Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 5/15 p. 21
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Ba Su Cika Alkawarinsu Ba
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Musa da Haruna Sun Nuna Karfin Zuciya
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • Musa Ya Bugi Dutsen
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Alƙalin da ke Manne wa Abin da ya Dace
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 5/15 p. 21

Tambayoyi Daga Masu Karatu

Tun da yake Jehobah ya hana bautar gunki, me ya sa bai hori Haruna ba don ya yi maraƙi na zinariya?

Lokacin da Haruna ya yi maraƙi na zinariya, kamar yadda aka rubuta a Fitowa sura 32, ya karya dokar Allah game da bautar gumaka. (Fit. 20:3-5) A sakamako, “Ubangiji kuma ya yi fushi da Haruna ƙwarai kamar za ya hallaka shi; [Musa] kuwa yi addu’a domin Haruna kuma a wannan loto.” (K. Sha 9:19, 20) Shin addu’ar Musa mai adalci ta sami “iko dayawa” a yanayin Haruna kuwa? (Yaƙ. 5:16) Hakika, domin irin wannan roƙo da kuma aƙalla wasu dalilai biyu, ya zama kamar Jehobah ya amsa addu’ar Musa kuma bai hori Haruna ba.

Dalili na ɗaya shi ne don ayyuka na aminci da Haruna ya yi. Sa’ad da aka umurci Musa ya bayana a gaban Fir’auna kuma ya fito da Isra’ilawa daga ƙasar Masar, Jehobah ya zaɓi Haruna ya raka Musa kuma ya yi magana a matsayin wakilinsa. (Fit. 4:10-16) Waɗannan mazaje biyu sau da yawa da biyayya suke bayana a gaban Fir’auna, suna jimrewa da taurin zuciyar Fir’auna. Saboda haka, sa’ad da suke a ƙasar Masar, Haruna ya gina halin aminci, da kuma yin hidima da gaba gaɗi ga Jehobah.—Fit. 4:21.

Ka yi la’akari da abin da ya sa Haruna ya yi maraƙi na zinariya. Musa ya yi kwanaki arba’in a Dutsen Sinai. Sa’ad da “mutanen suka gani Musa ya yi jinkirin saukowa daga dutsen,” sai suka lallaɓi Haruna ya yi musu gunki. Haruna kuwa ya yi biyayya ya kuma sifanta gunkin maraƙi na zinariyar. (Fit. 32:1-6) Amma dai, yadda Haruna ya aikata a gaba ya nuna cewa bai amince da wannan bautar gunkin ba. Da alama ya yi hakan ne don matsi. Alal misali, sa’ad da Musa ya kawo batun bautar gumaka ga gagarumar ƙarshe, dukan ’ya’yan Lawi haɗe da Haruna da ƙarfi suka goyi bayan Jehobah. Mutane dubu uku masu bautar gumaka waɗanda suka huɗa kansu ga bautar gumaka suka mutu.—Fit. 32:25-29.

Bayan haka Musa ya gaya wa jama’an: “Kun yi zunubi, zunubi mai-girma.” (Fit. 32:30) Saboda haka, ba Haruna kaɗai ne ke da hakkin yin laifi ba. Da shi da jama’a duk sun amfana daga jinƙan Jehobah.

Bayan wannan zance na maraƙi na zinariya, Jehobah ya umurci a naɗa Haruna a matsayin babban firist. “Za ka sa wa Haruna tufafin nan masu-tsarki kuma; za ka shafe shi, ka tsarkake shi,” Allah ya gaya wa Musa, “domin shi yi mani hidima cikin matsayin firist.” (Fit. 40:12, 13) Babu shakka, Jehobah ya gafarta wa Haruna domin kumamancinsa. A zuciya, Haruna mai aminci ne wajen riƙe bauta ta gaskiya, ba ta tawaye na bautar gumaka ba.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba