Ka Kasance Da Hali Irin Na Kristi
“Ku zama da hankali ɗaya da junanku bisa ga Kristi Yesu.”—ROM. 15:5.
1. Me ya sa ya kamata mu bi irin halin Kristi?
YESU ya ce: “Ku zo gareni . . . ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku.” (Mat. 11:28, 29) Wannan gayyata mai daɗaɗa zuciya ta nuna halin ƙauna da Yesu yake da shi. Babu ɗan Adam da zai iya nuna misalin da ta fi wannan kyau da za mu bi. Ko da yake Yesu Ɗan Allah ne mai iko sosai, ya nuna juyayi da ƙauna musamman ga waɗanda suke wahala.
2. Waɗanne fannonin halin Yesu ne za mu bincika?
2 A cikin wannan talifin da kuma guda biyu na gaba, za mu tattauna yadda za mu koya kuma mu kasance da irin halin Yesu kuma mu yi koyi da “nufin Kristi” a rayuwarmu. (1 Kor. 2:16) Za mu mai da hankali musamman ga fannoni biyar: Tawali’un Yesu, alherinsa, biyayyarsa ga Allah, gaba gaɗinsa, da kuma ƙaunarsa.
Ka Koya Daga Halin Tawali’u na Kristi
3. (a) Wane darassi a kan tawali’u ne Yesu ya koya wa almajiransa? (b) Yaya Yesu ya aikata sa’ad da almajiransa suka nuna kasawa?
3 Yesu, kamiltaccen Ɗan Allah, ya zo duniya da son rai don ya yi hidima tsakanin mutane ajizai masu zunubi. Kuma wasu daga cikin su ne za su kashe shi. Duk da haka, Yesu ya ci gaba da kasancewa da farin ciki kuma ya kame kansa. (1 Bit. 2:21-23) “Zuba ido” ga misalin Yesu zai taimake mu mu yi hakan sa’ad da laifin wasu da ajizancinsu suka shafe mu. (Ibran. 12:2) Yesu ya gayyaci almajiransa su ‘ɗauki karkiyarsa’ kuma su yi koyi da shi. (Mat. 11:29) Menene za su iya koya? Wani abu shi ne, Yesu ya nuna tawali’u da kuma haƙuri ga almajiransa duk da kurakuransu. A darensa na ƙarshe kafin ya mutu, Yesu ya wanke ƙafafunsu, ta hakan ya koya musu darasin da ba za su taɓa mantawa ba, na zama masu “ƙasƙantar zuciya.” (Karanta Yohanna 13:14-17.) Daga baya, sa’ad da Bitrus, Yakubu, da Yohanna suka kasa “yin tsaro,” Yesu ya fahimci kasawarsu. Ya yi tambaya: “Siman, kana barci? Ku yi tsaro ku yi addu’a, domin kada ku shiga cikin jaraba: gaskiya ruhu ya yarda, amma jiki rarrauna ne.”—Mar. 14:32-38.
4, 5. Ta yaya misalin Yesu zai taimake mu mu bi da kurakuran wasu?
4 Yaya muke aikatawa idan wani mai bi yana nuna hali na gasa, yana saurin fushi, ko kuma ba ya hanzarin bin umurnin dattawa ko kuma “bawan nan mai-aminci, mai-hikima”? (Mat. 24:45-47) Ko da yake za mu kasance a shirye mu gafarta wa ajizancin mutanen duniyar Shaiɗan, yana iya yi mana wuya mu gafarta wa ’yan’uwanmu sa’ad da suka nuna irin wannan ajizancin. Idan kurakuran wasu yana saurin ɓata mana rai, muna bukatar mu tambayi kanmu, ‘Yaya zan fi nuna “nufin Kristi”?’ Ka tuna cewa Yesu bai yi fushi da almajiransa ba, har a lokacin da suka nuna kasawa ta ruhaniya.
5 Ka yi la’akari da manzo Bitrus. Sa’ad da Yesu ya gaya wa Bitrus ya fito daga cikin jirgin ruwa kuma ya yi tafiya a kan ruwa ya zo inda yake, Bitrus ya yi hakan na ɗan lokaci. Sai Bitrus ya kalli yadda iska ke kaɗa ruwan kuma ya soma nitsewa. Yesu ya yi fushi ne da shi kuma ya ce masa: “Abin da ya cancance ka kenan! Hakan zai koya maka hankali?” A’a! “Nan da nan fa Yesu ya miƙa hannunsa, ya kama shi, ya ce masa, Kai mai-ƙanƙantar bangaskiya, don me ka yi shakka?” (Mat. 14: 28-31) Kamar yadda Yesu ya miƙa hannunsa ya taimaki Bitrus, za mu iya taimaka wa ɗan’uwa wanda yake bukatar ƙarin bangaskiya? Babu shakka, tawali’un da Yesu ya nuna wa Bitrus darassi ne.
6. Menene Yesu ya koya wa manzanninsa game da neman girma?
6 Bitrus yana cikin manzannin da suka ci gaba da yin jayayya game da wanda ya fi girma a cikinsu. Yakubu da Yohanna suna son ɗaya a cikin su ya zauna a hannun dama na Yesu ɗayan kuma a hannunsa na hagu a cikin Mulkinsa. Sa’ad da Bitrus da sauran manzannin suka ji hakan, sai suka yi fushi. Yesu ya sani cewa mai yiwuwa sun koyi wannan halin ne daga yankin da suka girma. Da ya kira su, ya ce: “Kun sani sarakunan al’ummai suna nuna musu sarauta, manyansu kuma suna gwada musu iko. Ba haka za ya zama a cikinku ba: amma dukan wanda ya ke so shi zama babba a cikinku, bawanku za ya zama.” Sai Yesu ya yi nuni ga kansa: “Kamar yadda Ɗan mutum ya zo ba domin a yi masa bauta ba, amma domin shi bauta wa waɗansu, shi bada ransa kuma abin fansar mutane dayawa.”—Mat. 20:20-28.
7. Ta yaya kowannenmu zai sa ikilisiya ta kasance da haɗin kai?
7 Yin tunani game da halin tawali’u na Yesu zai taimaka mana mu zama kamar ‘ƙanana’ tsakanin ’yan’uwanmu. (Luk 9:46-48) Yin hakan yana sa mu kasance da haɗin kai. Kamar uba na babban iyali, Jehobah yana son yaransa su “zauna tare kamar ’yan’uwa,” su yi dangantaka mai kyau. (Zab. 133:1, Littafi Mai Tsarki) Yesu ya yi addu’a ga Ubansa cewa dukan Kiristoci na gaskiya su kasance da haɗin kai, “domin duniya ta sani ka aiko ni, ka yi ƙaunarsu kuma kamar yadda ka ƙaunace ni.” (Yoh. 17:23) Da haka, haɗin kanmu yana sa a san cewa mu mabiyan Kristi ne. Don mu more irin wannan haɗin kai, dole ne mu ɗauki ajizancin wasu kamar yadda Kristi ya yi. Yesu yana gafartawa, kuma ya koyar da cewa sai mun gafarta wa mutane ne za mu sami gafara.—Karanta Matta 6:14, 15.
8. Menene za mu koya daga misalin waɗanda suka daɗe suna bauta wa Allah?
8 Za mu iya koyan abubuwa da yawa ta wajen yin koyi da bangaskiyar waɗanda suka yi shekaru da yawa suna yin koyi da Kristi. Kamar Yesu, waɗannan suna fahimtar ajizancin mutane. Sun koyi cewa nuna juyayi irin na Kristi yana taimaka mana mu “ɗauki kasawar raunana” kuma yana sa mu kasance da haɗin kai. Ƙari ga haka, yana ƙarfafa dukan mutanen ikilisiya su nuna halin Kristi. Fatan da suke yi wa ’yan’uwansu shi ne irin fatan da manzo Bulus yake yi wa Kiristocin da ke ƙasar Roma: “Allah na haƙuri da na ta’aziyya shi yarda muku ku zama da hankali ɗaya da junanku bisa ga Kristi Yesu: domin da zuciya ɗaya da baki ɗaya ku ɗaukaka Allah da Uba na Ubangijinmu Yesu Kristi.” (Rom. 15:1, 5, 6) Hakika, bautar da muke yi tare tana kawo yabo ga Jehobah.
9. Me ya sa muke bukatar ruhu mai tsarki don mu yi koyi da misalin Yesu?
9 Yesu ya haɗa kasancewa da “ƙasƙantar zuciya” da tawali’u, wanda sashe ne ta ɗiyar ruhu mai tsarki na Allah. Saboda haka, tare da yin nazarin misalin Yesu, muna bukatan ruhu mai tsarki na Jehobah, domin mu yi koyi da wannan misalin sosai. Muna bukatan mu yi addu’a don mu sami ruhu mai tsarki na Allah kuma mu yi ƙoƙari mu nuna fasalolin ’yarsa waɗanda suka ƙunshi ‘ƙauna, farin ciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, kamewa.’ (Gal. 5:22, 23) Ta wajen bin misalin tawali’u na Yesu, za mu faranta wa Jehobah, Ubanmu na samaniya rai.
Yesu Ya Nuna wa Mutane Nagarta
10. Yaya Yesu ya nuna nagarta?
10 Nagarta sashe ne na ɗiyar ruhu mai tsarki. Yesu ya nuna nagarta ga mutane a kowane lokaci. Dukan waɗanda suka nemi Yesu da gaske sun ga cewa “ya karɓe su.” (Karanta Luka 9:11.) Menene za mu iya koya daga nagartar da Yesu ya nuna? Mutum mai nagarta yana nuna abokantaka, yana da hankali, yana da juyayi, kuma yana daɗaɗawa. Yesu ya yi hakan. Ya ji tausayin mutane “domin suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi.”—Mat. 9:35, 36.
11, 12. (a) Ka kwatanta wani misali na juyayi da Yesu ya nuna. (b) Menene za ka iya koya daga misalin da aka tattauna a nan?
11 Yesu ya ji tausayi da juyayi, kuma ya yi iya ƙoƙarinsa don ya taimaki mutane. Yi la’akari da wannan misalin. Wata mata ta yi shekara 12 tana wahala daga rashin lafiyar zubar jini. Domin yanayin ta, ta san cewa a ƙarƙashin Dokar Musa ba ta da tsabta kuma ba za ta iya bauta wa Allah tare da sauran mutane ba, kuma duk wanda ya taɓa ta zai kasance marar tsabta. (Lev. 15:25-27) Duk da haka, halin Yesu da kuma yadda yake bi da mutane ya tabbatar mata cewa yana da ikon warkar da ita kuma zai so ya yi hakan. Ta ci gaba da cewa: “Idan na taɓa ko tufafinsa kaɗai, zan sami lafiya.” Ta yi ƙarfin zuciya kuma ta yi hakan, nan da nan ta ji cewa ta warke.
12 Yesu ya san cewa wani ya taɓa shi, kuma ya dudduba don ya ga ko wanene. Macen, wataƙila tana jin tsoro za a tsauta mata domin ta karya Doka, ta faɗi a gabansa tana rawan jiki kuma ta gaya masa gaskiya. Yesu ya tsauta wa wannan mace matalauciya kuwa, wadda take wahala? Ko kaɗan! Ya gaya mata cewa: “Ɗiya, bangaskiyarki ta warkadda ke; ki tafi lafiya.” (Mar. 5:25-34) Babu shakka, jin irin waɗannan kalaman da ke cike da nagarta ya ƙarfafa ta.
13. (a) Yaya halin Yesu ya yi dabam da na Farisawa? (b) Yaya Yesu ya bi da yara?
13 Akasin Farisawa masu taurin zuciya, Kristi bai yi amfani da ikonsa don ya daɗa wa mutane nauyi ba. (Mat. 23:4) Akasin haka, ya koyar da mutane hanyoyin Jehobah cikin haƙuri da sauƙin hali. Yesu mutum ne mai nuna ƙauna ga mabiyansa, kuma a koyaushe yana yin kirki, amini ne shi. (Mis. 17:17; Yoh. 15:11-15) Har yara sun saki jiki a wurin Yesu, kuma babu shakka ya saki jiki a wurin su. Aikinsa bai hana shi ba da lokaci ga yara ƙanana ba. A wani lokaci, almajiransa da har ila suna neman girma kamar shugabannan addinai da ke tare da su, sun yi ƙoƙari su hana mutane kawo yaransu ƙanana don Yesu ya taɓa su. Yesu bai yi farin ciki da almajiransa ba. Ya gaya musu: “Ku bar yara ƙanƙanana su zo gareni; kada ku hana su: gama na irin waɗannan mulkin Allah ya ke.” Sai ya yi amfani da yaran don ya koyar da darasi, ya ce: “Hakika ina ce muku, Dukan wanda ba ya karɓi mulkin Allah kamar yaro ƙanƙani ba, ba za ya shiga cikinsa ba daɗai.”—Mar. 10:13-15.
14. Wane amfani ne yara suke samu daga kulawa mai kyau?
14 Ka ɗan dakata, ka yi tunani yadda wasu cikin waɗannan yaran za su ji shekaru nan gaba sa’ad da suka yi girma, za su tuna cewa Yesu Kristi “ya rungume su, ya sa masu albarka.” (Mar. 10:16) Yaran yau ma da suka amfana don dattawa da wasu sun nuna suna son su, za su tuna da su da farin ciki. Mafi muhimmanci, yara da suka samu irin wannan kulawa a cikin ikilisiya tun suna ƙanana, sun koya cewa ruhun Jehobah yana tare da mutanensa.
Ka Nuna Kirki a Duniya Marar Kirki
15. Me ya sa ba za mu yi mamakin rashin kirki da ake nunawa a yau?
15 Mutane da yawa a yau suna ganin cewa ba su da lokacin yi wa mutane kirki. Mutanen Jehobah suna fuskantar halin duniya a makaranta, wajen aiki, sa’ad da suke tafiya, da kuma a hidima. Halin rashin kirki na iya sa mu sanyin gwiwa, amma bai kamata mu yi mamaki ba. Jehobah ya hure Bulus ya yi mana gargaɗi cewa rayuwa a wannan miyagun “kwanaki na ƙarshe” zai sa Kiristoci na gaskiya su sadu da “masu-son kansu . . . marasa-ƙauna irin na tabi’a.”—2 Tim. 3:1-3.
16. Ta yaya za mu yi kirki irin ta Kristi a cikin ikilisiya?
16 A wani ɓangaren kuma, yanayin da ke cikin ikilisiyar Kirista ya yi dabam da na wannan duniya marar kirki. Ta wajen yin koyi da Yesu, kowannenmu zai iya daɗa ga wannan yanayi mai kyau. Ta yaya za mu iya yin hakan? Mutane da yawa a cikin ikilisiya suna bukatar taimakonmu da ƙarfafawa domin suna fuskantar ciwo da wasu yanayi masu wuya. A waɗannan “kwanaki na ƙarshe” irin waɗannan matsaloli suna iya ƙaruwa, amma ba sabon abu ba ne. A lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, Kiristoci sun sha wahalar irin waɗannan matsaloli. Ayyukan ba da taimako sun dace yanzu kamar yadda yake ga Kiristoci da suka rayu a zamanin dā. Alal misali, Bulus ya gargaɗi Kiristoci su ‘ƙarfafa masu-raunanan zukata, su tokare marasa-ƙarfi, su yi haƙuri da kowa.’ (1 Tas. 5:14) Hakan ya ƙunshi yin kirki irin na Kristi.
17, 18. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya yin koyi da kirki da Yesu ya yi?
17 Kiristoci suna da hakkin su ‘karɓi ’yan’uwansu da kirki,’ su bi da su yadda Yesu zai bi da su, su riƙa nuna sun damu da waɗanda suka sani da daɗewa da waɗanda ba su taɓa saduwa da su ba. (3 Yoh. 5-8) Kamar yadda Yesu ne ya soma nuna juyayi ga mutane, ya kamata mu ma a koyaushe mu riƙa wartsake mutane.—Isha. 32:2; Mat. 11:28-30.
18 Kowannenmu zai iya nuna kirki ta wajen yin wani abu don mu nuna wa mutane muna damuwa da su da kuma cewa mun fahimci matsalolinsu. Mu nemi hanyoyi da zarafin yin hakan. Ya kamata mu yi ƙoƙari don mu riƙa taimakawa! Bulus ya aririta: “Ku yi zaman daɗin soyayya da junanku cikin ƙaunar ’yan’uwa; kuna gabatar da juna cikin bangirma.” (Rom. 12:10) Hakan yana nufin bin misalin Kristi, muna nuna wa mutane kirki, kuma mu koya nuna “ƙauna marar-riya.” (2 Kor. 6:6) Bulus ya kwatanta ƙauna irin na Kristi haka: “Ƙauna tana da yawan haƙuri, tana da nasiha; ƙauna ba ta jin kishi; ƙauna ba ta yin fahariya, ba ta yin kumbura.” (1 Kor. 13:4) Maimakon mu riƙe ’yan’uwanmu a zuciya, bari mu yi biyayya da wannan gargaɗin: “Ku kasance da nasiha zuwa ga junanku, masu-tabshin zuciya, kuna yi ma junanku gafara, kamar yadda Allah kuma cikin Kristi ya gafarta maku.”—Afis. 4:32.
19. Wane sakamako mai kyau za a samu ta wajen nuna kirki irin na Kristi?
19 Yin ƙoƙarin koya da kuma nuna kirki irin na Kristi a kowane lokaci da yanayi yana kawo mana albarka mai yawa. Ruhun Jehobah zai kasance cikin ikilisiya, zai taimaki kowa ya nuna waɗannan ’ya’yan ruhu. Ƙari ga haka, sa’ad da muka bi tafarkin da Yesu ya bar mana kuma muka taimaka wa mutane su yi hakan, bautarmu cikin haɗin kai za ta sa Allah farin ciki. Saboda haka, bari mu yi ƙoƙari mu nuna tawali’u da kirki irin na Yesu a sha’anoninmu da mutane.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Ta yaya Yesu ya nuna cewa shi “mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya”?
• Ta yaya Yesu ya nuna kirki?
• A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna tawali’u da kirki irin na Kristi a wannan lalataciyar duniya?
[Hotunan da ke shafi na 8]
Sa’ad da ɗan’uwa ya yi rashin bangaskiya, yadda Bitrus ya yi, za mu taimaka masa kuwa?
[Hotunan da ke shafi na 10]
Ta yaya za ka taimaka wajen sa ikilisiyar ta zama wurin da ake yin kirki?