Ka “Rinjayi Mugunta” Ta Wajen Kame Fushinka
“Kada ku ɗauka wa kanku fansa, ƙaunatattu, . . . amma ku rinjayi mugunta da nagarta.”—ROM. 12:19, 21.
1, 2. Wane misali mai kyau ne wasu Shaidu da suke tafiya suka nuna?
WASU Shaidun Jehobah su talatin da huɗu suna kan hanyarsu ta zuwa keɓewar wani ofishin reshe, sai wasu matsaloli suka taso da ya shafi jirginsu. Tsayawar da aka ce za a yi na awa ɗaya don a sha mai ya zama na awoyi arba’in da huɗu a wani tashar jirgin sama mai nisa, inda babu isashen abinci, ruwa, ko kuma wuri mai tsabta. Fasinjoji da yawa suka yi fushi kuma suka yi wa ma’aikatan tashar jirgin saman barazana. Amma ’yan’uwan maza da mata suka natsu.
2 Daga baya, Shaidun suka isa kuma samu sashe na ƙarshe na tsarin ayyukan keɓewar. Ko da yake sun gaji, sun tsaya bayan tsarin ayyukan don su more cuɗanya da ’yan’uwan da ke wajen. Daga baya, sun ji cewa an lura da misalinsu na haƙuri da kame kai. Ɗaya cikin fasinjojin ya gaya wa kamfanin jirgin saman cewa, “Da a ce ba Kiristoci talatin da huɗu da suka bi jirgin ba, da an yi tarzoma a tashar jirgin saman.”
Zama a Duniya Mai Cike da Fushi
3, 4. (a) Ta yaya kuma tun wane lokaci ne mugun fushi yake damun ’yan Adam? (b) Kayinu zai iya kame fushinsa ne? Ka ba da bayani.
3 Matsi na rayuwa a wannan mugun zamanin yana iya sa mutane fushi. (K. Sh. 28:34) Sau da yawa wannan fushin yana kai ga ƙiyayya har da mugunta. Ana yaƙe-yaƙe a ciki da wajen ƙasashe, kuma damuwa na iyali yana jawo faɗa a cikin gidaje da yawa. Irin wannan fushi da mugunta sun soma ne tun da daɗewa. Kayinu, ɗan fari na Adamu da Hauwa’u, ya kashe ƙaninsa Habila, saboda ƙishi. Kayinu ya aikata wannan muguntar ko da Jehobah ya aririce shi ya kame fushinsa kuma ya yi alkawarin zai albarkace shi idan ya yi hakan.—Karanta Farawa 4:6-8.
4 Duk da ajizanci da ya gāda, Kayinu yana da zaɓi a wannan batun. Zai iya kame fushinsa. Shi ya sa yake da alhakin wannan muguntar da ya aikata. Hakazalika, ajizancinmu yana sa ya yi wuya mu guje wa fushi da kuma ayyuka masu ban haushi. Kuma wasu matsaloli masu tsanani suna ƙara matsi a waɗannan “miyagun zamanu.” (2 Tim. 3:1) Alal misali, matsalolin tattalin arziki suna iya matsa wa motsin ranmu. ’Yan sanda da ƙungiyoyin taimakon iyali sun faɗi cewa matsaloli a tsarin tattalin arziki suna jawo ƙaruwan fushi da kuma zalunci a gida.
5, 6. Wane halin duniya game da fushi zai iya shafanmu?
5 Ƙari ga haka, mutane da yawa da muke saduwa da su suna “son kansu” “masu-girman kai” ne da “masu-zafin hali.” Yana da sauƙi irin waɗannan mugun halayen su yi tasiri a kanmu ko kuma su ba mu haushi. (2 Tim. 3:2-5) Hakika, fim da talabijin sau da yawa suna nuna cewa ramuwar gayya tana da kyau kuma mugunta ce hanyar da ta fi dacewa ta magance matsaloli. Irin waɗannan fina-finan suna sa masu kallo su yi ta ɗokin lokacin da mugun “ya fuskanci abin da ya cancance shi,” wanda sau da yawa mugun kisa ne a hannun jarumin labarin.
6 Irin wannan labarin ba ya ɗaukaka hanyoyin Allah amma “ruhun duniya” da kuma sarkinta mai fushi, Shaiɗan. (1 Kor. 2:12; Afis. 2:2; R. Yoh. 12:12) Wannan ruhun yana ɗaukaka gamsar da sha’awoyi na jiki kuma ya saɓa wa ruhu mai tsarki na Allah da ’yarsa. Hakika, koyarwa ta musamman na Kiristanci ita ce kada a yi ramuwar gayya. (Karanta Matta 5:39, 44, 45.) To, ta yaya za mu ƙara yin amfani da koyarwar Yesu sosai?
Misalai Masu Kyau da Marasa Kyau
7. Menene ya faru sa’ad da Simeon da Lawi suka ƙi kame fushinsu?
7 Littafi Mai Tsarki yana cike da gargaɗi game da kame fushi da kuma misalai masu kyau na abin da zai iya faruwa sa’ad da muka yi hakan da sa’ad da muka ƙi yin hakan. Ka yi la’akari da abin da ya faru sa’ad da ’ya’yan Yakubu Simeon da Lawi suka yi ramuwar gayya a kan Shechem don ya kwana da ƙanwarsu Dinah. “Ransu ya ɓāci, suka hasala ƙwarai kuma.” (Far. 34:7) Bayan hakan, wasu ’ya’yan Yakubu maza suka kai wa birnin Shechem hari, suka kwashi ganimar birnin kuma suka kwashe mata da yara zuwa zaman bauta. Sun yi dukan waɗannan abubuwan ba don Dinah kawai ba amma wataƙila domin hakan ya ɓata sunan su. A ganin su, Shechem ya yi wa su da babansu, Yakubu laifi. Amma yaya Yakubu ya ɗauki halinsu?
8. Menene labarin Simeon da Lawi ya nuna game da ramuwar gayya?
8 Babu shakka, mugun abin da ya sami Dinah ya sa Yakubu baƙin ciki sosai; duk da haka, ya yi Allah wadai da ramuwar gayyar da ’ya’yansa suka yi. Simeon da Lawi har ila sun yi ƙoƙarin su ba da hujjar abubuwan da suka yi, suna cewa: “Za ya yi da ƙanuwarmu kamar da karuwa?” (Far. 34:31) Amma, batun bai ƙare a nan ba, domin hakan ya ɓata wa Jehobah rai. Bayan shekaru da yawa, Yakubu ya annabta cewa domin ayyukan muguntar da Simeon da Lawi suka yi cikin fushi, za a watsar da zuriyarsu cikin ƙabilun Isra’ila. (Karanta Farawa 49:5-7.) Hakika, rashin kame fushinsu ya jawo rashin amincewar Allah da na mahaifinsu.
9. A wane lokaci ne fushi ya kusan rinjayar Dauda?
9 Sarki Dauda ya bambanta da su. Ya samu zarafi mai yawa na ɗaukan fansa, amma bai yi hakan ba. (1 Sam. 24:3-7) Amma, akwai lokacin da fushi ya kusan rinjayarsa. Wani mutum mai arziki mai suna Nabal ya zazzage mazajen Dauda, duk da cewa sun kāre awakai da makiyaya na Nabal. Wataƙila ya yi fushi musamman don mazajensa, Dauda ya kusan yin muguwar ramuwa. Sa’ad da Dauda da mazajensa suke kan hanyarsu ta kai wa Nabal da iyalinsa hari, wani saurayi ya gaya wa Abigail, mata mai hankali na Nabal, abin da ya faru kuma ya aririce ta ta ɗauki mataki. Nan da nan, ta tara kyauta mai yawa kuma ta tafi ta haɗu da Dauda. Cikin tawali’u ta nemi gafara saboda rashin kunyar Nabal kuma ta roƙi Dauda ya ji tsoron Jehobah. Sai Dauda ya koma cikin hayyacinsa kuma ya ce: “Mai-albarka ce ke kuma da kin hana ni yau daga alhakin jini.”—1 Sam. 25:2-35.
Halin Kirista
10. Wane irin hali ne ya kamata Kiristoci su nuna game da yin ramuwa?
10 Abin da ya sami Simeon da Lawi da kuma Dauda da Abigail ya nuna dalla-dalla cewa Jehobah ya ƙi jinin rashin kame fushi da mugunta kuma yana sa albarka ga ƙoƙarce-ƙoƙarcen yin salama. “Idan ya yiwu, ku zama lafiya da dukan mutane, gwargwadon iyawarku” in ji manzo Bulus. “Kada ku ɗauka wa kanku fansa, ƙaunatattu, amma ku kauce wa fushi: gama an rubuta, Ɗaukar fansa tawa ce; ni zan yi sakamako, in ji Ubangiji. Amma idan maƙiyinka yana jin yunwa, ka cishe shi; idan yana ƙishi, ka ba shi sha; gama garin yin haka, za ka tara masa garwashin wuta a kansa. Kada ku rinjayu ga mugunta, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.”—Rom. 12:18-21.a
11. Ta yaya wata ’yar’uwa ta koyi ta kame fushinta?
11 Muna iya yin amfani da wannan shawarar. Alal misali, wata ’yar’uwa ta kai ƙarar sabuwar manajarta na wajen aiki ga wani dattijo. Ta kira ta marar adalci da kirki. Ta yi fushi sosai da matar kuma tana son ta bar aikin. Dattijon ya gaya mata kada ta yi kome da garaje. Ya fahimci cewa yadda ’yar’uwa ta aikata da fushi ga yadda manajar take bi da ita ya daɗa sa yanayin ya yi muni. (Tit. 3:1-3) Dattijon ya gaya mata cewa ko da ta samu wani aikin daga baya, har ila tana bukatan ta canja yadda take aikatawa idan an ɓata mata rai. Ya ba ta shawara ta bi da manajar yadda za ta so a bi da ita, kamar yadda Yesu ya koya mana mu yi. (Karanta Luka 6:31.) ’Yar’uwa ta yarda ta gwada hakan. Menene sakamakon? Bayan wani lokaci, halin manajar ya canja, har ma ta gode wa ’yar’uwar don aikinta.
12. Me ya sa rashin jituwa tsakanin Kiristoci yake da ban haushi sosai?
12 Ba za mu yi mamaki ba sa’ad da irin waɗannan matsaloli suka faru da wanda ba ya cikin ikilisiyar Kirista. Mun san cewa rayuwa a duniyar Shaiɗan ba ta da sauƙi kuma muna bukatan mu yi ƙoƙari don kada mu ƙyale miyagu su sa mu fushi. (Zab. 37:1-11; M. Wa. 8:12, 13; 12:13, 14) Amma, sa’ad da matsala ta faru tsakaninmu da wanda yake cikin ikilisiya, hakan yana iya ɓata mana rai sosai. Wata Mashaidiya ta tuna, “Tangarɗa mafi girma da nake da ita sa’ad da nike son in shiga gaskiya ita ce amincewa da gaskiyar nan cewa mutanen Jehobah ba kamiltattu ba ne.” Mun fito daga duniya marar ƙauna da kula, muna sa ran cewa dukan waɗanda suke cikin ikilisiya za su bi da juna cikin alheri na Kirista. Saboda haka, idan ɗan’uwa Kirista, musamman wanda yake da hakki a cikin ikilisiya, ya ƙi nuna sanin ya kamata ko ya yi abin da bai dace da Kirista ba, hakan na iya ɓata mana rai ko ya ba mu haushi. Muna ma iya tambaya, ‘Me zai sa irin waɗannan abubuwa su faru tsakanin mutanen Jehobah?’ Hakika, irin waɗannan abubuwan sun faru tsakanin Kiristoci shafaffu a zamanin manzanni. (Gal. 2:11-14; 5:15; Yaƙ. 3:14, 15) Menene ya kamata mu yi sa’ad da hakan ya shafe mu?
13. Me ya sa za mu ƙoƙarta mu sha kan rashin jituwa kuma ta yaya za mu yi hakan?
13 ’Yar’uwa da aka ambata ɗazu ta ce: “Na koyi in yi addu’a wa wanda ya ɓata mini rai. Hakan na taimakawa a koyaushe.” Kamar yadda muka karanta, Yesu ya koya mana mu yi wa waɗanda suke tsananta mana addu’a. (Mat. 5:44) Balle ma ’yan’uwanmu na ruhaniya ya kamata mu yi musu addu’a! Kamar yadda uba yake son yaransa su ƙaunaci juna, haka Jehobah yake son bayinsa a duniya su ƙaunaci juna. Muna sa ran zama tare cikin salama da farin ciki har abada, kuma Jehobah yana koya mana mu yi hakan a yanzu. Yana son mu haɗa kai wajen yin aikinsa mai girma. Saboda haka, bari mu magance matsaloli ko kuma mu “ƙyale” laifi kuma mu kasance da haɗin kai. (Karanta Misalai 19:11.) Maimakon mu guji ’yan’uwanmu sa’ad da matsaloli suka taso, ya kamata mu taimaki juna mu kasance tsakanin mutanen Allah, cikin kāriyar “madawaman hannuwa” na Jehobah.—K. Sha 33:27.
Nuna Sauƙin Hali ga Kowa Yana Kawo Sakamako Mai Kyau
14. Ta yaya za mu yi tsayayya da rinjaya na rashin jituwa da Shaiɗan yake haddasawa?
14 Don ya hana mu yaɗa bishara, Shaiɗan da aljanu suna ƙoƙarin su watsar da iyalai masu farin ciki da kuma ikilisiyoyi. Suna ƙoƙarin su haddasa rashin jituwa, domin sun san cewa rarrabuwa na ciki yana da lahani. (Mat. 12:25) Don mu yi tsayayya da mugun rinjayarsu, yana da kyau mu bi shawarar Bulus: “Kada bawan Ubangiji kuwa ya yi husuma, amma sai ya yi nasiha ga duka.” (2 Tim. 2:24) Ka tuna cewa faɗanmu “ba da nama da jini take ba, amma da . . . rundunai masu-ruhaniya na mugunta cikin sammai.” Don mu yi nasara a wannan faɗan, muna bukatan mu yi amfani da makamai na ruhaniya, har da “shirin bishara ta salama.”—Afis. 6:12-18.
15. Me ya kamata mu yi sa’ad da mutanen da ba sa cikin ikilisiya suka kawo mana farmaki?
15 Magabtan Jehobah da ba sa cikin ikilisiya suna kai wa mutanensa masu salama mugun farmaki. Wasu cikin waɗannan magabtan suna kai wa Shaidun Jehobah farmaki a zahiri. Wasu suna ɓata sunanmu ta hanyoyin watsa labarai ko kuma a kotu. Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa za su fuskanci hakan. (Mat. 5:11, 12) Menene ya kamata mu yi? Ba za mu ‘sāka mugunta da mugunta ba,’ a furcinmu ko ta halinmu.—Rom. 12:17; karanta 1 Bitrus 3:16.
16, 17. Wane yanayi mai wuya ne wata ikilisiya ta fuskanta?
16 Ko da menene Iblis zai hadassa mana, ta wajen ‘rinjayar mugunta da nagarta,’ za mu iya ba da shaida mai kyau. Alal misali, wata ikilisiya a wani tsibirin Pasifik ta yi hayar wata majami’a don Tuna Mutuwar Yesu. Sa’ad da shugabannin cocin da ke yankin suka ji hakan, sai suka gaya wa mabiyansu su taru a wannan majami’ar don hidimarsu na coci a daidai lokacin da za mu soma namu taron. Amma, shugaban ’yan sanda ya umurci shugabannin cocin su bar wa Shaidun majami’ar a wannan lokacin. Duk da haka, sa’ad da lokacin ya yi, majami’ar ta cika da mutanen cocin kuma suka soma taronsu.
17 Sa’ad da ’yan sanda suke shirin su zo su kori mutanen ƙarfi da yaji, sai shugaban cocin ya je ya sami ɗaya daga cikin dattawanmu kuma ya tambaye shi: “Kuna da wani shiri na musamman ne da yamman nan?” Ɗan’uwan ya gaya masa game da Tuna Mutuwar Yesu, sai mutumin ya ce: “Oho, ai ban sani ba!” Sai ɗan sandan ya ce da babban murya: “Amma mun gaya muku da safe nan!” Shugaban cocin ya juya ga dattijon da murmushin munafunci ya ce: “Menene za ku yi yanzu? Majami’ar tana cike da mutane. Za ku sa ’yan sandan su kore mu ne?” Ya juya batun cikin dabara don ya zama kamar Shaidu ne suke tsananta musu! Menene ’yan’uwanmu za su yi?
18. Menene ’yan’uwan suka yi game da wannan abin ban haushi, kuma menene sakamakon?
18 Shaidun sun ce za su ƙyale cocin su yi hidima na minti 30, bayan hakan ’yan’uwan za su Tuna Mutuwar Yesu. Taron cocin ya wuce lokacin da aka ba su, amma bayan da mutanen cocin suka fita, sai aka soma Tuna Mutuwar Yesu. Washegari, gwamnatin ta kafa kwamitin da zai bincika batun. Bayan da aka bincika batutuwan, kwamitin ta tilasta wa cocin su sanar cewa shugaban cocin ne ya jawo matsalar ba Shaidu ba. Kwamitin ta kuma gode wa Shaidun Jehobah don haƙurin da suka nuna wajen bi da wannan yanayi mai wuya. Ƙoƙarce-ƙoƙarcen Shaidun na “zama lafiya da dukan mutane” ya kawo sakamako mai kyau.
19. Menene kuma zai ɗaukaka dangantaka na salama?
19 Wani abin da zai taimaka a ci gaba da yin dangantaka cikin salama da wasu shi ne yin amfani da furci mai ƙayatarwa. Talifi na gaba zai tattauna ko menene furci mai ƙayatarwa da yadda za mu koye shi kuma mu yi amfani da shi.
[Hasiya]
a “Garwashin wuta” yana nuni ga yadda ake narkar da ƙarfe a zamanin dā ta wajen ɗora garwashin wuta a bisa sinadarin da kuma ƙarƙashinsa don a ware ƙarafa. Nuna alheri ga waɗanda suka yi mana laifi, zai iya sa su canja halinsu kuma mu fito da halayensa masu kyau.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Me ya sa mutane a duniyar yau suke fushi sosai?
• Waɗanne misalai a cikin Littafi Mai Tsarki suka nuna sakamakon kame fushi da kuma rashin yin hakan?
• Yaya ya kamata mu aikata idan ɗan’uwa Kirista ya ɓata mana rai?
• Menene ya kamata mu yi idan mutanen da ba sa cikin ikilisiya suka ɓata mana rai?
[Hoton da ke shafi na 16]
Simeon da Lawi sun koma gida bayan fushi ya rinjaye su
[Hotuna da ke shafi na 18]
Nuna alheri zai iya sa mutane su canja halinsu