Alƙalin da ke Manne wa Abin da ya Dace
Littafin Lissafi 20:2-13
ALƘALAI ’yan adam za su iya yanke hukunci da ba daidai ba ko kuwa mai tsanani sosai amma Jehobah Allah ba ya yin hakan, domin shi mai “son shari’a” ne. (Zabura 37:28) Ko da yake mai haƙuri ne, ba ya sakaci. Yana tsayawa ne a kan gaskiya. Ka yi la’akari da yadda ya yanka hukunci game da wani faɗa da tawaye, kamar yadda yake rubuce a Littafin Lissafi sura ta 20.
Gab da ƙarshen tafiyarsu a jeji, Isra’ilawa sun fuskanci matsalar rashin ruwa.a Sai mutanen suka soma yin faɗa da Musa da kuma Haruna, suna cewa: “Don me fa kuka kawo jama’ar Ubangiji cikin jejin nan, domin mu mutu a nan, da mu da dabbobinmu?” (Aya ta 4) Mutanen sun yi kukan cewa jejin “mugun wuri” ne da babu “ɓaure, ko anab, ko rumana”—ainihin itatuwan da Isra’ilawa ’yan leƙen asiri suka kawo daga Ƙasar Alkawari shekaru da suka shige, kuma babu “ruwan sha ba.” (Aya ta 5; Littafin Lissafi 13:23) Suna ɗora laifin ne a kan Musa da Haruna domin jejin bai yi kama da ƙasa mai ni’ima da masu gunaguni na zamanin da ya gabata suka ƙi shiga!
Jehobah bai ƙi masu gunagunin ba. Maimakon haka, ya umurci Musa ya yi abubuwa guda uku: ya ɗauki sandarsa, ya tara jama’ar, kuma ya “yi magana da dutsen a gaban idonsu shi bada ruwansa.” (Aya ta 8) Musa ya yi biyayya ga umurni na ɗaya da na biyu, amma ya ƙi yin biyayya ga na ukun. Maimakon ya yi wa dutsen magana cikin imani ga Jehobah, ya yi wa mutanen magana cikin fushi, ya ce: “Ku ji dai, ku masu tawaye: mu za mu fito maku da ruwa daga cikin wannan dutse?” (Aya ta 10; Zabura 106:32, 33) Sai Musa ya bugi dutsen sau biyu, “ruwa kuwa ya fito dayawa.”—Aya ta 11.
Da hakan, Musa da Haruna sun yi zunubi mai tsanani sosai. Sai Allah ya ce musu, “Kun tayas wa maganata.” (Littafin Lissafi 20:24) Domin sun ƙi yin biyayya ga maganar Allah a wannan lokacin, Musa da Haruna sun zama ’yan tawaye kamar yadda suka kira mutanen. Jehobah ya bayyana hukuncinsa dalla-dalla: Musa da Haruna ba za su yi wa Isra’ilawa ja-gora ba zuwa Ƙasar Alkawari. Amma hukuncin yana da tsanani ne sosai? A’a, domin dalilai da yawa.
Na farko, Allah bai ce Musa ya yi magana da mutanen ba, balle ma ya yanke hukunci cewa su ’yan tawaye ne. Na biyu, Musa da Haruna sun ƙi su ɗaukaka Allah. Allah ya ce: “Ba ku . . . tsarkake ni” ba. (Aya ta 12) Ta wajen cewa ‘mu za mu fito maku da ruwa,’ Musa da Haruna sun yi magana kamar su ne suka ba da ruwan mu’ujizar, ba Allah ba. Na uku, hukuncin da ya yanke ya yi daidai da hukunce-hukuncensa na dā. Allah ya hana ’yan tawaye na dā su shiga cikin Ka’ana, shi ya sa ya yi hakan ga Musa da Haruna. (Littafin Lissafi 14:22, 23) Na huɗu, Musa da Haruna shugabannin Isra’ilawa ne. Waɗanda suke da hakki da yawa za su ba da lissafi sosai ga Allah.—Luka 12:48.
Jehobah yana nace wa yin adalci. Domin shi mai son adalci ne, ba ya iya yanke hukuncin da ba daidai ba. Babu shakka, irin wannan Alƙalin ya cancanci mu dogara da kuma mu daraja shi.
[Hasiya]
a Bayan Fitowarsu daga ƙasar Masar, Isra’ilawa suna shirye su shiga Ka’anan, ƙasar da Allah ya yi wa Ibrahim alkawari. Amma sa’ad da ’yan leƙen asiri guda goma suka ba da mugun labari, mutanen suka yi gunaguni game da Musa. Sai Jehobah ya faɗi cewa za su yi shekara arba’in a cikin jeji, domin dukan tsarar ’yan tawayen su mutu gaba ɗaya.