Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 12/1 pp. 8-13
  • Jehovah Ka Koya Mana Mu Ƙididdiga Kwanakinmu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehovah Ka Koya Mana Mu Ƙididdiga Kwanakinmu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Jehovah—Ne “Mazauninmu”
  • Jehovah Yana Shirye Koyaushe Ya Taimake Mu
  • Jehovah Yana Taimaka Mana Mu “Ƙididdiga Kwanukanmu”
  • Albarkar Jehovah Tana Kawo Mana Farin Ciki
  • Bari Mu Ci Gaba da Ƙididdiga Kwanakinmu
  • Darussa Daga Littafin Zabura na Uku da na Huɗu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Jehobah Ne Mazauninmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Allah yana da mafari kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Jehovah Yana Kula Da Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 12/1 pp. 8-13

Jehovah Ka Koya Mana Mu Ƙididdiga Kwanakinmu

“Ka koya mana mu ƙididdiga kwanukanmu, da za mu samo zuciya mai-hikima.”—ZABURA 90:12.

1. Me ya sa ya dace mu gaya wa Jehovah ya koya “mana mu ƙididdiga kwanukanmu”?

JEHOVAH ALLAH Mahaliccinmu ne kuma Mai Ba da Rai. (Zabura 36:9; Ru’ya ta Yohanna 4:11) Saboda haka, babu wani da ya dace ƙwarai ya koya mana yadda za mu yi amfani da shekarun rayukanmu a hanya mai kyau. Hakika, mai Zabura ya roƙi Allah: “Ka koya mana mu ƙididdiga kwanukanmu, da za mu samo zuciya mai-hikima.” (Zabura 90:12) Zabura ta 90, inda muka samu wannan roƙo, babu shakka ta cancanci mu bincika ta a hankali. Amma da farko, bari mu ɗan bincika wannan waƙar da Allah ya hure.

2. (a) Waye ne aka ce ya rubuta Zabura ta 90, yaushe ne wataƙila aka rubuta ta? (b) Yaya ya kamata Zabura ta 90 ta shafi yadda muke ɗaukan rayuwa?

2 Rubutun saman Zabura ta 90 ya kira ta “addu’ar Musa, mutumin Allah na gaskiya.” Tun da wannan Zabura ta mai da hankali a kan gajeriyar rayuwar mutum ne, wataƙila an rubuta ta ne bayan an ceci Isra’ilawa daga bauta a ƙasar Masar da kuma lokacin tafiyarsu ta shekara 40 cikin daji, lokacin da mutuwar dubbai ta kawo ƙarshen tsara marar aminci. (Litafin Lissafi 32:9-13) Ko yaya dai, Zabura ta 90 ta nuna cewa rayuwar mutane ajizai gajeriya ce. A bayyane yake, ya kamata mu yi amfani da kwanakinmu mai tamani da kyau.

3. Menene musamman ke cikin Zabura ta 90?

3 A Zabura ta 90, ayoyi 1 zuwa 6 sun nuna cewa Jehovah mazauninmu ne na har abada. Ayoyi 7 zuwa 12 sun nuna abin da muke bukata don mu yi amfani da shekarunmu da ke wucewa da sauri a hanyar da zai amince da shi. Yadda aka furta cikin ayoyi 13 zuwa 17, da gaske muna son mu samu alherin Jehovah da albarka. Hakika, wannan zabura ba ta zancen abin da muke fuskanta ba, kowannenmu bawan Jehovah. Duk da haka, ya kamata mu lura kuma mu yi koyi da halin ibada kamar yadda aka furta cikin addu’a a wannan Zabura. Saboda haka, bari mu bincika Zabura ta 90 a hankali ta wajen waɗanda suka keɓe kansu ga Allah.

Jehovah—Ne “Mazauninmu”

4-6. Ta yaya ne Jehovah yake “mazauninmu”?

4 Mai Zabura ya soma da kalmomin nan: “Ya Ubangiji kai ne mazauninmu tun cikin dukan tsararaki. Tun ba a ɓullo da duwatsu, tun ba ka ko sifanta ƙasa da duniya [kamar da naƙuda], tun fil’azal kai ne Allah har abada.”—Zabura 90:1, 2.

5 A gare mu “Allah madawwami,” Jehovah, ‘mazauni ne na gaske’—mafaka ta ruhaniya. (Romawa 16:26) Muna da kwanciyar rai domin yana nan a kowane lokaci ya taimake mu shi “mai-jin addu’a.” (Zabura 65:2) Domin mun zuba wa Ubanmu na samaniya damuwarmu ta wajen ƙaunacaccen Ɗansa, ‘salama ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, tana tsare zukatanmu da tunaninmu.’—Filibbiyawa 4:6, 7; Matta 6:9; Yohanna 14:6, 14.

6 Muna more kwanciyar rai ta ruhaniya domin, a alamance, Jehovah ne “mazauninmu.” Yana kuma tanadin ‘ɗakunan ciki’—mai yiwuwa wannan yana haɗe da ikilisiyoyi na mutanensa—mafaka ta ruhaniya, inda makiyaya masu ƙauna suke sa mu kasance da kwanciyar rai. (Ishaya 26:20; 32:1, 2; Ayukan Manzanni 20:28, 29) Bugu da ƙari, wasu cikinmu sun fito daga iyalai da suke da tarihin hidima na shekaru da yawa ga Allah kuma sun iske shi ‘mazauni ne na gaske tun cikin tsararaki.’

7. A wane azanci aka “ɓullo” da duwatsu kuma aka sifanta duniya kamar da ‘naƙuda’?

7 Jehovah yana wanzuwa kafin a “ɓullo” da duwatsu ko kuma duniya kamar da ‘naƙuda.’ Idan a ganin mutane ne, sifanta wannan duniya da duka fannoninta, kyamistare, da ƙwayoyin rayuwa masu wuya suna bukatar ƙoƙari sosai. Cewa an “ɓullo” da duwatsu kuma an sifanta duniya kamar da ‘naƙuda,’ mai Zabura yana daraja yawan aiki da ke ciki ne yayin da Jehovah ya halicce waɗannan abubuwa. Bai kamata mu kasance da irin wannan daraja da godiya ga aikin Mahalicci ba?

Jehovah Yana Shirye Koyaushe Ya Taimake Mu

8. Menene furcin cewa Jehovah Allah ne ‘tun dā har abada’ yake nufi?

8 “Tun [dā] kai ne Allah har abada,” waƙar da mai Zabura ya rera ke nan. ‘Tun dā’ zai iya nuna abubuwa da suke da ƙarshe amma ba a faɗa daidai tsawon lokacin ba. (Fitowa 31:16, 17; Ibraniyawa 9:15) Amma, a Zabura 90:2 da wasu wurare cikin Nassosin Ibrananci, ‘tun dā’ na nufin “dawwama.” (Mai-Wa’azi 1:4) Zuciyarmu ba za ta iya fahimtar yadda ya yiwu cewa Allah yana wanzuwa koyaushe ba. Amma, Jehovah ba shi da mafari kuma ba shi da ƙarshe. (Habakkuk 1:12, NW ) Zai kasance a raye ko da yaushe kuma a shirye ya taimake mu.

9. Da menene mai Zabura ya gwada shekaru dubu na wanzuwar ’yan Adam?

9 An hure mai Zabura ya gwada shekaru dubu na wanzuwar ’yan Adam da gajeren lokaci a rayuwar Mahalicci madawwami. Wajen magana da Allah, ya rubuta: “Kana juyadda mutum shi zama ƙura; kana kuwa cewa, Ku komo, ku ’yan Adam. Gama shekara dubu a gareka kamar jiya ne da ya shige, kamar tsaro guda na dare.”—Zabura 90:3, 4.

10. Ta yaya Allah yake sa mutum ‘ya koma yadda yake’?

10 Mutum yakan mutu, Allah yana sa ‘shi koma yadda yake.’ Watau, mutum ya koma “turɓayar ƙasa” ƙasa da take ragargajewa. Watau, Jehovah ya ce: ‘Ka koma turɓayar ƙasa inda aka ciro ka.’ (Farawa 2:7; 3:19) Wannan ya shafi duka—mai ƙarfi ko marar ƙarfi, mawadaci ko matsiyaci—don babu mutum ajizi da ‘ya ke da iko shi fanshi ɗan’uwansa, ko ba da abin fansa ga Allah dominsa, da za shi rayu har abada.’ (Zabura 49:6-9) Amma muna godiya cewa ‘Allah ya ba da Ɗansa, makaɗaici, domin dukan wanda yana ba da gaskiya gareshi ya sami rai na har abada’!—Yohanna 3:16; Romawa 6:23.

11. Me ya sa za mu ce dogon lokaci gare mu gajere ne sosai ga Allah?

11 A ganin Jehovah, har ma Methuselah da ya rayu shekaru 969 bai kai kwana ɗaya ba. (Farawa 5:27) Wajen Allah shekara dubu jiya jiya ce—awoyi 24 kawai—yayin da ya wuce. Mai zabura ya ambata cewa ga Allah shekara dubu kamar tsaron awa huɗu ne na mai tsaron sansani daddare. (Alƙalawa 7:19) A bayyane yake, dogon lokaci a ganinmu gajere ne sosai ga madawwamin Allah, Jehovah.

12. Ta yaya Allah ya “kawar da” mutane?

12 Akasin madawwamin wanzuwar Allah, rayuwar ’yan Adam gajeriya ce. In ji mai Zabura: “Kana kawar da su, sai ka ce da rigyawa; suna da kamar barci: da safe suna kama da ciyawa mai-tsirowa. Da safe tana da harka, tana girma; da maraice a kan datse, ta kan yi yaushi.” (Zabura 90:5, 6) Musa ya ga dubban Isra’ilawa sun mutu cikin daji, Allah ya “kawar da su” sai ka ce a rigyawa. An fassara wannan sashe na zabura: “Ka share mutane a barcin mutuwa.” (New International Version) A wata sassa, rayuwar ’yan Adam ajizai “kamar barci” ne na gajeren lokaci—daidai da barci na dare ɗaya kawai.

13. Ta yaya muke “kama da ciyawa,” yaya ya kamata wannan ya shafi tunaninmu?

13 Muna ‘kama da ciyawa mai tsirowa, da take da harka da safe’ amma ta yi yaushi da yamma domin zafin rana. Hakika, rayuwarmu kama take da ciyawa da take yaushi a rana guda. Saboda haka, kada mu ɓata wannan abu mai tamani. Maimako, ya kamata mu nemi ja-gorar Allah a yadda ya kamata mu yi amfani da sauran shekarunmu a wannan zamani.

Jehovah Yana Taimaka Mana Mu “Ƙididdiga Kwanukanmu”

14, 15. Zabura 90:7-9 ta samu wace cika a kan Isra’ilawa?

14 Game da Allah mai Zabura ya daɗa cewa: “Cikin zafin fushinka an cinye mu, a cikin hasalarka kuma muna shan wahala. Ka sanya muguntanmu a gabanka, zunubanmu kuma na ɓoye ka sanya cikin hasken fuskarka. Gama dukan kwanakinmu sun wuce cikin fushinka: muna ƙare shekarunmu kamar labarin da aka faɗi.”—Zabura 90:7-9.

15 Isra’ilawa marasa bangaskiya ‘sun kai ƙarshensu cikin zafin fushin Allah.’ Sun ‘sha wahala ta wurin fushinsa,’ ko ‘razana ta wurin hasalarsa.’ (New International Version) Wasu aka “jirkice su cikin jeji” a sakamakon hukuncin Allah. (1 Korinthiyawa 10:5) Jehovah ya ‘sanya muguntarsu a gabansa.’ Za su ba da lissafi don muguntarsu a fili, har ma ‘abubuwansu na ɓoye,’ ko zunubai na ɓoye, suna ‘cikin hasken fuskarsa.’ (Misalai 15:3) Da yake Allah yana fushi da su, Isra’ilawa da suka ƙi tuba sun ‘ƙare shekarunsu kamar labari da aka faɗi.’ Saboda haka, rayuwarmu da gajeriya ce kamar numfashi da ke fitowa ta leɓunanmu kamar labari da aka faɗi.

16. Idan wasu suna zunubi a ɓoye, me ya kamata su yi?

16 Idan kowannenmu za mu yi zunubi a ɓoye, za mu iya ɓoye irin wannan halin daga ’yan’uwa ’yan Adam na ɗan lokaci. Amma zunubinmu da muka ɓoye za su ‘zama cikin hasken fuskar Jehovah,’ kuma ayyukanmu za su lalata dangantakarmu da shi. Don mu sake soma dangantaka da Jehovah, za mu bukaci mu yi addu’a don ya gafarta mana, mu bar zunubanmu, kuma mu karɓi taimako na ruhaniya na dattawa Kirista da godiya. (Misalai 28:13; Yaƙub 5:14, 15) Wannan zai fi kyau da ‘ƙare shekarunmu kamar labari da aka faɗi,’ begenmu na rai madawwami zai kasance cikin haɗari!

17. Yaya tsawon rayuwar galibin mutane, kuma shekarunmu na cike da menene?

17 Game da tsawon rayuwa na mutane ajizai, mai zabura ya ce: “Kwanukan shekarunmu shekara hauya uku ce da goma, idan kuwa domin ƙarfi sun kai hauya huɗu; fahariyarsu wahala ce da baƙin ciki: gama da sauri ya kan wuce, mu kan tashi.” (Zabura 90:10) Galibin mutane suna da tsawon rayuwa na shekara 70, a shekararsa ta 85, Kalibu ya yi maganar ƙarfinsa na musamman. Mutane kamar su Haruna da ya kai shekara (123), Musa (120), da Joshua (110) sun bambanta. (Litafin Lissafi 33:39; Kubawar Shari’a 34:7; Joshua 14:6, 10, 11; 24:29) Amma tsara da ba su da bangaskiya da suka fito daga ƙasar Masar, waɗanda aka ƙirga su daga masu shekara 20 zuwa sama sun mutu cikin shekaru 40. (Litafin Lissafi 14:29-34) A yau, a ƙasashe da yawa tsawon rayuwa na mutane galibi ya kasance daidai da yadda mai Zabura ya faɗa. Shekarunmu suna cike da ‘wahala da baƙin ciki.’ Suna wucewa da sauri, “mu kan tashi.”—Ayuba 14:1, 2.

18, 19. (a) Menene yake nufi “mu ƙididdiga kwanukanmu, da za mu samo zuciya mai-hikima”? (b) Yin amfani da hikima za ta motsa mu mu yi menene?

18 Mai zabura ya ci gaba da rera waƙa: “Wa ke sane da ikon fushinka, zafin fushinka kuma gwargwadon tsoron da ya wajaba gareka? Ka koya mana mu ƙididdiga kwanukanmu, da za mu samo zuciya mai-hikima.” (Zabura 90:11, 12) Babu wani cikinmu da ya san cikakken zafin fushin Allah ko yawansa, wannan ya kamata ya ƙara tsoronmu na girmama Jehovah. Hakika, ya kamata ya motsa mu mu tambaye shi yadda za “mu ƙididdiga kwanukanmu da za mu samo zuciya mai-hikima.”

19 Kalmomin mai Zabura addu’a ce cewa Jehovah ya koya wa mutanensa yadda za su yi hikima a daraja da kuma amfani da sauran kwanakinsu a hanya da Allah yake so. Rayuwa ta shekaru 70 za ta sa a kasance da bege na wasu kwanaki 25,500. Amma, ko nawa ne shekararmu, ‘ba mu san abin da za ya faru gobe ba, domin rayuwarmu hazo ce da kan bayyana na ɗan lokaci kāna ya watse.’ (Yaƙub 4:13-15) Tun da yake ‘sa’a da tsausayi sukan sami kowannenmu,’ ba za mu iya faɗin tsawon yadda za mu rayu ba. Saboda haka, bari mu yi addu’a don hikima mu bi da gwaji, mu bi da wasu yadda ya dace, kuma mu yi iyakar ƙoƙarinmu a hidimar Jehovah a yanzu—a yau! (Mai-Wa’azi 9:11; Yaƙub 1:5-8) Jehovah yana yi mana ja-gora ta wurin Kalmarsa, ruhunsa, da ƙungiyarsa. (Matta 24:45-47; 1 Korinthiyawa 2:10; 2 Timothawus 3:16, 17) Amfani da hikima na motsa mu mu ‘biɗi Mulkin Allah da farko’ kuma mu yi amfani da kwanakinmu a hanyar da za ta kawo yabo ga Jehovah kuma ta faranta zuciyarsa. (Matta 6:25-33; Misalai 27:11) Bauta masa da dukan zuciyarmu ba za ta cire dukan matsalarmu ba, amma babu shakka za ta kawo mana farin ciki sosai.

Albarkar Jehovah Tana Kawo Mana Farin Ciki

20. (a) A wace hanya ce Allah ya yi ‘nadama’? (b) Yaya Jehovah zai bi da mu idan mun yi kuskure mai tsanani amma mun tuba da gaske?

20 Zai yi kyau sosai idan za mu yi farin ciki duk sauran rayuwarmu! Game da wannan, Musa ya yi roƙo: “Sai yaushe za ka juyo, ya Ubangiji? Ka [yi nadama] kuma ga zancen bayinka. Ka ƙosadda mu da jinƙanka [ko ƙauna ta aminci] da safe: domin mu yi farinzuciya, mu yi murna kuma dukan kwanakinmu.” (Zabura 90:13, 14; hasiya na NW ) Allah ba ya kuskure. Amma, yana ‘nadama’ kuma ya “juyo” daga fushinsa da kuma daga yin horo yayin da kashedinsa game da aikata hakan ya sa mai laifi da ya tuba ya canja halinsa. (Kubawar Shari’a 13:17) Saboda haka, ko idan mun yi kuskure mai tsanani ma amma muka tuba da gaske, Jehovah zai ‘cika mu da jinƙansa,’ kuma za mu samu dalilin ‘yin farin zuciya.’ (Zabura 32:1-5) Ta bin tafarki na adalci, za mu fahimci ƙaunar aminci na Allah dominmu za mu iya “murna kuma dukan kwanakinmu”—hakika, a sauran rayuwarmu.

21. A kalmomi da ke rubuce a Zabura 90:15, 16, menene ƙila Musa yake roƙo?

21 Mai Zabura ya yi addu’a sosai: “Ka faranta mana zuciya gwargwadon kwanakin da ka wahalshe mu, gwargwadon shekaru kuma inda mun ga mugunta. Ka bari aikinka shi bayyana ga bayinka, darajarka kuma bisa ’ya’yansu.” (Zabura 90:15, 16) Ƙila Musa yana gaya wa Allah ya albarkaci Isra’ila da farin ciki da ya yi daidai da ko kuma da daɗewarsa zai yi daidai da kwanakinsu na azaba da shekaru da suka wahala. Ya ce “aikin” Allah na yi wa Isra’ilawa albarka ya bayyana ga bayinsa kuma darajarsa ta bayyana a kan ’ya’yansu, ko kuma zuriyarsu. Zai yi kyau mu yi addu’a cewa a zuba wa mutane masu biyayya albarka a sabuwar duniya da Allah ya yi alkawarinta.—2 Bitrus 3:13.

22. In ji Zabura 90:17, menene ya dace mu yi addu’a a kai?

22 Zabura ta 90 ta kammala da wannan roƙon: “Bari jamalin Ubangiji Allahnmu shi zauna a bisanmu: ka tabbatar mana da aikin hannuwanmu; i, aikin hannuwanmu ka tabbatadda shi.” (Zabura 90:17) Waɗannan kalmomi sun nuna cewa za mu iya addu’a Allah ya albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu a hidimarsa. Shafaffu Kiristoci ko abokan tarayyarsu, “waɗansu tumaki,” muna farin ciki cewa “jamalin Ubangiji” ya kasance da mu. (Yohanna 10:16) Muna farin ciki cewa Allah ya ‘tabbatar da aikin hannuwanmu’ mu masu shelar Mulki da kuma a wasu hanyoyi!

Bari Mu Ci Gaba da Ƙididdiga Kwanakinmu

23, 24. Ta yaya za mu amfana a yin bimbini a kan Zabura ta 90?

23 Yin bimbini a kan Zabura ta 90 ya kamata ya ƙara dogararmu ga Jehovah, “mazauninmu.” Ta yin bimbini a kan kalmominta game da gajeriyar rayuwa, ya kamata mu daɗa sanin bukatar ja-gorar Allah a ƙididdiga kwanakinmu. Kuma idan mun nace a neman kuma nuna hikima ta ibada, mu tabbata za mu samu alheri da kuma albarkar Jehovah.

24 Jehovah zai ci gaba da koya mana yadda za mu ƙididdiga kwanakinmu. Idan mun bi gargaɗinsa, za mu iya ci gaba da ƙididdiga kwanakinmu har abada. (Yohanna 17:3) Amma, idan za mu saka rai madawwami a zuci, dole ne Jehovah ya zama mafakarmu. (Yahuda 20, 21) Yadda za mu gani a talifi na gaba, an bayyana wannan darasi a kalmomi mai ƙarfafawa na Zabura ta 91.

Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya ne Jehovah “mazauninmu”?

• Me ya sa za mu faɗi cewa Jehovah yana shirye koyaushe ya taimake mu?

• Ta yaya Jehovah yake taimaka mana mu “ƙididdiga kwanukanmu”?

• Me ke taimaka mana mu “yi murna kuma dukan kwanakinmu”?

[Hoto a shafi na 9]

Jehovah Allah ne “tun ba a ɓullo da duwatsu” ba

[Hoto a shafi na 10]

A ra’ayin Jehovah, Methuselah ɗan shekara 969 bai kai kwana ɗaya ba

[Hotuna a shafi na 12]

Jehovah ya ‘tabbatar da aikin hannuwanmu’

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba