Bari Ikilisiya Ta Yabi Jehobah
“Zan bayana sunanka ga ’yan’uwana, A tsakiyar jama’a zan raira yabonka.”—IBRANIYAWA 2:12.
1, 2. Me ya sa ikilisiya ke da amfani sosai, kuma menene muhimmancinta?
A TARIHI, mutane sun sami tarayya da kuma kāriya a cikin iyali. Amma, Littafi Mai Tsarki ya bayyana wani sashen iyali inda mutane marar iyaka a duka duniya a yau suke more tarayya da kuma kāriya wanda babu makamancinsa. Wannan ita ce ikilisiyar Kirista. Ko kana cikin iyalin da ke son juna sosai ko ba ka ciki, ya kamata ka nuna godiya domin tanadin da Allah ya yi na tsarin ikilisiya. Idan ka riga ka soma tarayya da ikilisiyar Shaidun Jehobah, za ka iya ba da shaidar tarayya na kud da kud da kake morewa a ciki da kuma irin kāriyar da kake samu.
2 Ikilisiya ba rukuni ba ne na jin daɗi kawai. Kuma ba majalisa ba ce ko kuma gidan kallo inda mutanen da suka fito daga wuri ɗaya suke taruwa don su kalli wasanni ba. Maimakon haka, an tsara ikilisiya ne ainihi don a yaba wa Jehobah Allah. Kuma haka yake tun a dā kamar yadda littafin Zabura ya nanata. Zabura 35:18 ta ce: “Zan yi maka godiya cikin babban taron jama’a: Zan yi yabonka a cikin babbar jama’a.” Hakazalika, Zabura 107:31, 32 sun ƙarfafa mu: “Da dai mutane suka yarda su yabi Ubangiji sabada alherinsa, Da al’ajibansa da ya ke yi ma yan adam kuma! Su ɗaukaka shi kuma cikin taron jama’a.”
3. Menene ikilisiya ke yi in ji Bulus?
3 Manzo Bulus Kirista ya taƙaita wani matsayi mai muhimmanci na ikilisiya sa’ad da ya yi nuni ga “gidan Allah, ikilisiyar Allah mai-rai ke nan, jigon gaskiya da ƙarfinta.” (1 Timothawus 3:15) Wace ikilisiya ce Bulus yake magana a kai? Ta waɗanne hanyoyi ne Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmar nan “ikilisiya”? Ta yaya ne ya kamata wannan ya shafi rayuwarmu da kuma begenmu? Don mu sami amsoshin, bari mu fara tattauna yadda aka yi amfani da kalmar nan “ikilisiya” a cikin Kalmar Allah.
4. Ta yaya ne ake amfani da kalmar nan “taron jama’a” a yawancin lokaci a Nassosi na Ibrananci?
4 Kalmar Ibrananci da aka fassara “ikilisiya,” an samo ta ne daga ma’anar da ke nufin taro ko “tattara.” (Kubawar Shari’a 4:10; 9:10) Mai zabura ya yi amfani da kalmar nan “taron jama’a” ko ikilisiya, ya yi nuni ga mala’ikun da ke sama, kuma za a iya amfani da ita a yi nuni ga rukunin miyagun mutane. (Zabura 26:5; 89:5-7) Amma, a yawancin lokaci Nassosi na Ibrananci yakan haɗa ta ne da Isra’ilawa. Allah ya faɗi cewa Yakubu zai “zama taron al’ummai,” kuma hakan ya faru. (Farawa 28:3; 35:11; 48:4) An kira Isra’ilawa ko kuwa an zaɓe su su zama “jama’ar Ubangiji,” “taron jama’ar Allah [na gaskiya].”—Litafin Lissafi 20:4; Nehemiah 13:1; Joshua 8:35; 1 Samuila 17:47; Mikah 2:5.
5. Wace kalmar Helenanci ce aka fassara “ikilisiya,” kuma ta yaya za a iya amfani da ita?
5 Kalmar Helenanci da ta yi daidai da wannan ita ce ek·kle·siʹa, wadda aka samo daga kalmomi biyu na Helenanci da ke nufin “waje” da kuma “taro.” Ana iya kiran mutanen da suka taru ba don addini ba da wannan kalmar, kamar ‘taron’ da Dimitriyus ya tayar wa Bulus a Afisa. (Ayukan Manzanni 19:32, 39, 41) Amma Littafi Mai Tsarki yana amfani da ita ce ga ikilisiyar Kirista. Wasu fassarar sun kira wannan kalmar “coci,” amma The Imperial Bible-Dictionary ya ce “ba ta . . . nufin ainihin ginin da Kiristoci suke taruwa don bauta.” Abin farin ciki shi ne, a cikin Nassosin Kirista na Helenanci, an yi amfani da kalmar nan “ikilisiya” a hanyoyi huɗu dabam dabam.
Shafaffun Ikilisiya ta Allah
6. Menene Dauda da Yesu suka yi a cikin ikilisiya?
6 Manzo Bulus ya yi nuni ga Yesu da kalmomin Dauda da ke Zabura 22:22 sa’ad da ya rubuta: “Zan bayana sunanka ga ’yan’uwana, A tsakiyar jama’a zan raira yabonka. Domin wannan fa ya wajabce [Yesu] shi kamantu ga ’yan’uwansa a cikin dukan abu, domin shi zama babban priest mai-jinƙai, mai-aminci, cikin matsaloli na wajen Allah.” (Ibraniyawa 2:12, 17) Dauda ya ɗaukaka Allah a tsakiyar jama’ar Isra’ila ta dā. (Zabura 40:9) Amma, menene Bulus yake nufi sa’ad da ya ce Yesu ya ɗaukaka Allah a ‘tsakiyar jama’a’? Wace jama’a ko ikilisiya ce wannan?
7. A wace hanya ta ainihi ce Nassosin Helenanci na Kirista ta yi amfani da kalmar nan “ikilisiya”?
7 Abin da muka karanta a Ibraniyawa 2:12, 17 yana da muhimmanci. Hakan ya nuna cewa Kristi yana cikin ikilisiya inda ya bayyana sunan Allah ga ’yan’uwansa. Su wanene ’yan’uwansa? Su ne “zuriyar Ibrahim,” ’yan’uwan Kristi shafaffu na ruhu, “masu-tarayya na kira basamaniya.” (Ibraniyawa 2:16–3:1; Matta 25:40) Hakika, ma’ana ta ainihi ta kalmar nan “ikilisiya” a cikin Nassosin Helenanci na Kirista ita ce rukunin mabiyan Kristi shafaffu na ruhu. Waɗannan shafaffun mutane 144,000 su ne “ikilisiya ta ’ya’yan fari waɗanda an rubuta sunayensu a sama.”—Ibraniyawa 12:23.
8. Ta yaya ne Yesu ya nuna tun a dā cewa za a kafa ikilisiyar Kirista?
8 Yesu ya faɗi cewa za a kafa wannan “ikilisiya” ta Kirista. Kusan shekara ɗaya kafin mutuwarsa, Yesu ya gaya wa wani manzo: “Kai ne Bitrus, a kan wannan dutse kuma zan gina ikilisiyata; ƙyamaren Hades kuma ba za su rinjaye ta ba.” (Matta 16:18) Bitrus da Bulus sun fahimci cewa Yesu ne dutsen da aka annabta. Bitrus ya rubuta cewa waɗanda aka gina a matsayin “rayayyen dutse” na gida na ruhaniya a kan dutsen, wato Kristi, su ne “jama’a abin mulki na Allah kansa, domin [su] gwada mafifitan halulluka,” na Wanda ya kira su.—1 Bitrus 2:4-9; Zabura 118:22; Ishaya 8:14; 1 Korinthiyawa 10:1-4.
9. A wane lokaci ne aka soma kafa ikilisiyar Allah?
9 A wane lokaci ne aka soma kafa wannan “jama’a abin mulki na Allah kansa” su zama ikilisiyar Kirista? An soma ne a Fentikos ta shekara ta 33 A.Z., sa’ad da Allah ya zuba ruhunsa mai tsarki a kan manzannin da suka taru a Urushalima. A wannan ranar, Bitrus ya ba da jawabi mai daɗi ga rukunin Yahudawa da shigaggu. Mutuwar Yesu ta motsa yawancinsu sosai; sai suka tuba kuma suka yi baftisma. Mun karanta a cikin rahoton da Littafi Mai Tsarki ya bayar cewa mutane dubu uku ne suka yi baftisma, da haka suka zama sashen sabuwar ikilisiyar Allah da ke tasowa. (Ayukan Manzanni 2:1-4, 14, 37-47) Ikilisiyar ta ci gaba da tasowa domin yawancin Yahudawa da shigaggu sun yarda cewa Isra’ila ta jiki ba ita ba ce ikilisiyar Allah ba kuma. Maimakon haka, shafaffun Kiristoci waɗanda su ne “isra’ila na Allah” na ruhaniya, sun zama ikilisiyar gaskiya ta Allah.—Galatiyawa 6:16; Ayukan Manzanni 20:28.
10. Wace dangantaka ce ke tsakanin Yesu da ikilisiyar Allah?
10 A yawancin lokaci, Littafi Mai Tsarki yakan bambance Yesu da shafaffu, kamar a furcin nan ‘zance na wajen Kristi da ikilisiya.’ Yesu ne Shugaban wannan ikilisiya ta shafaffun Kiristoci. Bulus ya rubuta cewa Allah “ya sanya [Yesu] kuma shi zama kai a bisa abu duka ga ikilisiya, jikinsa ke nan.” (Afisawa 1:22, 23; 5:23, 32; Kolossiyawa 1:18, 24) A yau, kaɗan daga cikin shafaffun da ke cikin wannan ikilisiyar ne suka rage a duniya. Muna da tabbaci cewa Shugabansu, Yesu Kristi, yana ƙaunarsu. An kwatanta yadda yake ji game da waɗannan a Afisawa 5:25: “Kristi kuma ya ƙaunaci ikilisiya, ya bada kansa dominta.” Yana ƙaunarsu domin suna “miƙa hadaya ta yabo ga Allah kullayaumi, watau, ’ya’yan leɓunan da su ke shaida sunansa,” kamar yadda Yesu ya yi sa’ad da yake duniya.—Ibraniyawa 13:15.
Wasu Hanyoyin da Aka Yi Amfani da Kalmar Nan “Ikilisiya”
11. A wace hanya ta biyu ce Nassosin Kirista na Helenanci ya yi amfani da kalmar nan “ikilisiya”?
11 A wasu lokatai, Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmar nan “ikilisiya” a wata hanya dabam, amma ba ga duka shafaffu 144,000 waɗanda su ne “ikilisiya ta Allah” ba. Alal misali, Bulus ya rubuta wa wani rukunin Kiristoci yana cewa: “Kada ku bada sanadin tuntuɓe, ko ga Yahudawa, ko ga Helenawa, ko ga ikilisiya ta Allah.” (1 Korinthiyawa 10:32) Babu shakka, idan Kirista a Koranti na dā ya yi abin da bai dace ba, hakan na iya sa wasu su yi tuntuɓe. Amma zai yiwu wannan abin ya sa duka Helenawa, Yahudawa, ko kuma shafaffu su yi tuntuɓe tun daga wannan lokacin zuwa yanzu? Da kyar. Kamar dai a wannan ayar “ikilisiya ta Allah” tana nuni ne ga Kiristocin da suke raye a wani lokaci. Saboda haka, ana iya cewa Allah yana ja-gora, yana yin tanadi, ko kuwa yana yi wa ikilisiya albarka, wato duka Kiristocin da ke raye a wani lokaci a duk inda suke. Ko kuwa muna iya yin nuni ga farin ciki da salama da ke ko’ina a cikin ikilisiyar Allah a yau, wato a cikin duka ’yan’uwantaka na Kirista.
12. A wace hanya ta uku ce aka yi amfani da kalmar nan “ikilisiya” a cikin Littafi Mai Tsarki?
12 Hanya ta uku da Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmar nan “ikilisiya” tana nuni ne ga duka Kiristocin da suke zaune a wani wuri. Mun karanta: “Ikilisiya fa ta sami salama, . . . cikin dukan Yahudiya da Galili da Samariya.” (Ayukan Manzanni 9:31) Akwai fiye da rukuni guda na Kiristoci a waɗannan manyan wurare, amma an kira dukansu da ke Yahudiya, Galili, da Samariya “ikilisiya.” Idan muka duba adadin waɗanda suka yi baftisma a Fentakos ta shekara ta 33 A.Z., da kuma waɗanda suka yi daga baya, za mu ga cewa wataƙila akwai fiye da rukuni ɗaya da ke taruwa a kowane lokaci a yankin Urushalima. (Ayukan Manzanni 2:41, 46, 47; 4:4; 6:1, 7) Hirudus Agaribas na I ya yi sarautar Yahudiya har sa’ad da ya mutu a shekara ta 44 A.Z., kuma a bayyane yake a 1 Tassalunikawa 2:14 cewa a shekara ta 50 A.Z., akwai ikilisiyoyi masu yawa a Yahudiya. Saboda haka, sa’ad da muka karanta cewa Hirudus yana “wulakanta waɗansu a cikin ikilisiya,” wataƙila hakan na nufin rukunoni fiye da ɗaya da suke taruwa a Urushalima.—Ayukan Manzanni 12:1.
13. Wace hanya ta huɗu ce kuma sananniya da Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmar nan “ikilisiya”?
13 Na huɗu, wata taƙaitacciya da kuma sananniyar hanyar da ake amfani da kalmar nan “ikilisiya” ita ce Kiristocin da suke cikin ikilisiya ɗaya, kamar a gida. Bulus ya ambata “ikilisiyoyi na Galatiya.” Akwai ikilisiya fiye da guda a wannan babban lardin Romawa. Sau biyu Bulus ya yi amfani da jam’i “ikilisiyoyi” ga Galatiya, wadda ta haɗa da waɗanda suke Antakiya, Darba, Listira, da Ikoniya. An naɗa dattawan da suka ƙware, ko kuwa masu kula a waɗannan ikilisiyoyin. (1 Korinthiyawa 16:1; Galatiyawa 1:2; Ayukan Manzanni 14:19-23) In ji Nassosi, duka waɗannan ‘ikilisiyoyi na Allah’ ne.—1 Korinthiyawa 11:16; 2 Tassalunikawa 1:4.
14. Menene za mu iya kammalawa daga yadda aka yi amfani da kalmar nan “ikilisiya” a cikin wasu ayoyi?
14 A wasu yanayi, rukunonin taron Kirista ba su da yawa, wanda hakan zai iya sa ɗaki ɗaya ya ɗauke su. Duk da haka, ana kiran waɗannan rukunonin da kalmar nan “ikilisiya.” Waɗansu da muka sani su ne ikilisiyoyin da ke gidan Bilkisu da Akila, Nimfa, da Filimon. (Romawa 16:3-5; Kolossiyawa 4:15; Filimon 2) Ya kamata wannan ya zama abin ƙarfafa ga ikilisiyoyin da ba su da yawa a yau kuma waɗanda wataƙila suna taruwa ne a gidan wani. Jehobah ya san da irin waɗannan ƙananan ikilisiyoyi a ƙarni na farko da kuma a yau, yana kuma yi musu albarka ta hanyar ruhunsa.
Ikilisiyoyi Suna Yabon Jehobah
15. Ta yaya ne aka nuna aikin ruhu mai tsarki a wasu ikilisiyoyi na farko?
15 Mun lura cewa ta wajen cikar Zabura 22:22, Yesu ya yi yabon Allah a tsakiyar jama’a. (Ibraniyawa 2:12) Mabiyansa masu aminci suna bukatar su yi haka. A ƙarni na farko sa’ad da aka shafa Kiristoci na gaskiya da ruhu mai tsarki su zama ’ya’yan Allah da kuma ’yan’uwan Kristi, ruhu mai tsarki ya yi aiki a kan wasu a hanya ta musamman. Wasu sun sami kyauta ta mu’ujiza ta ruhu. An nuna irin wannan kyautar ta wajen furci na musamman mai cike da hikima ko sani, da kuma ikon warkarwa ko annabci, ko kuwa iya yin magana a harsunan da ba na su ba.—1 Korinthiyawa 12:4-11.
16. Menene dalili ɗaya na ba da kyauta ta mu’ujiza ta ruhu?
16 Game da yin wani harshe, Bulus ya ce: “In raira waƙa da ruhu, in raira waƙa da azanci kuma.” (1 Korinthiyawa 14:15) Ya ga cewa yana da muhimmanci mutane su fahimci abin da yake cewa don su koyi wani abu. Makasudin Bulus shi ne ya yi yabon Jehobah a cikin ikilisiya. Ya aririci sauran da ke da kyautar ruhu: “Ku biɗi ku yalwata a cikinsu garin ginin ikilisiya,” wato a ikilisiyar da suke da irin wannan kyautar. (1 Korinthiyawa 14:4, 5, 12, 23) Babu shakka, Bulus yana ƙaunar ikilisiyoyin, domin ya san cewa Kiristoci za su sami damar yaba wa Allah a cikin kowace ikilisiya.
17. Wane tabbaci ne muke da shi game da ikilisiyoyi a yau?
17 Jehobah ya ci gaba da yin amfani da kuma tallafa wa ikilisiyarsa. Kuma yana yi wa duka rukunin shafaffun Kiristoci da ke duniya albarka a yau. Muna iya ganin wannan ta abinci na ruhaniya mai yawa da mutanen Allah suke morewa. (Luka 12:42) Yana yi wa ’yan’uwantaka na duka duniya albarka. Kuma yana yi wa ikilisiyoyi albarka, inda muke yin yabon Mahaliccinmu ta ayyukanmu da kuma kalamanmu na ruhaniya masu ƙarfafawa. A nan ne muke samun ilimi da koyarwa saboda mu yi yabon Allah a wasu wurare sa’ad da ba mu halarci taro a ikilisiyarmu ba.
18, 19. Menene Kiristoci na gaskiya a kowace ikilisiya suke son su yi?
18 Ka tuna cewa manzo Bulus ya aririci Kiristocin da ke ikilisiyar Filibi, a Makidoniya: “Abin da ni ke addu’a ke nan, . . . ku zama . . . cikakku da ’ya’yan adalci, waɗanda sun kasance zuwa darajar Allah da yabonsa ta wurin Yesu Kristi.” Wannan ya haɗa da maganar da suke yi wa wasu da ba sa cikin ikilisiya game da bangaskiyar da suke da ita a Yesu da kuma begensu. (Filibbiyawa 1:9-11; 3:8-11) Saboda haka, Bulus ya umurci Kiristoci: “Ta wurinsa [Yesu] fa bari mu miƙa hadaya ta yabo ga Allah kullayaumi, watau, ’ya’yan leɓunan da su ke shaida sunansa.”—Ibraniyawa 13:15.
19 Kana jin daɗin yin yabon Allah “a tsakiyar jama’a,” kamar yadda Yesu ya yi, da kuma yin amfani da leɓunanka ka yaba wa Jehobah a gaban waɗanda ba su san Allah ba tukun? (Ibraniyawa 2:12; Romawa 15:9-11) Amsarmu za ta iya dangana ne a kan yadda muke ji game da matsayin ikilisiyarmu a cikin tsarin Allah. A talifi na gaba, za mu tattauna yadda Jehobah yake ja-gora da kuma yin amfani da ikilisiyarmu, da kuma yadda za mu ɗauki matsayinta a rayuwarmu a yau.
Ka Tuna?
• Ta yaya ne “ikilisiyar Allah,” da ke ɗauke da shafaffun Kiristoci ta wanzu?
• Waɗanne ƙarin hanyoyi uku ne Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmar nan “ikilisiya”?
• Game da ikilisiya, menene Dauda, Yesu, da kuma Kiristoci na ƙarni na farko suka ƙudurta za su yi, kuma ta yaya ya kamata hakan ya shafe mu?
[Hoto a shafi na 7]
Yesu ne tushen wace ikilisiya?
[Hoto a shafi na 9]
Ikilisiyoyin Kiristoci suna taruwa a matsayin “ikilisiya ta Allah”
[Hoto a shafi na 10]
Kamar Kiristocin da ke Jamhuriyar Benin, muna iya yaba wa Jehobah a cikin taro na sujada