Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 24 p. 62-p. 63 par. 2
  • Ba Su Cika Alkawarinsu Ba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ba Su Cika Alkawarinsu Ba
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Ɗan Maraƙin Zinariya
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Yadda Za Ka San Hanyoyin Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Bishiya Mai Cin Wuta
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 24 p. 62-p. 63 par. 2
Isra’ilawa suna waka da kuma rawa yayin da suke kewaye karamin sā na gwal

DARASI NA 24

Ba Su Cika Alkawarinsu Ba

Jehobah ya ce wa Musa: ‘Ka zo ka same ni a kan dutse. Zan ba ka dokokina a kan allon dutse.’ Sai Musa ya hau kan dutsen kuma ya yi kwana 40 a wurin dare da rana. Yayin da yake wurin, Jehobah ya rubuta Dokoki Goma a kan allunan dutse guda biyu. Sai ya ba Musa allunan.

Musa ya jefar da alluna biyun a kasa

Bayan wani lokaci, sai Isra’ilawan suka soma tunanin cewa Musa ba zai dawo ba. Sai suka ce wa Haruna: ‘Muna son wani da zai ja-gorance mu. Ka ƙera mana allah!’ Haruna ya ce: ‘Ku ba ni gwal.’ Sai ya yi amfani da ita wajen ƙera musu ƙaramin sā na gwal. Mutanen suka ce: ‘Wannan ƙaramin sān ne Allahn da ya fito da mu daga ƙasar Masar.’ Suka soma bauta masa kuma suka yi babban biki. Shin yin hakan ya dace? A’a, domin mutanen sun yi alkawari cewa za su bauta wa Jehobah kaɗai. Amma yanzu, ba su cika alkawarinsu ba.

Jehobah yana ganin abin da yake faruwa sai ya gaya wa Musa cewa: ‘Ka koma wurin mutanen. Sun ƙi bin umurnina kuma suna bauta wa allahn ƙarya.’ Sai Musa ya sauko daga dutsen, yana riƙe da alluna biyu.

Da Musa ya zo kusa da wurin da mutanen suke, sai ya ji suna waƙa. Sai ya ga suna rawa kuma suna bauta wa ƙaramin sān. Musa ya yi fushi sosai. Sai ya jefar da alluna biyun a ƙasa kuma suka farfashe. Nan da nan sai ya yi kaca-kaca da gunkin. Sai ya tambayi Haruna: ‘Me ya sa ka saurari mutanen nan kuma ka yi musu gunki?’ Sai Haruna ya ce: ‘Kada ka yi fushi. Kai ma ka san halin mutanen nan. Sun ce a yi musu allah kuma da na saka gwal ɗinsu cikin wuta, sai ya zama wannan ƙaramin sā!’ Abin da Haruna ya yi bai dace ba. Sai Musa ya sake hawa dutsen kuma ya roƙi Jehobah ya gafarta wa mutanen.

Jehobah ya gafarta wa Isra’ilawa da suke so su yi masa biyayya. Wannan labarin ya nuna dalilin da ya sa yake da muhimmanci Isra’ilawa su bi ja-gorancin Musa, ko ba haka ba?

‘Sa’ad da kake yin [alkawari] a gaban Allah, ka biya ba tare da jinkiri ba; gama ba ya jin daɗin wawaye: sai ka biya abin da ka yi wa’adinsa.’​—Mai-Wa’azi 5:4

Tambayoyi: Mene ne Isra’ilawa suka yi sa’ad da Musa yake kan dutse? Mene ne Musa ya yi sa’ad da ya dawo?

Fitowa 24:​12-18; 32:​1-30

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba