Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 6/15 pp. 20-24
  • Furci Mai Ƙayatarwa Yana Kawo Dangantaka Mai Kyau

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Furci Mai Ƙayatarwa Yana Kawo Dangantaka Mai Kyau
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Ke Sa Furci Ya Kasance Mai Ƙayatarwa
  • “Lokacin Shuru da Lokacin Magana”
  • Ayyuka Masu Ƙayatarwa Suna Ɗaukaka Dangantaka Mai Kyau
  • Ka Ƙarfafa Mutane da Furci Mai Ƙayatarwa
  • Yin Amfani da Furci Mai Ƙayatarwa a Cikin Iyali
  • Faɗin Abubuwa Masu Ƙayatarwa Daga Zuciya
  • Gafartawa da Dukan Zuciya
  • Bari Furucinka Ya Kasance da Dadin Ji
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ku Fadi “Abin da ke Mai Kyau Garin Ginawa”
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Ku Rika Yin Maganganu Masu Dadin Ji
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Ka “Rinjayi Mugunta” Ta Wajen Kame Fushinka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 6/15 pp. 20-24

Furci Mai Ƙayatarwa Yana Kawo Dangantaka Mai Kyau

“Kullum maganarku ta zama mai kayatarwa.”—KOL 4:6, Littafi Mai Tsarki.

1, 2. Menene sakamakon magana mai ƙayatarwa da wani ɗan’uwa ya yi?

“SA’AD da nake wa’azi na ƙofa-ƙofa, na sadu da wani mutumin da ya yi fushi sosai har leɓunansa da dukan jikinsa suka soma rawa,” in ji wani ɗan’uwa. “Na yi ƙoƙarin tattaunawa da shi daga Nassosi, amma sai ya ƙara fusata. Matarsa da yaransa suka soma zagi na, sai na san cewa lokacin tafiya ya yi. Na tabbatar wa iyalin cewa ban zo da niyyar yin faɗa ba kuma zan tafi cikin salama. Na nuna musu Galatiyawa 5:22 da 23 inda aka ambata ƙauna, tawali’u, kame kai da salama. Sai na tafi.

2 “Daga baya, sa’ad da nake ziyarar gidajen da ke ketaren titin, na ga iyalin suna zaune a ƙofar gidansu. Sai suka kira ni. Sai na ce a zuciya ta, ‘Menene kuma suke son su yi?’ Mutumin yana riƙe da butar ruwan sanyi kuma ya ba ni in sha. Ya roƙi gafara saboda rashin kunyarsa kuma ya yaba mini saboda bangaskiyata mai ƙarfi. Sai muka rabu lafiya.”

3. Me ya sa dole ne mu guji ƙyale wasu su ba mu haushi?

3 A duniya ta yau da ke cike da matsi, sau da yawa ba za mu iya guje wa saduwa da mutanen da suke fushi ba, har a hidimarmu. Sa’ad da hakan ya faru, yana da muhimmanci mu nuna “tawali’u da ban girma.” (1 Bit. 3:15; LMT) Da a ce ɗan’uwan da aka ambata a baya ya ƙyale fushi da rashin kirki na maigidan su ba shi haushi, mai yiwuwa halin mutumin ba zai canja ba; kuma da ya ƙara yin fushi. Domin ɗan’uwan ya kame kansa kuma ya yi magana mai ƙayatarwa, hakan ya kawo sakamako mai kyau.

Abin da Ke Sa Furci Ya Kasance Mai Ƙayatarwa

4. Me ya sa yin amfani da furci mai ƙayatarwa yake da muhimmanci?

4 Ko muna ma’amala ne da waɗanda suke ciki ko wajen ikilisiya, har da waɗanda suke cikin iyalinmu, yana da muhimmanci mu bi shawarar manzo Bulus: “Kullum maganarku ta zama mai kayatarwa, mai daɗin ji.” (Kol. 4:6) Irin wannan furci mai daɗin ji yana da muhimmanci don yin sadarwa mai kyau da kuma kasancewa da salama.

5. Sadarwa da kyau ba ya nufin menene? Ka ba da misali.

5 Sadarwa mai kyau ba ya nufin faɗin duk wani abin da ke cikin zuciyarka da kuma yadda kake ji a kowane lokaci, musamman ma idan kana fushi. Nassosi ya nuna cewa kasa iya kame fushinmu alamar kasawa ce, ba ƙarfi ba. (Karanta Misalai 25:28; 29:11.) Akwai lokacin da Musa “mai-tawali’u . . . ƙwarai” ya ƙyale tawayen al’ummar Isra’ila ya sa shi fushi sosai kuma ya ƙi ɗaukaka Allah. Musa ya bayyana dalla-dalla yadda yake ji, amma Jehobah bai yi farin ciki ba. Bayan shekara arba’in na shugabantar Isra’ilawa, Musa bai samu gatan yi musu ja-gora zuwa Ƙasar Alkawari ba.—Lit. Lis. 12:3; 20:10, 12; Zab. 106:32.

6. Kasancewa da basira a furcinmu yana nufin menene?

6 Nassosi ya ce mu riƙa kame kanmu kuma mu kasance da basira, ko sanin ya kamata, sa’ad da muke magana. “A cikin yawan maganganu ba a rasa saɓo ba: amma wanda ya iya wa bakinsa aikin hikima ya ke yi.” (Mis. 10:19; 17:27) Duk da haka, kasancewa da basira ba ya nufin cewa mutum ba zai taɓa faɗin ra’ayinsa ba. Yana nufin yin magana da “kayatarwa,” wato, mu yi amfani da harshen mu mu ƙarfafa mutane maimakon mu ɓata musu rai.—Karanta Misalai 12:18; 18:21.

“Lokacin Shuru da Lokacin Magana”

7. Waɗanne irin abubuwa ne bai kamata mu faɗa ba, kuma me ya sa?

7 Kamar yadda muke bukatan mu nuna ƙayatarwa da kuma kame kai sa’ad da muke magana da abokan aikinmu ko kuma baƙi a hidimar fage, muna kuma bukatan mu yi hakan a cikin ikilisiya da kuma gida. Yin magana da fushi ba tare da damuwa da sakamakon hakan ba, zai iya jawo lahani mai tsanani ga ruhaniyarmu, motsin ranmu, lafiyarmu da kuma ta wasu. (Mis. 18:6, 7) Dole ne mu kame mugun tunani, wato, nuna ajizancinmu. Baƙar magana, ba’a, raini, da kuma ƙiyayya ba su da kyau. (Kol. 3:8; Yaƙ. 1:20) Suna iya ɓata dangantaka mai tamani da mutane da kuma Jehobah. Yesu ya koyar da cewa: “Kowa ke fushi da ɗan’uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan’uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta.”—Mat. 5:22, LMT.

8. A wane lokaci ne za mu faɗi yadda muke ji, amma yaya za mu yi hakan?

8 Amma, akwai wasu batutuwan da za mu iya kammala cewa ya fi kyau mu tattauna su. Idan wani abu da wani ɗan’uwa ya ce ko ya yi yana damunka sosai da ba za ka iya yafewa ba, kada ka riƙe shi a zuciyarka. (Mis. 19:11) Idan wani ya ɓata maka rai, ka kame kanka kuma ka ɗauki mataki da ake bukata don ku magance batun. Bulus ya rubuta: “Kada rana ta faɗi kuna kan fushinku.” Domin matsalar ta ci gaba da damunka, ka bi da batun da kyau a lokacin da ya dace. (Karanta Afisawa 4:26, 27, 31, 32.) Ka yi magana da ɗan’uwanka game da batun, ka yi hakan ɓaro-ɓaro amma da ƙayatarwa, da muradin sulhuntawa.—Lev. 19:17; Mat. 18:15.

9. Me ya sa za mu kame fushinmu kafin mu tattauna da juna?

9 Hakika, ya kamata ka zaɓi lokacin da ya dace. Akwai “lokacin shuru da lokacin magana.” (M. Wa. 3:1, 7) Bugu da ƙari, “zuciyar mai-adalci ta kan yi tunanin abin da za ta amsa.” (Mis. 15:28) Hakan zai ƙunshi jira don a tattauna matsalolin. Yin hakan sa’ad da mutumin yake fushi sosai zai ƙara ɓata al’amuran; amma kuma ba shi da kyau a jira na dogon lokaci.

Ayyuka Masu Ƙayatarwa Suna Ɗaukaka Dangantaka Mai Kyau

10. Ta yaya yin ayyuka masu ƙayatarwa zai kyautata dangantaka?

10 Furci mai ƙayatarwa da kuma sadarwa mai kyau suna taimaka mana mu kafa dangantaka na salama kuma mu riƙe ta. Hakika, yin iya ƙoƙarinmu don mu kyautata dangantakarmu da wasu zai iya kyautata tattaunawarmu da su. Yin ayyukan alheri ga mutane da dukan zuciyarmu ta wajen neman zarafin ba da taimako, ba da kyauta da muradi mai kyau, da kuma nuna karimci suna sa tattaunawa ba ɓoye-ɓoye. Zai iya ‘tara garwashin wuta’ a kan mutum kuma ya fito da halayensa masu kyau, wanda zai sa tattauna batutuwa cikin sauƙi kuma a magance su.—Rom. 12:20, 21.

11. Yaya Yakubu ya ɗauki mataki don ya daidaita dangantakarsa da Isuwa, menene sakamakon?

11 Uban iyali Yakubu ya fahimci wannan. Tagwayensa, Isuwa, ya yi fushi da shi sosai har sai da Yakubu ya gudu don tsoron cewa Isuwa zai kashe shi. Bayan shekaru da yawa, Yakubu ya dawo. Isuwa ya fito don ya sadu da shi tare da maza ɗari huɗu. Yakubu ya yi addu’a don taimakon Jehobah. Sai ya aika kyauta mai yawa na tumaki kafin su sadu. Kyautar ta cim ma manufarta. Sa’ad da suka sadu, zuciyar Isuwa ta riga ta tausasa, kuma ya ruga ya rungumi Yakubu.—Far. 27:41-44; 32:6, 11, 13-15; 33:4, 10.

Ka Ƙarfafa Mutane da Furci Mai Ƙayatarwa

12. Me ya sa za mu yi amfani da kalamai masu ƙayatarwa ga ’yan’uwanmu?

12 Kiristoci suna bauta wa Allah ba mutane ba. Duk da haka, muna son samun amincewar mutane. Kalamanmu masu ƙayatarwa za su iya sauƙaƙa alhinin ’yan’uwanmu. Amma, mugun sukan mutane zai nauyaya alhininsu kuma ya sa wasu su yi tunanin ko sun rasa amincewar Jehobah. Saboda haka, bari mu gaya wa mutane abin da zai ƙarfafa su, “abin da ke mai-kyau garin ginawa yayinda ake bukata, domin shi ba da alheri ga waɗanda suke ji.”—Afis. 4:29.

13. Ya kamata dattawa su riƙa tunawa da menene (a) sa’ad da suke ba da shawara? (b) sa’ad da suke rubuta wasiƙu?

13 Ya kamata dattawa musamman su kasance da “taushin hali” kuma su bi da tumaki cikin ƙauna. (1 Tas. 2:7, 8, LMT) Sa’ad da bukata ta kama dattawa su ba da shawara, makasudinsu shi ne su yi hakan da “tawali’u,” har da lokacin da suke magana da “masu jayayya.” (2 Tim. 2:24, 25) Ya kamata dattawa su nuna ƙayatarwa sa’ad da bukata ta kama su rubuta wasiƙa zuwa ga wani rukunin dattawa ko kuma ofishin reshe. Ya kamata su yi hakan a hanyar da ta dace kuma cikin basira, cikin jituwa da abin da ke Matta 7:12.

Yin Amfani da Furci Mai Ƙayatarwa a Cikin Iyali

14. Wace shawara ce Bulus ya ba magidanta, kuma me ya sa?

14 Muna iya raina yadda kalamanmu, yanayin fuskarmu, da halinmu suke shafan mutane. Alal misali, wasu maza ba su san yadda kalamansu ke shafan mata ba. Wata ’yar’uwa ta ce, “Ina tsorata sa’ad da maigidana ya ɗaga muryarsa a cikin fushi a gare ni.” Kalamai masu zafi suna iya shafan mace sosai fiye da namiji kuma tana iya daɗe tana tunawa da su. (Luk 2:19) Hakan gaskiya ne musamman idan wanda mace take so kuma take darajawa ne ya faɗi kalaman. Bulus ya shawarci magidanta: “Ku mazaje, ku yi ƙaunar matayenku, kada kuwa ku yi fushi da su.”—Kol. 3:19.

15. Ka kwatanta abin da ya sa maigida zai bi da matarsa da hankali.

15 Game da wannan, wani ɗan’uwa da ya yi aure da daɗewa ya kwatanta abin da ya sa maigida zai bi da matarsa a hankali a matsayin “wadda ta fi rashin ƙarfi.” “Sa’ad da ka riƙe wani abu mai tamani kuma marar ƙwari, ba za ka riƙe shi da ƙarfi ba ainun, idan ba haka ba zai tsage kuma ya lalace. Ko da an gyara, za a ci gaba da ganin inda ya tsage,” in ji shi. “Idan maigida yana amfani da kalamai masu zafi, zai ɓata wa matarsa rai. Hakan yana iya jawo tsagewa na dindindin ga dangantakarsu.”—Karanta 1 Bitrus 3:7.

16. Ta yaya mace za ta gina iyalinta?

16 Maza ma suna iya samun ƙarfafawa ko kuma sanyin gwiwa ta wajen kalaman wasu, har da ta matansu. “Mata mai-hankali” wadda mijinta zai iya “dogara” da ita tana la’akari da yadda yake ji, kamar yadda take son ya yi la’akari da ita. (Mis. 19:14; 31:11) Hakika, mata tana iya kasancewa da tasiri mai kyau ko marar kyau a cikin iyali. “Kowace mace mai-hikima ta kan gina ɗakinta: Amma mai-wauta ta kan rushe shi da hannuwa nata.”—Mis. 14:1.

17. (a) Yaya ya kamata matasa su bi da iyayensu? (b) Yaya ya kamata tsofaffi su bi da matasa, kuma me ya sa?

17 Ya kamata iyaye da yara su yi magana da juna cikin ƙayatarwa. (Mat. 15:4) Sa’ad da muke magana da yara, sanin ya kamata zai taimaka mana mu guji yi musu “cakuna” ko kuma sa su “fushi.” (Kol. 3:21; Afis. 6:4.) Ko da za a yi wa yaran horon, ya kamata iyaye da dattawa su yi musu magana cikin daraja. Ta hakan, tsofaffi suna sa ya yi wa matasa sauƙi su daidaita tafarkinsu kuma su riƙe dangantakarsu da Allah. Hakan ya fi kyau maimakon nuna cewa sun yi nisa ba za su ji kira ba, kuma hakan zai sa su ma su yi tunanin cewa ba za a iya taimaka musu ba. Matasa ba za su iya tuna dukan gargaɗin da aka yi musu ba, amma za su tuna yadda wasu suka yi magana da su.

Faɗin Abubuwa Masu Ƙayatarwa Daga Zuciya

18. Ta yaya za mu kawar da mummunan tunani daga zuciyarmu?

18 Kame fushinmu ba ya nufin kasancewa kawai da ruwan masu salama ba. Ya kamata makasudinmu ya wuce ɓoye yadda muke ji. Yin ƙoƙarin kame fushinmu a waje yayin da zuciyarmu take tafasa a ciki yana ƙara mana nauyi. Yana kama ne da taka birkin mota da totur a lokaci ɗaya. Hakan na ƙara nauyin aikin motar kuma zai iya ɓata ta. Saboda haka kada ka ɓoye fushinka kuma daga baya ya sake tasowa. Ka yi addu’a ga Jehobah don ya taimake ka ka kawar da mugun tunani daga zuciyarka. Ka bari ruhun Jehobah ya canja zuciyarka don ka aikata cikin jituwa da nufinsa.—Karanta Romawa 12:2; Afisawa 4:23, 24.

19. Waɗanne ayyuka za su taimaka mana mu guji yanayi masu sa fushi?

19 Ka ɗauki matakin da zai taimaka maka ka kawar da yadda kake ji. Idan ka samu kanka a cikin matsanancin yanayi kuma ka ga cewa ka soma yin fushi, zai fi kyau ka bar wurin, don ka samu lokaci ka huce. (Mis. 17:14) Idan wanda kake yin magana da shi ya soma yin fushi, ka yi ƙoƙari sosai ka yi magana mai ƙayatarwa. Ka tuna: “Mayasda magana da taushi ya kan juyarda hasala: Amma magana mai-zafi ta kan tada fushi.” (Mis. 15:1) Baƙar magana za ta daɗa sa yanayin ya yi muni ko idan an yi ta da murya mai taushi. (Mis. 26:21) Saboda haka, sa’ad da wani yanayi ya gwada kame kanka, ka yi “jinkirin yin magana, [da] jinkirin yin fushi.” Ka yi addu’a don ruhun Jehobah ya taimaka maka ka faɗi abubuwa masu kyau, ba mugun abu ba.—Yaƙ. 1:19.

Gafartawa da Dukan Zuciya

20, 21. Menene zai taimaka mana mu gafarta wa wasu, kuma me ya sa za mu yi hakan?

20 Abin baƙin ciki, babu wani a cikinmu da zai iya kame harshensa gabaki ɗaya. (Yaƙ. 3:2) Duk da ƙoƙarce-ƙoƙarcensu, har waɗanda suke cikin iyali da ’yan’uwanmu ƙaunatattu a cikin ikilisiya suna iya faɗin abubuwa da garaje da za su ɓata mana rai. Maimakon mu yi fushi da sauri, cikin haƙuri ka bincika abin da ya sa suka faɗi hakan. (Karanta Mai Wa’azi 7:8, 9.) Suna cikin matsi ne, tsoro, rashin lafiya, ko kuwa suna fama ne da wata matsala da ba ka sani ba?

21 Irin waɗannan abubuwa ba dalili ba ne na yin fushi. Amma sanin waɗannan abubuwa zai taimaka mana mu fahimci abin da ya sa mutane a wani lokaci suke faɗi da kuma yin abubuwa da bai kamata su yi ba kuma hakan zai motsa mu mu riƙa gafartawa. Dukanmu mun faɗi kuma mun yi abubuwa da suka ɓata wa mutane rai, kuma muna sa rai cewa za su gafarta mana cikin alheri. (M. Wa. 7:21, 22) Yesu ya ce idan muna son Allah ya gafarta mana, dole ne mu gafarta wa mutane. (Mat. 6:14, 15; 18:21, 22, 35) Saboda haka, ya kamata mu yi saurin neman gafara da saurin gafartawa, ta haka mu ci gaba da kasancewa da ƙauna, “magamin kamalta” a cikin iyalinmu da kuma cikin ikilisiya.—Kol. 3:14.

22. Me ya sa yake da kyau sosai mu yi amfani da furci mai ƙayatarwa?

22 Zai daɗa zama da wuya mu kasance da farin ciki da haɗin kai yayin da wannan zamani mai fushi yake kai wa ga ƙarshensa. Bin ƙa’idodin da ke cikin Kalmar Allah zai taimaka mana mu yi amfani da harshenmu mu faɗi abubuwa masu ƙayatarwa, ba marar ƙayatarwa ba. Za mu more dangantaka ta salama a cikin ikilisiya da cikin iyali, kuma misalinmu zai ba da shaida mafi kyau ga mutane game da ‘Allahnmu mai farin ciki,’ Jehobah.—1 Tim. 1:11, New World.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Me ya sa yake da muhimmanci ka zaɓi lokacin da ya dace don ka tattauna matsaloli?

• Me ya sa ya kamata waɗanda suke cikin iyali su yi magana da juna cikin “kayatarwa”?

• Ta yaya za mu guji faɗin baƙar magana?

• Menene zai taimaka mana mu riƙa gafartawa?

[Hotuna da ke shafi na 21]

Ka huce tukun, sai ka nemi lokacin da ya dace ka yi magana

[Hoton da ke shafi na 23]

Ya kamata mutum a koyaushe ya yi magana a hankali da matarsa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba