Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
MENENE ya motsa wani ɗan Rastafariyaa ya aske gashinsa kuma ya daina nuna ƙiyayya ga turawa? Kuma menene ya sa wani mugun matashi da ke karɓar wa masu sayar da ƙwaya kuɗi ya canja salon rayuwarsa? Ka yi la’akari da abubuwan da waɗannan mutanen za su ce.
“Na daina nuna ƙiyayya.”—HAFENI NGHAMA
SHEKARU: 34
ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: ZAMBIYA
TARIHI: ƊAN RASTAFARIYA
TARIHI NA NA DĀ: An haife ni a sansanin ’yan gudun hijira da ke ƙasar Zambiya. Mamata ta gudu ne daga Namibiya a lokacin yaƙi kuma ta shiga ƙungiyar South West Africa People’s Organization (SWAPO). Wannan ƙungiyar tana yaƙi da gwamnatin Afirka ta Kudu wanda ke mulka Namibiya a wannan lokacin.
Na zauna a sansanin ’yan gudun hijira dabam-dabam a cikin shekaru 15 na farkon rayuwata. Ana koyar da matasan da ke sansanonin SWAPO su zama masu yaɗa wannan neman ’yancin. An nitsar da mu cikin siyasa kuma an koya mana mu ƙi jinin turawa.
Sa’ad da nike ɗan shekara 11, ina son in zama Kirista a wani cocin sansanin wanda na haɗin gwiwa ne tsakanin Roma Katolika, Lutheran, Anglika, da sauransu. Faston da na tattauna da shi ya hana ni ɗaukan wannan matakin. Tun daga wannan lokacin, na zama kafiri. Sa’ad da na kai ɗan shekara 15, son da nike yi wa waƙar reggae da kuma muradi na na kawar da wasu rashin adalcin da baƙaƙen Afirka suka shaida ya sa na shiga ƙungiyar Rastafariya. Na ƙyale gashi na ya yi tsawo kuma ya lanƙwashe, na sha taba wi-wi, na daina cin nama, kuma na soma yaƙin neman ’yanci ga baƙaƙe. Amma, ban daina iskanci da kallon fim na mugunta ba. Kuma na ci gaba da yin batsa.
YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: A shekara ta 1995, sa’ad da nake gab da kai shekara 20, na soma tunani sosai game da abin da zan yi da rayuwata. Ina karanta dukan littattafan Rastafariya da na gani. Wasu daga cikinsu sun yi nuni ga Littafi Mai Tsarki, amma bayanan da suka yi bai gamshe ni ba. Sai na yanke shawarar karanta Littafi Mai Tsarki da kaina.
Bayan haka, wani abokina ɗan Rastafariya ya ba ni wani littafin da ke bayyana Littafi Mai Tsarki wanda Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi. Na yi nazarin wannan littafin tare da Littafi Mai Tsarki. Bayan haka, na haɗu da Shaidun Jehobah kuma na ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su.
Bayan ’yan ƙoƙarin da na yi, na daina shan taba da yawan shan giya. (2 Korintiyawa 7:1) Na tsabtace kamannina, na aske gashin kaina, na daina kallon hotunan batsa da fim ɗin mugunta, kuma na daina yin batsa. (Afisawa 5:3, 4) Daga bisani, na daina nuna ƙiyayya ga turawa. (Ayyukan Manzanni 10:34, 35) Yin waɗannan canje-canjen yana nufin yin watsi da waƙar da ke ƙarfafa nuna bambanci da kuma daina yin cuɗanya da abokaina na dā waɗanda suke ƙoƙarin su sake rinjayana don in koma ga salon rayuwata ta dā.
Bayan na yi waɗannan canje-canjen, na nemi Majami’ar Mulki na Shaidun Jehobah kuma na nemi damar shiga addinin. An yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. A lokacin da na yanke shawarar yin baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah, iyalina ba su yi farin ciki ba. Mahaifiyata ta gaya mini in zaɓi kowanne cikin sauran addinan “Kirista” amma ba Shaidun Jehobah ba. Wani kawuna, wanda babba ne a cikin gwamnati, yana yawan kushe ni domin shawarar da na yanke na yin tarayya da Shaidu.
Amma, koyan yadda Yesu ya bi da mutane da kuma yin amfani da shawararsa ya taimaka mini in jimre da wannan hamayyar da ba’a. Sa’ad da na gwada abin da Shaidu suke koyarwa da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, na gamsu cewa na samu addini na gaskiya. Alal misali, suna bin umurnin da ke cikin Littafi Mai Tsarki na yin wa’azin ga wasu. (Matta 28:19, 20; Ayyukan Manzanni 15:14) Kuma ba su saka hannu a siyasa.—Zabura 146:3, 4; Yohanna 15:17, 18.
YADDA NA AMFANA: Koyan yin rayuwa bisa ga mizanan Littafi Mai Tsarki ya taimaka mini a hanyoyi masu yawa. Alal misali, daina shan taba wi-wi ya taimaka mini in daina yin asarar ɗarurruwan daloli a kowane wata. Na daina mafarke-mafarke, kuma tunanina da lafiyar jikina sun ƙaru sosai.
A yanzu rayuwata ta kasance da manufa da daidaita wadda nike ɗokinsa tun ina matashi. Mafi muhimmanci, a yanzu ina jin cewa na kusaci Allah.—Yaƙub 4:8.
“Na koyi kame kaina idan na yi fushi.”—MARTINO PEDRETTI
SHEKARU: 43
ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: AUSTRALIYA
TARIHI: DILLALIN ƘWAYA
TARIHI NA NA DĀ: Iyayena suna yawan ƙaura sa’ad da nake girma. Na zauna a ƙananan garuruwa, babban birni, da kuma gidan mishan na Furotestan da ke nesa daga birni a ƙasar Australiya. Na tuna abubuwa masu kyau da na yi da ’yan’uwana da kawuna, kamar su kamun kifi, farauta, yin abubuwa na gargajiya, da kuma sassaƙa abubuwa.
Babana ɗan dambe ne kuma ya soma koya mini yin faɗa tuna iya yaro. Mugunta ya zama jinina. Kafin in kai shekara ashirin, na ɓata lokaci mai yawa ina shan giya a gidajen giya. Ni da abokaina muna tsokano faɗa. Muna amfani da wuƙaƙe da sanduna mu kai hari a kan mutane 20 ko fiye da hakan.
Ina samun kuɗi ta wajen sayar da ƙwayoyi da kuma kayayyakin da ma’aikatan inda ake sauƙe kaya daga jirgin ruwa suke satowa. Ina kuma karɓar wa dillalan ƙwaya kuɗinsu kuma in tsorata mutane ta wajen yin amfani da bindigogi. Makasudina shi ne in zama mai kisan gilla. Take na shi ne, Ka kashe wasu ko a kashe ka.
YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: Na ji labarin Shaidun Jehobah tun ina yaro. Sa’ad da na wuce ɗan shekara 20, na tuna cewa na taɓa tambayar mamata ko ta san inda suke. Kwana biyu bayan hakan, wani Mashaidi mai suna Dixon ya ƙwanƙwasa ƙofata. Bayan mun ɗan tattauna, ya gayyace ni zuwa taron Shaidun Jehobah. Na halarci wannan taron kuma fiye da shekaru 20 ke nan yanzu da nike yin hakan. Shaidun sun amsa dukan tambayoyin da nike da su daga Littafi Mai Tsarki.
Na ji daɗin koyan cewa Jehobah ya damu da mutane, har da waɗanda bauta masa. (2 Bitrus 3:9) Na gane cewa shi Uba ne mai ƙauna da zai kula da ni, ko da wasu sun ƙi yin hakan. Hankalina ya kwanta da na koyi cewa zai gafarta mini zunubaina idan na canja hanyoyina. Ayoyin Littafi Mai Tsarki da ke Afisawa 4:22-24 sun shafe ni sosai. Waɗannan ayoyin sun ƙarfafani in ‘tuɓe irin zama na na dā’ kuma in “yafa sabon mutum, wanda an halitta shi bisa ga Allah.”
Ya ɗauke ni lokaci kafin in canja salon rayuwata. A ranakun mako ba na taɓa ƙwayoyi, amma a ƙarshen mako, sa’ad da nike tare da abokaina, sai in sake komawa ruwa. Na fahimci cewa ina bukatan in ƙyale abokaina idan ina son in tsabtace rayuwata, saboda haka, sai na yanke shawarar komawa wata jihar. Wasu cikin abokaina sun ce za su raka ni a wannan tafiyar, kuma na yarda. A lokacin da muke tafiyar, sai suka soma shan wi-wi kuma suka miƙo mini. Na gaya musu cewa na tuba, kuma muka rabu a iyakar jihar. Daga baya na samu labari cewa ba da daɗewa ba bayan mun rabu, abokaina sun yi fashi da bindiga a wani banki.
YADDA NA AMFANA: Sa’ad da na daina yin cuɗanya da waɗannan abokan, yin canje-canje a rayuwata bai yi mini wuya ba. A shekara ta 1989, na yi baftisma a matsayin Mashaidi. Bayan na yi baftisma, sai ni da yayata, mamata, da babana muka soma bauta wa Jehobah tare.
Na yi aure shekaru 17 yanzu kuma ina da yara uku. Na koyi kame kaina idan na yi fushi, ko da wani ne ya ɓata mini rai. Kuma na koyi nuna ƙauna ga mutane daga dukan “kabilai da al’ummai da harsuna.” (Ru’ya ta Yohanna 7:9) Na ga cewa kalmomin Yesu sun zama gaskiya a batu na. Ya ce: “Idan kun zauna cikin maganata, ku ne almajiraina na gaske; za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ’yantar da ku.”—Yohanna 8:31, 32.
[Hasiya]
a ’Yan Rastafariya wata ɗarika ce a Jamaika, suna ajiye gashi lanƙwasashe kuma sun ɗauki Haile Selassie na Habasha a matsayin Allah.”
[Bayanin da ke shafi na 27]
Yin canje-canje ya ƙunshi yin watsi da waƙar da ke ƙarfafa wariyar al’umma
[Bayanin da ke shafi na 28]
Ni da abokaina muna tono faɗa. Muna yin amfani da wuƙa da sanduna don kai hari a kan mutane 20 ko fiye da hakan