Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 12/15 pp. 22-26
  • Yadda Ruhun Allah Ya Yi Ja-gora A Ƙarni Na Farko Da Kuma A yau

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Ruhun Allah Ya Yi Ja-gora A Ƙarni Na Farko Da Kuma A yau
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Ga Ni, Baiwar Ubangiji!”
  • Ruhu Mai Tsarki Ya Taimaki Bitrus
  • Bulus Ya “Cika da Ruhu Mai Tsarki”
  • “Aike Aike Iri-Iri”
  • Ka Ci Gaba da Roƙon Taimakon Ruhu Mai Tsarki
  • Ka Yi Tafiya Bisa Ga Ruhu Kuma Ka Yi Rayuwar Da Ta Jitu Da Keɓe Kanka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Me Ya Sa Ruhun Allah Zai Yi Mana Ja-gora?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Yadda Ruhu Mai Tsarki Yake Taimaka Mana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 12/15 pp. 22-26

Yadda Ruhun Allah Ya Yi Ja-gora A Ƙarni Na Farko Da Kuma A yau

“Dukan waɗannan shi wannan Ruhu ɗaya ya ke aikata su.”—1 KOR. 12:11.

1. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

ABUBUWA masu ban mamaki sun faru a ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z. (A. M. 2:1-4) A wannan ranar ce Allah ya soma yin amfani da ruhunsa don yi wa mutanensa ja-gora a sabuwar hanya. A talifin da ya gabata, mun tattauna waɗansu hanyoyin da ruhun Allah ya sa mutane masu aminci a zamanin dā su cika aikinsu. Amma wanne bambanci ne yake tsakanin yadda ruhun Allah ya yi aiki kafin zamanin Kiristoci da kuma a ƙarni na farko? Kuma yaya Kiristoci suke amfana daga yadda ruhu mai tsarki na Allah yake aiki a yau? Bari mu tattauna wannan.

“Ga Ni, Baiwar Ubangiji!”

2. Ta yaya Maryamu ta ga ikon ruhu mai tsarki?

2 Maryamu ma tana tare da almajiran a gidan bene da ke Urushalima sa’ad da aka zubo musu ruhu mai tsarki. (A. M. 1:13, 14) Amma duk da haka, fiye da shekara talatin kafin wannan aukuwar, ta shaida yadda ruhun Jehobah yake aiki a hanyoyi masu ban al’ajabi. Jehobah ya tura ran Ɗansa daga sama zuwa duniya, kuma ya sa wata budurwa mai suna Maryamu ta ɗauki ciki. Abin da ke juna biyu a cikinta “daga wurin Ruhu Mai-tsarki ne.”—Mat. 1:20.

3, 4. Wane hali ne Maryamu ta nuna, kuma yaya za mu iya yin koyi da ita?

3 Me ya sa Jehobah ya zaɓi Maryamu? Bayan da mala’ikan ya bayyana wa Maryamu nufin Jehobah, sai ta ce: “Ga ni, baiwar Ubangiji; bisa ga faɗinka shi zama mani.” (Luk 1:38) Ta waɗannan kalmominta, Maryamu ta nuna wani hali da Allah ya riga ya lura da shi. Yadda ta amsa nan da nan ya nuna cewa ta amince nufin Jehobah ya kasance a kanta. Ba ta yi tambaya game da yadda maƙwabta za su ɗauki cikin da take da shi ba ko kuma yadda hakan zai shafi dangantakarta da saurayinta ba. Ta kalamin da Maryamu ta furta cewa ita baiwar Jehobah ce, ta nuna cewa ta dogara gabaki ɗaya ga Jehobah.

4 Ka taɓa damuwa sosai saboda wani ƙalubale ko kuma wani aikin da kake da shi a ƙungiyar Jehobah? Ya kamata kowannenmu ya tambayi kansa, ‘Shin na dogara gabaki ɗaya ga Jehobah don abubuwan su kasance bisa nufinsa? Shin ina nuna yardar rai?’ Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ba da ruhunsa ga waɗanda suke dogara gare shi da dukan zuciyarsu kuma suke biyayya gare shi a matsayin mai ikon mallaka.—A. M. 5:32.

Ruhu Mai Tsarki Ya Taimaki Bitrus

5. A waɗannan hanyoyi ne Bitrus ya shaida ikon ruhu mai tsarki kafin ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z.?

5 Kamar Maryamu, manzo Bitrus ma ya shaida ikon ruhu mai tsarki na Allah kafin ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z., Yesu ya ba shi da sauran manzannin iko don su fitar da aljanu daga cikin mutane. (Mar. 3:14-16) Ko da yake Nassosi bai ba da bayanai da yawa game da wannan ba, amma kamar Bitrus ya yi amfani da wannan ikon. Kuma, sa’ad da Yesu ya ce Bitrus ya yi tafiya a kan Tekun Galili, Bitrus ya yi hakan da taimakon ruhu mai tsarki. (Karanta Matta 14:25-29.) Babu shakka, Bitrus ya dogara ga ruhu mai tsarki don cim ma abubuwa da yawa. Ba da daɗewa ba, wannan ruhun zai taimaka wa Bitrus da sauran manzanni su yi abubuwa masu yawa.

6. Mene ne Bitrus ya cim ma a lokacin Fentakos na 33 A.Z., da kuma bayan hakan da taimakon ruhu mai tsarki?

6 A idin Fentakos na shekara ta 33 A.Z., an ba Bitrus da sauran iko ta mu’ujiza su tattauna da baƙin da suka halarci Urushalima da harsunansu. Kuma Bitrus ya yi ja-gora wajen tattauna da jama’ar. (A. M. 2:14-36) A wasu lokatai Bitrus ya ji tsoro ko kuma yi abubuwa bisa motsin rai, amma bayan da ya samu taimakon ruhu mai tsarki sai ya kasance da gaba gaɗin yin wa’azi duk da yake an tsananta masa da kuma gaya masa ya daina wa’azi. (A. M. 4:18-20, 31) Allah ya yi amfani da ruhunsa don ya ba Bitrus ilimi ta musamman. (A. M. 5:8, 9) Kuma an ma ba shi ƙarfin ta da matattu.—A. M. 9:40.

7. Waɗanne koyarwar Yesu ne Bitrus ya fahimta bayan da aka shafa shi da ruhu mai tsarki?

7 Kafin ranar Fentakos, Bitrus ya fahimta wasu gaskiyar da Yesu ya koyar. (Mat. 16:16, 17; Yoh. 6:68) Amma akwai wasu koyarwar Yesu da Bitrus bai fahimta ba kafin ranar Fentakos. Alal misali, Bitrus bai fahimci cewa Kristi zai tashi daga matattu zuwa sifar ruhu a rana ta uku ba, kuma Bitrus bai fahimci cewa Mulkin zai kasance a cikin sama ba. (Yoh. 20:6-10; A. M. 1:6) Batun zama ruhu da kuma yin sarauta a Mulki na sama sabon abu ne ga Bitrus. Sai bayan da aka yi wa Bitrus baftisma da ruhu mai tsarki kuma aka ba shi begen zuwa sama ne ya fahimci ma’anar koyarwar Yesu.

8. Wane ilimi ne shafaffu da kuma “waɗansu tumaki” suke da shi?

8 Bayan da aka shafa almajiran Yesu da ruhu mai tsarki, sai suka fahimci koyarwar da ba su fahimta ba a dā. Ruhu mai tsarki ya taimaka wa marubucin Nassosin Helenanci na Kirista su bayyana gaskiya masu ban al’ajabi game da ƙudurin Jehobah. (Afis. 3:8-11, 18) A yau, shafaffu da kuma “waɗansu tumaki” suna nazarta da kuma fahimtar gaskiya iri ɗaya. (Yoh. 10:16) Kana godiya don wannan ilimi da fahimi na Kalmar Allah da ruhu mai tsarki na Allah yake taimaka mana mu samu?

Bulus Ya “Cika da Ruhu Mai Tsarki”

9. Mene ne ruhu mai tsarki ya taimaki Bulus ya cim ma?

9 Wajen shekara guda bayan Fentakos na shekara ta 33 A.Z., wani dabam ya samu kyautar ruhu mai tsarki na Allah. Wannan Shawulu ne, wanda ya zama Bulus daga baya. Ruhu mai tsarki ya ba Bulus ingancin yin abubuwa da yawa da ke amfanar mu a yau. An hure Bulus ya rubuta littattafai 14 na Littafi Mai Tsarki. Kuma kamar yadda ruhu mai tsarki ya taimaki Bitrus, ya taimaki Bulus ya fahimci kuma ya rubuta sarai game da begen samun rai marar mutuwa da kuma marar aibi a cikin sama! Da taimakon ruhu mai tsarki Bulus ya fitar da aljanu da warkar da masu ciwo da kuma ta da wasu matattu. Amma dai, ruhu mai tsarki ya ƙarfafa Bulus ya yi abu da ya fi muhimmanci. Kuma bayin Allah ma a yau suna samun wannan ikon a yau, ko da ba sa samun hakan ta mu’ujiza.

10. Ta yaya ruhu mai tsarki ya taimaki Bulus ya yi magana?

10 Bulus “cike da Ruhu Mai-tsarki,” da gaba gaɗi ya tsauta wa wani maƙiyin bauta ta gaskiya. Hakan ya shafi shugaban birnin Cyprus, wanda shi ma yana saurarar tattaunawar! Wannan shugaban ya karɓi gaskiya, kuma “yana mamaki da sanarwar Ubangiji.” (A. M. 13:8-12) Babu shakka, Bulus ya san cewa ruhu mai tsarki na Allah ne kaɗai zai iya ƙarfafa shi ya faɗi gaskiya da gaba gaɗi. (Mat. 10:20) Daga baya ya roƙi ikilisiyar da ke Afisa cewa su yi masa addu’a don Allah ya ba shi ‘ikon faɗin’ magana da gaba gaɗi.—Afis. 6:18-20.

11. Ta yaya ruhu mai tsarki na Allah ya yi wa Bulus ja-gora?

11 Ruhu mai tsarki ya taimaki Bulus ya yi magana, amma a wasu lokatai, ya hana shi yin magana a wasu wurare. Yayin da Bulus ya soma hidimarsa na wa’azi a ƙasashen waje, ruhu mai tsarki na Allah ya taimake shi. (A. M. 13:2; karanta Ayyukan Manzanni 16:6-10.) Har yau, Jehobah yana ja-goranci aikin wa’azi da ruhunsa mai tsarki. Kamar Bulus, dukan bayin Jehobah masu biyayya suna ƙoƙartawa don yin wa’azin gaskiya da gaba gaɗi da kuma ƙwazo. Ko da alamar ja-gorar Allah bai fita sarai ba kamar yadda ya kasance a zamanin Bulus, amma za mu iya kasance da tabbaci cewa Jehobah yana yin amfani da ruhunsa mai tsarki don ya tabbata cewa masu zukatan kirki sun san gaskiya.—Yoh. 6:44.

“Aike Aike Iri-Iri”

12-14. Shin ruhu mai tsarki na Allah yana aiki iri ɗaya ga dukan bayin Allah? Ka bayyana.

12 Karanta game da yadda Jehobah ya albarkaci ikilisiyar shafaffu a ƙarni na farko yana ƙarfafa mu a yau kuwa? Babu shakka! Ka lura da hurarrun kalmomin da Bulus ya faɗa wa ikilisiyar da ke Korinti game da baiwar ruhu mai tsarki ta mu’ujiza a zamaninsa: ‘Akwai dai bayebaye iri iri, amma Ruhu ɗaya ne. Akwai hidimomi kuma iri iri, Ubangiji kuwa ɗaya ne. Akwai kuma aike aike iri iri, amma Allah ɗaya ne, shi wanda ya ke aikata dukan abu cikin dukan kowa.’ (1 Kor. 12:4-6, 11) Hakika, ruhu mai tsarki zai iya yin aiki a hanyoyi dabam-dabam a kan bayin Allah dabam-dabam don cim ma manufa guda. Babu shakka, ruhu mai tsarki yana ja-gorar “ƙaramin garke” na Kristi da kuma “waɗansu tumaki.” (Luk 12:32; Yoh. 10:16) Amma yana aiki a hanyoyi dabam-dabam a kan kowanne mutum a cikin ikilisiya.

13 Alal misali, ruhu mai tsarki ne ya naɗa dattawa. (A. M. 20:28) Amma ba dukan shafaffu ba ne dattawa a cikin ikilisiya. Hakan yana nufin cewa ruhun Allah yana aiki a hanyoyi dabam-dabam a kan ’yan’uwa a cikin ikilisiya.

14 Ruhun da ya sa shafaffu su san cewa su ’ya’yan Allah ne ma Jehobah ya yi amfani da shi don ya ta da Yesu daga matattu zuwa sama. (Karanta Romawa 8:11, 15.) Kuma da wannan ruhun ne Jehobah ya halicci dukan sararin samaniya. (Far. 1:1-3) Jehobah ya kuma yi amfani da wannan ruhun wajen ba Bezalel ingancin yin aiki na musamman a mazaunin da kuma Samson don ya yi ayyukan da babu wanda zai iya yi, da kuma sa Bitrus ya yi tafiya a kan Teku. Saboda haka, idan aka ce ruhu mai tsarki na Allah ya yi wa mutum ja-gora, hakan ba ɗaya ba ne da shafe mutum. Shafa mutum da ruhu mai tsarki wata hanya ta musamman ce da ruhu mai tsarki na Allah yake aiki. Allah ne yake zaɓar waɗanda zai shafa da ruhu mai tsarki.

15. Shin yin baftisma da ruhu mai tsarki zai ci gaba ne har abada? Ka bayyana.

15 Ruhu mai tsarki na Allah ya daɗe yana aiki a hanyoyi dabam-dabam a kan bayin Allah masu aminci, kuma yana hakan shekaru dubbai kafin a fara shafa mutane da ruhu mai tsarki. A ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z., ruhun ya soma aiki a sabuwar hanya, amma hakan ba zai kasance har abada ba. Za a daina yin baftisma da ruhu mai tsarki, amma ruhu mai tsarki zai ci gaba da aiki a kan bayin Allah don su ci gaba da yin nufinsa har abada.

16. Mene ne ruhu mai tsarki yake taimaka wa bayin Jehobah su cim ma a yau?

16 Mene ne bayin Jehobah suke cim ma a yau da taimakon ruhu mai tsarki? Ru’ya ta Yohanna 22:17 ya amsa: “Ruhu da amarya suna cewa, Zo. Mai ji kuma, bari ya ce, Zo. Mai jin ƙishi kuma, bari ya zo: wanda ya ke so, bari ya ɗiba ruwa na rai kyauta.” Da taimakon ruhu mai tsarki, Kiristoci a yau suna gayyatar “wanda ya ke so” ya karɓi ruwa na rai da Jehobah ke bayarwa. Kiristoci shafaffu ne ke yin ja-gora a wannan aikin. Amma, waɗansu tumaki suna saka hannu don yin wannan gayyatar. Ruhu mai tsarki na Allah ne ke taimaka wa waɗannan rukuni biyu su cim ma wannan aikin. Waɗannan rukuni biyu sun nuna cewa sun keɓe kansu ga Jehobah ta yin baftisma “cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki.” (Mat. 28:19) Kuma waɗannan rukuni biyu suna nuna ’yar ruhu a rayuwarsu. (Gal. 5:22, 23) Da taimakon ruhu mai tsarki na Allah, suna yin iya ƙoƙarinsu don su yi ayyukan da suke faranta wa Allah rai.—2 Kor. 7:1; R. Yoh. 7:9, 14.

Ka Ci Gaba da Roƙon Taimakon Ruhu Mai Tsarki

17. Yaya za mu iya nuna cewa muna da ruhu mai tsarki?

17 Ko kana da begen yin rayuwa har abada a cikin sama ko kuma a duniya, Jehobah zai iya ba ka “mafificin girman iko” don ka kasance da aminci kuma ka samu ladar. (2 Kor. 4:7) Mutane za su tsananta muku don kuna wa’azi. Amma ku tuna cewa “idan kuna shan zargi sabili da sunan Kristi masu-albarka ne ku; domin Ruhu na daraja da Ruhu na Allah yana zaune a kanku.”—1 Bit. 4:14.

18, 19. Ta yaya Jehobah zai taimaka maka ta ruhunsa mai tsarki kuma mene ne ka ƙudurta?

18 Jehobah yana ba da ruhunsa ga waɗanda suke roƙon shi da dukan zuciya. Zai iya kyautata ingancinka da kuma muradinka don yin iya ƙoƙarinka a hidimar Allah. “Allah ne yana aiki a cikinku da za ku yi nufi har ku aika kuma, zuwa abin da ya gamshe shi.” Baiwa mai tamani na ruhu mai tsarki, da kuma ƙoƙarinmu don mu riƙe “zancen rai” zai sa mu “yi aikin ceton[mu] da tsoro da rawan jiki” kuma.—Filib. 2:12, 13, 16.

19 Ta wajen dogara gabaki ɗaya ga ruhun Allah, bari mu yi iya ƙoƙarinmu a aikin da Jehobah ya ba mu, kuma mu ƙware a aikin da muke yi muna neman taimakon Jehobah a dukan abin da muke yi. (Yaƙ. 1:5) Zai ba ka abin da kake bukata don ka fahimci Kalmar Allah da jimre da matsalolin rayuwa da kuma yin wa’azin bishara. “Ku [ci gaba da] roƙa, za a ba ku; ku [ci gaba da] nema, za ku samu; ku [ci gaba da] ƙwanƙwasa, za a buɗe muku,” kuma hakan ya haɗa da samun ruhu mai tsarki. (Luk 11:9, 13) Hakika, ku ci gaba da roƙon Jehobah don ku zama kamar amintattu na zamanin dā da kuma na zamaninmu, waɗanda ruhun Allah ya yi musu ja-gora.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Kamar Maryamu, wane hali ne za mu nuna don mu samu albarka?

• A wane azanci ne ruhun Allah ya yi wa Bulus ja-gora?

• Ta yaya ruhu mai tsarki yake wa bayin Allah ja-gora a yau?

[Hoto a shafi na 24]

Ruhun Allah ya taimaka wa Bulus ya shawo kan rinjayar miyagun ruhohi

[Hoto a shafi na 26]

A yau, ruhu mai tsarki yana taimaka wa Kiristoci ko suna da begen yin rayuwa a sama ko a duniya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba