Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 6/15 pp. 9-14
  • Ku Ci Gaba Da Ƙarfafa Ikilisiya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Ci Gaba Da Ƙarfafa Ikilisiya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Suka Ɗauke Shi”
  • “Suna Shaidarsa”
  • “Ku Ƙarfafa Masu-Raunanan Zukata”
  • “Ku Gafarta Masa Ku Yi Masa Ta’aziya”
  • “Yana da Amfani Gare Ni”
  • Da Kai da Ikilisiya
  • Kiristoci Suna Bukatar Juna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ka Yi Wa’azi Da Nufin Almajirantarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • “Ku Yi Ta Gina Juna”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • “Dana Cikin Ubangiji, Kaunatacce, Mai-Aminci.”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 6/15 pp. 9-14

Ku Ci Gaba Da Ƙarfafa Ikilisiya

“Ku yi ma junanku ta’aziya, ku gina juna.”—1 TAS. 5:11.

1. Waɗanne albarka ne ake samu ta wajen kasancewa cikin ikilisiyar Kirista, amma waɗanne matsaloli ne har ila za a iya fuskanta?

KASANCEWA cikin ikilisiyar Kirista albarka ne mai girma. Kana da dangantaka mai kyau da Jehobah. Dogarar da ka yi ga Kalmarsa a matsayin abin ja-gora yana kāre ka daga mugun sakamakon salon rayuwa da ba na Kirista ba. Abokai na ƙwarai da suke son ka yi abin da yake da kyau sun kewaye ka. Hakika, albarkar tana da yawa. Amma, yawancin Kiristoci suna fama da matsaloli dabam-dabam. Wataƙila wasu a cikinsu suna bukatan taimako don su fahimci abubuwa masu zurfi na Kalmar Allah. Wasu suna rashin lafiya ko baƙin ciki, ko kuma suna shan wahalar sakamakon wasu shawarwari marar kyau da suka yanke. Kuma dukanmu muna zama a duniyar da ba ta bin Allah.

2. Menene ya kamata mu yi sa’ad da ’yan’uwanmu suke fuskantar matsaloli, kuma me ya sa?

2 Babu wani cikinmu da yake son ganin ’yan’uwa Kiristoci suna shan wahala ko fama. Manzo Bulus ya kamanta ikilisiya da jiki kuma ya ce “idan gaɓa ɗaya kuwa ya sha raɗaɗi, dukan gaɓaɓuwa suna shan raɗaɗi tare da shi.” (1 Kor. 12:12, 26) A irin wannan yanayin, ya kamata mu yi ƙoƙari mu tallafa wa ’yan’uwanmu maza da mata. Da akwai labarai masu yawa da ke cikin Nassi na waɗanda suke cikin ikilisiya da suka taimaka wa wasu su bi da ƙalubalensu kuma su sha kansu. Yayin da muke bincika waɗannan labaran, ka yi tunanin yadda za ka ba da taimako a irin hanyoyi da aka kwatanta. Ta yaya za ka taimaka wa ’yan’uwanka a ruhaniya kuma ka ƙarfafa ikilisiyar Jehobah?

“Suka Ɗauke Shi”

3, 4. A wace hanya ce Akila da Biriskilla suka taimaka wa Afolos?

3 Sa’ad da Afolos ya soma zama a Afisa, ya riga ya zama mai wa’azin bishara da himma. “Domin yana da zafin himma a ruhu,” in ji labarin Ayyukan Manzanni, “ya yi ta zance, yana koyarwa da zancen Yesu bisa ga hankali, baftismar Yohanna kaɗai ya ke sane da ita.” Rashin sanin baftisma da Afolos ya yi “cikin sunan Uba da na Ɗa da na ruhu mai-tsarki” wataƙila yana nufin cewa almajiran Yohanna Mai Baftisma ko kuma mabiyan Yesu sun yi masa wa’azi kafin Fentakos na shekara ta 33 A.Z. Ko da yake Afolos yana da himma, da akwai batutuwa masu muhimmanci da bai fahimta ba. Ta yaya yin cuɗanya da ’yan’uwa masu bi ya taimaka masa?—A. M. 1:4, 5; 18:25; Mat. 28:19.

4 Sa’ad da ma’aurata Kirista, Akila da Biriskilla suka ji Afolos yana magana da gaba gaɗi a cikin majami’a, suka ɗauke shi kuma suka ƙara koyar da shi. (Karanta A. M. 18:24-26.) Abin da suka yi yana da kyau. Hakika, Akila da Biriskilla sun tuntuɓi Afolos cikin basira da halin taimakawa, ba su sa ya ji kamar ana sūkarsa ba. Ba shi da cikakken sani game da somawar ikilisiyar Kirista. Kuma babu shakka, Afolos ya yi godiya ga sababbin abokansa da suka koya masa waɗannan bayanai masu muhimmanci. Sa’ad da ya samu wannan bayanin, sai Afolos ya yi wa ’yan’uwansa da ke Akaya “taimako da yawa” kuma ya ba da shaida ƙwarai.—A. M. 18:27, 28.

5. Wane taimako ne dubban masu shelar Mulki suke ba da wa, da wane sakamako?

5 Mutane da yawa da suke cikin ikilisiyar Kirista a yau suna godiya sosai ga waɗanda suka taimaka musu su fahimci Littafi Mai Tsarki. Ɗalibai da waɗanda suka koyar da su sun ƙulla abota da ya jure. A yawancin lokaci, taimaka wa mutane su fahimci gaskiya yana bukatan tattaunawa da su a kai a kai har tsawon watanni da yawa. Amma, masu shelar Mulki suna shirye su yi wannan sadaukarwar ne domin sun fahimci cewa batun ya shafi rayuwar mutane. (Yoh. 17:3) Abin farin ciki ne a ga cewa mutane sun fahimci gaskiya, suna rayuwa da ta jitu da ita, kuma suna amfani da rayuwarsu don su yi nufin Jehobah!

“Suna Shaidarsa”

6, 7. (a) Me ya sa Bulus ya zaɓi Timotawus ya zama abokin tafiyarsa? (b) Wane ci gaba ne aka taimaka wa Timotawus ya yi?

6 Sa’ad da manzanni Bulus da Sila suka ziyarci Listra a lokacin tafiyarsu ta wa’azi ta biyu, sun sadu da wani matashi mai suna Timotawus a wajen, wataƙila sa’ad da yake gab da shekara ashirin ko a farkon shekararsa ta ashirin. “’Yan’uwa da ke cikin Listra da Ikoniya suna shaidarsa.” Mahaifiyar Timotawus, Afiniki, da kakarsa, Lois, Kiristoci ne da suka keɓe kansu, amma babansa marar bi ne. (2 Tim. 1:5) Mai yiwuwa Bulus ya san wannan iyalin a ziyararsa ta farko zuwa wurin ’yan shekaru da suka shige. Amma yanzu manzon ya mai da hankali musamman ga Timotawus domin shi matashi ne da ya yi fice. Saboda haka, da amincewar rukunin dattawan ikilisiya, Timotawus ya zama mataimakin Bulus a aikin wa’azi a ƙasar waje.—Karanta A. M. 16:1-3.

7 Timotawus yana da abubuwa da yawa da zai koya daga abokinsa dattijo. Ya yi koyin sosai, wanda hakan ya sa bayan wani lokaci, Bulus da gaba gaɗi ya aika Timotawus ya ziyarci ikilisiyoyi kuma ya zama wakilinsa. A cikin shekaru goma sha biyar da Timotawus ya more cuɗanya da Bulus, matashin da bai ƙware ba kuma wataƙila mai jin kunya ya samu ci gaba har ya kai ga zama mai kula fitacce.—Filib. 2:19-22; 1 Tim. 1:3.

8, 9. Menene waɗanda suke cikin ikilisiya za su iya yi don su ƙarfafa matasa? Ka ba da misali.

8 Matasa da yawa maza da mata a cikin ikilisiyar Kirista a yau suna da iyawa sosai. Idan abokai masu ruhaniya suka kula da su kuma suka ƙarfafa su, waɗannan matasan suna iya ƙoƙartawa sosai kuma su biɗi hakkoki masu girma a cikin mutanen Jehobah. Ka duba ikilisiyarku! Ka ga matasa waɗanda za su iya ba da kansu, kamar yadda Timotawus ya yi? Idan ka taimaka musu kuma ka ƙarfafa su, suna iya zama majagaba, masu hidima a Bethel, masu wa’azi a ƙasashen waje, ko kuma masu kula masu ziyara. Menene za ka iya yi don ka taimaka musu su cim ma waɗannan makasudan?

9 Martin, wanda yanzu ya yi shekara ashirin yana hidima a Bethel, cikin godiya, ya tuna yadda wani mai kula da da’ira ya mai da masa hankali shekara talatin da ta shige sa’ad da su biyun suka fita hidimar fage tare. Mai kula da da’irar ya yi magana da himma game da hidimarsa a Bethel sa’ad da yake matashi. Ya ƙarfafa Martin ya yi tunani game da ba da kansa ga ƙungiyar Jehobah a wannan hanya. Martin yana jin cewa wannan tattaunawar da ba zai taɓa mantawa ba ita ce ta shafi zaɓin da ya yi daga baya. Wa ya sani, kana iya motsa abokai matasa ta wajen tattaunawa da su game da makasudai na ruhaniya.

“Ku Ƙarfafa Masu-Raunanan Zukata”

10. Yaya Abafroditus ya ji, kuma me ya sa?

10 Abafroditus ya yi tafiya mai nisa kuma mai gajiyarwa daga Fillibi zuwa Roma don ya ziyarci manzo Bulus, wanda aka saka a kurkuku don bangaskiyarsa. Wannan matafiyi wakili ne na Filibiyawa. Ya ɗauki kyautarsu zuwa ga manzon kuma ya yi shirin kasancewa tare da shi ya yi duk abin da zai iya don ya taimaka wa Bulus a yanayinsa mai wuya. Amma, sa’ad da yake Roma, Abafroditus ya yi rashin lafiyar da “saura kaɗan ya mutu.” Ganin cewa ya kasa cim ma aikinsa, Abafroditus ya yi baƙin ciki.—Filib. 2:25-27.

11. (a) Me ya sa ba za mu yi mamaki ba idan wasu a cikin ikilisiya suka yi baƙin ciki? (b) Menene Bulus ya ce a yi wa Abafroditus?

11 Matsaloli dabam-dabam suna sa mutane su yi baƙin ciki a yau. Ƙididdigar da aka samu daga Ƙungiyar Lafiya ta Duniya ya nuna cewa mutum ɗaya cikin biyar yana iya yin fama da baƙin ciki a wani lokaci na rayuwarsa. Mutanen Jehobah ma suna baƙin ciki. Matsalolin yin tanadi ga iyali, rashin lafiya, sanyin gwiwa don kasawa, ko kuma wasu abubuwa suna iya sa mutum ya yi sanyin gwiwa. Menene Filibiyawa za su iya yi don su taimaka wa Abafroditus? Bulus ya rubuta: “Ku karɓe shi da matuƙar farin ciki saboda Ubangiji, ku kuma girmama irin waɗannan mutane, domin ya kusa ya mutu saboda aikin Almasihu, yana sai da ransa domin ya cikasa ɗawainiyarku gare ni.”—Filib. 2:29, 30, Littafi Mai Tsarki.

12. Menene zai iya zama abin ƙarfafa ga masu raunanan zukata?

12 Ya kamata mu ma mu ƙarfafa ’yan’uwa da suke sanyin gwiwa ko kuma baƙin ciki. Babu shakka, da akwai abubuwa masu kyau da za mu iya faɗa game da hidimarsu ga Jehobah. Wataƙila sun yi canje-canje da yawa a rayuwarsu domin su zama Kiristoci ko kuma su yi hidima na cikakken lokaci. Muna godiya don ƙoƙarce-ƙoƙarcensu, kuma muna tabbatar musu cewa Jehobah ma yana godiya don ƙoƙarinsu. Idan tsufa ko rashin lafiya ya hana wasu masu aminci yin dukan abubuwan da suke yi a dā, sun cancanci mu daraja su don shekarunsu na hidima. Ko yaya yanayinsu yake, shawarar Jehobah ga dukan masu aminci a gare shi ita ce: “Ku ƙarfafa masu-raunanan zukata, ku tokare marasa-ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa.”—1 Tas. 5:14.

“Ku Gafarta Masa Ku Yi Masa Ta’aziya”

13, 14. (a) Wane mataki mai tsanani ne ikilisiyar Koranti ta ɗauka, kuma me ya sa? (b) Menene sakamakon yankan zumuncin?

13 Ikilisiyar Koranti na ƙarni na farko ta fuskanci yanayi na mutumin da ya ci gaba da yin fasikanci. Halinsa yana yi wa tsabtar ikilisiyar zagon ƙasa kuma abin ban kunya ne har a tsakanin waɗanda ba masu bi ba ne. Saboda haka, Bulus ya ba da umurnin da ya dace cewa a cire mutumin daga cikin ikilisiya.—1 Kor. 5:1, 7, 11-13.

14 Wannan horon ya kawo sakamako mai kyau. An kāre ikilisiyar daga tasiri marar kyau, kuma mai zunubin ya amince da zunubinsa kuma ya tuba da dukan zuciyarsa. Domin mutumin ya nuna ayyukan tuba da suka dace, Bulus ya nuna a wasiƙarsa ta biyu zuwa ga ikilisiyar cewa a dawo da mutumin. Amma, ba wannan kaɗai ake bukata ba. Bulus ya kuma ba da umurni ga ikilisiyar cewa “ku gafarta masa, ku yi masa [mai zunubi da ya tuba] ta’aziya kuwa, kada ya zama da ko ƙaƙa irin wannan shi dulmaya domin yawan baƙincikinsa.”—Karanta 2 Korantiyawa 2:5-8.

15. Yaya ya kamata mu ɗauki masu zunubi da suka tuba da aka dawo da su a ikilisiya?

15 Menene muka koya daga wannan labarin? Muna baƙin ciki sa’ad da aka yi wa mutane yankan zumunci. Yana yiwuwa cewa sun kunyata sunan Allah kuma sun ɓata sunan ikilisiyar. Wataƙila ma sun yi mana zunubi. Duk da haka, sa’ad da dattawan da aka naɗa su bincika batun, bisa ga ja-gorar Jehobah, suka ga cewa ya kamata a dawo da mai zunubin ga ikilisiyar, hakan ya nuna cewa Jehobah ya gafarta masa. (Mat. 18:17-20) Bai kamata ba ne mu yi koyi da shi ba? Hakika, kasancewa marar tausayi kuma marar gafartawa yana nufin yin hamayya da Jehobah. Domin mu daɗa ga salama da haɗin da ke ikilisiyar Allah kuma mu samu amincewar Jehobah, ya kamata mu tabbatar da ‘ƙaunarmu’ ga masu zunubi da suka tuba da gaske kuma aka dawo da su, ko ba haka ba?—Mat. 6:14, 15; Luk 15:7.

“Yana da Amfani Gare Ni”

16. Me ya sa Bulus ya yi fushi da Markus?

16 Wani labari kuma da ke cikin Nassi ya nuna cewa bai kamata mu riƙe waɗanda suka yi mana laifi a zuciya ba. Alal misali, Yohanna Markus ya ɓata wa manzo Bulus rai sosai. Yaya? Sa’ad da Bulus da Barnaba suka soma tafiyarsu ta farko na wa’azi, Markus ya bi su don ya taimaka musu. Amma, a wani lokaci a cikin tafiyarsu kuma don dalilin da ba a ambata ba, Yohanna Markus ya bar abokansa kuma ya koma gida. Bulus ya yi fushi sosai game da wannan shawarar kuma sa’ad da suke shiri don tafiya ta biyu, ya samu saɓani da Barnaba game da ko ya kamata Markus ya sake bin su. Domin abin da ya faru a tafiyarsu ta farko, Bulus ba ya son Markus ya yi tafiya tare da su.—Karanta A. M. 13:1-5, 13; 15:37, 38.

17, 18. Yaya muka san cewa Bulus da Markus sun magance matsalar da ke tsakaninsu, kuma menene za mu iya koya daga wannan?

17 Hakika, Markus bai ƙyale ƙin da Bulus ya nuna masa ya sa shi sanyin gwiwa ba, gama ya ci gaba da aikinsa na wa’azi a ƙasar waje a wani yankin tare da Barnaba. (A. M. 15:39) Abin da Bulus ya rubuta game da shi shekaru da yawa bayan hakan ya nuna cewa ya kasance da aminci. Bulus, da yanzu yake kurkuku a Roma, ta hanyar wasiƙa ya aika a kira Timotawus. Kuma a cikin wasiƙar, Bulus ya ce: “Ka ɗauko Markus, ka kawo shi tare da kai: gama yana da amfani gare ni wajen hidima.” (2 Tim. 4:11) Hakika, Bulus yanzu ya gaskata cewa Markus ya samu ci gaba.

18 Da akwai darassi da za mu koya daga wannan. Markus ya koyi halaye na ƙwararren mai wa’azi a ƙasashen waje. Bai yi sanyin gwiwa ba don Bulus ya ƙi shi da farko. Da shi da Bulus maza ne masu ruhaniya, kuma ba su ci gaba da nuna wa juna ƙiyayya ba. Akasin haka, Bulus daga baya ya amince da Markus a matsayin mataimaki mai amfani. Saboda haka, sa’ad da ’yan’uwa suka sha kan matsaloli, abin da ya dace su yi shi ne su ci gaba da taimaka wa mutane su samu ci gaba a ruhaniya. Mai da hankali ga halaye masu kyau na wasu yana ƙarfafa ikilisiya.

Da Kai da Ikilisiya

19. Wane taimako ne dukan waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista za su yi wa juna?

19 A waɗannan “miyagun zamanu,” kana bukatan taimakon ’yan’uwanka maza da mata a cikin ikilisiya, kuma suna bukatar naka. (2 Tim. 3:1) Ba a koyaushe ba ne Kiristoci suke sanin abin da za su yi don su bi da irin yanayin da suke fuskanta, amma Jehobah ya sani. Kuma yana iya yin amfani da mutane dabam-dabam a cikin ikilisiya, har da kai, don ya taimaka wa mutane su bi tafarkin da ya dace. (Isha. 30:20, 21; 32:1, 2) Saboda haka, ko ta yaya, ka bi shawarar manzo Bulus! Ku ci gaba da “yi ma junanku ta’aziya, ku gina juna, kamar yadda ku ke yi fa.”—1 Tas. 5:11.

Yaya Za Ka Amsa?

• Menene muka koya daga labarin marubucin Zabura ta 73?

• Menene abin da ya samu Dinah ya koya mana?

• Me ya sa za mu samu kāriya a cikin ikilisiyar Kirista?

• Me ya sa muke bukatan taimakon wasu a cikin ikilisiyarmu?

[Hoton da ke shafi na 11]

Sa’ad da ɗan’uwa Kirista yake fama da wani yanayi mai wuya muna iya ba da taimako

[Hoton da ke shafi na 12]

Matasa da yawa maza da mata a cikin ikilisiyar Kirista a yau suna da iyawa sosai

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba