Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 12/1 pp. 14-19
  • Ka Yi Wa’azi Da Nufin Almajirantarwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Wa’azi Da Nufin Almajirantarwa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Mai da Hankali ga Bukatun Mutane
  • Ka Koya Daga Misalin Wasu Masu Koyarwa
  • Ka Nemi Zarafi na Almajirantarwa
  • Ka Ci Gaba da Neman Waɗanda Suka Cancanta
  • Kiristoci Suna Bukatar Juna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ku Ci Gaba Da Ƙarfafa Ikilisiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ka Amfana Sosai Daga Karatun Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Kada Ku Yi Gasa da Juna, Ku Bidi Zaman Lafiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 12/1 pp. 14-19

Ka Yi Wa’azi Da Nufin Almajirantarwa

“Sa’anda Biriskilla da Akila suka ji [Afolos], suka ɗauke shi, suka ƙara buɗe masa tafarkin Allah sosai.”—AYUKAN MANZANNI 18:26.

1. Ko da “yana da zafin himma,” menene Afolos yake bukata?

BIRISKILLA da Akila, ma’aurata Kirista na ƙarni na farko, sun lura cewa Afolos yana magana a majami’ar birnin Afisus. Da yake ya ƙware wajen magana kuma yana da ikon rinjaya, Afolos ya jawo hankalin masu sauraronsa. “Yana da zafin himma,” kuma “yana koyarwa da zancen Yesu bisa ga hankali.” Amma, a bayyane yake cewa Afolos “baftismar Yohanna kaɗai ya ke sane da ita.” Abin da Afolos ya koyar game da Kristi gaskiya ne amma iyakar yadda ya sani ke nan. Ba shi da cikakken sani game da Kristi. Afolos yana bukatar ya ƙara saninsa game da matsayin Yesu Kristi wajen cikar nufin Jehovah.—Ayukan Manzanni 18:24-26.

2. Wane aiki mai wuya Biriskilla da Akila suka yarda su yi?

2 Ba da ɓata lokaci ba, Biriskilla da Akila suka ba da kansu su taimaki Afolos ya zama wanda zai iya kiyaye “dukan iyakar” abin da Kristi ya umurta. (Matta 28:19, 20) Labarin ya ce suka jawo Afolos kusa “suka ƙara buɗe masa tafarkin Allah sosai.” Amma, da akwai wasu abubuwa game da Afolos da zai sa wasu Kiristoci su yi jinkirin koyar da shi. Waɗanne abubuwa ne? Me za mu iya koya daga ƙoƙarin da Biriskilla da Akila suka yi su tattauna Nassosi da Afolos? Ta yaya maimaita wannan labarin zai taimake mu mu mai da hankali ga soma nazarin Littafi Mai Tsarki na gida?

Ka Mai da Hankali ga Bukatun Mutane

3. Me ya sa inda Afolos ya fito bai hana Biriskilla da Akila su koyar da shi ba?

3 Da yake shi Bayahude ne, a bayyane yake cewa Afolos ya yi girma a birnin Iskandariya. Iskandariya babban birnin Masar ne a lokacin kuma cibiyar manyan makarantu ne, an san ta da babban laburare. Akwai Yahudawa da yawa a birnin, har da masana. Shi ya sa, aka buga juyin Helenanci na Nassosin Ibrananci da ake kira Septuagint a wajen. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne da Afolos “mai-iko ne a cikin littattafai”! Akila da Biriskilla maɗinkan tanti ne. Sun ji ba su cancanta ba ne su taimaki Afolos saboda ya ƙware wajen magana? A’a. Domin suna ƙaunarsa, suka yi tunanin bukatunsa, da yadda za su taimake shi.

4. Daga ina kuma ta yaya Afolos ya sami taimako da yake bukata?

4 Ko da yaya Afolos ya ƙware wajen magana, ya bukaci ja-gora. Ba za a sami taimako da yake bukata daga wata jami’a ba amma an samu tsakanin ’yan’uwa da suke cikin ikilisiyar Kirista. Afolos zai amfana daga darussa da zai sa ya ƙara fahimta tsarin Allah don ceto. Biriskilla da Akila “suka ɗauke shi, suka ƙara buɗe masa tafarkin Allah sosai.”

5. Me za ka ce game da ruhaniyar Biriskilla da Akila?

5 Biriskilla da Akila masu ruhaniya ne kuma sun kahu sosai cikin bangaskiya. Babu shakka, a ‘shirye suke su amsa ma kowane mai-tambayansu dalilin begen da ke cikinsu,’ ko mai arziki ne, matalauci, masani, ko kuma bawa. (1 Bitrus 3:15) Akila da matarsa sun ‘fassara kalmar gaskiya daidai.’ (2 Timothawus 2:15) Hakika, ɗaliban Nassosi ne masu himma. Koyarwa da ke bisa ‘maganar Allah da mai-rai ce, mai aikatawa,’ ta motsa Afolos sosai kuma ya shafi zuciyarsa.—Ibraniyawa 4:12.

6. Yaya muka sani cewa Afolos ya yi godiya da taimako da ya samu?

6 Afolos ya yi godiya ga misalin masu koyarwarsa kuma ya ƙara gwaninta wajen almajirantarwa. Ya yi amfani da iliminsa sosai a aikin shelar bishara, musamman tsakanin Yahudawa. Afolos yana da amfani ƙwarai wajen rinjayar Yahudawa game da Kristi. Da yake ‘ya san Nassosi ƙwarai da gaske,’ ya tabbatar musu cewa dukan annabawa na dā sun saurari zuwan Kristi. (Ayukan Manzanni 18:24) Labarin ya daɗa cewa Afolos sai ya tafi Akaya inda “ya isa ya yi taimako dayawa ga waɗanda suka bada gaskiya ta wurin alheri, gama da ƙarfi ya kayarda Yahudawa, a sarari kuwa, yana bayyanawa daga cikin littattafai Yesu Kristi ne.”—Ayukan Manzanni 18:27, 28.

Ka Koya Daga Misalin Wasu Masu Koyarwa

7. Ta yaya Akila da Biriskilla suka zama masu koyarwa da suka ƙware?

7 Ta yaya Akila da Biriskilla suka zama masu koyar da Kalmar Allah da suka ƙware? Ban da ƙwazonsu a nazari na kansu da halartan taro, tarayyarsu ta kurkusa da manzo Bulus ya taimake su sosai. Bulus ya zauna a gidan su Biriskilla da Akila watanni 18 a Koranti. Sun yi aiki tare suna ɗinka kuma suna gyaran tanti. (Ayukan Manzanni 18:2, 3) Ka yi tunanin taɗi na Nassi da suka yi. Babu shakka wannan tarayya da Bulus ta kyautata ruhaniyarsu! “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima,” in ji Misalai 13:20. Tarayya mai kyau ta kyautata ruhaniyarsu.—1 Korinthiyawa 15:33.

8. Menene Biriskilla da Akila suka koya ta wajen lura da Bulus a hidimarsa?

8 Sa’ad da Biriskilla da Akila suka lura da Bulus mai shelar Mulki, suka ga misali na koyarwa da ya fi kyau. Labarin da ke Ayukan Manzanni ya ce Bulus “yana muhawara cikin majami’a [a Koranti] kowane asabarci, yana nema ya rinjayi Yahudawa da Helenawa.” Daga baya da Sila da Timothawus suka bi shi, Bulus “ya taƙure da magana, yana shaida ma Yahudawa Yesu Kristi ne.” Sa’ad da ya ga cewa waɗanda suke cikin majami’ar suna ɗan son saƙon, Biriskilla da Akila sun lura cewa Bulus ya matsa zuwa gefen da ya fi kyau ya soma wa’azi a wajen, a gida dab da majami’ar. A wajen, Bulus ya taimaki Kirisbus, “shugaban majami’a,” ya zama almajiri. Biriskilla da Akila sun lura cewa samun wannan almajiri musamman ya ba da amfani mai kyau a yankin. Labarin ya ce: “Kirisbus . . . ya bada gaskiya ga Ubangiji tare da gidansa duka; mutane dayawa kuma daga cikin Korinthiyawa sa’anda suka ji suka bada gaskiya, aka yi musu baftisma.”—Ayukan Manzanni 18:4-8.

9. Yaya Biriskilla da Akila suka aikata ga misalin Bulus?

9 Wasu masu shelar Mulki, kamar su Biriskilla da Akila sun yi koyi da misalin Bulus a hidimar fage. Manzon ya yi wa Kiristoci gargaɗi: “Ku zama masu-koyi da ni, kamar yadda ni kuma na Kristi ne.” (1 Korinthiyawa 11:1) Cikin jituwa da misalin Bulus, Biriskilla da Akila sun taimaki Afolos ya fahimci koyarwar Kirista da kyau. Shi kuma har ila ya taimaki wasu. Babu shakka, Biriskilla da Akila sun samu almajirai a Roma, Koranti, da Afisus.—Ayukan Manzanni 18:1, 2, 18, 19; Romawa 16:3-5.

10. Menene ka koya daga Ayukan Manzanni sura ta 18 da zai taimake ka a aikin almajirantarwa?

10 Menene za mu iya koya daga bincika Ayukan Manzanni sura ta 18? To, yadda Akila da Biriskilla suka koya daga Bulus, za mu iya kyautata iyawarmu na samun almajirai ta bin misalin masu koyar da Kalmar Allah da kyau. Za mu iya tarayya da waɗanda suke “taƙure da magana” da kuma waɗanda ‘suke tabbatar wa’ wasu. (Ayukan Manzanni 18:5) Za mu iya lura da yadda suka motsa zuciyar mutane ta yin amfani da rinjaya a koyarwa. Irin wannan gwani zai taimake mu mu samu almajirai. Sa’ad da mutum yake nazarin Littafi Mai Tsarki da mu, za mu iya gaya masa ya gayyaci waɗanda suke cikin iyalinsa ko maƙwabta ne su bi shi a nazarin. Ko kuma ya gaya mana wasu da za mu iya nazarin Littafi Mai Tsarki da su.—Ayukan Manzanni 18:6-8.

Ka Nemi Zarafi na Almajirantarwa

11. Ina za a iya samun sababbin almajirai?

11 Bulus da ’yan’uwansa Kiristoci sun nemi su samu almajirai ta wa’azi gida gida, a kasuwa, sa’ad da suke tafiya—hakika, a ko’ina. Da yake kai ma’aikaci na Mulki ne mai himma, za ka iya faɗaɗa ayyukanka na hidimar fage? Za ka yi amfani da zarafi da kake da shi ka nemi waɗanda suka cancanta kuma ka yi musu wa’azi? Waɗanne hanyoyi ne ’yan’uwanmu masu shelar bishara suke samun almajirai? Da farko bari mu duba fagen wa’azi ta tarho.

12-14. Don ka nuna amfanin wa’azi ta tarho, ka ba da naka labari ko kuma ɗaya cikin waɗanda suke cikin waɗannan sakin layi.

12 Sa’ad da suke wa’azi gida gida a Brazil, wata Kirista da muke kira Maria ta ba wa wata mata da take fitowa daga wani gida warƙa. Maria ta yi amfani da jigon warƙar nan “Za ka so ka ƙara sanin Littafi Mai Tsarki?” wajen gabatarwa. Matar ta ce: “Zan so. Matsalar ita ce ni malama ce, kuma koyarwa na cin dukan lokacina.” Maria ta ce suna iya tattauna darussa na Littafi Mai Tsarki ta tarho. Matar ta ba Maria lambarta, kuma da maraicen ranar, ta soma nazari ta tarho, ta yi amfani da mujallar nan Menene Allah Yake Bukata a Garemu? a

13 Sa’ad da take wa’azi ta tarho, wata mai hidima ta cikakken lokaci a Habasha ta damu lokacin da ta yi magana da wani mutum amma ta ji ana fāɗa. Mutumin ya ce an jima ta sake kira. Sa’ad da ta yi kiran, ya roƙi gafara ya ce lokacin da ta kira, shi da matarsa suna fāɗa. ’Yar’uwar ta yi amfani da wannan zarafi ta gaya masa taimako mai kyau da Littafi Mai Tsarki ya ba da game da matsaloli na iyali. Ta gaya masa cewa Asirin Farinciki na Iyali ya taimaki iyalai da yawa, littafin da Shaidun Jehovah suka buga. Bayan ’yan kwanaki da ta ba shi wannan littafin, ’yar’uwar ta sake kiran mutumin. Mutumin ya ce: “Wannan littafin ya ceci aurena!” Hakika, ya yi taro na iyali don ya gaya musu darussa masu kyau da ya karanta cikin littafin. Aka soma nazarin Littafi Mai Tsarki na gida, ba da daɗewa ba mutumin ya soma halartar taron Kirista a kai a kai.

14 Wata mai shelar Mulki a Denmark da ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki ta wajen wa’azi ta tarho ta ce: “Mai kula da hidima ya ƙarfafa ni na yi wa’azi ta tarho. Da farko na yi jinkiri, ina cewa: ‘Ba abin da nake son yi ba ne.’ Amma, wata rana na yi ƙarfin zuciya na kira mutum na farko. Sonja ta amsa kuma bayan mun yi ɗan taɗi, ta yarda ta karɓa littafi da ke da tushe a Littafi Mai Tsarki. A wani maraice muka tattauna batun halitta, kuma ta so ta karanta littafin nan Life—How Did It Get Here? By Evolution or by Creation.b Na ce zai yi kyau mu sadu mu tattauna batun. Ta yarda. Sonja ta yi shirin nazarin lokacin da na isa, kuma tun lokacin muna nazari kowane mako.” ’Yar’uwarmu Kirista ta kammala: “Shekaru da yawa na yi addu’a na sami yin nazarin Littafi Mai Tsarki, amma ban tsammani zan samu ta wa’azi ta tarho ba.”

15, 16. Waɗanne labarai za ka iya ba da don ka nuna amfanin kasance a faɗake ka san hanyoyi dabam dabam na soma nazarin Littafi Mai Tsarki?

15 Mutane da yawa suna samun nasara domin suna amfani da shawarwari na a yi wa mutane wa’azi a ko’ina da suke. Wata mata Kirista a Amirka ta ajiye motarta kusa da wata motar haya a inda ake ajiye motoci. Sa’ad da matar da ke cikin motar ta gan ta, ’yar’uwar ta soma bayyana mata aikinmu na ilimantarwa na Littafi Mai Tsarki. Matar ta saurara, ta fito daga motar, ta je wajen motar ’yar’uwar. Ta ce: “Na yi farin ciki sosai da ki ka tsaya ki yi mini magana. Ban samu littattafanku na Littafi Mai Tsarki ba da daɗewa. Ban da haka, ina son in sake yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Za ki yi nazari da ni?” A ta haka, ’yar’uwarmu ta nemi yanayi mai kyau na wa’azin bishara.

16 ’Yar’uwa a Amirka ta ba da wannan labari sa’ad da ta ziyarci gidan kula da tsofaffi: Ta yi magana da darekta na wasu ayyuka a wurin, ta gaya masa cewa za ta so ta ba da taimako a biyan bukatu na ruhaniya na waɗanda suke zama a wajen. ’Yar’uwarmu ta daɗa cewa za ta yi farin ciki ta gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki kowane mako da dukan waɗanda suke so su halarta kyauta. Darektan ya ba ta izini ta ziyarci gidaje dabam dabam da suke wajen. Ba da daɗewa ba, ta soma gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki sau uku a mako da mutane 26 da suke zama a wurin, ɗaya kuma yana halartar dukan taronmu a kai a kai.

17. Soma nazarin Littafi Mai Tsarki na gida ta yaya yake kasance da amfani sau da yawa?

17 Ga wasu masu shelar Mulki, soma nazarin Littafi Mai Tsarki kai tsaye ya kawo amfani mai kyau. Wata rana da safe, ikilisiya da take da masu shela 105 ta yi ƙoƙari ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da kowa da suka sadu da shi. Masu shela 86 suka fita hidimar fage, kuma bayan sun yi aikin wa’azi na sa’o’i biyu, suka soma aƙalla sababbin nazari na Littafi Mai Tsarki guda 15.

Ka Ci Gaba da Neman Waɗanda Suka Cancanta

18, 19. Wane umurni mai muhimmanci daga Yesu ya kamata muna tunawa, domin wannan me ya kamata mu ƙudura niyyar yi?

18 Da yake kai mai shelar Mulki ne, za ka so ka gwada shawarwari da aka ambata cikin wannan talifin. Hakika, zai yi kyau ka yi la’akari da al’adu na yankin sa’ad da kake son ka yi amfani da wasu hanyoyi na wa’azi. Mafi muhimmanci kuma, bari mu tuna da ja-gorar Yesu na mu nemi waɗanda suka cancanta kuma mu taimake su su zama almajirai.—Matta 10:11; 28:19.

19 Don mu cim ma wannan, bari mu ‘fassara kalmar gaskiya daidai.’ Za mu yi haka ta amfani da rinjaya da ke bisa Nassosi. Wannan zai taimake mu mu motsa zuciyar waɗanda suke saurara kuma mu sa su aikata. Idan mun dogara ga Jehovah cikin addu’a, za mu taimaki wasu su zama almajiran Yesu Kristi. Wannan aikin na kawo albarka! Saboda haka bari mu ‘yi ƙoƙari mu miƙa kanmu yardaje ga Allah,’ koyaushe muna ɗaukaka Jehovah mu masu shelar Mulki da himma, waɗanda suke wa’azi da nufin samun almajirai.—2 Timothawus 2:15.

[Hasiya]

a Shaidun Jehovah ne suka buga.

b Shaidun Jehovah ne suka buga.

Ka Tuna?

• Me ya sa Afolos yake bukata a ƙara bayyana masa tafarkin Allah sosai?

• A waɗanne hanyoyi ne Biriskilla da Akila suka koya daga manzo Bulus?

• Me ka koya daga Ayukan Manzanni sura ta 18 game da aikin almajirantarwa?

• Ta yaya za ka nemi zarafi na samun almajirai?

[Hoto a shafi na 14]

Biriskilla da Akila “suka ɗauke [Afolos], suka ƙara buɗe masa tafarkin Allah sosai”

[Hoto a shafi na 16]

Afolos ya zama gwani a samun almajirai

[Hoto a shafi na 17]

Bulus ya yi wa’azi a ko’ina da ya je

[Hotuna a shafi na 19]

Ka nemi zarafi ka yi wa’azi

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba