Ka sa Koyarwarka Ta Kasance Mai Rinjaya
1. A yawancin lokaci, menene yin amfani da Kalmar Allah sosai a hidimarmu ya ƙunsa?
1 Ƙwararrun masu wa’azi, kamar manzo Bulus, sun fahimci cewa “rarrabe kalmar gaskiya sosai” ya ƙunshi fiye da yin ƙaulin Nassosi Masu Tsarki kawai. (2 Tim. 2:15) Sa’ad da muke yin amfani da Kalmar Allah, ta yaya za mu iya yin amfani da “rinjaya” a koyarwarmu?—A. M. 28:23.
2. Ta yaya za mu iya sa a ƙara daraja Kalmar Allah?
2 Ka Nuna Abin da Kalmar Allah Ta Ce: Na farko, ka jawo hankali ga Littafi Mai Tsarki yadda zai sa a daraja hikimar Allah da ke cikinsa. Gaba gaɗinmu ga Kalmar Allah zai iya motsa mai sauraronmu ya mai da hankali sosai ga nassin da za mu karanta. (Ibran. 4:12) Za mu iya cewa: “Na fahimci cewa yana da amfani mu san ra’ayin Allah game da wannan batun. Ka lura da abin da Kalmarsa ta ce.” A duk lokacin da ya yiwu, ka sa Kalmar Allah ta yi magana ta wajen karantata kai tsaye.
3. Bayan ka karanta nassi, menene za ka iya yi don taimaka wa mai sauraro ya fahimci ma’anar?
3 Na biyu, ka bayyana nassin da ka karanta. Yana yi wa mutane da yawa wuya su fahimci aya sa’ad da aka karanta ta da farko. Saboda haka, muna bukatan mu bayyana muhimmancinta. (Luk 24:26, 27) Ka fito da muhimman bayanan. Yin tambaya zai taimaka wajen tabbatar da cewa an fahimci bayanin sosai.—Mis. 20:5; A. M. 8:30.
4. Wane mataki na ƙarshe ne ake bukata don yin rinjaya a koyarwarmu?
4 Tattauna Nassosi: Na uku, ka yi ƙoƙarin taɓa tunani da zuciya. Ka taimaka wa maigida ya ga yadda ayar ta shafe shi. Tattauna Nassosin zai iya motsa mutum ya canja tunaninsa. (A. M. 17:2-4; 19:8) Alal misali, bayan mun karanta Zabura 83:18 za mu iya bayyana yadda koyon sunan wani yake da muhimmanci wajen ƙulla dangantaka da shi. Bayan haka, kana iya tambayarsa, “Kana jin cewa sanin sunan Allah zai ƙara kyautata addu’arka kuwa?” Nuna yadda nassin ya shafi rayuwar maigidan a wannan hanyar zai nuna amfaninsa. Irin wannan koyarwa da rinjaya daga Kalmar Allah yana jawo masu zukatan kirki su bauta wa Allah mai gaskiya kuma mai rai, Jehobah.—Irm. 10:10.