Yesu Kristi Yadda Saƙonsa Ya Shafi Mutane
“Hakika abu mafi tabbaci game da wannan Yesu mai hikima daga Kafarnahum shi ne ya ci gaba da taɓa zukatan da tunanin mutane da kalamansa.”a—AUTHOR GREGG EASTERBROOK.
KALAMANSA suna da iko. Kalaman hikima wanda aka zaɓa sosai za su iya motsa zukata, ba da bege, da kuma canja rayuka. Babu mutum da ya taɓa samun ikon yin magana kamar Yesu Kristi. Mutumin da ya saurari Yesu sa’ad da ya ba da sanannen Huɗuba a kan Dutse ya rubuta daga baya: “Ananan sa’anda Yesu ya gama waɗannan zantattuka, taron mutane suka yi mamaki da koyarwansa.”—Matta 7:28.
Har yau, mutane da yawa a dukan duniya sun san kalaman Yesu da yawa. Ka yi la’akari da wasu kalamai da suke cike da ma’ana.
“Ba ku da iko ku bauta wa Allah da dukiya.”—Matta 6:24.
“Dukan abu fa iyakar abin da ku ke so mutane su yi maku, ku yi musu hakanan kuma.”—Matta 7:12.
“Ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar; Allah kuma abin da ke na Allah.”—Matta 22:21.
“Bayarwa ta fi karɓa albarka.”—Ayyukan Manzanni 20:35.
Amma abubuwan da Yesu ya yi sun fi kalamai kawai. Wa’azin da ya yi yana da iko sosai domin yana ɗauke da gaskiya game da Allah, ya koyar da mutane yadda za su samu ainihi ma’ana a rayuwa, kuma ya nuna ainihi sauƙi ga dukan wahalar ’yan Adam, wato, Mulkin Allah. Yayin da muke tattauna wannan saƙon a shafofi na gaba, za mu ga dalilai da suka sa Yesu ya ci gaba da taɓa “zukata da tunanin” miliyoyin mutane da kalamansa.
[Hasiya]
a An ɗauki Kafarnahum a matsayin birnin da Yesu yake da zama a gundumar Galili.—Markus 2:1.