Ka Amfana Sosai Daga Karatun Littafi Mai Tsarki
“Ina murna da shari’ar Allah.”—ROM. 7:22.
1-3. Ta yaya karanta da kuma yin abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa zai taimaka mana?
WATA ’yar’uwa da ta manyanta ta ce: “Kowane safe ina gode wa Jehobah domin ya taimaka mini na fahimci Littafi Mai Tsarki.” Ko da yake ta karance Littafi Mai Tsarki sau 40, ta ci gaba da karantawa. Wata ’yar’uwa matashiya ta ce karanta Littafi Mai Tsarki ya taimaka mata ta san cewa Jehobah Allah ne na ƙwarai. A sakamakon haka, ta ƙara kusantarsa. Ta ce: “Na fi yin farin ciki yanzu!”
2 Manzo Bitrus ya ƙarfafa dukan Kiristoci su “yi marmarin” kalmar Allah. (1 Bit. 2:2) Sa’ad da muka karanta Littafi Mai Tsarki kuma muka aikata abin da muka koya, za mu kasance da lamiri mai kyau kuma mu yi rayuwa mai ma’ana. Zai kuma taimake mu mu samu abokan kirki da suke ƙauna da kuma bauta wa Allah. Waɗannan dalilai ne na yin “murna da shari’ar Allah.” (Rom. 7:22) Amma, a waɗanne hanyoyi ne kuma karanta Littafi Mai Tsarki zai amfane mu?
3 Idan ka ci gaba da koyo game da Jehobah da kuma Ɗansa, za ka riƙa ƙaunarsu da kuma mutane sosai. Sanin Nassi zai taimaka maka ka ga yadda Allah zai ceci mutane masu biyayya sa’ad da ya halaka wannan muguwar duniya. Kana da albishiri da za ka gaya wa mutane a hidimarka. Kuma ka tabbata cewa Jehobah zai taimake ka sa’ad da kake koya wa mutane abin da ka koya.
KA KARANTA KUMA KA YI BIMBINI
4. Mene ne karanta Littafi Mai Tsarki a hankali yake nufi?
4 Jehobah yana son mu yi bimbini kuma mu fahimci abin da muka karanta a cikin Littafi Mai Tsarki. Ya gaya wa Joshua cewa: ‘Wannan littafin shari’a ba za ya rabu da bakinka ba, amma za ka riƙa bincikensa dare da rana.’ (Josh. 1:8; Zab. 1:2) Shin hakan yana nufin cewa za mu riƙa furta duk kalmomin Littafi Mai Tsarki da ƙaramar murya? A’a. Yana nufin ka karanta shi a hankali don ka iya yin bimbini a kan abin da kake karantawa. Yin hakan zai taimake ka ka mai da hankali ga ayoyi masu amfani sosai da kuma ban ƙarfafa. Sa’ad da ka ga kalami ko kuma labari mai ƙarfafawa, ka karanta shi a hankali kuma ka furta kalmomin a hankali. Hakan zai sa abin da kake karantawa ya shiga zuciyarka sosai. Me ya sa hakan yake da muhimmanci? Domin idan ka fahimci ƙa’idojin Allah sosai, za ka so ka aikata su.
5-7. Ka ba da misalai da suka nuna cewa karanta Kalmar Allah a hankali zai taimake ka (a) ka kasance da tsabta ta ɗabi’a; (b) ka bi da mutane cikin haƙuri da kuma kirki; (c) ka dogara ga Jehobah a mawuyacin lokaci.
5 Sa’ad da muke karanta wani littafi na Littafi Mai Tsarki da yake mana wuyan fahimta, yana da kyau mu karanta shi a hankali yadda za mu iya yin bimbini a kansa. Alal misali, ka yi tunani a kan yanayi guda uku. Na farko, a ce wani ɗan’uwa yana karanta littafin Hosea. Sa’ad da ya kai sura ta 4, sai ya dakata ya yi bimbini a kan abin da ya karanta a ayoyi ta 11 zuwa 13. (Karanta Hosea 4:11-13.) Me ya sa ya mai da hankali ga ayoyin? Domin ya taɓa fuskantar gwaji yin lalata a makaranta. Amma, bayan ya yi bimbini a kan ayoyin, sai ya ce: ‘Jehobah yana ganin duk abu marar kyau da mutane suke yi, ko ma a ɓoye. Kuma ba na son in yi masa laifi.’ Ɗan’uwan ya tsai da shawarar kasancewa da tsabta ta ɗabi’a a gaban Allah.
6 Yanayi na biyu, a ce wata ’yar’uwa tana karanta littafin Joel sura ta 2, kuma ta karanta aya ta 13 a hankali. (Karanta Joel 2:13.) Wannan ayar ta sa ta fahimci cewa ya kamata ta yi koyi da Jehobah, wanda shi “mai-alheri ne, cike da juyayi, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai” kuma. Sai ta tsai da shawarar daina yin fushi da yi wa mijinta da kuma wasu baƙar magana.
7 Yanayi na uku, a ce Uba da ya rasa aikinsa, yana tunanin yadda zai kula da iyalinsa. Ya karanta a littafin Nahum 1:7 cewa Jehobah “ya kuwa san waɗanda ke sa danganarsu gareshi,” kuma yana kāre su kamar ‘kagara . . . cikin ranar wahala.’ Waɗannan kalamai sun ƙarfafa shi. Ya ga cewa Jehobah yana kula da mu, kuma ya daina damuwa ainun. Sai ya karanta aya ta 15 a hankali. (Karanta Nahum 1:15.) Wannan ɗan’uwan ya ga cewa idan yana yin wa’azin bishara a wannan mawuyacin lokaci, zai nuna cewa Jehobah ne kagararsa. Ya ci gaba da neman aiki, kuma yana fita wa’azi tare da ikilisiya a tsakiyar mako.
8. Ka ɗan bayyana abin da ka koya daga karatun Littafi Mai Tsarki da kake yi.
8 Waɗannan misalan da muka tattauna suna cikin littattafai na Littafi Mai Tsarki da wasu suke ganin suna da wuyan fahimta. Amma, idan ka karanta ayoyi masu ban ƙarfafa sosai, za ka so ka riƙa karanta waɗannan littattafan. Za su ta’azantar da kai kuma su sa ka kasance da hikima. Hakazalika, dukan littattafai na Littafi Mai Tsarki za su taimake ka. Kalmar Allah tana kamar fili mai cike da lu’u lu’u. Sa’ad da kake karanta Littafi Mai Tsarki, ka ci gaba da neman lu’u lu’u, ko kuma ja-gora da kuma ƙarfafa da ke cikinsa.
KA YI ƘOƘARI KA FAHIMCI MA’ANAR
9. Mene ne za mu yi don mu fahimci Littafi Mai Tsarki sosai?
9 Yana da muhimmanci ka karanta Littafi Mai Tsarki kullum, amma, ka tabbata ka fahimci abin da ka karanta. Kuma ka yi amfani da littattafanmu don ka koya game da mutane da wurare da kuma abubuwan da ka karanta. Za ka iya gaya wa dattijo ko wani Kirista da ya manyanta, ya taimake ka ka ƙara sanin yadda za ka aikata abin da ka koya. Haka ma wani Kirista mai suna Afollos a zamanin dā ya yi.
10, 11. (a) Ta yaya aka taimaka wa Afollos ya ƙware a hidimarsa? (b) Mene ne za mu koya daga misalin Afollos? (Ka duba akwatin nan, “Ka San Bayani na Kwanan Nan Kuwa?”)
10 Afollos Kirista ne Bayahude da ya san Nassosi sosai, kuma shi mai ƙwazo ne a hidima. Littafin Ayyukan Manzanni ya ce: “Ya yi ta zance, yana koyarwa da zancen Yesu bisa ga hankali, baftismar Yohanna kaɗai yake sane da ita.” Amma bai san cewa Yesu ya koya wa almajiransa sabon abu game da baftisma ba. Sa’ad da Biriskilla da Akila suka ji koyarwarsa a Afisa, sai suka “ƙara buɗe masa tafarkin Allah sosai.” (A. M. 18:24-26) Ta yaya Afollos ya amfana?
11 Bayan Afollos ya kammala wa’azi a Afisa, sai ya tafi Akaya. Ya yi amfani da Nassi wajen tabbatar wa Yahudawa cewa koyarwarsu ba daidai ba ne, kuma Yesu ne Kristi. Ya taimaka wa waɗanda suka karɓi bishara. (A. M. 18:27, 28) Yanzu da ya samu ƙarin fahimi a kan baftisma, ya taimaka wa sababbi da yawa su samu ci gaba a bautarsu ga Jehobah. Mene ne muka koya daga wannan? Muna iya bin misalin Afollos ta wajen ƙoƙartawa mu fahimci abin da muka karanta a Littafi Mai Tsarki. Amma, ya kamata mu ƙasƙantar da kanmu kuma mu karɓi shawara da za ta sa mu ƙware a koyarwarmu.
KA TAIMAKI MUTANE DA ABIN DA KA KOYA
12, 13. Ta yaya za mu yi amfani da Nassosi cikin basira a hanyar da za ta sa ɗalibinmu ya samu ci gaba?
12 Muna iya taimaka wa mutane kamar yadda Biriskilla da Akila da kuma Afollos suka yi. Yaya kake ji sa’ad da ka taimaki wanda yake son saƙonmu ya yi gyara a salon rayuwarsa, domin ya samu ci gaba a bautarsa ga Jehobah? Ko kuma idan kai dattijo ne, yaya kake ji sa’ad da wani Kirista ya gode maka don ka ba shi shawara daga Littafi Mai Tsarki a lokacin da yake da wata matsala? Babu shakka, yin amfani da Kalmar Allah don taimaka wa wasu su samu ci gaba a rayuwarsu, yana kawo farin ciki sosai.a Ta yaya za ka yi hakan?
13 A zamanin Iliya, yawancin Isra’ilawa ba su tsai da shawara ko za su bi bauta ta gaskiya ko ta ƙarya ba. Gargaɗin da Iliya ya ba wa Isra’ilawa zai iya taimaka wa ɗalibinmu da bai tsai da shawarar bauta wa Jehobah ba tukuna. (Karanta 1 Sarakuna 18:21.) Ko kuma, idan wani mai son saƙonmu yana tsoron abin da abokansa ko iyalinsa za su ce idan yana nazarin Littafi Mai Tsarki, za ka iya taimaka masa ya tsai da shawarar bauta wa Jehobah ta wajen yin amfani da littafin Ishaya 51:12, 13.—Karanta.
14. Mene ne zai taimake ka ka tuna da ayoyin Littafi Mai Tsarki da kake bukata domin ka taimaki wasu?
14 Saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki zai iya ƙarfafa mutum kuma ya taimaka masa ya gyara halinsa. Amma kana iya yin tunani, ‘Ta yaya zan san Nassosin da suka dace a lokacin da nake bukatarsu?’ Ka riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kullum, kuma ka yi bimbini a kan abin da ka karanta. Ta hakan, za ka san Littafi Mai Tsarki sosai, kuma Jehobah zai yi amfani da ruhunsa don ya taimake ka ka tuna abin da ka karanta.—Mar. 13:11; karanta Yohanna 14:26.
15. Mene ne zai taimake ka ka fahimci Kalmar Allah sosai?
15 Kamar sarki Sulemanu, ka yi addu’a ga Jehobah ya ba ka hikima don ka yi hidima kuma ka cika ayyukanka na ikilisiya. (2 Laba. 1:7-10) Kamar annabawan dā, kai ma ka bincika Kalmar Allah sosai. Hakan zai taimake ka ka san gaskiya game da Jehobah da kuma nufinsa. (1 Bit. 1:10-12) Manzo Bulus ya gargaɗi Timotawus cewa, ya koyi “zantattukan imani, da na koyarwar kirki.” (1 Tim. 4:6) Idan kai ma ka yi hakan, za ka ƙware wajen taimaka wa wasu. Hakan kuma zai sa ka ƙarfafa imaninka.
KARATUN LITTAFI MAI TSARKI YANA KĀRE MU
16. (a) Ta yaya mutanen Biriya suka amfana daga bincika “littattafai kowace rana”? (b) Me ya sa karatun Littafi Mai Tsarki yake da muhimmanci a gare mu?
16 A zamani dā, Yahudawa da ke garin Biriya suna karanta Nassi kullum. Sa’ad da Bulus ya yi musu wa’azi, suna bincika “littattafai kowace rana, su gani ko waɗannan al’amura haka suke.” A sakamako, da yawa cikinsu sun amince da koyarwarsa, kuma sun “ba da gaskiya.” (A. M. 17:10-12) Hakan ya nuna cewa karanta Littafi Mai Tsarki kullum yana ƙarfafa imaninmu ga Jehobah. Domin mu shiga sabuwar duniya, muna bukatar bangaskiya wadda ke nufin “ainihin abin da mu ke begensa.”—Ibran. 11:1.
17, 18. (a) Ta yaya bangaskiya da kuma ƙauna suke kāre zuciyarmu ta alama? (b) Ta yaya bege ke kāre mu?
17 Bulus yana da ƙwaƙƙwaran dalili na cewa: “Amma da shi ke na rana ne mu, mu yi natsuwa, muna yafe da sulke na bangaskiya da ƙauna; kuma da bege na ceto, kwalkwali ke nan.” (1 Tas. 5:8) Soja yana bukatar ya kāre zuciyarsa daga hari. Hakazalika, zuciyarmu ta alama tana bukatar kāriya daga zunubi. Idan Kirista ya gaskata da Alkawuran Allah kuma yana ƙaunarsa da kuma mutane sosai, yana kāre zuciyarsa ta alama. Kamar dai yana yafe da sulke. Kuma da kyar zai yi abin da zai sa ya rasa tagomashin Allah.
18 Bulus ya kuma kwatanta “bege na ceto” da kwalkwali. Idan soja a zamanin dā bai kāre kansa ta wajen saka kwalkwali ba, za a iya kashe shi da sauƙi. Amma idan yana sanye da kwalkwalin, ba zai ji mugun rauni a kai ba. Muna ƙarfafa begenmu ta wajen karanta yadda Jehobah yake ceton mutanensa. Kuma wannan begen zai sa mu tsani kowace irin koyarwar ’yan ridda da ke iya yaɗuwa kamar cuta a cikin ikilisiya. (2 Tim. 2:16-19) Begenmu zai kuma sa mu guji halayen da za su ɓata wa Jehobah rai.
YADDA ZA KA TSIRA
19, 20. Me ya sa muke daraja Kalmar Allah, kuma ta yaya za mu nuna godiyarmu? (Ka duba akwatin nan “Jehobah Ya Ba Ni Ainihin Abin da Nake Bukata.”)
19 Yayin da muke daɗa kusantar ƙarshen wannan zamanin, ya kamata mu dogara ga kalmar Allah fiye da dā. Gargaɗin da muke samu daga cikinta yana taimaka mana mu ƙi munanan halaye da kuma sha’awar zunubi. Zai kuma ta’azantar da mu da ƙarfafa mu mu jimre da duk gwaji da Shaiɗan da kuma duniyarsa za su yi mana. Ja-gorar da ke cikin Kalmar Jehobah za ta taimaka mana mu ci gaba da yin tafiya a hanyar rai.
20 Ka tuna cewa nufin Allah shi ne “dukan mutane su tsira.” Kuma sun haɗa da dukan bayinsa da kuma waɗanda muke taimaka musu ta wajen wa’azi da kuma koyarwar da muke yi. Amma, dukan waɗanda suke son su tsira suna bukatar su “kawo ga sanin gaskiya.” (1 Tim. 2:4) Hakan ya nuna cewa wajibi ne mu karanta Littafi Mai Tsarki kuma mu bi ja-gorar da ke cikinsa idan muna son mu tsira. Hakika, za mu nuna cewa muna daraja Kalmar Allah ta wajen karanta ta kullum.—Yoh. 17:17.
a Hakika, bai kamata mu yi amfani da gargaɗin Littafi Mai Tsarki don sūkar wasu ba ko mu tilasta musu su yi canji a salon rayuwarsu. Ya kamata mu yi koyi da Jehobah ta wajen yin haƙuri da kuma nuna wa ɗalibanmu alheri.—Zab. 103:8.