Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 10/15 pp. 12-16
  • Wane Irin Hali Ne Kake Da Shi?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wane Irin Hali Ne Kake Da Shi?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YADDA ZA MU GUJI HALIN MUTANEN DUNIYA
  • KA RIƘA DARAJA MUTANE A CIKIN IKILISIYA
  • KA KASANCE DA HALI MAI KYAU A DANGANTAKARKA DA MUTANE
  • KA CI GABA DA HALI MAI KYAU A ƘUNGIYAR JEHOBAH
  • Ka Kāre Hali Mai Kyau na Ikilisiyar
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Yadda Ruhun Allah Ya Yi Ja-gora A Ƙarni Na Farko Da Kuma A yau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Yi Tafiya Bisa Ga Ruhu Kuma Ka Yi Rayuwar Da Ta Jitu Da Keɓe Kanka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Me Ya Sa Ruhun Allah Zai Yi Mana Ja-gora?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 10/15 pp. 12-16

Wane Irin Hali Ne Kake Da Shi?

‘Alherin Ubangijinmu Yesu Kristi shi zauna tare da halinku.’​—FIL. 25.

MECE CE AMSARKA?

Me ya sa muke bukatar mu yi tunani game da halinmu?

Waɗanne halaye ne ya kamata mu guje wa kuma mene ne zai taimaka mana?

Mene ne za mu yi don mu kasance da hali mai kyau a cikin ikilisiya?

1. Mene ne Bulus ya ambata sau da yawa ga ikilisiyoyi?

A WASIƘAR da manzo Bulus ya rubuta wa Kiristoci na zamanin dā, ya ambata sau da yawa cewa yana fatan cewa Allah da Yesu za su amince da halayensu. Alal misali, sa’ad da ya rubuta wa Galatiyawa wasiƙa, ya ce: ‘Alherin Ubangijinmu Yesu Kristi ya zauna tare da halinku, ’yan’uwa. Amin.’ (Gal. 6:18) Wane “hali” ne Bulus yake magana a kai?

2, 3. (a) Bulus ya ƙarfafa Kiristoci su kasance da wane irin hali? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi wa kanmu game da halinmu?

2 Halinmu ko yadda muke tunani yana sa mu ce ko mu yi wasu abubuwa. Akwai wasu mutane da suke da sauƙin kai da karimci kuma ba su da tsattsauran ra’ayi. Littafi Mai Tsarki ya ce yana da kyau mu kasance da ‘hali mai kyau’ kuma mu zama ‘natsattsu.’ (1 Bit. 3:4; Mis. 17:27) Wasu ma ba su da kan gado kuma suna saurin fushi da kuma son kuɗi. Wasu kuma suna yawan tunanin iskanci da kuma tawaye da Allah.

3 Bulus ya yi amfani da furucin nan ‘Ubangiji shi saka muku don halinku,’ kuma ya yi hakan ne don ya ƙarfafa ’yan’uwansa su yi koyi da Yesu kuma su riƙa faranta wa Allah rai. (2 Tim. 4:22; karanta Kolosiyawa 3:9-12.) Yana da kyau mu yi wa kanmu waɗannan tambayoyin: ‘Wane irin hali ne nake da shi? Ta yaya zan iya kyautata halina don na faranta wa Allah rai? Ta yaya zan iya ƙarfafa ’yan’uwa a cikin ikilisiya don su kasance da hali mai kyau?’ Alal misali, a cikin ɗaurin tsintsiya, kowace tsinke tana da amfani. Kai ma kana kamar wannan tsinken tsintsiyar? Babu shakka, ya kamata mu zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya a cikin ikilisiya. Yanzu za mu tattauna yadda za mu kasance da halin da zai faranta wa Allah rai.

YADDA ZA MU GUJI HALIN MUTANEN DUNIYA

4. Mene ne halin mutanen duniya?

4 Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Ba halin duniya muka karɓa ba, amma halin da ke daga wurin Allah.’ (1 Kor. 2:12) Mene ne ‘halin’ duniya? Littafin Afisawa 2:2 ya ambata wannan halin, ya ce: ‘Inda kuke tafiya a dā bisa ga zamanin wannan duniya, ƙarƙashin sarkin ikon sararin sama, halin da ke aiki yanzu a cikin ’ya’yan kangara.’ Wannan halin yadda mutane suke tunani ne kuma yana ko’ina kamar iska. Alal misali, mutane da yawa ba sa son kowa ya faɗa musu abin da za su yi ko kuma suna son ’yanci. Hakan ya sa su “’ya’yan kangara” ne.

5. Wane irin mugun hali ne wasu a ƙasar Isra’ila suka nuna?

5 Irin wannan halin ba sabon abu ba ne. Alal misali, a zamanin Musa, Kora ya yi tawaye da hukumar ƙasar Isra’ila. Haruna da ’ya’yansa Firistoci ne, kuma ya yi gunaguni game da su. Wataƙila, Kora ya san da kurakurensu. Ko kuma ya yi tunani cewa Musa ya nuna son kai domin Haruna da ’ya’yansa danginsa ne kuma su ne Firistoci. Ba mu san ainihin dalilin da ya sa Kora ya yi tawaye ba, amma tabbas, ra’ayinsa bai dace ba. Sa’ad da Kora ya ce: “Kun cika alfarma,” ya nuna cewa ya raina bayin Jehobah. Sai kuma ya ce: “Menene fa ku ke ɗaukaka kanku gaba da taron jama’ar Ubangiji?” (Lit. Lis. 16:3) Hakazalika, Dathan da Abiram sun yi gunaguni game da Musa. Sun gaya masa cewa “kana so ka maida kanka sarkinmu?” Kuma sa’ad da ya aiko a kirawo su, suka ce: “Ba mu zuwa.” (Lit. Lis. 16:12-14) Halinsu bai sa Jehobah farin ciki ba. Ya kashe duk ’yan tawayen.—Lit. Lis. 16:28-35.

6. Ta yaya wasu a ƙarni na farko suka nuna cewa suna da mugun hali, kuma me ya sa suka yi hakan?

6 A ƙarni na farko, wasu Kiristoci ba su daraja “shugabanci” ba. Sun yi gunaguni game da waɗanda suke shugabanci a cikin ikilisiya. (Yahu. 8) Waɗannan mutanen sun yi zato cewa ya kamata a ba su ƙarin gata. Kuma sun yi ƙoƙari su rinjayi mutane don su yi tawaye da waɗanda suke shugabanci da kuma hidima a cikin ikilisiya.—Karanta 3 Yohanna 9, 10.

7. Wane irin hali ne bai kamata mu kasance da shi ba a cikin ikilisiya?

7 Bai kamata mu kasance da irin wannan halin ba a cikin ikilisiya. Ya kamata mu yi hankali sosai. A yau, dattawa ba kamiltattu ba ne, kamar yadda Musa da kuma dattawan ikilisiya na zamanin Yohanna ba kamiltattu ba ne. Dattawa za su iya yin kuskuren da zai ɓata mana rai. Idan hakan ya faru mana, kada mu nuna irin halin mutanen duniya waɗanda suke cewa, ‘Dole ne a ɗauki mataki a kan wannan ɗan’uwan.’ Mu tuna cewa Jehobah zai iya yafe wasu kurakuren da dattawa suka yi. Ya kamata mu ma mu yi hakan. Wasu ’yan’uwa sun san kurakuren wasu dattawa, don hakan, idan sun yi laifi kuma dattawan suna son su taimaka musu, sai su ƙi da hakan. Hakan yana kamar majiyyacin da ya je wurin likita, amma sa’ad da likitan ya ba shi magani sai ya ƙi sha domin sun taɓa saɓawa da shi.

8. Waɗanne nassosi ne za su taimaka mana mu riƙa daraja dattawan ikilisiya?

8 Idan muna son mu yi tir da irin wannan hali, dole ne mu tuna cewa Yesu yana riƙe da “taurari bakwai” a hannun damarsa. Waɗannan taurarin suna wakiltar dattawan da shafaffu ne, amma abin da aka ce musu zai iya shafan dukan dattawan ikilisiya. Yesu zai iya yin duk abin da yake so da waɗannan taurarin. (R. Yoh. 1:16, 20) Yesu ne Shugaban Ikilisiyar Kirista, kuma ya san abin da dattawa suke yi. “Idanunsa kuma kamar harshen wuta ne,” kuma yana ganin dukan abin da suke yi. Saboda haka, idan Yesu ya ga cewa wani dattijo yana bukatar gyara, zai yi hakan a hanya da kuma a lokacin da ya dace. (R. Yoh. 1:14) Tun da Yesu ne yake da ikon yin hakan, dole ne mu ci gaba da daraja dattawa, waɗanda suke ‘hannun dama’ na Yesu. Manzo Bulus ya ce: “Ku yi biyayya da waɗanda ke shugabanninku, ku sarayar da kanku gare su: gama suna yin tsaro sabili da rayukanku, kamar waɗanda za su amsa tambaya; su yi shi da farinciki, ba da baƙinciki ba: gama wannan marar-amfani ne gare ku.”—Ibran. 13:17.

9. (a) Wane hali ne Kirista zai iya nuna idan aka masa gyara? (b) Me ya kamata mu yi sa’ad da aka mana gyara?

9 Za a iya sanin halin wani ɗan’uwa a cikin ikilisiya sa’ad da dattawa suka masa gyara, ko suka karɓi wani gata daga wurinsa. Akwai wani ɗan’uwa matashi da dattawa suka wa gargaɗi game da yin wasan bidiyon da ake mugunta. Abin baƙin ciki, ya yi taurin kai, kuma aka sauƙe shi a matsayin bawa mai hidima domin abin da ya yi ya saɓa wa ƙa’idojin Littafi Mai Tsarki. (Zab. 11:5; 1 Tim. 3:8-10) Bayan haka, sai ɗan’uwan ya soma tara jama’a, yana gaya musu cewa an cuce shi. Har ma ya rubuta wasiƙa sau da yawa ga ofishin reshe yana faɗa baƙar magana game da dattawan. Ya ma gaya wa wasu ’yan’uwa a cikin ikilisiya cewa su ma su rubuta wasiƙa zuwa ofishin reshe. Amma gaskiyar ita ce, idan muna neman hujja don kurakuren da muka yi, za mu hana ikilisiyar baki ɗaya ta kasance da salama, kuma yin hakan babu riba. Idan an yi mana gyara, ya kamata mu amince cewa zarafi ne na sanin kurakuranmu.—Karanta Makoki 3:28, 29.

10. (a) Mene ne littafin Yaƙub 3:16-18 ya koya mana game da ra’ayi mai kyau da marar kyau? (b) Mene ne sakamakon nuna “hikimar Allah”?

10 Littafin Yaƙub 3:16-18 ya bayyana abin da ya kamata mu yi da kuma abin da bai kamata mu yi ba a cikin ikilisiya. Ya ce: “Wurin da kishi da tsaguwa su ke, nan akwai yamutsai da kowane irin mugun al’amari. Amma hikima mai-fitowa daga bisa tsatsarka ce dafari, bayan wannan mai-salama ce, mai-sauƙin hali, mai-siyasa, cike da jinƙai da kyawawan ’ya’ya, marar-kokanto, marar-riya ce. Kuma ana shuka ɗiyan adalcin cikin salama domin masu-yin salama.” Idan muka yi ayyukan da suka jitu da hikimar Allah, za mu yi koyi da shi. Idan mun yi hakan, za mu ƙarfafa juna, kuma salama za ta kasance cikin ikilisiya.

KA RIƘA DARAJA MUTANE A CIKIN IKILISIYA

11. (a) Mene ne kasance da hali mai kyau zai hana mu yi? (b) Wane darasi ne muka koya daga misalin Dauda?

11 Ya kamata mu tuna cewa Jehobah yana son dattawa su “yi kiwon ikilisiyar Allah.” (A. M. 20:28; 1 Bit. 5:2) Idan mu dattawa ne ko ba dattawa ba ne, ya kamata mu riƙa daraja yadda Allah yake aikatawa. Idan muna da halin da ya dace, ba za mu riƙa mutuwar son matsayi ba. Sa’ad da Sarki Saul ya soma zato cewa Dauda zai yi masa juyin mulki, sai ya soma “harari Dauda.” (1 Sam. 18:9) Saul ya samu ra’ayi marar kyau kuma ya so ya kashe Dauda. Kada mu zama kamar Saul wanda yake yawan son matsayi, amma ya kamata mu zama kamar Dauda. Ko da an yi masa rashin mutunci, amma Dauda ya ci gaba da girmama waɗanda Allah ya naɗa.—Karanta 1 Sama’ila 26:23.

12. Mene ne zai sa ikilisiyar ta kasance da haɗin kai?

12 Muna ɓata wa juna rai a wasu lokatai domin muna da ra’ayi dabam-dabam. Hakan zai iya faruwa tsakanin dattawa. Littafi Mai Tsarki ya ba da shawarar da za ta taimaka mana. Ya ce: “Wajen ba da girma, kowa ya riga ba ɗan’uwansa” kuma, “Kada ku aza kanku masu-hikima ne.” (Rom. 12:10, 16, Littafi Mai Tsarki) Bai kamata mu riƙa nace wa ra’ayinmu ba, maimakon haka, ya kamata mu san cewa ra’ayin wasu ma yana da kyau. Idan muka yi ƙoƙari muka fahimci ra’ayin wasu, za mu sa ikilisiyar ta kasance da haɗin kai.—Filib. 4:5.

13. Yaya ya kamata mu ɗauki ra’ayinmu, kuma wane misali ne da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya nuna hakan?

13 Hakan yana nufin cewa laifi ne mu faɗi ra’ayinmu idan muka ga cewa akwai wani abu da ke bukatar a daidaita a cikin ikilisiyar? A’a. Akwai wani abu da mutane da yawa a cikin ikilisiya na ƙarni na farko ba su amince da shi ba. ’Yan’uwan suka “sanya Bulus da Barnaba, da waɗansu daga cikinsu, su tafi Urushalima wurin manzanni da dattiɓai a kan wannan matsala.” (A. M. 15:2) Babu shakka, kowannensu yana da ra’ayi game da yadda za a magance matsalar. Amma, sa’ad da ruhu mai tsarki ya taimaka musu su tsai da shawara, ’yan’uwan suka daina nace wa ra’ayinsu. Sa’ad da ikilisiyoyi suka samu wasiƙa da ta sanar musu game da shawarar da aka tsai da, sai “suka yi murna saboda wannan gargaɗi” kuma “suka ƙarfafa cikin imani.” (A. M. 15:31; 16:4, 5) Hakan ma yake a yau, idan muka gaya wa dattawa abin da ke damunmu, ya kamata mu gaskata cewa za su yi tunani sosai game da abin da muka faɗa kuma su ga ko za a yi wani abu akan batun.

KA KASANCE DA HALI MAI KYAU A DANGANTAKARKA DA MUTANE

14. Ta yaya za mu iya nuna hali mai kyau a dangantakarmu da mutane?

14 Muna da zarafi masu yawa na kasancewa da hali mai kyau a dangantakarmu da mutane. Alal misali, yana da kyau kowannenmu ya riƙa gafarta wa mutane da sauri idan sun ɓata mana rai. Kalmar Allah ta gaya mana: “Kuna haƙuri da juna, kuna gafarta ma juna, idan kowane mutum yana da maganar ƙara game da wani; kamar yadda Ubangiji ya gafarta maku, hakanan kuma sai ku yi.” (Kol. 3:13) Furucin nan “idan kowane mutum yana da maganar ƙara” ya nuna cewa muna iya samun ƙwaƙƙwarar dalili na yin fushi da wasu. Bai kamata mu bar abubuwa da ba su taka ƙara ya karye ba su ɓata mana rai. Hakan yana iya hana ikilisiya kasancewa da salama. Maimakon haka, mu yi ƙoƙari mu yi koyi da Jehobah wajen kasancewa a shirye mu gafarta wa ’yan’uwanmu kuma mu ci gaba da bauta masa tare.

15. (a) Ta yaya za mu koyi gafarta wa mutane daga wurin Ayuba? (b) Ta yaya addu’a za ta taimaka mana mu kasance da halin da ya dace?

15 Za mu koyi gafarta wa mutane daga Ayuba. Mutane uku da ya kamata su ƙarfafa shi suna ta masa baƙar magana. Duk da haka, Ayuba ya gafarta musu. Ta yaya ya yi hakan? “Ya yi wa abokansa addu’a.” (Ayu. 16:2; 42:10) Ambata mutane a addu’armu yana iya canja ra’ayinmu game da su. Idan muka yi addu’a a madadin ’yan’uwanmu, zai yi sauƙi mu ɗauke su yadda Yesu yake ɗaukansu. (Yoh. 13:34, 35) Ya kamata mu roƙi Jehobah ya ba mu ruhunsa. (Luk 11:13) Ruhun Allah zai taimaka mana mu kasance da hali mai kyau a dangantakarmu da mutane.—Karanta Galatiyawa 5:22, 23.

KA CI GABA DA HALI MAI KYAU A ƘUNGIYAR JEHOBAH

16, 17. Wane hali ne kake son ka kasance da shi?

16 Dukan ikilisiya za ta amfana idan kowannenmu ya kasance da hali mai kyau. Wataƙila wannan talifin ya taimake ka ka ga cewa kana bukatar ka soma kasancewa da hali mai kyau. Idan haka ne, bari Littafi Mai Tsarki ya gyara ka. (Ibran. 4:12) Bulus yana son ya kafa misali mai kyau a cikin ikilisiya, shi ya sa ya ce: “Gama ban san wani aibi a kaina ba; ko da haka wannan ba ya sa na barata ba: amma mai-yi mini ƙwanƙwanto Ubangiji ne.”—1 Kor. 4:4.

17 Dukanmu muna da gatar ƙarfafa ’yan’uwanmu a cikin ikilisiya kuma mu taimaka wajen sa ikilisiyar ta kasance da hali mai kyau. Za mu iya yin hakan idan muka yi ƙoƙarin yin koyi da halayen Allah. Hakan zai taimaka mana mu daina nace wa ra’ayinmu da kuma ɗaukan kanmu fiye da yadda ya dace. Za mu yi zaman salama da ’yan’uwanmu idan muna saurin gafartawa, kuma muka kasance da ra’ayi mai kyau game da su. (Filib. 4:8) Idan muka yi waɗannan abubuwan, za mu kasance da tabbacin cewa Jehobah da Yesu za su yi farin ciki da halinmu.—Fil. 25.

[Hoto a shafi na 14]

Ta yaya yin bimbini a kan matsayin Yesu zai taimaka mana mu karɓi gyara?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba