Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 2/15 pp. 18-22
  • Ka Kāre Hali Mai Kyau na Ikilisiyar

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kāre Hali Mai Kyau na Ikilisiyar
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA ƘARFAFA HALI MAI KYAU A CIKIN IKILISIYA
  • KA RIƘA YIN WA’AZI DA ƘWAZO
  • KADA KA YI GUNAGUNI DA KUMA ƁOYE ZUNUBANKA
  • KA ƘARFAFA ’YAN’UWA SU KASANCE DA “ƊAYANTUWAR RUHU”
  • Wane Irin Hali Ne Kake Da Shi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Bari Ikilisiya Ta Yabi Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Bari Ikilisiya Ta Ingantu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ka Yi Tafiya Bisa Ga Ruhu Kuma Ka Yi Rayuwar Da Ta Jitu Da Keɓe Kanka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 2/15 pp. 18-22

Ka Kāre Hali Mai Kyau na Ikilisiyar

“Alherin Ubangiji Yesu Kristi ya zauna tare da ruhunku.”—FILIB. 4:23.

TA YAYA ZA MU SA ’YAN’UWA A IKILISIYA SU KASANCE DA HALI MAI KYAU . . .

․․․․․

sa’ad da muke cuɗanya da su?

․․․․․

sa’ad da muka kasance da ƙwazo a yin wa’azi?

․․․․․

sa’ad da muka kai ƙarar zunubi mai tsanani da wani ya yi?

1. Me ya sa Bulus ya yaba wa ikilisiyoyi da ke Filibi da kuma Tiyatira?

KIRISTOCIN ƙasar Filibi a ƙarni na farko ba su da wadata. Amma suna karimci kuma suna ƙaunar ’yan’uwansu masu bi sosai. (Filib. 1:3-5, 9; 4:15, 16) Sa’ad da manzo Bulus yake kammala wasiƙarsa ga waɗannan Filibiyawa, ya ce: “Alherin Ubangiji Yesu Kristi ya zauna tare da ruhunku.” (Filib. 4:23) Yesu ya furta kalmomi na gaba ga Kiristoci a Tiyatira domin su ma sun yi karimci da kuma ƙauna: “Na san ayyukanka, ƙaunarka, bangaskiyarka, hidimarka da haƙurinka, na sani kuma ayyukanka na ƙarshe sun ɗara na fari.”—R. Yoh. 2:19.

2. Ta yaya halinmu mai kyau zai iya shafar ikilisiya?

2 Kowacce ikilisiya ta Shaidun Jehobah a yau tana nuna irin wannan halin. An san wasu ikilisiyoyi da nuna ƙauna. Wasu kuma suna da ƙwazo a wa’azin Mulki kuma suna son hidima ta cikakken lokaci sosai. Idan muka nuna hali mai kyau za mu sa haɗin kai ya kasance a cikin ikilisiya. Kuma kowa zai samu ci gaba a bautarsa ga Jehobah. (1 Kor. 1:10) Amma idan wasu suna da hali marar kyau, hakan zai iya sa ’yan’uwa a cikin ikilisiya su rage ƙwazonsu a hidima kuma su ƙi ce uffan idan wani ya yi zunubi a cikin ikilisiya. (1 Kor. 5:1; R. Yoh. 3:15, 16) Wane hali ne ’yan’uwa a cikin ikilisiyarku suke da shi? Mene ne za ka iya yi don a ci gaba da nuna hali mai kyau a cikin ikilisiya?

KA ƘARFAFA HALI MAI KYAU A CIKIN IKILISIYA

3, 4. A wace hanya ce za mu yabi Jehobah a “cikin babban taron jama’a”?

3 Marubucin wannan zaburar ya rera waƙa: “Zan yi maka [Jehobah] godiya cikin babban taron jama’a: zan yi yabonka a cikin babbar jama’a.” (Zab. 35:18) Marubucin zabura ya yabi Jehobah sa’ad da yake tare da bayin Jehobah. Tarurrukan da muke yi a kowanne mako, har da Nazarin Hasumiyar Tsaro, suna ba mu zarafin nuna ta kalamanmu cewa muna da ƙwazo da kuma bangaskiya. Ya kamata dukanmu mu tambayi kanmu: ‘Shin ina sa ƙwazo a yin kalami a tarurruka? Shin ina shirya tarurruka sosai domin na ba da kalami masu ƙarfafawa? A matsayina na magidanci, ina taimaka wa yarana kafin su halarci taro su shirya kalamin da za su ba da a taro? Kuma ina taimaka musu su furta waɗannan kalamin daga zuciyarsu?’

4 Dauda, marubucin wannan zabura ya faɗa cewa yadda muke rera waƙa a tarurruka yana nuna cewa mun ƙudurta mu yi abin da ya dace. Ya ce: “Zuciyata ta kahu, ya Allah, zuciyata ta kahu: zan rera, i, zan rera yabbai.” (Zab. 57:7) Waƙoƙin da muke rerawa a tarurruka na Kirista tana ba mu zarafi mai kyau na “rera yabbai” ga Jehobah da dukan zuciya. Idan ba mu san wasu cikin waƙoƙin mu ba, zai dace mu yi amfani da yamma da muke Bauta ta Iyali don koyon waɗannan waƙoƙin. Ya kamata mu ƙudurta cewa za mu riƙa ‘raira ga Ubangiji muddar ranmu kuma mu raira yabo ga Allahnmu muddar akwai mu.’—Zab. 104:33.

5, 6. A wace hanya ce za mu iya nuna alheri ga baƙi da kuma karimci kuma yaya hakan zai ƙarfafa ’yan’uwa a ikilisiya?

5 Idan muna nuna alheri ga ’yan’uwanmu, hakan zai sa ƙauna ta kasance a cikin ikilisiya. Bulus ya haɗa wannan umurnin a cikin wasiƙarsa ta ƙarshe ga Ibraniyawa: “Bari ƙaunar ’yan’uwa ta lizima. Kada a manta a nuna ƙauna ga baƙi.” (Ibran. 13:1, 2) Idan mun ba ’yan’uwa masu kula masu ziyara da matansu ko kuma wasu da suke hidima ta cikakken lokaci abinci, hakan hanya ce mai kyau ta nuna ƙauna ga baƙi. Za mu kuma iya gayyatar iyali mai iyaye guda ko kuma wasu su ci abinci tare da mu ko kuma su halarci bautarmu ta iyali.

6 Bulus ya gaya wa Timotawus ya umurci ’yan’uwa su “yi alheri, su zama mawadata cikin kyawawan ayyuka, su kasance da niyar babbayarwa, masu-son zumunta; suna ajiye wa kansu tushe mai-kyau domin lokaci mai-zuwa, da za su ruski rai wanda ya ke hakikanin rai.” (1 Tim. 6:17-19) A wannan ayar, Bulus yana ƙarfafa ’yan’uwansa su riƙa karimci. Kuma za mu iya yin hakan a mawuyacin lokaci. Hanya mai kyau da za mu iya yin hakan ita ce mu taimaka wa waɗanda suke bukatar sufuri zuwa da kuma dawowa daga wa’azi da kuma tarurruka. Kuma waɗanda aka taimaka ma za su iya ba da gudummawar kuɗi don nuna godiya. Wata hanya da za mu iya nuna cewa muna ƙaunar ’yan’uwanmu ita ce ta kasancewa tare da su. Idan muna yin abubuwa masu kyau ga “waɗanda su ke cikin iyalin imani” kuma muna a shirye mu yi amfani da lokacinmu da kuma dukiyarmu don taimaka musu, hakan zai sa mu riƙa ƙaunarsu sosai kuma zai sa ’yan’uwa a cikin ikilisiya su yi koyi da mu.—Gal. 6:10.

7. Ta yaya ƙin fallasa abin da wani ya faɗa mana zai iya sa ikilisiya ta kasance da salama?

7 Wasu abubuwan da suke sa ƙaunarmu ga ’yan’uwa ta daɗa ƙarfi su ne, zaman abokin kirki da kuma riƙe sirri. (Karanta Misalai 18:24.) Abokan kirki ba sa fallasa abin da abokinsu ya faɗa musu. Idan ɗan’uwanmu ya faɗa mana abu game da kansa ko kuma game da yadda yake ji kuma ya tabbata cewa ba za mu fallasa su ba, hakan yana sa mu daɗa ƙaunar juna sosai. Ya dace dukanmu mu zama abokan da suke riƙe sirri kuma mu riƙa taimaka wa ikilisiyar ta kasance kamar iyali mai ƙaunar juna.—Mis. 20:19.

KA RIƘA YIN WA’AZI DA ƘWAZO

8. Wace shawara ce Yesu ya ba Kiristocin da ke Lawudikiya kuma me ya sa?

8 Ga abin da Yesu ya ce wa ikilisiyar da ke Lawudikiya: “Na san ayyukanka, ba sanyi kake ko zafi ba: da ma kana sanyi ko zafi! Da yake fa kana tsaka tsaka, ba ka zafi ko sanyi ba, zan zubar da kai daga cikin bakina.” (R. Yoh. 3:15, 16) Kiristocin da ke Lawudikiya ba su da ƙwazo. Wataƙila wannan halin ne ya shafi yadda suke cuɗanya da ’yan’uwa a cikin ikilisiya. Saboda haka, Yesu ya gaya musu: “Iyakar waɗanda na ke ƙauna, ina tsauta su ina masu horo kuma: ka yi himma fa, ka tuba.”—R. Yoh. 3:19.

9. Ta yaya ƙwazonmu a wa’azi zai iya ƙarfafa ikilisiya?

9 Idan muna son hali mai kyau ya kasance a cikin ikilisiya, ya kamata mu riƙa wa’azi da ƙwazo. Dalili ɗaya da ya sa aka kafa ikilisiya shi ne a riƙa neman mutane a yankin kuma a koya musu gaskiya. Saboda haka, muna bukatar mu yi koyi da Yesu kuma mu kasance da ƙwazo a aikin wa’azi. (Mat. 28:19, 20; Luk 4:43) Idan muna da ƙwazo sosai a hidima hakan zai sa mu kasance da haɗin kai a matsayin “abokan aiki na Allah.” (1 Kor. 3:9) Idan muka fita yin wa’azi tare da wasu kuma muka ga yadda suke bayyana imaninsu kuma suke nuna ƙaunarsu ga Jehobah hakan yana sa mu daɗa daraja su sosai. Kuma bauta wa Jehobah da “zuciya ɗaya” tana sa ikilisiyar ta kasance da haɗin kai.—Karanta Zafaniya 3:9.

10. Yaya ƙoƙarin da muke yin don kyautata yadda muke wa’azi yake shafan ’yan’uwa a cikin ikilisiya?

10 Ƙoƙarin da muke yi don kyautata hidimarmu yana kuma amfanar wasu mutane. Idan muna nuna ƙauna ga mutanen da muke wa wa’azi kuma muna ƙoƙari mu taimaka musu su fahimci gaskiya, hakan zai sa ƙwazonmu a hidima ya ƙaru. (Mat. 9:36, 37) Idan muna da ƙwazo, ’yan’uwa ma za su kasance da ƙwazo. Sa’ad da Yesu ya aika almajiransa yin wa’azi, ya tura su biyu-biyu ba ɗai-ɗai ba. (Luk 10:1) Hakan yana sa su samu zarafin ƙarfafa da kuma koyar da juna. Kuma yana sa su kasance da ƙwazo sosai a aikin yin wa’azi. Shin ba ma yin farin ciki sa’ad da muka fita yin wa’azi tare da ’yan’uwa masu ƙwazo? Ƙwazonsu yana ƙarfafa mu mu ci gaba da yin wa’azi.—Rom. 1:12.

KADA KA YI GUNAGUNI DA KUMA ƁOYE ZUNUBANKA

11. Wane irin hali ne wasu Isra’ilawa a zamanin Musa suke da shi kuma mene ne hakan ya sa su yi?

11 Bayan ’yan makonni da Jehobah ya mai da Isra’ila al’umma, suka fara gunaguni. Hakan ya sa suka yi tawaye da Jehobah da kuma wakilansa, Musa da Haruna. (Fit. 16:1, 2) Mutane kalila cikin waɗanda suka bar ƙasar Masar ne kawai suka shiga Ƙasar Alkawari. Jehobah ya hana Musa ma shiga wannan ƙasar saboda yadda ya aikata sa’ad da Isra’ilawa suka yi laifi. (K. Sha 32:48-52) Mene ne za mu iya yi a yau don mu guji mugun hali?

12. Mene ne zai taimaka mana mu guji yin gunaguni?

12 Ya kamata mu yi hankali don kada mu kasance da halin yin gunaguni. Abin da zai taimaka mana kada mu faɗa cikin wannan tarkon shi ne, kasancewa da tawali’u da yin biyayya ga hukuma. Wani abu kuma da zai taimaka mana shi ne zaɓan abokan kirki. Za mu faɗa cikin matsala idan ba mu zaɓi kaɗe-kaɗe da fina-finai masu kan gado ba. Kuma idan muna yawan cuɗanya da abokan aikinmu da abokan makarantarmu da ba sa bauta wa Jehobah. Zai dace mu rage yadda muke cuɗanya da waɗanda suke gunaguni da kuma waɗanda ba sa daraja hukuma.—Mis. 13:20.

13. Waɗanne matsaloli ga bautarmu ga Jehobah ne yin gunaguni zai iya jawo a cikin ikilisiya?

13 Idan mutum ya ci gaba da yin gunaguni a cikin ikilisiya, hakan zai iya sa ya yi abin da zai ɓata dangantakarsa da Jehobah. Alal misali, yin gunaguni zai iya hana ikilisiyar ta kasance da salama da kuma haɗin kai. Bugu da ƙari, yin gunaguni game da ’yan’uwanmu Kiristoci zai sa su baƙin ciki sosai kuma zai iya sa mai gunagunin ya zama matsegunci da kuma mai alfasha. (Lev. 19:16; 1 Kor. 5:11) Wasu masu gunaguni a ikilisiyar Kirista na ƙarni na farko suna “waƙala shugabanci, suna zagin sarautai.” (Yahu. 8, 16) Allah bai amince da yin gunaguni da dattawa a cikin ikilisiya ba.

14, 15. (a) Mene ne zai iya faru a cikin ikilisiya idan mun ƙyale zunubi mai tsanani ya ci gaba? (b) Mene ne ya kamata mu yi idan mun san cewa wani ya yi zunubi kuma ya ɓoye abin da ya yi?

14 Mene ne ya kamata mu yi idan mun san cewa wani ya yi zunubi kuma yana ɓoye wannan zunubin. Kamar yin maye da kallon hotunan batsa da kuma yin lalata? (Afis. 5:11, 12) Idan mun ƙi ɗaukan mataki, Jehobah zai iya janye ruhunsa mai tsarki daga ikilisiyar. Kuma hakan zai jawo matsala sosai a cikin ikilisiyar. (Gal. 5:19-23) Kiristoci na ƙarni na farko sun cire duk wani mai hali marar kyau daga cikin ikilisiyarsu. Ya kamata Kiristoci ma a yau su cire duk wani da zai iya gurɓatar da ikilisiyar. Mene ne za ka iya yi don ikilisiyarku ta kasance da salama?

15 Kamar yadda muka tattauna a dā, bai dace mu fallasa wasu sirrin da mutane suka faɗa mana ba, musamman idan mutumin ya amince da mu kuma ya faɗa mana yadda yake ji. Bai dace ba sam sam mu fallasa sirrin da wani ya faɗa mana. Amma duk da haka, idan wani ya yi zunubi mai tsanani, akwai waɗanda ya dace mu faɗa wa. Waɗannan su ne dattawa na ikilisiya. (Karanta Levitikus 5:1.) Saboda haka, idan mun san cewa wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ya yi zunubi, ya kamata mu ƙarfafa shi ya je ya gaya wa dattawa don su taimaka masa. (Yaƙ. 5:13-15) Idan ya ƙi ya faɗa abin da ya yi, bayan kwanakin da muka ƙayyade masa, zai dace mu kai ƙararsa.

16. Idan mun kai ƙarar wani da ya yi laifi wajen dattawa, ta yaya hakan zai sa a kāre ikilisiyar?

16 Ya kamata mutane su samu kwanciyar rai a cikin ikilisiyar Kirista, kuma wajibi ne mu kāre ta ta wajen faɗa wa dattawa zunubi mai tsanani da wani ya yi. Idan dattawa suka taimaka wa wanda ya yi zunubi ya fahimci cewa zunubin da ya yi mai tsanani ne sosai, kuma ya tuba, ikilisiyar za ta kasance da salama. Amma idan mutumin da ya yi zunubi mai tsanani bai tuba ba kuma bai amince da ƙaunar da dattawa suka nuna masa kuma fa? Zai dace a yi masa yankan zumunci. Kuma idan an yi hakan, za a kāre ikilisiyar daga gurɓatarwa. (Karanta 1 Korintiyawa 5:5.) Aikin kowannenmu ne a cikin ikilisiya mu kai ƙarar wani da ya yi zunubi wajen dattawa kuma mu bi umurnin da suka ba da. Zai fi kyau mu yi abin da ya dace ga ’yan’uwanmu kuma da hakan za mu kāre ikilisiyar.

KA ƘARFAFA ’YAN’UWA SU KASANCE DA “ƊAYANTUWAR RUHU”

17, 18. Mene ne ya kamata mu yi don ikilisiya ta kasance da haɗin kai?

17 “Lizima a cikin koyarwar manzanni” ya taimaka wa mabiyan Yesu na ƙarni na farko su kasance da haɗin kai a cikin ikilisiya. (A. M. 2:42) Sun daraja shawarar Littafi Mai Tsarki da dattawa suka ba su. Hakan ma a yau, ikilisiya tana samun taimako da kuma ƙarfafar da take bukata don ta kasance da haɗin kai domin dattawa suna bin ja-gorar bawan nan mai-aminci, mai-hikima. (1 Kor. 1:10) Idan mun saurari shawarar Littafi Mai Tsarki da Jehobah ya ba mu ta ƙungiyarsa kuma muka bi ja-gorar dattawa, muna nuna cewa muna ‘ƙwazo mu kiyaye ɗayantuwar Ruhu cikin ɗaurin salama.’—Afis. 4:3.

18 Ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don mu kāre ikilisiyarmu daga gurɓatarwa. Idan mun yi hakan, za mu kasance da tabbaci cewa ‘alherin Ubangiji Yesu Kristi zai zauna tare da ruhunmu.’—Filib. 4:23.

[Hoto a shafi na 19]

Kana sa ’yan’uwa su kasance da hali mai kyau a cikin ikilisiya ta wajen shirya kalami mai kyau?

[Hoto a shafi na 20]

Ka ƙarfafa ’yan’uwa su kasance da hali mai kyau ta wajen iya rera waƙoƙinmu sosai

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba