Masu Karatu Sun Yi Tambaya . . .
Allah yana da mafari kuwa?
▪ Littafi Mai Tsarki ya amsa cewa Allah ba shi da mafari. Allah yana wanzuwa a koyaushe. Ba za mu iya yin watsi da batun cewa Allah yana wanzuwa ba, ko da yake fahimtar hakan yana da wuyan sosai.
Ya dace mu sa rai cewa za mu iya fahimtar dukan hanyoyin Allah kuwa? Manzo Bulus ya ce: “Oh! zurfin wadata na hikimar Allah duk da na saninsa! ina misalin wuyan binciken shari’unsa, al’amuransa kuma sun fi gaban a bincika su duka!” (Romawa 11:33) Ba za mu iya samun cikakken fahimtar zurfin hikima da sanin Allah ba kamar yadda jariri ba zai iya fahimtar kome game da iyayensa ba. Ko da yake waɗannan hurarrun kalamai na Bulus ainihi suna magana ne game da zurfin hikima da jin ƙan Allah, sun nuna cewa akwai fasalolin Jehobah Allah da ayyukansa da ba za mu iya fahimta ba. Batun cewa Allah ba shi da mafari yana ɗaya daga cikinsu. Duk da haka, za mu iya gaskata da abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da Allah. Game da littattafai masu tsarki, Yesu Kristi ya ce: “Maganarka ita ce gaskiya.”—Yohanna 17:17.
Musa ya ce a cikin addu’arsa ga Jehobah: “Tun fil’azal kai ne Allah har abada.” (Zabura 90:2) A nan Musa ya kwatanta wanzuwar Allah a hanyoyi biyu. Ɗayan game wanzuwarsa ce wadda ba ta da ƙarshe. Jehobah shi ne yake “rayuwa har zuwa zamanun zamanai.” (Ru’ya ta Yohanna 4:10) Saboda haka, Allah zai ci gaba da wanzuwa. Na biyun kuma ita ce game da wanzuwarsa wadda ba ta da mafari. Wato, ba a halicci Allah ba ko kuma ba shi da mafari. Maimakon haka, wanzuwarsa ba ta da iyaka.
Shi ya sa ya dace cewa Allah ne kaɗai yake da wannan laƙabin da babu kamarsa, wato, “Sarki na zamanu.” (1 Timotawus 1:17) Ka yi tunani: Yesu Kristi, mala’iku masu yawa a sama, da dukan mutanen da ke duniya suna da mafari domin an halicce su. (Kolosiyawa 1:15, 16) Amma ba haka yake da Allah ba. Nacewa an halicce Allah zai sa mu ci gaba da yin tunani marar ma’ana game da wanda ya halicci Mahaliccin. Amma, Jehobah ne kaɗai ya wanzu “tun fil’azal.” (Zabura 90:2) Wato, Jehobah ya wanzu “tun gaban zamanai duka.”—Yahuda 25.
Ka tuna cewa, zancen da aka yi cewa Allah ba shi da mafari ba ƙage ba ne. Yin la’akari da addu’ar Musa sosai ya bayyana cewa dawwamar Allah ya tabbatar da alkawari da aka yi mana na rai madawwami. Akasin rayuwarmu mai saurin wucewa, an kwatanta Allah a matsayin “mazauninmu tun cikin dukan tsararaki.” A matsayin Uba mai ƙauna, Jehobah ya wanzu, yana wanzuwa, kuma zai ci gaba da wanzuwa ga mutanensa. Bari wannan gaskiyar ta ƙarfafa ka.—Zabura 90:1.