Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 2/15 pp. 10-14
  • Ka Yi Amfani Da “Takobin Ruhu” Daidai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Amfani Da “Takobin Ruhu” Daidai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Kalmar Allah Tana da Iko’
  • Ka Yi Amfani da Shi Yadda Ya Kamata
  • Ka Yi Amfani da Ita da Rinjaya
  • Ka Ci Gaba da Yin Amfani da Ita Daidai
  • Ka ‘Fassara Kalmar Allah Daidai’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ka sa Koyarwarka Ta Kasance Mai Rinjaya
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Kalmar Allah Tana da Iko
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • “Ku Yi Ɗamara Da Dukan Makamai Na Allah”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 2/15 pp. 10-14

Ka Yi Amfani Da “Takobin Ruhu” Daidai

“Ku ɗauki . . . takobin Ruhu, wato maganar Allah.”—AFIS. 6:17.

1, 2. Yaya ya kamata mu aikata ga bukatan ƙarin masu shelar Mulki?

DA YA ga bukata ta ruhaniya na taron, Yesu ya gaya wa almajiransa: “Girbi hakika yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Ku yi addu’a fa ga Ubangijin girbi, shi aiko ma’aikata cikin girbinsa.” Yesu bai tsaya a nan ba. Bayan ya yi waɗannan kalaman, “ya kirawo almajiransa goma sha biyu,” kuma ya aika su wa’azi, ko zagaya na ‘girbi.’ (Mat. 9:35-38; 10:1, 5) Daga baya, Yesu “ya zaɓo waɗansu saba’in, ya aike su biyu biyu” su yi irin wannan aikin.—Luk. 10:1, 2.

2 Ana bukatan ƙarin masu shelar Mulki sosai a yau. Waɗanda suka halarci Tuna Mutuwar Yesu a dukan duniya a shekarar hidima na 2009 sun kai 18,168,323. Hakan ya ɗara adadin Shaidun Jehobah da fiye da miliyan goma. Hakika, gonaki sun isa girbi. (Yoh. 4:34, 35) Saboda haka, ya kamata mu yi addu’a kuma mu yi roƙo don ƙarin masu aiki. Amma yaya za mu aikata cikin jituwa da irin wannan roƙon? Za mu yi hakan ta wajen zama masu hidima da suka ƙware yayin da muka kasance da himma a aikin wa’azin Mulki da almajirantarwa.—Mat. 28:19, 20; Mar. 13:10.

3. Ta yaya ruhun Allah yake da matsayi na musamman wajen taimakon mu mu zama ƙwararrun masu hidima?

3 Talifin da ya gabata ya tattauna yadda ja-gorancin ruhun Allah yake taimaka mana wajen ‘faɗin maganar Allah da ƙarfin zuciya.’ (A. M. 4:31) Wannan ruhun zai taimaka mana mu zama ƙwararrun masu hidima. Hanya ɗaya da za mu kyautata ƙwarewarmu a hidima ita ce ta yin amfani da kyau da kayan aiki mafi kyau da Jehobah Allah ya yi tanadinsa, wato, rubutacciyar Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Ta hanyar ruhu mai tsarki ne aka rubuta shi. (2 Tim. 3:16) Allah ne ya hure saƙon da ke ciki. Saboda haka, sa’ad da muka bayyana gaskiyar da ke cikin Nassi a hanya mai kyau a hidimarmu, ruhu mai tsarki ne yake yi mana ja-gora. Kafin mu bincika yadda za mu iya yin hakan, bari mu yi tunani a kan yadda wannan Kalmar take da iko.

‘Kalmar Allah Tana da Iko’

4. Yaya saƙon Allah da ke cikin Littafi Mai Tsarki zai iya canja mutum?

4 Babu shakka, kalmar Allah ko kuma saƙo, yana da iko! (Ibran. 4:12) A alamance, saƙon da ya fito daga cikin Littafi Mai Tsarki ya fi takobi da ɗan Adam ya yi kaifi, domin a alamance tana ratsa ƙasusuwa da ɓargonsu. Gaskiyar Nassi tana shiga can cikin jikin mutum kuma ta ratsa tunaninsa da motsin ransa, ta fallasa abin da yake a ciki. Wannan gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki tana iya nuna ikonta kuma ta canja mutum. (Karanta Kolosiyawa 3:10.) Hakika, Kalmar Allah tana iya canja rayuka!

5. A waɗanne hanyoyi ne Littafi Mai Tsarki zai yi mana ja-gora, da wane sakamako?

5 Bugu da ƙari, Littafi Mai Tsarki na ɗauke da hikima da babu kamarta. Yana ɗauke da bayanai masu kyau da za su iya nuna wa mutane yadda za su yi rayuwa a wannan rikitacciyar duniya. Kalmar Allah tana haskaka sawayenmu a yanzu da kuma tafarkinmu na nan gaba. (Zab. 119:105) Tana taimakawa sosai sa’ad da muke bi da matsaloli ko kuma sa’ad da muke tsai da shawarwari game da zaɓan abokai, nishaɗi, aiki, tufafi, da sauransu. (Zab. 37:25; Mis. 13:20; Yoh. 15:14; 1 Tim. 2:9) Bin ƙa’idodin da ke cikin Kalmar Allah yana sa mu kasance da dangantaka mai kyau da mutane. (Mat. 7:12; Filib. 2:3, 4) Sa’ad da muka ƙyale kalmar Allah ta haskaka hanyar da ke gabanmu a alamance, za mu iya ganin yadda shawarwarinmu za su shafe mu a nan gaba. (1 Tim. 6:9) Nassosi ya kuma annabta nufin Allah don nan gaba, hakan yana taimaka mana mu biɗi salon rayuwar da ta jitu da wannan nufin. (Mat. 6:33; 1 Yoh. 2:17, 18) Mutum zai iya more rayuwa mai ma’ana idan ya ƙyale ƙa’idodi na Allah su yi masa ja-gora a rayuwa!

6. Yaya Littafi Mai Tsarki ya zama makami mai iko a yaƙinmu na ruhaniya?

6 Littafi Mai Tsarki makami ne kuma mai iko a yaƙinmu na ruhaniya. Bulus ya kira maganar Allah “takobin Ruhu.” (Karanta Afisawa 6:12, 17.) Sa’ad da aka yi amfani da shi da kyau, saƙon Littafi Mai Tsarki zai iya ’yantar da mutane daga bauta ta ruhaniya na Shaiɗan. Takobi ne da ke ceton rai maimakon ya halaka ta. Ya kamata mu yi ƙoƙari mu yi amfani da shi daidai, ko ba haka ba?

Ka Yi Amfani da Shi Yadda Ya Kamata

7. Me ya sa yake da muhimmanci mu koyi yin amfani da “takobin ruhu” da kyau?

7 Soja zai iya yin amfani da makamansa da kyau a yaƙi idan ya gwada kuma ya koyi yadda ake amfani da su da kyau. Hakan yake da yin amfani da “takobin ruhu” a yaƙinmu na ruhaniya. Bulus ya rubuta, “ka himmantu ka miƙa kanka yardajje ga Allah, ma’aikaci wanda ba hanya ya kunyata, mai kuma fassara maganar gaskiya daidai.”—2 Tim. 2:15; Littafi Mai Tsarki.

8, 9. Menene zai taimaka mana mu fahimci abin da Littafi Mai Tsarki ya ce? Ka ba da misali.

8 Menene zai taimaka mana mu ‘fassara maganar gaskiya daidai’ a hidimarmu? Kafin mu koya wa mutane abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar da kyau, muna bukatan mu da kanmu mu fahimce shi sosai. Hakan na bukatan mu mai da hankali ga mahallin ayar ko bayanin da ke cikin littafin. In ji wani ƙamus, “mahallin kalma, jimla, ko rubutu ta ƙunshi kalmomi, jimloli, ko rubutun da suka bayyana kafin ko bayan hakan kuma wadda ta taimaka wajen bayyana ma’anarta dalla-dalla.”

9 Fahimtar bayanin da ke cikin Nassi sosai na bukatan mu duba mahallin bayanin. Furcin Bulus da ke Galatiyawa 5:13 ya kwatanta wannan misalin. Ya rubuta: “Gama ku, ’yan’uwa, domin ɗiyanci aka kira ku; sai dai kada ɗiyanci naku shi zama dalili ga jiki amma ta wurin ƙauna ku zama masu-bauta ma juna.” Wane ’yanci ne Bulus yake maganarsa a nan? Yana magana ne game da ’yanci daga zunubi da mutuwa, daga bautar imanin ƙarya, ko kuma daga wani abu dabam? Mahallin ya nuna cewa Bulus yana maganar ’yancin da ake samu daga ‘fansar mu daga la’anar shari’a.’ (Gal. 3:13, 19-24; 4:1-5) Yana nuni ne ga ’yancin Kiristanci. Waɗanda suke nuna godiya domin wannan ’yancin suna yin hidima ga juna cikin ƙauna. Waɗanda ba sa nuna ƙauna suna yin baƙar magana da faɗa.—Gal. 5:15.

10. Don mu fahimci ma’anar Nassosi daidai, wane irin bayani ne ya kamata mu bincika, kuma yaya za mu samu bayanin?

10 Kalmar nan “mahalli” tana da wata ma’ana. Wata ma’anar kalmar nan “mahalli” ta haɗa da “yanayi.” Don mu fahimci ma’anar nassi da kyau, ya kamata mu yi la’akari da cikakken bayanin, kamar wanda ya rubuta littafin da ke cikin Littafi Mai Tsarki, da lokacin da aka rubuta, da kuma cikin yanayin da aka yi hakan. Yana da muhimmanci kuma mu san abin da ya sa aka rubuta littafin, kuma idan zai yiwu, al’adun mutanen, halayensu da abin da suke so da kuma irin bautar da suke yi.a

11. Me ya sa ya kamata mu mai da hankali sa’ad da muke bayyana nassosi?

11 “Fassara maganar gaskiya daidai” ya wuce bayyana gaskiya na Nassi da kyau kawai. Ya kamata mu mai da hankali kada mu yi amfani da Littafi Mai Tsarki don mu tsoratar da mutane. Ko da yake muna iya yin amfani da Nassosi don mu kāre gaskiya, kamar yadda Yesu ya yi sa’ad da Iblis ya gwada shi, bai kamata mu yi amfani da Littafi Mai Tsarki don mu cusa imanin ga masu sauraronmu ba. (K. Sha 6:16; 8:3; 10:20; Mat. 4:4, 7, 10) Ya kamata mu yi biyayya ga gargaɗin manzo Bitrus: “Cikin zukatanku ku tsarkake Kristi kamar Ubangiji: kullum a shirye kuke ku amsa ma kowane mai-tambayarku dalilin begen da ke cikinku, amma dai da ladabi da tsoro.”—1 Bit. 3:15.

12, 13. Waɗanne abubuwa “masu ƙarfi” ne gaskiyar Kalmar Allah za ta iya rushewa? Ka ba da misali.

12 Idan aka bayyana ta yadda ya kamata, mecece gaskiyar Kalmar Allah za ta cim ma? (Karanta 2 Korantiyawa 10:4, 5.) Gaskiyar Nassi za ta iya rushe abubuwa “masu-ƙarfi,” wato, tana iya fallasa koyarwar ƙarya, ayyuka masu lahani, da kuma falsafar da ke nuna hikima na ’yan Adam ajizai. Muna iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki wajen kawar da duk wani ra’ayoyi da aka “ɗaukaka domin gāba da sanin Allah.” Za a iya yin amfani da koyarwar Littafi Mai Tsarki a taimaki mutane su gyara tunaninsu don ya jitu da gaskiya.

13 Ka yi la’akari da batun wata mata mai shekara casa’in da uku wadda take da zama a ƙasar Indiya. Tun tana ƙarama an koya mata ta yi imani da sake haifan mutumin da ya riga ya mutu a wani wuri. Sa’ad da ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki ta hanyar wasiƙa da ɗanta da ke zama a wata ƙasa yake aika mata, ta yarda da abin da take koya game da Jehobah da alkawuransa. Amma, koyarwar sake haihuwar mutumin da ya riga ya mutu a wani wuri ya kahu a zuciyarta sosai da har ta ƙi yarda da abin da ɗanta ya ce sa’ad da ya rubuta mata game da yanayin matattu. Ta ce: “Na kasa fahimtar gaskiyar Nassosinka. Dukan addinai suna koyar da cewa akwai wani abu a cikinmu da ba ya mutuwa. Tun da daɗewa na yi imani cewa jiki yana mutuwa kuma cewa wani gefe da ba a gani yana komawa cikin wasu jikuna sau da sau har sau 8,400,000. Yaya hakan zai zama ƙarya? Yawancin addinai suna ƙarya ne?” “Takobin ruhu” zai iya rushe irin wannan imani mai ƙarfi kuwa? Bayan ƙarin bayani na Nassi a kan batun, ta rubuta bayan wasu makonni: “A ƙarshe, na soma fahimtar ainihin gaskiya game da mutuwa. Sanin cewa, sa’ad da aka yi tashin matattu, za mu sadu da ƙaunatattunmu da suka mutu yana sa ni farin ciki sosai. Da ma a ce Mulkin Allah ya zo ba da daɗewa ba.”

Ka Yi Amfani da Ita da Rinjaya

14. Menene rinjayar masu sauraronmu yake nufi?

14 Yin amfani da Littafi Mai Tsarki da kyau a hidima ba batun ƙaulin nassosi kawai ba ne. Bulus ya yi magana da “rinjaya,” kuma ya kamata mu yi hakan. (Karanta A. M. 19:8, 9; 28:23.) “Rinjaya” yana nufin a “jawo mutum.” Wanda aka rinjaya “yana da tabbaci sosai cewa hakan zai sa ya gaskata da wani abu.” Sa’ad da muka rinjayi mutum ya amince da koyarwar Littafi Mai Tsarki, muna jawo shi ne ya dogara da wannan koyarwar. Don mu cim ma wannan, muna bukatan mu tabbatar wa mai sauraronmu gaskiyar abin da muka faɗa. Muna iya yin hakan a hanyoyin da ke gaba.

15. Yaya za ka jawo hankali ga Littafi Mai Tsarki a hanyar da za ta sa a daraja shi?

15 Ka jawo hankali ga Kalmar Allah a hanyar da za ta sa a daraja ta. Sa’ad da ka gabatar da nassi, ka mai da hankali ga muhimmancin sanin ra’ayin Allah a kan batun. Bayan ka yi wata tambaya kuma mai gidan ya amsa, kana iya faɗan wani abu kamar haka, ‘Bari mu ga yadda za mu san ra’ayin Allah a kan wannan batun.’ Ko kuma kana iya yin tambaya, ‘Menene Allah ya faɗa game da wannan yanayin?’ Gabatar da ayar a wannan hanyar yana nuna cewa Littafi Mai Tsarki ya fito ne daga wurin Allah kuma yana sa masu sauraro su daraja shi sosai. Yin hakan yana da muhimmanci sosai sa’ad da muke yin wa’azi ga wanda ya yi imani da Allah amma bai san abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar ba.—Zab. 19:7-10.

16. Menene zai taimaka maka ka bayyana nassosi da kyau?

16 Kada ka karanta nassosi kawai amma ka bayyana su. Al’adar Bulus ne ya yi ‘bayani kuma ya tabbatar’ da abubuwan da ya koyar. (A. M. 17:3) Aya ta Nassi sau da yawa tana ɗauke da fiye da darassi guda, kuma kana iya ka nanata furci masu muhimmanci da suka shafi abin da kake tattaunawa. Kana iya yin hakan ta wajen maimaita kalamai da ke ɗauke da darussa masu muhimmanci ko kuma yin tambayoyi da za su taimaka wa maigida ya fahimce su. Sai, ka bayyana ma’anar wannan nassin. Bayan ka yi hakan, ka taimaka wa mai sauraronka ya ga yadda ayar ta shafe shi.

17. Ta yaya za ka tattauna da wani daga Nassosi a yadda zai gaskata?

17 Ka tattauna da mutane daga cikin Nassosi a hanyar da za ta gamsar da su. Ta wajen yin amfani da roƙo da tabbatarwa, Bulus ya yi ‘mahawara da wasu daga cikin littattafai.’ (A. M. 17:2, 4) Kamar shi, ka yi ƙoƙari ka motsa zuciyar mai sauraronka. Ka “jawo” abin da ke cikin zuciyar ta wajen yin amfani da tambayoyi da ke nuna cewa ka damu da mutumin. (Mis. 20:5) Ka guji yin magana da raini. Ka gabatar da bayanin a hanyar da ta fita sarai da kuma cikin basira. Ya kamata ka tallafa musu ta wajen ba da shaida mai gamsarwa. Ya kamata furcinka ya kasance bisa Kalmar Allah. Ya fi kyau ka yi amfani da nassi ɗaya da kyau ta wajen ba da bayani da kuma kwatanta darasin maimakon ka karanta nassosi biyu ko kuma uku ba tare da ba da wani bayani a kansu ba. Yin amfani da ƙarin tabbaci zai ƙara wa ‘leɓunanka sani.’ (Mis. 16:23) A wasu lokatai, zai dace mu yi bincike kuma mu ba da ƙarin bayani. Mata mai shekara casa’in da uku da aka ambata ɗazu tana bukatar ta san abin da ya sa ake koyar da kurwa marar mutuwa (ko ruhu) a ko’ina. Fahimtar tushen koyarwar da kuma yadda yawancin addinai na duniya suka yi imani da koyarwar yana da muhimmanci don a rinjaye ta ta amince da abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar a kan batun.b

Ka Ci Gaba da Yin Amfani da Ita Daidai

18, 19. Me ya sa za mu ci gaba da yin amfani da “takobin ruhu” daidai?

18 “Ƙa’idar duniyan nan tana shuɗewa,” in ji Littafi Mai Tsarki. Miyagun mutane suna daɗa mugunta gaba gaba. (1 Kor. 7:31; 2 Tim. 3:13) Saboda haka yana da muhimmanci mu ci gaba da rushe abubuwa “masu-ƙarfi” ta wajen yin amfani da “takobin ruhu, wato, maganar Allah.”

19 Mu masu farin ciki ne da yake muna da Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, kuma muna amfani da saƙonsa mai iko don mu tuge koyarwar ƙarya kuma mu kai ga masu zuciyar kirki! Babu abu mai ƙarfi da ya fi wannan saƙon. Saboda haka, bari mu yi iyakar ƙoƙarinmu mu yi amfani da “takobin ruhu” daidai a aikin shelar Mulki da Allahnmu ya ba mu.

[Hasiya]

a Littattafan da za su taimaka sosai wajen samun bayani game da littattafan Littafi Mai Tsarki su ne All Scripture Is Inspired of God and Beneficial,” Insight on the Scriptures da talifofi kamar “Maganar Jehobah Rayayya Ce,” a cikin Hasumiyar Tsaro.

b Ka duba mujallar nan Minene Yakan Faru Mana Sa’anda Muka Mutu? shafuffuka na 5-16.

Menene Ka Koya?

• Yaya Kalmar Allah take da iko?

• Ta yaya za mu “fassara maganar gaskiya daidai”?

• Menene saƙon Littafi Mai Tsarki zai cim ma a batun abubuwa “masu-ƙarfi”?

• Yaya za ka kyautata rinjayarka a hidima?

[Akwati/Hoton da ke shafi na 12]

Yadda Za Mu Yi Amfani da Kalmar Allah da Rinjaya

▪ Ka sa a daraja Littafi Mai Tsarki

▪ Ka bayyana Nassosin

▪ Ka tattauna da tabbaci don ka motsa zuciyar mutane

[Hoton da ke shafi na 11]

Dole ka koyi yin amfani da “takobin Ruhu” da kyau

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba