Domin Matasanmu
Yadda Aka Ɓatar da Aljanna
Umurni: Ka yi wannan aikin a inda za ka iya mai da hankalinka wuri ɗaya. Sa’ad da kake karanta nassosin, ka ji kamar kana wurin sa’ad da abin ke faruwa. Ka yi tunanin yanayin a zuciyarka. Ka ji muryoyin mutanen. Ka ji yadda ainihin mutanen da ke ciki suke ji. Ka sa labarin ya zama rayayye.
KA YI TUNANI A KAN YANAYIN NAN.—KARANTA FARAWA 3:1-24.
Kana tsammani yaya Hawa’u ta ji sa’ad da macijin ya soma yi mata magana?
․․․․․
Sanin cewa Adamu da Hawa’u sun yi zunubin ne da ganga, a ganinka yaya suka ji, kamar yadda ayoyi ta 7 zuwa 10 suka nuna?
․․․․․
Yaya aka kori Adamu da Hawa’u daga gonar Adnin, kamar yadda aka bayyana a ayoyi ta 22 zuwa 24?
․․․․․
KA BINCIKE SOSAI.
Menene matsayin idanun Hawa’u a faɗuwar ta? (Sake karanta aya ta 6.)
․․․․․
Me ya sa itacen ya zamar wa Hawa’u “abin sha’awa”? (Sake karanta ayoyi ta 4 da 5.)
․․․․․
Menene wataƙila ya motsa Adamu ya bi Hawa’u yin zunubi? (Sake karanta aya ta 6.)
․․․․․
Yaya zunubi zai shafi dangantakar da ke tsakanin namiji da mace a ƙarnuka na gaba? (Sake karanta aya ta 16.)
․․․․․
Menene ya nuna cewa kishi ya taso tsakanin Adamu da Hawa’u saboda zunubi? (Sake karanta aya ta 12.)
․․․․․
Ta yaya Jehobah ya daidaita matsalar don nufinsa ta kasance? (Sake karanta aya ta 15.)
․․․․․
KA YI AMFANI DA ABIN DA KA KOYA. KA RUBUTA ABIN DA KA KOYA GAME DA . . .
Haɗarin halin ’yancin kai.
․․․․․
Yadda idanu za su iya tasar da sha’awa marar kyau.
․․․․․
Wautar aza wa wasu laifuffukanmu.
․․․․․
WANE ƁANGAREN WANNAN LABARI NE YA FI MA’ANA A GARE KA, KUMA ME YA SA?
․․․․․