Ka Ɗauki Hakkinka A Cikin Ikilisiya Da Tamani
“Allah ya sanya gaɓaɓuwa kowane ɗaya a cikinsu cikin jiki, yadda ya gamshe shi.”—1 KOR. 12:18.
1, 2. (a) Menene ya nuna cewa kowa a cikin ikilisiya zai iya kasancewa da matsayin da zai ɗauka da tamani? (b) Waɗanne tambayoyi ne za a tattauna a wannan talifin?
TUN zamanin Isra’ila ta dā, ikilisiya ce tsarin da Jehobah yake amfani da shi ya ciyar da mutanensa a ruhaniyance da kuma yi musu ja-gora. Alal misali, bayan da Isra’ilawa suka kame birnin Ai, Joshua “ya karanta dukan zantattukan shari’a, da albarka da la’ana, bisa ga dukan abin da aka rubuta cikin littafin shari’a . . . a gaban dukan taron jama’ar Isra’ila.”—Josh. 8:34, 35.
2 A ƙarni na farko A.Z., manzo Bulus ya gaya wa Timotawus dattijo cewa ikilisiyar Kirista ita ce “jama’ar Allah” da kuma “jigon gaskiya da kuma ginshiƙinta.” (1 Tim. 3:15, Littafi Mai Tsarki) A yau “jama’ar” Allah ita ce ’yan’uwanci na Kiristoci na gaskiya a dukan duniya. A sura ta 12 ta hurarriyar wasiƙarsa ta farko zuwa ga Korantiyawa, Bulus ya kwatanta ikilisiya da jikin ’yan Adam. Ya faɗi cewa ko da yake kowace gaɓa tana aiki dabam, dukansu suna da muhimmanci. Bulus ya rubuta: “Allah ya sanya gaɓaɓuwa kowane ɗaya a cikinsu cikin jiki, yadda ya gamshe shi.” Ya kuma nuna cewa “gaɓaɓuwan jiki fa da mu ke maishe su kamar marasa-daraja, mu kan bada mafificiyar daraja garesu.” (1 Kor. 12:18, 23) Saboda haka, matsayin mutum guda mai adalci a gidan Allah bai fi na wani Kirista mai aminci kyau ba ko kuma ya fi shi muni. Ya bambanta ne kawai. To, ta yaya za mu sami matsayinmu a tsarin Allah kuma mu ɗauke shi da tamani, ko kuma mu daraja shi? Waɗanne abubuwa ne za su iya shafan matsayinmu? Kuma ta yaya za mu sa ‘ci gabanmu ya bayyana ga kowa’?—1 Tim. 4:15.
Ta Yaya Za Mu Ɗauki Hakkinmu da Tamani?
3. Wace hanya ɗaya ce za mu kasance da hakki a cikin ikilisiya kuma mu nuna cewa muna ɗaukansa da tamani?
3 Hanya ɗaya da za mu kasance da hakki a cikin ikilisiya kuma mu nuna cewa muna ɗaukansa da tamani ita ce ta wajen ba da haɗin kai ga “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” da kuma wakilinsa Hukumar Mulki. (Karanta Matta 24:45-47.) Muna bukatar mu bincika yadda muke yin biyayya ga ja-gorancin da muke samu daga rukunin bawan nan. Alal misali, shekaru da yawa yanzu, muna samun ja-gora game da saka tufafi da yin ado, nishaɗi, da kuma yin amfani da Intane yadda bai dace ba. Muna yin biyayya kuwa ga wannan gargaɗin mai kyau don mu samu kāriya ta ruhaniya? Shawarar da aka ba mu ta kafa tsarin yin bauta ta iyali a kai a kai kuma fa? Muna bin wannan shawarar kuma mun keɓe wata yamma don wannan nazarin kuwa? Idan ba mu yi aure ba, muna keɓe lokaci don nazarin Nassosi na kanmu kuwa? Jehobah zai albarkace mu ɗaɗɗaya da kuma a matsayin iyalai idan muka bi ja-gorar rukunin bawan.
4. Me ya kamata mu yi la’akari da shi sa’ad da muke zaɓi na kanmu?
4 Wasu suna iya tunanin cewa ya kamata a ƙyale kowane Kirista ya tsai da nasa shawara game da sa tufafi da yin ado. Amma, ga Kiristan da ya keɓe kansa kuma yake ɗaukan matsayinsa a cikin ikilisiya da tamani, bai kamata abubuwan da yake so su zama abubuwan da za su taimaka masa wajen tsai da shawara ba. Dole ne a bincika ra’ayin Jehobah kamar yadda aka bayyana ta ta hanyar Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Ya kamata saƙonsa ya zama ‘fitilla ga sawayenmu, haske kuma a tafarkinmu.’ (Zab. 119:105) Yana da kyau mu yi la’akari da yadda zaɓin da muke yi a batutuwa na kanmu suke shafan hidimarmu da kuma wasu, a cikin ikilisiya da kuma a waje.—Karanta 2 Korintiyawa 6:3, 4.
5. Me ya sa za mu guji halin son ’yancin kai?
5 “Ruhun da ke aiki yanzu a cikin ’ya’yan kangara” yana ko’ina yanzu kamar iskar da muke shaƙa. (Afis. 2:2) Wannan ruhun zai iya sa mu yi tunanin cewa ba ma bukatar ja-gora daga ƙungiyar Jehobah. Hakika ba ma son mu zama kamar Diyoturifis, wanda ‘ba ya karɓan’ kome daga manzo Yohanna da daraja ba. (3 Yoh. 9, 10) Muna bukatar mu guji koyan ruhun son ’yancin kai. Ta wurin abin da muke faɗi ko kuma ayyukanmu, kada mu yi rashin biyayya ga hanyar da Jehobah yake amfani da ita ya yi mana magana a yau. (Lit. Lis. 16:1-3) Akasin haka, ya kamata mu ɗauki gatanmu da tamani kuma mu ba da haɗin kai ga rukunin bawan nan. Ya kamata mu yi ƙoƙari mu yi biyayya da kuma miƙa kai ga waɗanda suke shugabanci a cikin ikilisiyarmu.—Karanta Ibraniyawa 13:7, 17.
6. Me ya sa za mu bincika yanayinmu?
6 Wata hanya da za mu nuna cewa muna daraja hakkinmu a cikin ikilisiya ita ce ta wajen bincika yanayinmu sosai kuma mu yi iyakar ƙoƙarinmu mu ‘daraja hidimarmu’ kuma mu ɗaukaka Jehobah. (Rom. 11:13) Wasu suna hidimar majagaba na kullum. Wasu kuma suna hidima ta cikakken lokaci na musamman a matsayin masu wa’azi a ƙasashen waje, masu kula masu ziyara, da waɗanda suke hidima a Bethel a dukan duniya. ’Yan’uwa maza da mata da yawa suna taimakawa wajen gina Majami’ar Mulki. Yawancin mutanen Jehobah suna iya ƙoƙarinsu su kula da bukatu na ruhaniya na iyalinsu kuma su fita hidima kowane mako. (Karanta Kolosiyawa 3:23, 24.) Muna da tabbaci cewa sa’ad da muka ba da kanmu da son rai a hidimar Allah kuma muka yi iya ƙoƙarinmu mu bauta masa da dukan zuciyarmu, a koyaushe za mu kasance da hakki a tsarinsa.
Abubuwan da ke Shafan Hakkinmu a Cikin Ikilisiya
7. Ka bayyana yadda yanayinmu zai shafi hakkinmu a cikin ikilisiya.
7 Yana da muhimmanci mu bincika yanayinmu sosai, domin suna shafan abin da za mu iya yi a cikin ikilisiya. Alal misali, hakkin ɗan’uwa a cikin ikilisiya ya bambanta a wasu hanyoyi da na ’yar’uwa. Shekaru, rashin lafiya, da wasu abubuwa suna iya shafan abin da za mu iya yi a hidimar Jehobah. Misalai 20:29 ta ce: “Fahariyar samari ƙarfinsu ne: Jamalin tsofaffi kuma furfura ne.” Matasa da suke cikin ikilisiya suna iya yin abubuwa da yawa a zahiri domin ƙarfinsu na ƙuruciya, amma tsofaffi suna da amfani ga ikilisiya sosai domin hikimarsu da abin da suka shaida a rayuwa. Muna bukatar kuma mu tuna cewa kome da za mu iya yi a ƙungiyar Jehobah ta dangana da alherin Allah.—A. M. 14:26; Rom. 12:6-8.
8. Yaya sha’awa take shafan abin da muke yi a cikin ikilisiya?
8 Misalin ’yan’uwa mata biyu matasa daga iyaye ɗaya ya nuna wani abu da ke shafan hakkinmu a cikin ikilisiya. Su biyu sun sauke karatu daga makarantar sakandare. Suna da yanayi iri ɗaya. Iyayensu sun yi iya ƙoƙarinsu su ƙarfafa su su shiga hidimar majagaba na kullum bayan sun gama makaranta. Bayan sun sauke karatu, ɗaya ta shiga hidimar majagaba, ɗayan kuma ta soma yin aiki na cikakken lokaci. Me ya sa suka tsai da shawara dabam dabam? Domin abin da suke so. A ƙarshe, kowannensu ta yi abin da take so. Ba hakan yake da yawancinmu ba? Muna bukatar mu yi tunani sosai game da abin da za mu so mu yi a hidimar Allah. Za mu iya ƙara yin ta sosai, ko da hakan yana nufin daidaita yanayinmu?—2 Kor. 9:7.
9, 10. Menene ya kamata mu yi idan ba mu da motsawa na ƙara ƙwazo a hidimar Jehobah?
9 Idan ba abin da ke motsa mu mu ƙara ƙwazo a hidimar Jehobah kuma muna da halin yin abin da kawai ake bukata a cikin ikilisiya kuma fa? A cikin wasiƙarsa zuwa ga Filibiyawa, Bulus ya ce: “Allah ne yana aiki a cikinku da za ku yi nufi har ku aika kuma.” Hakika, Jehobah yana iya aiki a cikinmu kuma ya shafe nufinmu, ko sha’awoyinmu.—Filib. 2:13; 4:13.
10 Saboda haka, ya dace ne mu gaya wa Jehobah ya sa mu so yin nufinsa? Sarki Dauda na Isra’ila ta dā ya yi hakan. Ya yi addu’a: “Ya Ubangiji, ka nuna mini tafarkunka; Ka koya mini hanyoyinka. Ka bishe ni cikin gaskiyarka, ka koya mani; gama kai ne Allah na cetona; a gareka na ke sauraro dukan yini.” (Zab. 25:4, 5) Muna iya yin hakan ta yin addu’a cewa Jehobah ya sa mu so yin abin da ke faranta masa rai. Sa’ad da muka yi tunani a kan yadda Jehobah Allah da Ɗansa suke ji game da abin da muke yi don hidimarsu, za mu yi godiya sosai a gare su. (Mat. 26:6-10; Luk 21:1-4) Yin godiya zai motsa mu mu roƙi Jehobah ya sa mu so samun ci gaba na ruhaniya. Annabi Ishaya ya ba da misalin halin da ya kamata mu kasance da shi. Sa’ad da ya ji muryar Jehobah ya yi tambaya: “Wa zan aika, kuma wanene za ya tafi domin mu?” annabin ya amsa: “Ga ni; ka aike ni.”—Isha. 6:8.
Yaya Za Ka Samu Ci Gaba?
11. (a) Ana bukatar ’yan’uwa maza su ɗauki wane hakki a cikin ƙungiya? (b) Ta yaya ɗan’uwa zai samu gatar hidima?
11 A bayane yake cewa ana bukatar ’yan’uwa maza sosai su yi shugabanci da yake mutane 289,678 sun yi baftisma a dukan duniya a shekarar hidima ta 2008. Yaya ya kamata ɗan’uwa ya aikata ga wannan bukata? Ta wajen yin ƙoƙarin cika bukatun da aka kafa a cikin Nassosi na zama bayi masu hidima ko dattawa. (1 Tim. 3:1-10, 12, 13; Tit. 1:5-9) Ta yaya ɗan’uwa zai ƙoƙarta ya cika bukatu na Nassi? Ta wajen fita hidimar fage sosai, ta wajen kula da ayyukansa na ikilisiya da kyau, ta wajen yin aiki tuƙuru don kyautata kalamansa a taron Kirista, da kuma nuna cewa ya damu da ’yan’uwa masu bi. Ta hakan yana nuna cewa yana ɗaukan hakkinsa a cikin ikilisiya da tamani.
12. Ta yaya matasa za su nuna ƙwazonsu don gaskiya?
12 Menene ’yan’uwa maza matasa, musamman waɗanda suke cikin shekarunsu na goma sha uku zuwa sha tara za su yi don su samu ci gaba a cikin ikilisiya? Suna iya yin iyakar ƙoƙarinsu su ƙaru cikin “hikima mai-ruhaniya da fahimi kuma” ta wajen samun sani na Nassosi. (Kol. 1:9) Zama ɗaliban Kalmar Allah masu ƙwazo da kuma sa hannu sosai a taron ikilisiya za su sa su cim ma hakan. Maza matasa suna iya yin ƙoƙari su cancanta shigar “kofa mai-faɗi mai-yalwar aiki” a fannoni dabam dabam na hidima ta cikakken lokaci. (1 Kor. 16:9) Yin hidimar Jehobah a rayuwarmu hanyar rayuwa ce mai gamsarwa da kuma tafarki da ke kawo albarka mai girma.—Karanta Mai Wa’azi 12:1.
13, 14. A waɗanne hanyoyi ne ’yan’uwa mata za su nuna cewa suna ɗaukan hakkinsu a cikin ikilisiya da tamani?
13 ’Yan’uwa mata ma suna iya nuna cewa suna ɗaukan gatarsu na sa hannu wajen cika Zabura 68:11 da tamani. Wurin ya ce: “Ubangiji ya bada sako: Mata masu-shelar bisharan kuwa babbar runduna ne.” Hanya ɗaya da ta fi muhimmanci da mata za su nuna godiyarsu don hakkinsu a cikin ikilisiya ita ce ta wajen sa hannu a aikin almajirantarwa. (Mat. 28:19, 20) Saboda haka, ta wajen fita hidima sosai da kuma yin sadaukarwa da son rai don wannan aikin, ’yan’uwa mata suna nuna cewa suna ɗaukan hakkinsu a cikin ikilisiya da tamani.
14 Sa’ad da yake rubuta wa Titus wasiƙa, Bulus ya ce: “Tsofaffin mata kuma su yi ladabi cikin al’amuransu, . . . masu-koyar da nagarta; su hankaltar da ƙananan mata domin su yi ƙaunar mazajensu, su yi ƙaunar ’ya’yansu, su zama masu-hankali, masu-tsabtan rai, masu-aiki a gidajensu, masu-nasiha, masu-biyayya ga mazajensu, domin kada a saɓa maganar Allah.” (Tit. 2:3-5) ’Yan’uwa mata da suka manyanta suna da amfani sosai a ikilisiya! Ta wajen yin ladabi ga ’yan’uwa maza da suke shugabanci da kuma tsai da shawarwari masu kyau a yin ado da saka tufafi da kuma nishaɗi, suna kafa wa mutane misali mai kyau kuma suna daraja hakkinsu sosai a cikin ikilisiya.
15. Menene ’yar’uwa da ba ta yi aure ba za ta yi don to jimre da kaɗaici?
15 A wani lokaci, yana iya yin wuya ’yar’uwa da ba ta yi aure ba ta samu matsayi a cikin ikilisiya. Wata ’yar’uwa da ta fuskanci hakan ta ce: “A wani lokaci wadda ba ta yi aure ba takan kaɗaita.” Sa’ad da aka tambaye ta yadda take jimre da yanayin, ta ce: “Addu’a da nazari sun taimaka mini na samu matsayi ta kuma. Na yi nazari game da yadda Jehobah ya ɗauke ni. Sai na yi ƙoƙari na riƙa taimaka wa mutane a cikin ikilisiya. Hakan yana taimaka mini na riƙa yin tunanin wasu maimakon kaina kaɗai.” Jehobah ya gaya wa Dauda a Zabura 32:8: “Da idona a kanka zan ba ka shawara.” Hakika, Jehobah yana damuwa da dukan bayinsa, har da ’yan’uwa mata da ba su yi aure ba, kuma zai taimaka wa dukansu su samu hakki a cikin ikilisiya.
Ka Riƙe Hakkinka!
16, 17. (a) Me ya sa yin na’am da gayyatar Jehobah mu kasance cikin ƙungiyarsa, shawara mafi kyau da muka tsai da? (b) Ta yaya za mu ci gaba da riƙe hakkinmu a cikin ƙungiyar Jehobah?
16 Jehobah cikin ƙauna ya jawo kowanne cikin bayinsa ya ƙulla dangantaka da shi. Yesu ya ce: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi.” (Yoh. 6:44) A cikin dukan biliyoyin mutane da suke duniya, Jehobah ya gayyace mu mu zama sashen ikilisiyarsa a yau. Yin na’am da wannan gayyatar shi ne shawara mafi kyau da muka tsai da. Ya sa rayuwarmu ta kasance da ma’ana. Kuma muna samun farin ciki da gamsuwa domin muna da wuri a cikin ikilisiya!
17 “Ubangiji, ina ƙaunar zaman gidanka,” in ji mai zabura. Ya kuma rera: “Ƙafata tana tsayawa cikin wuri mai-bai ɗaya: Zan albarkaci Ubangiji cikin taron jama’a.” (Zab. 26:8, 12) Allah na gaskiya yana da wuri don kowanenmu a cikin ikilisiyarsa. Ta wajen ci gaba da bin ja-gora na tsarin Allah da kuma yin aiki tuƙuru a hidimar Allah, za mu ci gaba da kasancewa da hakkinmu mai tamani a cikin tsarin Jehobah.
Ka Tuna?
• Me ya sa ya dace mu kammala cewa dukan Kiristoci suna da hakki a cikin ikilisiya?
• Ta yaya muke nuna cewa muna daraja hakkinmu a cikin ƙungiyar Allah?
• Waɗanne abubuwa ne za su shafi hakkinmu a cikin ikilisiya?
• Ta yaya matasa Kirista da manya za su nuna cewa suna ɗaukan hakkinsu a cikin tsarin Allah da tamani?
[Hotunan da ke shafi na 16]
Ta yaya ’yan’uwa maza za su sami gata a cikin ikilisiya?
[Hotunan da ke shafi na 17]
Ta yaya ’yan’uwa mata za su nuna cewa suna ɗaukan hakkinsu a cikin ikilisiya da tamani?