Ƙaunar Kristi Tana Motsa Mu Mu Ƙaunaci ’Yan’uwanmu
“[Yesu] ya yi ƙaunar nasa da ke cikin duniya, ya ƙaunace su har matuƙa.”—YOH. 13:1.
1, 2. (a) Me ya sa ƙaunar Yesu ta yi fice? (b) Waɗanne fannoni na ƙauna za mu tattauna a wannan talifin?
YESU ya kafa kamiltaccen misali na ƙauna. Kome game da shi, halinsa da furcinsa, koyarwarsa, da kuma saɗaukar da rayuwarsa da ya yi, duk sun nuna ƙaunarsa. Har ƙarshen rayuwarsa a duniya, Yesu ya nuna ƙauna ga waɗanda ya sadu da su, musamman ga almajiransa.
2 Fitacciyar ƙauna da Yesu nuna ta kafa mizani mai girma da mabiyansa za su bi. Yana kuma motsa mu mu nuna irin wannan ƙaunar ga ’yan’uwanmu na ruhaniya da kuma dukan mutane. A wannan talifin, za mu bincika abin da dattawa a cikin ikilisiya za su iya koya daga Yesu game da nuna ƙauna ga waɗanda suka yi kuskure, har masu tsanani. Za mu kuma tattauna yadda ƙaunar Yesu take motsa Kiristoci su taimaka wa ’yan’uwansu da wasu a lokacin wahala, bala’i, da kuma ciwo.
3. Duk da kuskure mai tsanani da Bitrus ya yi, yaya Yesu ya bi da shi?
3 A daren Yesu na ƙarshe kafin ya mutu, manzo Bitrus ya yi musun saninsa sau uku. (Mar. 14:66-72) Duk da haka, sa’ad da Bitrus ya tuba, kamar yadda Yesu ya annabta, Yesu ya gafarta masa. Yesu ya ɗanka wa Bitrus hakkoki masu girma. (Luk 22:32; A. M. 2:14; 8:14-17; 10:44, 45) Menene muka koya daga halin Yesu ga waɗanda suka yi zunubi mai tsanani?
Ka Nuna Halin Kristi ga Waɗanda Suka Yi Zunubi
4. A wane yanayi ne musamman ake bukatan mu nuna hali irin na Kristi?
4 A cikin yanayi masu yawa da muke bukatar mu nuna halin Kristi, wanda shi ne mafi baƙin ciki shi ne mugun zunubin da wasu suka yi, a cikin iyali ko kuma a cikin ikilisiya. Abin baƙin ciki, yayin da kwanaki na tsarin Shaiɗan suka kai ƙarshe, ruhun duniya yana ƙara lalace ɗabi’ar mutane. Mugun halaye ko kuma halin ko-in-kula da wannan duniyar take nunawa game da ɗabi’a yana iya shafan yara da manya, ya raunana ƙudurinsu na yin abin da ke daidai. A ƙarni na farko, an yi wa wasu yankan zumunci daga cikin ikilisiyar Kirista, kuma an tsauta wa wasu. Hakan yake a yau. (1 Kor. 5:11-13; 1 Tim. 5:20) Duk da haka, sa’ad da dattawa da suka yi wannan shari’a suka nuna ƙauna irin na Kristi, hakan yana shafan mai zunubin sosai.
5. Yaya dattawa za su yi koyi da halin Kristi ga waɗanda suka yi zunubi?
5 Kamar Yesu, dole ne dattawa su ɗaukaka mizanan adalci na Jehobah a kowane lokaci. Idan suka yi hakan, suna nuna tawali’u, alheri, da ƙauna ta Jehobah. Sa’ad da mutum ya tuba da gaske, ya zama mai “karyayyar zuciya” kuma yana da “ruhu mai-tuba” domin kuskurensa, ba zai yi wa dattawa wuya “cikin ruhun tawali’u [su] komo da irin wannan” mutumin ba. (Zab. 34:18; Gal. 6:1) Amma yaya za su bi da wanda ya nuna taurin kai kuma bai nuna ya tuba ba?
6. Menene dattawa za su guje wa sa’ad da suke bi da masu laifi, kuma me ya sa?
6 Sa’ad da mai laifi ya ƙi shawarar da aka ba shi daga Nassi ko kuma ya yi ƙoƙarin ya ɗaura wa wasu laifi, dattawa da wasu suna iya yin fushi. Domin ɓarnar da mutumin ya riga ya jawo, suna iya furta yadda suke ji game da halin mutumin. Duk da haka, fushi yana jawo lahani kuma ba ya nuna “nufin Kristi.” (1 Kor. 2:16; karanta Yaƙub 1:19, 20.) Yesu ya yi wa wasu a zamaninsa gargaɗi sosai, amma bai taɓa furta kalmar da ke nuna ƙiyayya ba ko kuwa wadda za ta jawo baƙin ciki. (1 Bit. 2:23) Maimakon haka, ta kalmominsa da ayyuka, ya bayyana wa masu laifi sarai cewa suna iya su tuba kuma su samu tagomashin Jehobah. Hakika, ɗaya daga cikin ainihin dalilai da suka sa Yesu ya zo duniya ita ce “ceton masu-zunubi.”—1 Tim. 1:15.
7, 8. Menene ya kamata ya yi wa dattawa ja-gora sa’ad da suke shari’a?
7 Yaya misalin Yesu a wannan batun zai shafi yadda muke ɗaukan waɗanda aka yi musu horo a cikin ikilisiya? Ka tuna cewa ja-gorar Littafi Mai Tsarki na yi wa mutane hukunci a cikin ikilisiya yana kāre garken kuma yana iya motsa mai laifi da aka yi masa horo ya tuba. (2 Kor. 2:6-8) Abin baƙin ciki ne cewa wasu ba su tuba ba kuma dole ne a yi musu yankan zumunci, duk da haka, yana da ban ƙarfafa cewa mutane da yawa a cikinsu daga baya sun komo ga Jehobah da kuma ikilisiyarsa. Sa’ad da dattawa suka nuna hali irin na Kristi, suna sa ya yi wa mutumin sauƙi ya tuba kuma daga baya ya dawo. A nan gaba, wasu cikin waɗanda suka yi zunubi a dā ba za su iya tuna dukan shawarar ta Nassi da dattawa suka ba su ba, amma babu shakka za su tuna cewa dattawan sun daraja su kuma sun bi da su da ƙauna.
8 Saboda haka, dole ne dattawa su nuna ‘’yar ruhu,’ musamman ƙauna irin na Kristi, ko da masu laifi ba su amince da abin da ke cikin Nassi ba. (Gal. 5:22, 23) Bai kamata su yi hanzarin yi wa mai laifi yankan zumunci ba. Dole ne su nuna cewa suna son su taimaka wa masu laifi su komo ga Jehobah. Saboda haka, daga baya sa’ad da mai zunubi ya tuba, yadda yawanci suke yi, zai yi godiya sosai ga Jehobah da kuma “kyautai ga mutane” waɗanda suka sa koma ikilisiya ta yi masa sauƙi.—Afis. 4:8, 11, 12.
Ka Nuna Ƙauna Irin ta Kristi a Zamanin Ƙarshe
9. Ka ba da misalin yadda Yesu ya nuna ƙauna ga almajiransa.
9 Luka ya rubuta wani labari inda Yesu ya nuna ƙauna ta musamman. Sanin cewa da shigewar lokaci, sojojin Roma za su zagaye Urushalima da za a halaka kuma su hana kowa fita, Yesu cikin ƙauna ya yi wa almajiransa gargaɗi: “Sa’anda kuka ga Urushalima tana kewaye da dāgar yaƙi, sa’annan ku sani rushewarta ta kusa.” Menene za su yi? Yesu ya ba da umurni a kan lokaci da ya fita sarai. “Sa’annan waɗanda ke cikin Yahudiya su gudu zuwa duwatsu; waɗanda suke cikin tsakiyarta su fita waje; waɗanda ke cikin ƙauyuka kada su shigo ciki. Gama waɗannan kwanaki na ramawa ne, domin a cika dukan abin da aka rubuta.” (Luk 21:20-22) Da sojojin Roma suka kewaye Urushalima a shekara ta 66 A.Z., masu biyayya sun bi wannan umurnin.
10, 11. Ta yaya yin la’akari da guduwan da Kiristoci na farko suka yi daga Urushalima zai taimaka mana wajen shirya mu don “ƙunci mai-girma”?
10 Sa’ad da suke guduwa daga Urushalima, Kiristoci suna bukatar su nuna ƙauna irin ta Kirista ga juna, kamar yadda Kristi ya ƙaunace su. Kuma suna bukatan su raba kome da suke da shi da juna. Amma annabcin Yesu yana da cika mai girma fiye da halakar wannan birni na dā. Ya annabta: “Za a yi ƙunci mai-girma, irin da ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har yanzu, ba kuwa za a yi ba daɗai.” (Mat. 24:17, 18, 21) Kafin da kuma lokacin “ƙunci mai-girma” da ke nan gaba, yana yiwuwa mu ma mu sha wahala kuma mu yi rashin abin biyan bukata. Kasancewa da halin Kristi zai taimaka mana mu jimre.
11 A lokacin, muna bukatan mu bi misalin Yesu, mu nuna ƙauna marar son kai. Game da wannan, Bulus ya yi gargaɗi: “Bari kowanen mu ya gami ɗan’uwansa wajen abin da ke nagari, zuwa ginawa. Gama Kristi kuma bai yi son kai ba . . . Yanzu dai Allah na haƙuri da na ta’aziyya shi yarda muku ku zama da hankali ɗaya da junanku bisa ga Kristi Yesu.”—Rom. 15:2, 3, 5.
12. Wace irin ƙauna ce muke bukatar mu koya yanzu, kuma me ya sa?
12 Bitrus, wanda Yesu ya nuna wa ƙauna, ya aririci Kiristoci su koyi “sahihiyar ƙauna ta ’yan’uwa” kuma su yi ‘biyayya ga gaskiya.’ Za su yi ‘ƙaunar juna daga zuciya mai gaskiya.’ (1 Bit. 1:22) A yau, fiye da dā, muna bukatar mu kasance da irin waɗannan halaye na Kristi. A yanzu ma haka, mutanen Allah suna fuskantar ƙarin matsi. Bai kamata kowa ya sa rai a kowane sashe na wannan duniyar ba, kamar yadda taɓarɓarewar tattalin arziki na kwanan nan a duniya ya nuna sarai. (Karanta 1 Yohanna 2:15-17.) Maimakon haka, yayin da ƙarshen wannan zamanin ya yi kusa, muna bukatar mu kusaci Jehobah da kuma junan mu, mu ƙulla abokantaka na kud da kud a cikin ikilisiya. Bulus ya yi gargaɗi: “Ku yi zaman daɗin soyayya da junanku cikin ƙaunar ’yan’uwa; kuna gabatar da juna cikin bangirma.” (Rom. 12:10) Kuma Bitrus ya ƙara nanata batun, yana cewa: “Gaba da kome kuma ku zama da ƙauna mai-huruwa zuwa ga junanku; gama ƙauna tana suturtar da tulin zunubai.”—1 Bit. 4:8.
13-15. Yaya wasu ’yan’uwa suka nuna ƙauna irin na Kristi bayan aukuwar bala’i?
13 A dukan duniya an san Shaidun Jehobah da nuna tabbataciyar ƙauna. Ka yi la’akari da Shaidu da suka ba da kansu don su ba da taimako bayan da hadari da guguwa suka yi ɓarna a wurare da yawa a kudancin ƙasar Amirka a shekara ta 2005. Ta wajen bin misalin Yesu na ƙauna, fiye da Shaidu 20,000 suka ba da kansu, da yawa cikinsu sun bar gidajensu masu kyau da aikinsu don su taimaka wa ’yan’uwansu da suke wahala.
14 A wani wuri, ruwan tekun ya kai har mil hamsin a tsakiyar ƙasar, kuma yawan ruwan ya kai tsawon kafa 30. Sa’ad da ruwan ya janye, kashi uku na gidaje da wasu gine-gine da ke hanyar da ruwan ya bi sun rushe gabaki ɗaya. Shaidu da suka ba da kansu sun zo daga ƙasashe da yawa, wasu da suke da fasaha da ake bukata sun zo su taimaka, sun kawo kayan aiki kuma suna shirye su yi kowane aiki da ake bukatar a yi. ’Yan’uwa mata su biyu ’yan gida guda, gwauraye, sun kwashi kayansu suka sa a cikin babbar mota suka yi tafiyar mil fiye da 2,000 don su ba da taimako. Ɗaya cikinsu ta ci gaba da zama a wajen, har ila tana taimaka wa kwamitin agaji da ke wajen kuma tana hidima na majagaba na kullum.
15 An sake gina ko kuma gyara fiye da gidaje 5,600 na Shaidu da kuma wasu da ke yankin. Yaya Shaidu da ke yankin suka ji game da samun wannan taimako na ƙauna ta musamman? Wata ’yar’uwa wadda gidanta ya rushe ta ƙaura zuwa cikin ƙaramin daki da rufin ke yoyo kuma rasho ɗin ta ya lalace. ’Yan’uwan sun gina mata gida mai kyau. Da ta tsaya a gaban sabon gidanta mai kyau, ta yi kuka, domin tana godiya ga Jehobah da kuma ’yan’uwanta. A yanayi da yawa, Shaidu da gidajen su suka rushe sun kasance a inda suke har tsawon shekara guda ko fiye da haka bayan da aka sake gina gidajensu. Don me? Domin ’yan agaji su zauna a sabon gidajensu. Hakika wannan misali ne na halin Kristi!
Nuna Halin Kristi ga Marasa Lafiya
16, 17. A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna halin Kristi ga marasa lafiya?
16 Mutane kaɗan ne kawai a cikinmu suka taɓa fuskantar tsarar bala’i. Amma kusan kowa ne yake fuskantar matsalolin rashin lafiya, ko nasa ko na waɗanda suke cikin iyalinsa. Halin da Yesu ya nuna wa marasa lafiya misali ne mai kyau a gare mu. Ƙaunarsa ta motsa shi ya ji tausayinsu. Sa’ad da taron jama’a suka kawo masa masu ciwo, “ya warkadda masu-ciwo duka.”—Mat. 8:16; 14:14.
17 A yau, Kiristoci ba su da ikon yin mu’ujiza kamar Yesu don su warkar da masu ciwo, amma kamar Yesu suna jin tausayin marasa lafiya. Yaya suka nuna hakan? Alal misali, dattawa sun nuna cewa suna da halin Kristi ta wajen tsara aikin taimakon marasa lafiya a cikin ikilisiya da kuma tabbatar da cewa an taimaka musu, bisa ga mizanin da aka ambata a Matta 25:39, 40.a (Karanta.)
18. Ta yaya ’yan’uwa mata biyu suka nuna ƙauna ta gaske ga wata ’yar’uwa, menene sakamakon?
18 Hakika, ba sai mutum ya zama dattijo ba zai nuna alheri ga mutane. Ka yi la’akari da Charlene ɗan shekara 44, wadda take da ciwon daji kuma an gaya mata za ta mutu bayan kwanaki goma. Ganin bukatarta da kuma yadda mijinta yake faman kula da ita, ’yan’uwa mata biyu, Sharon da Nicolette, suka ba da kansu su taimaka mata har zuwa kwanakin rayuwarta na ƙarshe. Waɗannan kwanakin sun kai makonni shida, amma ’yan’uwa mata biyun sun nuna ƙaunarsu har ƙarshen rayuwarta. “Yana da wuya sosai idan ka san cewa mutumin ba zai warke ba,” in ji Sharon. “Duk da haka, Jehobah ya ƙarfafa mu. Abin da ya faru ya sa mun kusaci Jehobah da kuma junan mu.” Mijin Charlene ya ce: “Ban zan taɓa manta da yadda waɗannan ’yan’uwa mata ƙaunatattu suka taimaka mana ba. Manufa mai kyau da halin kirki da suka nuna ya sa wannan gwaji na ƙarshe ya yi wa matata Charlene mai aminci sauƙin jimrewa kuma ya ba ni ta’aziyya na zuciya da na zahiri da nake bukata sosai. Zan ci gaba da yi musu godiya. Sadaukar da kai da suka yi ya ƙarfafa bangaskiya ta ga Jehobah da kuma ƙaunata ga dukan ’yan’uwa.”
19, 20. (a) Waɗanne fannoni biyar na halin Kristi muka tattauna? (b) Menene ka ƙuduri aniya za ka yi?
19 A waɗannan talifofi guda uku, mun bincika fannoni biyar na halin Yesu da kuma yadda za mu yi tunani kuma mu aikata yadda ya yi. Bari mu kasance masu ‘tawali’u, masu ƙasƙantar zuciya’ kamar Yesu. (Mat. 11:29) Bari mu yi ƙoƙari mu yi wa mutane kirki, har sa’ad da muka san ajizancinsu da kasawarsu. Bari mu yi biyayya ga dukan dokokin Jehobah da gaba gaɗi, har sa’ad da muke fuskantar gwaji.
20 A ƙarshe, bari mu nuna ƙauna irin na Kristi ga dukan ’yan’uwanmu, yadda Kristi da kansa ya yi, “har matuƙa.” Irin wannan ƙauna tana nuna cewa mu mabiyan Yesu ne na gaske. (Yoh. 13:1, 34, 35) Hakika, “bari ƙaunar ’yan’uwa ta lizima.” (Ibran. 13:1) Kada ka ƙi nuna ta! Ka yi amfani da rayuwarka ka yabi Jehobah kuma ka taimaki mutane! Jehobah zai albarkace ƙoƙarce-ƙoƙarcenka.
[Ƙarin bayani]
a Ka duba talifin nan “Do More Than Say: ‘Keep Warm and Well Fed’” (Ka Yi Fiye da Cewa: ‘Ku ji Ɗumi, Ku Ƙoshi’) a fitowar Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 1986.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Ta yaya dattawa za su nuna hali irin na Kristi ga waɗanda suka yi laifi?
• Me ya sa yin koyi da ƙaunar Kristi yake da muhimmanci musamman a wannan zamani na ƙarshe?
• Ta yaya za mu nuna halin Kristi ga marasa lafiya?
[Hotunan da ke shafi na 17]
Dattawa suna son waɗanda suka yi laifi su dawo ga Jehobah
[Hotunan da ke shafi na 18]
Ta yaya Kiristoci da suka bar Urushalima suka nuna halin Kristi?
[Hotunan da ke shafi na 19]
An san Shaidun Jehobah da nuna ƙauna irin na Kristi