Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 9/15 pp. 21-25
  • Koyarwa Na Allah Ya Fi Ba Da Amfani

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Koyarwa Na Allah Ya Fi Ba Da Amfani
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Gatar Zama Waɗanda Allah Yake Koyar da Su
  • Ikon Kyautata Rayuwa
  • Shiri don Nan Gaba
  • Samun Albarka Don Yin Sadaukarwa
  • ‘Ku Bauta wa Jehobah’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 9/15 pp. 21-25

Koyarwa Na Allah Ya Fi Ba Da Amfani

“Ina lissafta dukan abu hasara kuma bisa ga fifikon sanin Kristi Yesu.”—FILIB. 3:8.

1, 2. Wane zaɓi ne wasu Kiristoci suka yi, kuma me ya sa?

TUN daga lokacin da ya soma makaranta, Robert ɗalibi ne mai ƙwazo sosai. Sa’ad da yake shekara takwas, ɗaya cikin malamansa ta kai masa ziyara a gidansu kuma ta gaya masa cewa zai iya cim ma dukan abin da yake so. Ta yi fatar cewa wata rana zai zama likita. Jarabawa da ya ci a makarantar sakandare ta sa ya cancanta zuwa kowanne cikin jami’o’i mafi kyau a ƙasarsu. Amma Robert ya zaɓa ya yi watsi da abin da mutane da yawa suke ɗaukan zarafi da ba zai sake samu ba don ya biɗi makasudinsa na hidimar majagaba na kullum.

2 Kamar Robert, Kiristoci da yawa, yara da manya suna da zarafin samun ci gaba a wannan zamanin. Wasu sun zaɓa ba za su cika moriyar waɗannan zarafin ba, don su biɗi makasudai na ruhaniya. (1 Kor. 7:29-31) Menene yake motsa Kiristoci kamar Robert su kasance a shirye don su yi aikin wa’azi sosai? Sun yi hakan musamman domin suna ƙaunar Jehobah, kuma sun fahimci mafificiyar daraja da ke tattare da koyarwa na Allah. Kwanan nan, ka yi tunanin yadda rayuwarka za ta kasance da a ce ba ka koyi gaskiya ba? Yin tunani game da wasu albarka na musamman da muka samu domin Jehobah ya koyar da mu zai taimake mu mu ci gaba da daraja bishara kuma mu kasance da himma wajen yi wa mutane wa’azi.

Gatar Zama Waɗanda Allah Yake Koyar da Su

3. Me ya sa muka tabbata cewa Jehobah yana shirye ya koyar da mutane ajizai?

3 Da yake shi nagari ne, Jehobah yana shirye ya koyar da mutane ajizai. Sa’ad da yake magana ta annabci game da Kiristoci shafaffu, Ishaya 54:13 ya ce: “Dukan ’ya’yanki kuma za su zama masu-koyi na Ubangiji: lafiyar ’ya’yanki kuma mai-girma ce.” Bisa ƙa’ida, waɗannan kalaman sun shafi “waɗansu tumaki” na Kristi. (Yoh. 10:16) Hakan a bayane yake ta annabci da yake cika a zamaninmu. A cikin wahayi, Ishaya ya ga mutane daga dukan al’ummai suna rugawa zuwa bauta ta gaskiya. Ya kwatanta cewa suna gaya wa juna: “Ku zo, mu hau zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub; shi ma za ya koya mana tafarkunsa, mu kuma mu kama tafiya cikin hanyoyinsa.” (Isha. 2:1-3) Gata ne Allah ya koyar da mu!

4. Menene Jehobah yake bukata daga waɗanda yake koyar da su?

4 Menene muke bukatar mu yi don Jehobah ya koyar da mu? Bukata ta musamman shi ne mutum ya zama mai tawali’u da wanda za a iya koyar da shi. Mai zabura Dauda ya rubuta: “Ubangiji nagari ne mai-adalci . . . Za ya koya wa masu-tawali’u tafarkinsa.” (Zab. 25:8, 9) Kuma Yesu ya ce: “Ina gode maka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, da ka ɓoye wa masu-hikima da masu-fahimi waɗannan al’amura, ka bayyana su ga jarirai.” (Luk 10:21) Sanin hakan yana sa mu kusaci Allah wanda yake “ba da alheri ga masu-tawali’u.”—1 Bit. 5:5.

5. Me ya sa ya yiwu mu san Allah?

5 A matsayin bayin Jehobah, iyawarmu ne ko hikima ne ya sa muka san gaskiya? A’a. Hakika, ba za mu taɓa sanin Allah ba, sai da taimakonsa. Yesu ya ce: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi.” (Yoh. 6:44) Ta wurin aikin wa’azi da kuma ruhu mai tsarki, Jehobah yana jawo masu kama da tumaki, “muradin dukan dangogi.” (Hag. 2:7) Ba ka godiya cewa kana cikin waɗanda Jehobah ya jawo zuwa ga Ɗansa?—Karanta Irmiya 9:23, 24.

Ikon Kyautata Rayuwa

6. Yaya samun “sanin Ubangiji” yake shafan mutane sosai?

6 Ta wajen yin amfani da kwatanci mai kyau, annabcin Ishaya ya nuna yadda mutane suke canja halayensu a zamaninmu. Mutane masu nuna ƙarfi a dā sun zama masu zaman lafiya. (Karanta Ishaya 11:6-9.) Waɗanda suke magabta da juna a dā domin bambancin launin fata, ƙasa, ƙabila, ko kuma wani dalili na al’ada sun koya su kasance tare cikin haɗin kai. A alamance, sun “bubbuge takubansu su zama garmuna.” (Isha. 2:4) Menene dalilin waɗannan canje-canje na musamman. Mutane sun koyi “sanin Ubangiji” kuma sun yi amfani da shi a rayuwarsu. Ko da yake bayin Allah ajizai ne, sun kafa ’yan’uwanci na gaskiya a dukan duniya. Yadda mutane suke son bishara a dukan duniya da kuma ’ya’ya masu kyau da take bayarwa sun ba da tabbaci cewa koyarwar Allah yana da amfani sosai.—Mat. 11:19.

7, 8. (a) Waɗanne abubuwa ne “masu-ƙarfi” da koyarwa na Allah ya taimaka wa mutane su daina? (b) Menene ya nuna cewa koyarwa na Allah yana sa a yabi Jehobah?

7 Manzo Bulus ya kamanta aikin wa’azi na bayin Allah da yaƙi na ruhaniya. Ya rubuta: “Makaman yaƙinmu ba na jiki ba ne, amma masu-iko ne gaban Allah da za su rushe wurare masu-ƙarfi; muna rushe zace-zace da kowane maɗaukakin abu wanda aka ɗaukaka domin gāba da sanin Allah.” (2 Kor. 10:4, 5) Menene wasu cikin abubuwa “masu-ƙarfi” da koyarwar Allah take ’yantar da mutane? Kalilan su ne nauyin koyarwar ƙarya, camfi, da falsafa na ’yan adam. (Kol. 2:8) Koyarwa na Allah na taimaka wa mutane su daina ayyuka marasa kyau kuma su kasance da halaye masu kyau. (1 Kor. 6:9-11) Yana kyautata rayuwar iyali. Kuma yana sa waɗanda ba su da bege su kasance da manufa mai ma’ana a rayuwa. Irin wannan koyarwar ne ake bukata a yau.

8 Hali ɗaya da Jehobah yake taimaka wa mutane su koya shi ne faɗan gaskiya, kamar yadda labari na gaba ya nuna. (Ibran. 13:18) Wata mata a ƙasar Indiya ta amince a riƙa nazarin Littafi Mai Tsarki da ita, da shigewar lokaci ta zama mai shela da ba ta yi baftisma ba. Wata rana da take komawa gida bayan ta yi aiki a wurin da ake gina Majami’ar Mulki, ta samu sarƙa na zinariya da ta kai dalla ɗari takwas a ƙasa kusa da tashar safa. Ko da yake talaka ce, ta ɗauki sarƙar ta kai ofishin ’yan sanda kuma ta ba su su nemi mai sarƙar. Ɗan sanda da ke wajen ya yi mamaki sosai! Daga baya wani ɗan sanda ya tambaye ta, “Me ya sa ba ki ɗauki sarƙar ba?” Ta ba da bayani, “koyarwar Littafi Mai Tsarki ya canja ni, yanzu ni mai yin gaskiya ce.” Hakan ya burge shi sosai, sai ya gaya wa dattijon da ya raka ta zuwa ofishin ’yan sanda: “Da akwai mutane fiye da miliyan talatin da takwas a wannan jihar. Idan za ka iya taimaka wa mutane goma su canja kamar wannan matar, za a cim ma babban abu.” Sa’ad da muka yi la’akari da rayuwar mutane da yawa da koyarwar Allah ya kyautata su, muna da dalilai masu yawa na yabon Jehobah.

9. Ta yaya zai yiwu mutane su yi canje-canje na musamman a rayuwarsu?

9 Ikon da Kalmar Allah yake da shi na canja rayuwa, tare da taimakon da Jehobah ke tanadinsa ta wurin ruhunsa mai tsarki, yana taimaka wa mutane su yi canje-canje sosai a rayuwarsu. (Rom. 12:2; Gal. 5:22, 23) Kolosiyawa 3:10 ta ce: Ku “yafa kuma sabon mutum, wanda ake sabunta shi zuwa ilimi bisa ga surar mahaliccinsa.” Saƙon da ke cikin Kalmar Allah, Littafi Mai Tsaki, yana iya bayyana ainihin mutum na ciki, kuma yana iya canja yadda yake tunani har da yadda yake ji game da abubuwa. (Karanta Ibraniyawa 4:12.) Ta wajen samun cikakken sani na Nassosi da kuma bin mizanan adalci na Jehobah, mutum yana iya zama abokin Allah, da begen rayuwa har abada.

Shiri don Nan Gaba

10. (a) Me ya sa Jehobah ne kaɗai zai iya shirya mu don nan gaba? (b) Waɗanne canje-canje ne ba da daɗewa ba za su shafi dukan duniya?

10 Jehobah ne kaɗai zai iya taimaka mana mu yi shiri don nan gaba domin ya san abin da zai faru ba da daɗewa ba. Shi zai tsai da abin da zai faru ga ’yan adam a nan gaba. (Isha. 46:9, 10) Annabcin Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa “babbar ranar Ubangiji ta kusa.” (Zeph. 1:14) Game da wannan ranar, kalaman Misalai 11:4 za su zama gaskiya: “Wadata ba ta anfana kome a ranar hasala ba. Amma adalci yana ceto daga mutuwa.” Sa’ad da lokaci ya yi da Jehobah zai zartar da hukunci a kan duniyar Shaiɗan, abin da zai fi muhimmanci shi ne samun amincewar Allah. Kuɗi ba zai kasance da amfani ba. Ezekiel 7:19 ya ce: “Za su jefarda azurfarsu a cikin hanyoyin gari, zinariyarsu kuma za ta zama kamar abu mai-ƙazanta.” Sanin wannan kafin ya faru zai taimaka mana mu tsai da shawarwari masu kyau yanzu.

11. Wace hanya ɗaya ce koyarwa na Allah take taimaka mana mu yi shiri don nan gaba?

11 Wata hanya ta musamman da koyarwa na Allah yake shirya mu don ranar Jehobah da ke zuwa ita ce ta wajen taimakon mu mu kafa abubuwa da suka fi muhimmanci. Manzo Bulus ya rubuta wa Timotawus: “Ka dokace waɗanda ke mawadata cikin wannan zamani na yanzu, kada su yi girman kai, kada su ratayi begensu bisa wadata marar-tsayawa, amma bisa Allah.” Ko da ba mu da arziki, za mu iya amfana daga wannan gargaɗin da Allah ya ba da. Menene ya ƙunsa? Maimakon mu tara abubuwan mallaka, ya kamata mu yi ƙoƙari mu “yi alheri” kuma mu zama “mawadata cikin kyawawan ayyuka.” Ta wajen saka abubuwa na ruhaniya farko a rayuwarmu, za mu ‘ajiye wa kanmu tushe mai kyau domin lokaci mai zuwa.’ (1 Tim. 6:17-19) Irin wannan tafarki na sadaukar da kai yana nuna cewa muna tunanin kirki, domin kamar yadda Yesu ya ce, “ina abin da mutum ya ribato, ko da ya sami dukan duniya, ya ruɓusadda ransa?” (Mat. 16:26, 27) Domin ranar Jehobah ta yi kusa, ya kamata kowannenmu ya tambayi kansa: ‘Ina ne nake tara dukiya? Ina bauta wa Allah ne ko kuma Arziki?’—Mat. 6:19, 20, 24.

12. Me ya sa ba za mu yi sanyin gwiwa ba idan wasu mutane sun rena hidimarmu?

12 Mafi muhimmanci cikin “kyawawan ayyuka” da aka tsara cikin Kalmar Allah da Kiristoci za su yi, shi ne aikin ceton rai na wa’azin Mulki da kuma almajirantarwa. (Mat. 24:14; 28:19, 20) Kamar yadda yake a ƙarni na farko, wasu suna iya rena hidimarmu. (Karanta 1 Korantiyawa 1:18-21.) Amma hakan bai canja amfanin saƙonmu ba, kuma bai rage muhimmancin ba kowane mutum zarafin ba da gaskiya ga saƙon ba, kafin lokaci ya ƙure. (Rom. 10:13, 14) Yayin da muke taimaka wa mutane su amfana daga koyarwa na Allah, za mu samu albarka masu yawa.

Samun Albarka Don Yin Sadaukarwa

13. Wane sadaukarwa ne manzo Bulus ya yi don bishara?

13 Kafin ya zama Kirista, an koyar da manzo Bulus ya yi nasara a zamanin Yahudawa. Sa’ad da wataƙila yake shekara 13, ya ƙaura daga garinsu Tarsus zuwa Urushalima don ya yi karatu a ƙarƙashin Gamaliel, malamin Doka da ake daraja sosai. (A. M. 22:3) Da shigewar lokaci, Bulus ya soma yin fice tsakanin tsaransa, kuma da a ce ya ci gaba a wannan tafarkin, da ya zama sananne a Yahudanci. (Gal. 1:13, 14) Sa’ad da ya karɓi bishara kuma ya soma aikin wa’azi, ya yi watsi da dukan waɗannan abubuwa. Bulus ya yi nadama ne da zaɓin da ya yi? A’a. Ya rubuta: “Ina lissafta dukan abu hasara kuma bisa ga fifikon sanin Kristi Yesu Ubangijina: wanda na sha hasarar dukan abu sabili da shi, kamar kayan banza kuwa na ke maishe su.”—Filib. 3:8.

14, 15. Wace albarka muke samu a matsayin “abokan aiki na Allah”?

14 Kamar Bulus, Kiristoci a yau suna yin sadaukarwa don su yi wa’azin bishara. (Mar. 10:29, 30) Muna rashin wani abu ne domin yin hakan? Robert, da aka ambata ɗazu yana jin yadda mutane da yawa suke ji sa’ad ya ce: “Ban yi da na sani ba. Hidima ta cikakken lokaci ta sa ni farin ciki da gamsuwa, kuma ta sa na ‘ɗanɗana na ga cewa Ubangiji nagari ne.’ Duk lokacin da na sadaukar da abin duniya domin na biɗi makasudai na ruhaniya, Jehobah yana yi mini albarka fiye da abin da na sadaukar. Yana zama kamar ban sadaukar da kome ba. Na ci riba ne kawai!”—Zab. 34:8; Mis. 10:22.

15 Idan kana aikin wa’azi da kuma koyarwa da daɗewa yanzu, babu shakka kai ma ka samu zarafin ɗanɗana da kuma gani cewa Jehobah nagari ne. Akwai lokacin da ka fahimci taimakon ruhunsa sa’ad da kake gaya wa mutane game da bishara? Ka ga yadda wasu suka aikata cikin farin ciki yayin da Jehobah ya buɗe zuciyarsu su saurari saƙon? (A. M. 16:14) Jehobah ya taimaka maka ka sha kan tangarɗa, wataƙila ya buɗe maka hanyar faɗaɗa hidimarka? Ya tallafa maka ne a lokacin wahala, ya taimake ka ka ci gaba da bauta masa sa’ad da kake ji ba za ka iya ci gaba kuma ba? (Filib. 4:13) Sa’ad da muka shaida cewa Jehobah yana taimaka mana mu yi hidimarmu, zai kasance da gaske a gare mu kuma za mu ji muna kusa da shi sosai. (Isha. 41:10) Ba albarka ba ce mu zama “abokan aiki na Allah” a aiki mai girma na koyarwa?—1 Kor. 3:9.

16. Yaya kake ji game da ƙoƙarce-ƙoƙarce da sadaukarwa da ka yi game da koyarwa na Allah?

16 Mutane da yawa suna begen cim ma wani abu mai muhimmanci na dindindin a rayuwarsu. Mun ga cewa abubuwa na musamman da aka cim ma a wannan duniya sau da yawa ana mantawa da su ba da daɗewa ba. Amma, ayyukan da mutanen Jehobah suke yi a yau don su tsarkaka sunansa zai zama sashe na dindindin na tarihin mutanensa. Za a tuna da waɗannan ayyuka har abada. (Mis. 10:7; Ibran. 6:10) Bari mu daraja gatarmu na koya wa mutane game da Jehobah, aikin da ba za a taɓa mantawa ba.

Yaya Za Ka Amsa?

• Menene Jehobah yake bukata daga waɗanda yake koyar da su?

• Yaya koyarwa na Allah yake kyautata rayuwar mutane?

• A waɗanne hanyoyi ne aka albarkace mu don taimakon da muke yi wa mutane su amfana daga koyarwa na Allah?

[Hotunan da ke shafi na 23]

Waɗanda Jehobah ya koyar da su sun kafa ’yan’uwanci na gaske a dukan duniya

[Hotunan da ke shafi na 24]

Ba albarka ba ce ka kasance cikin “abokan aiki na Allah”?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba