Domin Matasa
Ka Manne wa Imaninka!
Umurni: Ka yi wannan aikin a inda babu surutu. Sa’ad da kake karanta nassosi, ka sa kanka cikin yanayin. Ka yi tunanin yanayin a zuciyarka. Ka ji muryoyin mutanen. Ka ji yadda ainihin mutanen da ke ciki suke ji. Ka sa labarin ya kasance kamar yanzu yake faruwa.
Taurarin labarin: Irmiya, Ebed-melek, Sarki Zadakiya
Taƙaitawa: Irmiya ya fuskanci hamayya mai tsanani sa’ad da yake shelar saƙon Allah cewa Yahudawa su miƙa kansu ga Kaldiyawa.
1 KA YI TUNANI A KAN YANAYIN NAN.—KARANTA IRMIYA 38:1-5.
Ya kake ganin Irmiya ya ji sa’ad da yake yi wa Yahudawa magana?
․․․․․
Wace irin murya ce kake ji take fita daga bakin Irmiya yayin da yake faɗin gargaɗin Jehobah?
․․․․․
KA BINCIKA SOSAI.
Waɗanne tabbaci ne Irmiya yake da su da suka sa ya faɗi irin wannan umurni da gaba gaɗi?
․․․․․
2 KA YI TUNANI A KAN YANAYIN NAN.—KARANTA IRMIYA 38:6-13.
Ta yin amfani da tunaninka, ka kwatanta ramin—faɗinta, zurfinta, da kuma warin.
․․․․․
Waɗanne irin tunani ne Irmiya yake sa’ad da ya soma ‘nutsewa cikin laka’? (Sake karanta aya ta 6.)
․․․․․
KA BINCIKA SOSAI.
Ka yi amfani da littattafan bincike da kake da su don bincika abin da ba ka sani ba a dā game da ramukan da ake amfani da su a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki.
․․․․․
Wane tabbaci ne Ebed-melech yake da shi da ya motsa shi ya ceto Irmiya? (Sake karanta ayoyi ta 7-9.)
․․․․․
Me ya sa hakimai da Ebed-melech suka rinjayi Zadakiya sosai? (Sake karanta ayoyi ta 5 da 10.) Menene hakan ya nuna game da halinsa? Me ya sa za ka ce ba shi da gaba gaɗi?
․․․․․
Wanene a wannan labarin ya nuna gaba gaɗi, kuma wanene bai nuna ba? Me ya sa ka ce hakan?
․․․․․
3 KA YI AMFANI DA ABIN DA KA KOYA. KA RUBUTA ABIN DA KA KOYA GAME DA . . .
Ƙarfin zuciya.
․․․․․
Gaba gaɗi.
․․․․․
Kāriyar Jehobah ga waɗanda suke yi masa biyayya da gaba gaɗi.
․․․․․
Sa’ad da kake fuskantar matsi, ta yaya kasancewa da gaba gaɗi zai shafi iyawarka na yin abin da ya dace?
․․․․․
4 WANE ƁANGAREN WANNAN LABARIN NE YA FI MA’ANA A GARE KA, KUMA ME YA SA?
․․․․․
KA ƘARA KOYO GAME DA LITTAFI MAI TSARKI, A DUNIYAR GIZON www.watchtower.org DA www.pr418.com