Ka Yi Tafiya Bisa Ga Ruhu Kuma Ka Yi Rayuwar Da Ta Jitu Da Keɓe Kanka
“Ku yi tafiya bisa ga ruhu, ba kuwa za ku biya sha’awar jiki ba.”—GAL. 5:16.
1. Waɗanne baftisma ne aka yi a ranar Fentakos?
SA’AD da mabiyan Yesu suka yi magana a harsuna dabam-dabam a ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z., sun yi hakan ne bayan an yi musu baftisma da ruhu mai tsarki. Sun nuna sun samu kyautar ruhu ta hanyar mu’ujiza. (1 Kor. 12:4-10) Menene sakamakon wannan kyautar da kuma jawabin da manzo Bitrus ya ba da? Mutane da yawa sun “soku cikin zuciyarsu.” Bisa ariritar su da Bitrus ya yi, suka tuba kuma suka yi baftisma. Labarin ya ce: “Waɗannan fa da suka karɓi maganatasa, aka yi musu baftisma: a cikin wannan rana fa aka ƙara musu masu-rai wajen talata.” (A. M. 2:22, 36-41) Kamar yadda Yesu ya ba da umurni, an yi musu baftisma a cikin ruwa cikin sunan Uba, Ɗa, da kuma ruhu mai tsarki.—Mat. 28:19.
2, 3. (a) Ka bayyana bambancin da ke tsakanin yin baftisma da ruhu mai tsarki da kuma yin baftisma cikin sunan ruhu mai tsarki. (b) Me ya sa ake bukatan dukan waɗanda suka zama Kiristoci na gaskiya a yau su yi baftisma cikin ruwa?
2 Amma, da akwai bambanci ne tsakanin yin baftisma da ruhu mai tsarki da kuma yin baftisma cikin sunan ruhu mai tsarki? E. An sake haifan waɗanda aka yi musu baftisma da ruhu mai tsarki a matsayin haifaffun ’ya’yan Allah na ruhu. (Yoh. 3:3) An shafa su su zama sarakuna da mataimakan firistoci a nan gaba a Mulkin Allah na samaniya, kuma su sashe ne na jiki na ruhaniya na Kristi. (1 Kor. 12:13; Gal. 3:27; R. Yoh. 20:6) Saboda haka, baftisma da ruhu mai tsarki shi ne Jehobah ya yi sa’ad da a ranar Fentakos da kuma bayan haka, ya zaɓi mutane su zama masu tarayyar gādo da Kristi. (Rom. 8:15-17) Amma, baftisma a cikin ruwa cikin sunan ruhu mai tsarki kuma fa, wadda ake yi a kai a kai a manyan taro da taron gunduma na mutanen Jehobah a zamaninmu?
3 Kiristoci na gaskiya suna yin baftisma cikin ruwa don su nuna sun keɓe kansu gabaki ɗaya ga Jehobah Allah. Hakan yake da waɗanda aka kira su zuwa sama. Amma, yin baftisma a cikin ruwa tilas ne ga maza da mata miliyoyi a wannan zamanin da suke da begen zama a duniya har abada. Ko da wane bege ne mutum yake da shi, yin baftisma cikin ruwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na ruhu mai-tsarki mataki ne mai muhimmanci da dole ne mutum ya ɗauka domin Allah ya amince da shi. Ana bukatan dukan Kiristoci da aka yi musu baftisma a wannan hanyar su “yi tafiya bisa ga ruhu.” (Karanta Galatiyawa 5:16.) Kana tafiya bisa ga ruhu kuma da hakan kana rayuwa da ta jitu da keɓe kanka kuwa?
Abin da Yin “Tafiya Bisa ga Ruhu” Yake Nufi
4. Menene yin “tafiya bisa ga ruhu” yake nufi?
4 Yin “tafiya bisa ga ruhu” ya ƙunshi amincewa da aikin da ruhu mai tsarki yake yi a kanka, ka ƙyale ruhu mai tsarki ya yi tasiri a kanka. A wata sassa, yana nufin ƙyale ruhu mai tsarki ya yi maka ja-gora a ayyukanka na yau da kullum. Galatiyawa sura ta 5 ta nuna bambancin da ke tsakanin kasancewa a ƙarƙashin ja-gorancin ruhu mai tsarki da kuma jiki.—Karanta Galatiyawa 5:17, 18.
5. Kasancewa a ƙarƙashin ja-gorancin ruhu mai tsarki ya ƙunshi guje wa waɗanne ayyuka?
5 Idan kana ƙarƙashin ja-gorancin ruhu mai tsarki, za ka guji ayyuka na jiki. Ayyukan jiki sun haɗa da “fasikanci . . . ƙazanta, lalata, bautar gumaka, sihiri, magabtaka, husuma, kishekishe, hasala, tsatsaguwa, rabuwa, hamiya, hasada, maye, nishatsi.” (Gal. 5:19-21) A wani azanci, idan kana yin tafiya “bisa ga ruhu [kana] kashe ayyukan jiki.” (Rom. 8:5, 13) Hakan zai taimaka maka ka kafa zuciyarka a kan abubuwa na ruhu kuma ka ba da haɗin kai ga ja-gorarsa, maimakon ka bar sha’awoyi na jiki su yi maka ja-gora.
6. Ka kwatanta abin da ake bukata domin a nuna ’yar ruhu.
6 Yayin da ruhu mai tsarki yake aiki a kanka, za ka nuna halaye na ibada, ‘’yar ruhu.’ (Gal. 5:22, 23) Amma, ka fahimci cewa hakan na bukatan ƙoƙari a gare ka. Alal misali: Manomi ya yi noma. Hakika, rana da ruwa suna da muhimmanci idan zai girbe abin da ya shuka. Za mu iya kwatanta ruhu mai tsarki da rana. Muna bukatan ruhu mai tsarki don mu nuna ’yar ruhu. Amma, menene manomi zai girbe idan bai yi aiki tuƙuru ba? (Mis. 10:4) Hakika, yadda ka nome zuciyarka zai nuna adadi da kuma halayen ’yar ruhu mai tsarki da ka samu. Saboda haka ka tambayi kanka, ‘Ina ƙyale ruhu mai tsarki ya ba da ’yarsa ta wajen yin aiki tare da shi kuwa?’
7. Me ya sa nazari da bimbini suke da muhimmanci sosai idan kana so ka samu ’yar ruhu mai tsarki?
7 Don su yi girbi mai kyau, manoma suna bukatan ruwa. Domin ka samu ’yar ruhu, kana bukatan ruwaye na gaskiya da ake samu a cikin Littafi Mai Tsarki da kuma ikilisiyar Kirista a yau. (Isha. 55:1) Wataƙila ka nuna wa mutane da yawa cewa an hure Nassosi Masu Tsarki ta hanyar ruhu mai tsarki. (2 Tim. 3:16) Rukunin bawan nan mai aminci, mai hikima suna tanadin fahimi da ake bukata na ruwaye na gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. (Mat. 24:45-47) Sakamakon a bayyane yake. Idan muna so mu kasance a ƙarƙashin ja-gorancin ruhu mai tsarki, dole ne mu karanta Kalmar Allah kuma mu yi bimbini a kanta. Idan kana yin hakan, kana yin koyi da misalai masu kyau na annabawa da suka ‘biɗa, suka bincika kuma da himma’ bayanin da aka ba su. Yana da kyau mu lura cewa mala’iku ma sun nuna suna son gaskiya na ruhaniya game da Zuriyar da aka yi alkawarinsa da kuma ikilisiyar Kirista da aka shafa da ruhu.—Karanta 1 Bitrus 1:10-12.
Yaya Ruhun Zai Yi Tasiri a Kanka?
8. Me ya sa yake da muhimmanci ka roƙi Jehobah ya ba ka ruhunsa?
8 Ba wai yin nazarin Nassosi da yin bimbini kawai ba ne ake bukata. Kana bukatan ka ci gaba da roƙon taimakon Jehobah da ja-gorarsa. Zai iya “aikata ƙwarai da gaske gaba da dukan abin da muke roƙo ko tsammani.” (Afis. 3:20; Luk 11:13) Yaya za ka amsa idan wani ya tambaye ka, “Me ya sa zan ci gaba da roƙon Allah idan ya riga ya san ‘abin da nake bukata, tun ban roƙe shi ba’?” (Mat. 6:8) To, dai, ta wajen yin addu’a don samun ruhu mai tsarki, ka amince cewa kana bukatan ka dogara ga Jehobah. Alal misali, idan wani ya zo wajenka yana neman taimako, za ka yi duk abin da za ka iya yi don ka taimake shi, dalili ɗaya don ya gaya maka ka taimaka masa, hakan ya nuna yana da tabbaci a gare ka. (Gwada da Misalai 3:27.) Hakazalika, Jehobah yana jin daɗi idan ka roƙe shi ruhunsa, kuma zai ba ka.—Mis. 15:8.
9. Ta yaya halartan taron Kirista zai taimaka maka ka kasance cikin ja-gorancin ruhun Allah?
9 Za ka yi godiya cewa wata hanya da za ka kasance a ƙarƙashin ja-gorancin ruhun Allah ya ƙunshi tarurrukanmu, manyan tarurruka, da tarurrukan gunduma. Yin ƙoƙari ka halarta kuma ka saurari tsarin ayyukan yana da muhimmanci sosai. Yin hakan zai taimaka maka ka fahimci ‘zurfafan abu na Allah.’ (1 Kor. 2:10) Yin kalami a kai a kai kuma yana da amfani. Ka yi tunanin taron da ka halarta makonni huɗu da suka wuce. Sau nawa ka ɗaga hannunka, ka ba da amsa don ka furta bangaskiyarka? Ka ga inda kake bukatan yin gyara a wannan batu? Idan ka ga wurin, ka tsai da shawarar abin da za ka yi a makonni na gaba. Jehobah zai ga cewa kana son ka yi kalami kuma zai ba ka ruhunsa, wanda zai taimaka maka ka ƙara amfana daga taron da ka halarta.
10. Yin tafiya bisa ga ruhu ya ƙunshi miƙa wace gayyata ga mutane?
10 Yin tafiya bisa ga ruhu ya ƙunshi amsa gayyatar da ke Ru’ya ta Yohanna 22:17: “Ruhu da amarya suna cewa, Zo. Mai ji kuma, bari ya ce, Zo. Mai jin ƙishi kuma, bari ya zo: wanda ya ke so, bari ya ɗiba ruwa na rai kyauta.” Ruhun da ke aiki ta hanyar rukunin amarya shafaffu, yana miƙa wannan gayyatar game da ruwa na rai. Idan ka karɓi wannan gayyatar “zo!” ka ƙuduri aniya ka ce “Zo!”? Gata ne mu sa hannu a wannan aiki na ceton rai!
11, 12. Yaya ruhu mai tsarki yake ba da taimako a wannan aikin wa’azi?
11 Ana cim ma wannan aiki mai muhimmanci yanzu a ƙarƙashin ja-gorancin ruhu mai tsarki. Mun karanta yadda ruhu mai tsarki ya taimaka a ƙarni na farko wajen buɗe sababbin yankuna don masu hidima a ƙasashen waje. “Ruhu mai-tsarki ya hana [manzo Bulus da abokansa] faɗin maganar cikin Asiya” kuma bai ƙyale su su tafi Bitiniya ba. Ba mu san ainihin yadda ruhun ya hana su zuwa waɗannan wuraren ba, amma a bayyane yake cewa ruhun ya yi wa Bulus ja-gora zuwa cikin wurare masu faɗi na Turai. Ya samu wahayi na wani mutumin Makidoniya da yake roƙon taimako.—A. M. 16:6-10.
12 A yau, ruhun Jehobah yana yin ja-gora a aikin wa’azi na dukan duniya. Ba a yin amfani da wahayi na mu’ujiza don a ba da ja-gora; maimako, Jehobah yana yi wa shafaffu ja-gora ta hanyar ruhu mai tsarki. Kuma ruhun yana motsa ’yan’uwa maza da mata su yi iyakar ƙoƙarinsu a wa’azi da koyarwa. Babu shakka kana sa hannu a wannan aikin mai muhimmanci. Za ka iya daɗa farin cikinka a wannan aikin mai ban sha’awa?
13. Yaya za ka iya miƙa kai ga ja-gorancin ruhu mai tsarki? Ka kwatanta.
13 Za ka iya miƙa kai ga ja-gorancin ruhu mai tsarki ta wajen yin amfani da bayanin da aka yi tanadinsa ga mutanen Allah. Ka yi la’akari da matashiya Mihoko daga ƙasar Japan. Da yake ita sabuwar majagaba ce, ta ji cewa ba ta cancanci koma ziyara ba; tana ganin ba ta san yadda za ta yi magana da zai sa maigidan ya so saƙon ba. A daidai wannan lokacin, an yi tanadin shawarwari masu kyau a kan yadda za a koma ziyara a cikin Hidimarmu Ta Mulki. Sa’annan aka wallafa mujallar nan A Satisfying Life—How to Attain It. Ya kasance da amfani sosai a ƙasar Japan. Mihoko ta yi amfani da shawarwarin da aka ba da a kan yadda za a yi amfani da mujallar, musamman yadda za a koma ziyara. Ba da daɗewa ba ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da waɗanda a dā sun ƙi yin nazari. Ta ce, “Na samu mutane da yawa da nake nazari da su, sun kai guda goma sha biyu a wani lokaci, har na gaya wa wasu su jira kafin na soma nazari da su!” Hakika, idan ka yi tafiya bisa ga ruhu, kana amfani da umurnin da aka ba bayin Jehobah, za ka yi girbi mai yawa.
Ka Dogara ga Ruhun Allah
14, 15. (a) Yaya zai yiwu ’yan Adam ajizai su yi rayuwar da ta jitu da keɓe kansu? (b) Yaya za ka samu abokai mafi kyau?
14 A matsayin mai hidima da aka naɗa, kana da hidimar da za ka yi. (Rom. 10:14) Wataƙila za ka ji ba ka cancanci ɗaukan irin wannan hakkin ba. Amma, kamar shafaffu, Allah ne ya sa ka cancanta. (Karanta 2 Korantiyawa 3:5.) Za ka iya yin rayuwar da ta jitu da keɓe kanka ta wajen yin iya ƙoƙarinka kuma ka dogara ga ruhun Allah.
15 Hakika, ba shi da sauƙi mu ajizai mu yi rayuwar da ta jitu da keɓe kanmu ga kamiltaccen Allahnmu, Jehobah. Wata matsala ita ce wasu da kake tarayya da su a dā suna iya yin mamaki game da sabon tafarki na rayuwa da kake bi kuma suna iya ‘aibatanka.’ (1 Bit. 4:4) Duk da haka, kada ka manta cewa ka samu sababbin abokai, waɗanda suka fi muhimmanci su ne Jehobah da Yesu Kristi. (Karanta Yaƙub 2:21-23.) Yana da muhimmanci kuma ka san ’yan’uwa maza da mata da suke cikin ikilisiyarku, sashen “’yan’uwanci” a dukan duniya. (1 Bit. 2:17; Mis. 17:17) Jehobah ta hanyar ruhunsa zai taimaka maka ka samu abokai waɗanda za su ci gaba da zama tasiri mai kyau a gare ka.
16. Kamar Bulus, me ya sa za ka ji “daɗi cikin kumamanci.”
16 Duk da taimakon abokai da suka kewaye ka a cikin ikilisiya, har ila yana iya yi maka wuya ka jimre da kaluɓale na yau da kullum. A wani lokacin, abin da kake jimrewa da shi yana iya sa ka gaji, kamar kana ɗauke da matsaloli masu yawa. A wannan lokacin na musamman ne kake bukatan ka juya ga Jehobah, ka roƙe shi ruhunsa mai tsarki. Manzo Bulus ya rubuta: “Sa’anda ina rashin ƙarfi, sa’annan mai-ƙarfi na ke.” (Karanta 2 Korantiyawa 4:7-10; 12:10.) Bulus ya san cewa ruhun Allah zai daidaita kumamancin ’yan Adam, ko yaya suke. Saboda haka, ikon da Allah yake aiki da shi zai iya ƙarfafa ka a duk lokacin da ka ji ka gaji kuma kana bukatar taimako. Bulus ya rubuta cewa zai iya “jin daɗi cikin kumamanci.” A lokacin da ya gaji ne ya ji cewa ruhu mai tsarki yana aiki a kansa. Kana iya shaida hakan!—Rom. 15:13.
17. Yaya ruhu mai tsarki zai taimaka maka yayin da kake tafiya zuwa inda za ka?
17 Muna bukatar ruhun Allah don mu yi rayuwa na keɓe kanmu a gare shi. Ka ɗauki kanka a matsayin kyaftin na kwalekwale. Makasudinka shi ne ka bauta wa Jehobah har abada. Ruhu mai tsarki yana kama da bin inda iska yake kaɗawa domin ka isa inda za ka lafiya. Ba ka son ruhun duniyar Shaiɗan ya riƙa jujjuya ka. (1 Kor. 2:12) Kana bukatan ka san inda iska yake kaɗawa don ka bi shi. Ruhu mai tsarki ke nan. Ta wurin Kalmar Allah da ikilisiyarsa da ruhu yake yi wa ja-gora, ruhu mai tsarki zai yi maka ja-gora zuwa hanyar da ta dace.
18. Menene ƙudurinka yanzu, kuma me ya sa?
18 Idan kana nazari da Shaidun Jehobah, kana more cuɗanya na ruhaniya da su, amma ba ka ɗauki matakai masu muhimmanci na keɓe kanka da yin baftisma ba, ka tambayi kanka, ‘Me ya sa nake jinkiri?’ Idan ka fahimci hakkin ruhu mai tsarki wajen cika nufin Jehobah a yau kuma kana godiya don aikinsa, sai ka ɗauki matakan da ka koya cewa su ne daidai. Jehobah zai albarkace ka sosai. Zai ba ka ruhunsa mai tsarki a yalwace. Idan ka riga ka yi baftisma shekaru da yawa da suka shige, babu shakka ka shaida taimakon ruhu mai tsarki. Ka gani kuma ka shaida yadda Allah zai iya ƙarfafa ka da ruhunsa. Za ka iya ci gaba da shaida hakan, hakika, har abada. Saboda haka, ka ƙuduri aniya ka ci gaba da tafiya bisa ga ruhu mai tsarki.
Ka Tuna?
• Menene “yin tafiya bisa ga ruhu” yake nufi?
• Menene zai taimaka maka ka ci gaba da “yin tafiya bisa ga ruhu”?
• Yaya za ka yi rayuwar da ta jitu da keɓe kanka?
[Hoton da ke shafi na 15]
Nome zuciyarka yana bukatan ƙoƙari
[Hoton da ke shafi na 16, 17]
Ruhun Allah yana yi maka ja-gora kuwa?