Maganar Jehobah Rayayya Ce
Darussa Daga Littafin Zabura na Uku da na Huɗu
DA YAKE wa Allah addu’a, mai zabura ya yi tambaya: “Za a bada labarin rahamarka cikin kabari? Ko kuwa amincinka cikin Hallaka?” (Zabura 88:11) Amsar a’a ne. Idan ba mu da rai ba za mu iya yabon Jehobah ba. Yabon Jehobah dalili ne mai kyau na kasancewa a raye, kuma kasancewa a raye dalili ne mai kyau na yabonsa.
Littafin Zabura na Uku da na Huɗu da suka ƙunshi Zabura ta 73 zuwa 106 sun ba da dalilai masu yawa na yabon Mahaliccinmu da kuma sunansa. Yin bimbini a kan wannan zabura ya kamata ya zurfafa godiyarmu ga “maganar Allah” kuma ya motsa mu mu faɗaɗa da kuma kyautata furcinmu na yabo ga Allah. (Ibraniyawa 4:12) Da marmari na ƙwarai, bari mu fara duba Littafin Zabura na Uku.
“YA YI MINI KYAU IN KUSANCI ALLAH”
(Zabura 73:1–89:52)
Asaph ko kuma waɗanda suke gidansa ne suka rubuta surori 11 na farko na wannan littafi na uku. Waƙar buɗewa ta bayyana abin da ya ceci Asaph daga bauɗewa ta wurin mummunan tunani. Ya kammala da kyau. Ya ce: “Ya yi mini kyau in kusanci Allah.” (Zabura 73:28) A Zabura ta 74 an yi makoki domin an halaka Urushalima. Zabura ta 75, 76, da 77 sun nuna cewa Jehobah Alƙali ne Mai adalci, Mai Ceton adalai, da kuma Mai Jin addu’a. Zabura ta 78 ta maimaita rayuwar Isra’ila ta dā daga lokacin Musa zuwa na Dauda. Zabura ta 79 ta yi makokin halaka haikalin. Sai kuma addu’ar maidowar mutanen Allah. Zabura ta 81 ta yi gargaɗi ne a yi wa Jehobah biyayya. Zabura ta 82 da 83 addu’a ce Jehobah ya zartar da hukuncinsa a kan lalatattun alƙalai da kuma abokan gaban Allah.
“Raina yana marmari, har ya yi yaushi domin muradin gidajen Ubangiji” in ji waƙar ’ya’yan Kora. (Zabura 84:2) Zabura ta 85 roƙo ne don albarkar Allah a kan waɗanda suka dawo daga bauta. Wannan zabura ta nanata cewa albarka ta ruhaniya ta fi albarka ta zahiri amfani. A Zabura ta 86, Dauda ya roƙi Allah ya tsare shi kuma ya koyar da shi. A Zabura ta 87, an rera waƙa game da Sihiyona da waɗanda aka haifa a wajen, bayan haka aka yi wa Jehobah addu’a a Zabura ta 88. A Zabura ta 89 an nanata ƙauna ta alherin Jehobah yadda aka furta a alkawarin da aka yi wa Dauda, da Ethan ya rubuta, wataƙila yana cikin maza huɗu masu hikima a kwanakin Sulemanu.—1 Sarakuna 4:31.
Tambayoyin Nassi da aka Amsa:
73:9—Ta yaya miyagu suka “kafa bakinsu a sama, harshensu kuwa yana yawo a ƙasa”? Tun da yake miyagu ba sa daraja kowa a sama ko kuma a duniya, suna saɓa wa Allah da bakinsu. Suna kuma tsegunta mutane da harshensu.
74:13, 14—Yaushe ne Jehobah ya ‘farfasa kawunan dodanni a cikin ruwaye kuma ya ragargaza kawunan Leviathan’? An kira “Fir’auna sarkin Masar,” “babban dragon mai-kwantawa ciki rafufukansa.” (Ezekiel 29:3) Mai yiwuwa Leviathan na wakiltar mutane masu ƙarfi na Fir’auna. (Zabura 74:14) Ragargaza kawunansu mai yiwuwa na nufin yadda aka ci Fir’auna da sojojinsa sa’ad da Jehobah ya ceci Isra’ilawa daga bautar Masar.
75:4, 5, 10—Menene kalmar nan “ƙaho” yake nufi? Ƙahonin dabba makami ne mai ƙarfi. Saboda haka, kalmar nan “ƙaho” a alamance na nuna iko, ko kuma ƙarfi. Jehobah ya ta da ƙahonin mutanensa, ya ɗaukaka su, amma ‘ƙahonin miyagu ya datse.’ An gargaɗe mu kada mu ‘ta da kahonmu a sama’ domin kada mu kasance da halin fahariya ko girman kai. Tun da yake Jehobah ne yake ɗaukaka mutum, hakki na ikilisiya daga wajensa ne.—Zabura 75:7.
76:10—Ta yaya “fushin mutum” zai yi yabon Jehobah? Sa’ad da Allah ya ƙyale ’yan adam su nuna fushinsu a kanmu domin mu bayinsa ne, za a sami sakamako mai kyau. Kowace wahala da muke fuskanta za ta iya koya mana wani abu. Jehobah ya ƙyale wahala don mu sami irin wannan koyarwa. (1 Bitrus 5:10) ‘Sauran fushi Allah zai hana.’ Idan muka wahala har muka mutu fa? Wannan ma zai yabi Jehobah domin waɗanda suka ga mun jimre cikin aminci su ma za su soma ɗaukaka Allah.
78:24, 25;—Me ya sa aka kira manna “hatsin sama” da “abincin mai-iko”? Duka furcin ba sa nufin cewa manna abincin masu iko ne. “Hatsin sama” ne domin daga sama ne ya fito. (Zabura 105:40) Tun da yake mala’iku ko kuma ‘masu iko’ suna zama a sama, furcin nan “abincin mai-iko” mai yiwuwa yana nufin cewa Allah wanda yake sama ne ya yi tanadinsa. (Zabura 11:4) Wataƙila Jehobah ya yi amfani da mala’iku wajen yi wa Isra’ilawa tanadin manna.
82:1, 6—Su waye aka kira “alloli” da “ ’ya’yan Maɗaukaki”? Duka furcin na nuni ga alƙalai na ’yan adam a Isra’ila. Wannan daidai ne da yake suna hidima na kakakin Allah da kuma wakilai.—Yohanna 10:33-36.
83:2—Menene “tada kai” yake nufi? Alamar kasancewa a shirye ne wajen nuna iko ko kuma aikatawa, don a hukunta, a yi faɗa ko kuma zalunta.
Darussa Dominmu:
73:2-5, 18-20, 25, 28. Kada mu yi kishin arzikin miyagu kuma mu soma bin hanyoyinsu na rashin ibada. Miyagu suna wuri mai santsi. Babu shakka za su sha “magangarin halaka.” Ƙari ga haka, tun da yake ba za a iya cire mugunta a sarautar ’yan adam ajizai ba, yin ƙoƙarin kawar da ita zai zama aikin banza. Kamar Asaph, yana da kyau mu jimre mugunta ta wajen ‘kusantar Allah’ da kuma kasancewa da dangantaka ta kud da kud da shi.
73:3, 6, 8, 27. Dole ne mu kauce wa yin fahariya, girman kai, ba’a, da yin zamba. Ya kamata mu yi hakan ko da irin waɗannan halaye za su kasance kamar za su amfane mu.
73:15-17. Ko da mun rikice, bai kamata mu furta mamakinmu a fili ba. ‘Faɗan’ irin wannan labarin zai sa wasu sanyin gwiwa. Ya kamata mu yi bimbini game da damuwarmu kuma mu magance su ta wajen yin tarayya da ’yan’uwanmu masu bi.—Misalai 18:1.
73:21-24. An kamanta ‘damuwa’ domin zaman lafiyar miyagu da dabbobi da ba sa tunani. Ana wannan bisa motsin rai ne. Maimakon haka, ya kamata umurnin Jehobah ya yi mana ja-gora, mu kasance da tabbaci cewa zai ‘riƙe mu a hannunmu na dama’ kuma ya tallafa mana. Ƙari ga haka, Jehobah zai ‘karɓe mu zuwa daraja,’ wato mu soma dangantaka na kud da kud da shi.
77:6. Damuwa don gaskiya ta ruhaniya da kuma bincika su sosai na bukatar nazari da yin bimbini. Yana da muhimmanci mu nemi inda babu kowa don mu riƙa yin bimbini!
79:9. Jehobah yana saurarar addu’armu, musamman sa’ad da muka yi ta domin tsarkakewar sunansa.
81:13, 16. Saurarar muryar Jehobah da kuma tafiya a hanyoyinsa suna kawo albarka mai yawa.—Misalai 10:22.
82:2, 5. Rashin gaskiya ta sa “tussan duniya” su girgiza. Ayyukan ta da hankali na damun zaman lafiyar jam’iyyar ’yan adam.
84:1-4, 10-12. Yadda masu zabura suke daraja wurin bautar Jehobah da yadda suke gamsuwa da gatar hidimarsu ya kafa mana misali mai kyau.
86:5. Muna farin ciki cewa Jehobah “mai-hanzarin gafartawa” ne! Yana neman kowane tabbaci da zai ba shi dalilin nuna jinƙai ga mai laifin da ya tuba.
87:5, 6. Waɗanda za su yi rayuwa a cikin Aljanna a duniya za su taɓa sanin sunayen waɗanda aka tashe su zuwa rayuwa na sama kuwa? Waɗannan ayoyin sun nuna cewa zai yiwu.
88:13, 14. Idan bai amsa addu’armu game da wata matsala da sauri ba, yana nufin cewa Jehobah yana son mu nuna tabbacin bautarmu a gare shi.
“KU YI MASA GODIYA, KU ALBARKACI SUNANSA”
(Zabura 90:1–106:48)
Ka yi la’akari da dalilai dabam dabam da ya sa za mu ɗaukaka Jehobah da aka ambata a littafi na huɗu na zabura. A Zabura ta 90, Musa ya bambanta “Sarki na zamanu” da rayuwar ɗan adam mai saurin wucewa. (1 Timothawus 1:17) A Zabura 91:2, Musa ya ce Jehobah ne ‘mafakarsa da marayarsa’ wato, Tushen kwanciyar ransa. Sauran zabura na gaba sun yi magana a kan halayen Allah masu kyau, tunaninsa mafifici, da ayyukansa masu ban al’ajabi. Zabura uku sun soma da wannan furci “Ubangiji ya ke mulki.” (Zabura 93:1; 97:1; 99:1) Da yake magana cewa Jehobah ne Mahaliccinmu, mai zabura ya gayyace mu mu ‘yi masa godiya, mu albarkaci sunansa.’—Zabura 100:4.
Ta yaya ya kamata sarkin da yake jin tsoron Jehobah ya ja-goranci harƙoƙinsa? Zabura ta 101 da Sarki Dauda ya rubuta ta ba da amsar. Zabura ta gaba ta gaya mana cewa Jehobah zai “ji addu’ar masu-mayata, ba ya rena addu’arsu ba.” (Zabura 102:17) Zabura ta 103 ta jawo hankali ga ƙaunar alherin Jehobah da kuma jinƙansa. Da yake maganar abubuwa da yawa da Allah ya yi a duniya, mai zabura ya ce: “Ya Ubangiji, ayyukanka ina misalin yawansu! Da hikima ka yi su duka.” (Zabura 104:24) Waƙoƙi biyu na ƙarshe na Littafi na Huɗu sun yabi Jehobah don ayyukansa masu ban al’ajabi.—Zabura 105:2, 5; 106:7, 22.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
91:1, 2—Menene “sitirar Maɗaukaki,” ta yaya za mu ‘zauna’ a wajen? Wannan wuri ne na alama na mafaka da kwanciyar rai na ruhaniya, wato, yanayin kāriya daga lahani na ruhaniya. Wannan wuri ne na asiri domin waɗanda ba su dogara da Allah ba ba su san wurin ba. Muna mai da Jehobah sitirarmu ta wurin sa ya zama mafakarmu da marayarmu, ta wajen yabonsa a matsayin Mamallakin sararin samaniya, da kuma ta wurin wa’azin bisharar Mulki. Muna da kwanciyar rai na ruhaniya domin mun san cewa Jehobah yana shirye ya taimake mu.—Zabura 90:1.
92:12—A wace hanya ce adalai suke “yabanya kamar giginya”? An san icen giginya da ba da ’ya’ya masu yawa. Mai adalci yana kamar giginya domin adali ne a gaban Jehobah kuma ya ci gaba da ba da “ ’ya’yan kirki” waɗanda suka haɗa da ayyuka masu kyau.—Matta 7:17-20.
Darussa Dominmu:
90:7, 8, 13, 14. Laifinmu koyaushe na ɓata dangantakarmu da Allah na gaskiya. Kuma ba za a iya ɓoye masa zunubai ba. Amma, idan muka tuba da gaske kuma muka daina bin mummunar tafarkinmu, Jehobah zai mai da mana tagomashinsa, kuma ya ‘ƙosarda mu da jinƙansa.’
90:10, 12. Tun da yake rayuwa gajeriya ce, ya kamata muna “ƙididdiga kwanukanmu.” Ta yaya? Ta wajen “samo zuciya mai-hikima,” ko kuma ta wajen nuna hikima domin kada mu ɓata sauran kwanakinmu, amma mu yi rayuwa yadda zai faranta wa Jehobah rai. Muna bukatar mu sa abubuwa na ruhaniya farko kuma mu yi amfani da lokacinmu da kyau.—Afisawa 5:15, 16; Filibbiyawa 1:10.
90:17. Ya dace mu yi addu’a Jehobah ya “tabbatar mana da aikin hannuwanmu” kuma ya albarkace ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu a hidima.
92:14, 15. Ta wajen zama ɗalibai da suke nazarin Kalmar Allah sosai da kuma tarayya da mutanen Jehobah a kai a kai, tsofaffi sun ci gaba “cike da romo da ɗanyantaka” wato, ƙwazo a ruhaniya, kuma suna da tamani a ikilisiya.
94:19. Ko menene dalilin “wasuwasi” da muke yi, karatu da kuma bimbini a kan ‘ta’aziyya’ da ke cikin Littafi Mai Tsarki zai ƙarfafa mu.
95:7, , 8. Saurarar gargaɗin Nassi, mai da hankali gare shi, da kuma yin biyayya da gargaɗin zai hana mu zama masu taurin zuciya.—Ibraniyawa 3:7, 8.
106:36, 37. Waɗannan ayoyin sun kwatanta bauta wa gumaka da yi wa aljannu hadaya. Wannan ya nuna cewa aljani ne ke rinjayar mutum da ke amfani da gumaka. Littafi Mai Tsarki ya aririce mu: “Ku tsare kanku daga gumaka.”—1 Yohanna 5:21.
Ku Yabi Jehobah
Waƙoƙi uku na ƙarshe na Littafin Zabura na Huɗu sun kammala da wannan umurnin: “Hallelujah,” wadda ke nufin ku yabi Jehobah. Zabura na ƙarshe ma ya soma da hakan. (Zabura 104:35; 105:45; 106:1, 48) Hakika, furcin nan “Hallelujah” ya bayyana sau da yawa a Littafin zabura na Huɗu.
Muna da dalilai da yawa na yabon Jehobah. Zabura 73 zuwa 106 sun ba da dalilai da yawa na yin bimbini, don mu yi godiya ga Ubanmu na samaniya. Idan muka yi tunanin dukan abubuwa da ya riga ya yi mana kuma zai yi mana a nan gaba, za mu motsa mu ‘yabi Jehobah’ da dukan ƙarfinmu.
[Hoto a shafi na 28]
Kamar Asaph, za mu jimre wa mugunta ta ‘kusantar Allah’
[Hoto a shafi na 29]
An ci Fir’auna a Jar Teku
[Hoto a shafi na 29]
Ka san abin da ya sa aka kira manna abincin ‘masu iko’?
[Hoto a shafi na 31]
Menene zai kawar da ‘waswasinmu’?