubuce a cikin Littafi Mai Tsarki.

Amma wani abokin aikina ya taimake ni in daidaita tunani game da wannan batun. Shi Mashaidin Jehobah ne, kuma ya nuna mini ƙarfafawa da ke Kolosiyawa 1:9, 10. Wannan wurin ya ce muna bukatar mu ci gaba da samun ‘ƙaruwa kuma cikin sanin Allah.’ Abokin aikina ya taimake ni in fahimci cewa zan ci gaba da koyon sabon abu, saboda haka bai kamata in ƙyale rashin ilimina ya hana ni yin baftisma ba.

Na yi farin ciki sosai sa’ad da na soma yin tarayya da Shaidun Jehobah. Na ga mutane daga al’adu dabam-dabam suna bauta wa Allah tare cikin haɗin kai. Wannan haɗin kan ya sa na amince cewa na samu addinin gaskiya, saboda hakan a shekara ta 1985, na yi baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah.

YADDA NA AMFANA: Na iya karatu sosai yanzu, kuma ina amfani da sa’o’i da yawa a kowane mako wajen taimaka wa mutane su koyi karatu da nazarin Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga hakan, budurwar da ta fara ba ni mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! ta yi nazari da Shaidu, ta yi baftisma, kuma ita ce ƙaunatacciyar matata yanzu. Muna samun farin cikin taimaka wa mutane tare a yankin Aboriginal don su koya game da Jehobah Allah.

[Hasiya]

a Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

[Bayanin da ke shafi na 21]

Matata da ni muna samun farin cikin taimaka wa mutanen a yankin Aboriginal don su koya game da Allah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba