Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 4/1 pp. 12-15
  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • “Na Daina Zalunci”
    Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
  • “Yanzu Na Sami ’Yanci na Ƙwarai.”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • “Kamar Dai Ina da Kome da Nake So”
    Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 4/1 pp. 12-15

Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane

ME YA sa wani mutumi ya koma ga bin tafarkin addinin da ya bauɗe wa a dā? Ta yaya wani matashi ya sami irin uban da yake begen samu a rayuwarsa? Ka karanta abin da waɗannan mutanen suka ce.

“Ina bukatar komawa ga bauta wa Jehobah.”—ELIE KHALIL

SHEKARAR HAIHUWA: 1976

ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: ƘUBRUS

TARIHI: ƊA MUBAZZARI

RAYUWATA A DĀ: An haife ni ne a Ƙubrus amma na girma a ƙasar Ostareliya. Iyayena Shaidun Jehobah ne, sun ƙoƙarta su ga cewa na bauta wa Jehobah kuma na bi Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Na yi wa iyayena tawaye kafin in kai ɗan shekara sha tara. Ina fita daga gidanmu da dare ba tare da wani ya sani ba don in tafi yawo da matasa maza da mata. Mun sace motoci kuma mun faɗa matsaloli da dama.

Da farko, na yi waɗannan abubuwan ne a ɓoye domin kada in ɓata wa iyayena rai. Amma da sannu-sannu, na daina jin tsoro. Na ƙulla abota da mutanen da suka girme ni sosai waɗanda ba sa ƙaunar Jehobah, kuma sun koya mini mummunar hali. A ƙarshe, na gaya wa iyayena cewa babu ruwana da addininsu. Sun yi ƙoƙarin su taimaka mini, amma na ƙi ƙememe. Iyayena sun yi baƙin ciki ƙwarai.

Bayan na bar gida, na soma shan ƙwayoyi masu sa maye, na yi noman wi-wi kuma na zama dillalin taɓa wi-wi. Na iskance kuma ina yawan zuwa inda ake yin fati da dare. Na zama mai saurin fushi. Idan mutane suka faɗi abin da ba na so ko kuma suka yi abin da ya ba ni haushi, ina dakā musu tsawa kuma in naushe su. Na yi dukan abubuwan da suka saɓa watafarkin Kiristoci na gaskiya.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: Na yi abota da wani mashayin ƙwaya wanda mahaifinsa ya mutu tun yana yaro. Mukan yi hira har dare. A wasu lokatai sa’ad da muke taɗi da daddare, yakan gaya mini cewa yana kewar mahaifinsa sosai. Tun da yake ina sane da begen tashin matattu tun ina yaro, na soma gaya masa game da Yesu, yadda ya ta da matattu sa’ad da yake duniya da kuma alkawarin da ya yi na yin hakan a nan gaba. (Yohanna 5:28, 29) Nakan gaya masa cewa: “Ka yi tunanin yadda za ka ji sa’ad da ka sake ganin mahaifinka. Dukanmu za mu iya rayuwa har abada a cikin Aljanna a duniya.” Kalmomin nan sun taɓa zuciyar abokina.

A wasu lokatai, abokina yakan kawo zancen kwanaki na ƙarshe ko kuma koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya. Ina yin amfani da nasa Littafi Mai Tsarki don in nuna masa nassi da dama da suka bayyana gaskiya game da Allah Jehobah da Yesu da kuma kwanaki na ƙarshe. (Yohanna 14:28; 2 Timotawus 3:1-5) Tattaunawar da na yi da abokina game da Jehobah ya sa na ƙara yin tunani game da Jehobah.

Da sannu-sannu, gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki, wadda iyayena suka koya mini sa’ad da nake yaro wadda ba ta ratsa zuciyata ba, ta fara yin tasiri a kaina. Alal misali, a wasu lokatai sa’ad da nake shan ƙwayoyi da abokaina, kawai sai in ga na soma tunanin Jehobah. Abokaina da yawa suna da’awar sanin Allah, amma halinsu ya musanta hakan. Tun da yake ba na son in zama kamar su, na fahimci abin da nake bukatar in yi. Ina bukatar komawa ga bauta wa Jehobah.

Hakika, sanin abin da nake bukatar yi ba shi da wuya, amma yin hakan ne yake da wuya. Wasu canjin da na yi ba su da wuya; na daina shan ƙwayoyi masu sa maye cikin sauƙi. Na daina tarayya da abokaina na dā, kuma na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da wani Kirista wanda dattijo ne a ikilisiya.

Wasu canjin kuwa sun zo da wuya sosai. Kame fushina yana yi mini wuya. A wasu lokatai ina ƙoƙartawa sosai wajen kame fushina, amma a wasu lokatai ina komawa gidan jiya. A duk lokacin da hakan ya faru, ina yin baƙin ciki sosai, sai kuma in fara tunanin cewa ba zan iya canjawa ba. Cike da baƙin ciki, na tinkare dattijon da ke nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Dattijon mutumi ne mai haƙuri da kirki, kuma ya ƙarfafa ni sosai. Akwai lokacin da ya sa na karanta wani talifi a Hasumiyar Tsaro game da muhimmancin ƙin yin ƙasa a gwiwa.a Mun tattauna matakan da zan ɗauka idan na yi fushi. Da sannu-sannu, talifin da na karanta da kuma addu’o’in da nake yi ga Jehobah, sun taimaka mini in kame fushina. Daga baya, a watan Afrilu na shekara ta 2000, na yi baftisma kuma na zama Mashaidin Jehobah. Hakan ya faranta ran iyayena sosai.

YADDA NA AMFANA: Ina da kwanciyar hankali kuma zuciyata ta daina damu na, domin na daina ɓata jikina da lalata da kuma shan ƙwayoyi masu sa maye. Yanzu, ko da ina aiki ne ko halartan taron Kirista, ko kuma nishaɗi, ina farin ciki sosai. Ina da ra’ayi mai kyau game da rayuwa.

Ina godiya ga Jehobah domin irin iyayen da ya ba ni, waɗanda ba su gaji da taimaka mini ba. Na kuma yi tunani a kan kalmomin Yesu da ke Yohanna 6:44: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi.” Ina yabon Jehobah a duk lokacin da na tuna cewa shi ne ya sake jawo ni cikin ƙungiyarsa.

“Na yi begen samun uba.”—MARCO ANTONIO ALVAREZ SOTO

SHEKARAR HAIHUWA: 1977

ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: CHILE

TARIHI: MAWAƘIN WAƘAR DA KE ƘARFAFA KISA DA RASHIN IMANI DA RAUNATA MUTANE

RAYUWATA A DĀ: Mahaifiyata ce ta raine ni a birnin Punta Arenas, a Amirka ta Kudu. Iyayena sun rabu da juna sa’ad da nake ɗan shekara biyar, kuma hakan ya sa na fara tunanin cewa ba ni da kowa. Na yi begen samun mahaifi.

Mahaifiyata ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah, kuma takan kai ni taron Kirista a Majami’ar Mulki. Amma na ƙi jinin zuwa taron, kuma ina yawan yin rigima da mahaifiyata a kan hanyarmu ta zuwa taro. Sa’ad da na kai ɗan shekara sha uku, sai na daina zuwa taron kwata-kwata.

A lokacin, na riga na soma sha’awar yin waƙa, kuma na ga cewa ina da wannan baiwar. Sa’ad da na kai ɗan shekara 15, na fara rera waƙar da ke da kiɗa mai ƙarar gaske da kuma waƙar da ke ƙarfafa kisa da rashin imani da raunata mutane a bukukuwa da hotal da kuma a taro. Na bi ƙwararrun mawaƙa, kuma hakan ya sa na fara sha’awar yin waƙoƙi masu daɗi. Na soma koyon waƙa a wata makarantar da ake koyar da waƙa. Sa’ad da na kai ɗan shekara 20, na tafi birnin tarayya, Santiago, don in ci gaba da karatun da nake yi. Na kuma ci gaba da rera irin waƙoƙin da nake yi a dā.

A kullum ina cikin baƙin ciki. Don in rage baƙin cikin da nake yi, ina mugun shan giya da ƙwayoyi masu sa maye har in bugu tare da abokan da muke rera waƙa tare. Da ka gan ni, ka ga ɗan tawaye. Ina saka baƙaƙen tufafi, na bar saje da gemu, kuma na bar gashin kaina har ƙugu.

Sau da yawa, halina ya sa ni yin faɗa da mutane kuma na shiga matsala a hannun hukuma. Akwai ranar da na sha giya na bugu kuma na kai hari kan dillalan ƙwayoyin da suke damu na da abokaina. Waɗannan dillalan sun yi mini dukan tsiya kuma suka karya mini mummuƙe.

Amma, abin da ya fi ɓata mini rai ƙwarai shi ne wani abin da abokaina na kud da kud suka yi mini. Wata rana, na gano cewa budurwata ta yi shekaru tana kwana da babban abokina, kuma ko da yake abokaina sun san da hakan, sun ƙi su gaya mini. Hakan ya sa ni baƙin ciki sosai.

Na koma Punta Arenas, inda na zama malami mai koyar da waƙa da kuma mai kaɗa goge. Na kuma ci gaba da rera waƙar da ke da kiɗa mai ƙarar gaske da kuma waƙar da ke ƙarfafa kisa da rashin imani da raunata mutane. Na haɗu da wata kyakkyawar yarinya mai suna Sussan, kuma muka soma zama tare. Bayan wani lokaci, Sussan ta gano cewa mahaifiyarta ta gaskata da koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya, alhali kuwa ni ban gaskata da hakan ba. Sai ta tambaye ni: “Mece ce gaskiyar?” Na gaya mata cewa koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya ba gaskiya ba ce ba amma ban san inda aka faɗi hakan a cikin Littafi Mai Tsarki ba. Amma na san waɗanda za su taimaka mata. Na gaya mata cewa Shaidun Jehobah za su iya koya mata gaskiya daga Littafi Mai Tsarki. A lokacin ne na yi wani abu da na yi shekaru ban yi ba, wato, na roƙi Allah ya taimake ni.

’Yan kwanaki bayan hakan, na ga wani mutumin da ya yi kama da wanda na sani, sai na tambaye shi ko shi Mashaidin Jehobah ne. Ko da yake kamannina ya ba shi tsoro, ya amsa tambayoyin da na yi masa game da lokacin taro a Majami’ar Mulki. Na tabbata cewa Jehobah ne ya amsa addu’ata. Na je Majami’ar Mulki kuma na zauna a kujerar baya domin kada mutane su gane ni. Amma, sa’ad da suka gan ni, yawancin su sun gane cewa ina zuwa taro sa’ad da nake yaro. Sun yi mini kyakkyawar maraba kuma hakan ya kwantar mini da hankali sosai. Ji na yi kamar na dawo gida. Sa’ad da na ga ɗan’uwan da ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni lokacin da nake yaro, na ce masa ya sake yin nazari da ni.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA: Wata rana, na karanta littafin Misalai 27:11, inda ta ce: “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata.” Na yi farin cikin sanin cewa yana yiwuwa ɗan Adam ya faranta ran Mahaliccin sararin sama. A lokacin ne na farga cewa Jehobah ne Uban da nake begen samu duk rayuwata!

Ina son in faranta wa Ubana na sama rai kuma in yi nufinsa, amma ga shi na yi shekaru ina bala’in shan giya da ƙwayoyi masu sa maye. Na fahimci kalmomin Yesu a Matta 6:24, inda ta ce “ba wanda ke da iko shi bauta wa ubangiji biyu.” Yayin da nake ƙoƙarin yin canji, ƙa’idar da ke 1 Korintiyawa 15:33 ta taɓa zuciyata. Wurin ya ce: “Zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki.” Na gane cewa ba zan iya canja halayen banza da nake da su ba idan ban daina zuwa wuraren da ake aikata su da kuma yin tarayya da abokaina ba. Gargaɗin da Littafi Mai Tsarki ya bayar ya fita sarai: Ina bukatar in ɗauki tsauraran matakai don in kauce wa abubuwan da suke sa ni yin zunubi.—Matta 5:30.

Mataki mafi wuya da na ɗauka a rayuwata ita ce daina ji da kuma rera waƙa marar kyau da nake yi a dā, domin ina matuƙar son irin wannan waƙar. Amma da taimakon abokai a cikin ikilisiya, na yi nasarar daina waɗannan abubuwan. Na daina shan ƙwayoyi kuma na daina yawan shan giya. Na aske sumana da gemuna, kuma na daina saka baƙaƙen tufafi kawai. Sa’ad da na gaya wa Sussan cewa zan aske sumana, hakan ya sa ta soma ɗokin sanin abin da nake yi a Majami’ar Mulki. Sai ta ce: “Zan bi ka zuwa wannan Majami’ar Mulki don in san abin da ke faruwa a wurin!” Ta so abin da ta gani a wurin, kuma ba da daɗewa ba, ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Daga baya, ni da Sussan muka yi aure. A shekara ta 2008, mun yi baftisma kuma muka zama Shaidun Jehobah. Muna farin cikin bauta wa Jehobah tare da mahaifiyata

YADDA NA AMFANA: Na daina bin abubuwan da nake zaton cewa za su sa ni farin ciki har da abokai maci amana. Har yanzu ina son waƙa, amma ba kowace irin waƙa ba. Ina yin amfani da abubuwan da na koya na amfane iyalita da sauransu, musamman matasa. Ina son in taimake su su gane cewa ko da yake abubuwan da wannan duniyar take bayarwa suna da ban sha’awa, amma a ƙarshe, duk “kayan banza” ne.—Filibiyawa 3:8.

Na sami abokai masu aminci a ikilisiyar Kirista, inda ake samun ƙauna da salama. Abu mafi muhimmanci shi ne, na kusaci Jehobah kuma ya zama Uban da nake nema.

[Hasiya]

a Talifin nan, mai jigo “Success Through Perseverance,” ya fito ne a cikin Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Fabrairu, 2000, shafuffuka na 4-6 na Turanci.

[Bayanin da ke shafi na 13]

“Jehobah ne ya sake jawo ni cikin ƙungiyarsa”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba