Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 6/1 pp. 29-31
  • Darussa Daga Littafin Zabura na Ɗaya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Littafin Zabura na Ɗaya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “ALLAHNA PANA MAI-ƘARFI”
  • (Zabura 1:1–24:10)
  • “KANA RIƘE DA NI CIKIN KAMALATA”
  • (Zabura 25:1–41:13)
  • “Albarka ga Ubangiji”
  • Hurarrun Waƙoƙi da Suke Ƙarfafawa da Koyarwa
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
  • Darussa Daga Littafin Zabura na Biyu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Darussa Daga Littafin Zabura na Biyar
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Darussa Daga Littafin Zabura na Uku da na Huɗu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 6/1 pp. 29-31

Maganar Jehobah Rayayyiya Ce

Darussa Daga Littafin Zabura na Ɗaya

WANE jigo ne ya dace da Littafin da ke ɗauke da yabon Jehobah Allah Mahalicci? Babu sunan da ya dace fiye da Zabura, ko kuma Yabo. Wannan Littafi mai tsawo a cikin Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da waƙoƙi masu kyau da suka ambaci shahararun ingancin Allah da ayyukansa masu girma da kuma annabce-annabcensa. Yawanci suna furta ra’ayin waɗanda suka rubuta waƙoƙin ne sa’ad da suke cikin wahala. Wannan furcin ya ɗauki tsawun shekara dubu daga zamanin annabi Musa zuwa zamanin Yahudawa. Waɗanda suka rubuta su ne Musa, Sarki Dauda, da sauran su. An yaba wa firist Ezra, saboda yadda ya shirya Littafin har ƙarshe.

Tun a zamanin dā, an raba Littafin Zabura zuwa waƙoƙi kashi biyar, ko kuma sashe: (1) Zabura 1–41; (2) Zabura 42-72; (3) Zabura 73-89; (4) Zabura 90-106; da kuma (5) Zabura 107–150. Wannan talifi yana ɗauke da sashe na farko. Zabura uku ne kawai cikin wannan sashe ba a ce Sarki Dauda na Isra’ila ta dā ne ya rubuta ba. Ba a ambata waɗanda suka rubuta Zabura ta 1,10, da ta 33 ba.

“ALLAHNA PANA MAI-ƘARFI”

(Zabura 1:1–24:10)

Bayan da surar farko ta Zabura ta sanar cewa mai albarka ne mutum wanda marmarinsa cikin shari’a ta Jehobah yake, ta biyu kuma ta yi magana a kan jigon Mulki.a Roƙo zuwa ga Allah ne ya cika wannan sashe na Zabura. Alal misali, Zabura ta 3-5,7,12,13 da kuma 17, suna ɗauke ne da roƙe-roƙe don samun ceto daga hannun maƙiya. Zabura ta 8 ta kwatanta girman Jehobah da kuma ƙanƙantan mutum.

Dauda ya kwatanta Jehobah a matsayin mai kāre mutanensa, sa’ad da ya ce: “Allah pana mai-ƙarfi, a cikinsa zan dogara.” (Zabura 18:2) An yabi Jehobah a matsayin Mahalicci da kuma mai ba da doka a cikin Zabura sura 19, mai ceto a Zabura sura 20, kuma mai ceton shafaffen Sarkinsa a Zabura ta 21. Zabura sura 23 ta ce da shi makiyayi mai girma, sa’an nan Zabura ta 24 ta ƙira shi Sarki Mai-Girma.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

2:1, 2—Wane “al’amarin wofi” ne al’ummai suke tunaninsa? “Al’amarin wofi” shi ne damuwa ta kullum ta gwamnatin ’yan Adam na su ci gaba da kula da ikonsu. Wannan al’amarin wofi ne saboda ba za su ci nasara ba. Al’ummai za su iya cin nasara kuwa, bayan “suna gaba da Jehobah da Masihansa”?

2:7—Menene ‘ƙadaran Jehobah’? Wannan ƙadarar alkawari ne na Mulki, wanda Jehobah ya yi da ƙaunataccen Ɗansa, Yesu Kristi.—Luka 22:28, 29.

2:12—Ta yaya ne masu sarautar al’ummai za su “yi ma ɗa sumba”? A lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, sumba alama ce mai nuna abokantaka da kuma aminci. Hanyar karɓan baki ce. An umurci sarakunan duniya su sumbace ɗan wato, su marabci Sarki Almasihu.

3:Rubutu na sama a Zabura ta Ainihi—Menene ma’anar rubutu na sama da aka rubuta a Zabura ta ainihi? A wani lokacin ana amfani da rubutu na sama domin bayyana wanda ya rubuta littafin ko kuma a yi bayani akan yanayin da ake ciki sa’ad da aka shirya Zaburar, alal misali Zabura ta 3. Rubutu na sama kuma yana bayyana manufar waƙar (Zabura sura 4 da sura 5) da kuma umurni a kan kiɗe-kiɗe (Zabura sura 6).

3:2—“Menene Selah” a Zabura ta ainihi? Wannan kalmar tana nufin lokacin dakatawa a yi bimbini a lokacin waƙa ko kuma waƙa da kiɗe-kiɗe. Ana amfani da Kalmar ne don bayyana manufar waƙar. Babu amfanin karanta wannan kalmar a lokacin karatun Zabura a gaban jama’a.

11:3—Waɗanne tushe ne aka rushe? Ainihin tushe ne na rayuwar mutane wato, doka, ka’ida, da kuma shari’a. Sa’ad da waɗannan suka birkice, za a sami rashin zaman lafiya da kuma rashin aminci. A cikin irin waɗannan yanayin, dole ne “mai-adalci” ya dogara ga Allah.—Zabura 11:4-7.

21:3—Menene ma’anar “kambi na zaɓaɓɓiyar zinariya”? Ba a faɗi ko kambin na zahiri ne ko kuma na alama ne ba domin ya daɗa ɗaukaka Dauda domin nasarori masu yawa da ya yi. Amma, wannan ayar cikin annabci tana nufin kambi na sarauta da Yesu ya karɓa a hannun Jehobah a shekara ta 1914. Da yake an yi kambin da zinariya, wannan ya nuna cewa sarautar mai girma ce.

22:1, 2—Me ya sa Dauda ya ji kamar Jehobah ya yi watsi da shi? Dauda yana cikin matsi ne sosai a hannun maƙiyansa waɗanda suka sa ‘zuciyarsa kamar sham’a take ta narke a tsakiyar cikinsa.’ (Zabura 22:14) A ganinsa Jehobah ya yi watsi da shi ne. Yesu ya ji haka sa’ad da aka rataye shi. (Matta 27:46) Kalmomin Dauda sun nuna yadda ya ji a cikin irin wannan yanayi. Hakika, a cikin addu’arsa a Zabura 22:16-21 Dauda ya nuna cewa bai taɓa yin rashin bangaskiya ga Allah ba.

Darussa Dominmu:

1:1. Mu guji yin abokantaka da waɗanda ba sa ƙaunar Allah.—1 Korinthiyawa 15:33.

1:2. Ka da mu bar rana guda ta wuce ba tare da yin la’akari da al’amura na ruhaniya ba.

4:4. Idan mu na cikin fushi, kada mu faɗi abin da zai sa mu yi da na sani.—Afisawa 4:26.

4:5. Hadayarmu na ruhaniya ‘hadaya ce ta adalci’ idan ta fito daga cikin zuciyar kirki da kuma hali da ya yi daidai da dokokin Jehobah.

6:5. Menene ainihin dalilin da ya sa ka ke son ka ci gaba da rayuwa?—Zabura 115:17.

9:12. Jehobah yana duban waɗanda suka yi kisan kai domin ya hukunta su, amma yana tunawa da ‘kukan talakawa.’

15:2, 3; 24:3-5. Dole ne masu bauta ta gaskiya su faɗi gaskiya kuma su guji ƙarya da tsegumi.

15:4. Mu yi ƙoƙari mu cika alkawarin mu, ko da yana da wuya, sai dai idan muka fahimci cewa ya saɓa wa Nassosi.

15:5. Dole ne masu bauta wa Jehobah su kula da yadda suke amfani da kuɗi.

17:14,15. “Mutanen duniya” sun ba da kansu ga neman rayuwa mai kyau, kula da iyali, da kuma tara dukiya. Abu mai muhimmanci a rayuwar Dauda shi ne ya yi nagarin suna a gaban Allah saboda ya ‘duba fuskarsa,’ ko kuma ya sami alherin Jehobah. Da zarar ya “farka” sa’ad da Jehobah ya cika alkawarinsa, Dauda ya yi farin ciki cewa Jehobah yana tare da shi. Kamar Dauda, ya kamata mu kula da dukiya ta ruhaniya.

19:1-6. Idan har halitta da ba ta iya magana ba, ko kuma ta fahimci abubuwa, tana ɗaukaka Jehobah, mai zai hana mu, mu da muke tunani da magana mu bauta wa Allah?—Ru’ya ta Yohanna 4:11.

19:7-11. Farillan Jehobah na da amfani a garemu!

19:12,13. Kuskure da girman kai zunubai ne da ya kamata mu guje wa.

19:14. Ka da mu kula da abin da muke yi kawai amma mu kula da abin da muke faɗa da kuma muke tunani.

“KANA RIƘE DA NI CIKIN KAMALATA”

(Zabura 25:1–41:13)

A cikin Zabura biyu na farko a wannan sashen, Dauda ya furta sha’awarsa ta zuci da kuma ƙudurinsa mai ƙarfi don ci gaba da riƙe amincinsa! Dauda ya ce: “Amma ni, a cikin gaskiyata zan yi zamana.” (Zabura 26:11) A cikin addu’arsa ta neman gafarta daga zunubi, ya ce: “Lokacin da na yi shuru, ƙasusuwana suka tsufa domin rurina da na yina ina yi.” (Zabura 32:3) Dauda ya ba amintattun Jehobah wannan tabbaci: “Idanun Ubangiji suna fuskanta wajen masu-adalci; kunnuwansa kuma a buɗe su ke ga jin ƙararsu.”—Zabura 34:15.

Shawarar da aka ba da a Zabura sura 37 na da muhimmanci ga Isra’ilawa da kuma mu da muke cikin kwanaki na ƙarshe na wannan zamani! (2 Timothawus 3:1-5) Sa’ad da ya ke yin annabci game da Yesu Kristi, Zabura 40:7, 8 sun ce: “Ga ni, na zo; a cikin naɗaɗɗen littafi rubutacce ne a kaina: Murna ni ke yi in yi nufinka, ya Allahna, hakika, shari’arka tana cikin zuciyata.” Zabura ta ƙarshe ta kunshi roƙon Dauda ga Jehobah don ya taimake shi a lokacin wahalarsa bayan da ya yi zina da Bath-sheba. Ya ce: “Ni dai kana riƙe da ni cikin kamalata.”—Zabura 41:12.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

26:6—Kamar Dauda, ta yaya ne muka kewaye bagadin Jehobah a alamance? Bagadin na nuna nufin Jehobah ya karɓi hadayar fansa ta Yesu Kristi domin fansar mutane. (Ibraniyawa 8:5; 10:5-10) Muna kewaye bagadin Jehobah ta wajen ba da gaskiya ga hadayar.

29:3-9—Menene ake nufi sa’ad da aka ce muryar Jehobah tana kama da tsawa da ke da ban tsoro? Ma’anarsa ita ce: Iko mai girma na Jehobah!

31:23—Ta yaya ne masu girman kai suke samun sakamako mai yawa? Sakamakon shi ne hukunci. Jehobah yana ba wa mutum mai aminci sakamakonsa idan ya yi kuskure ba da gangan ba. Tun da mai girman kai ba zai canza mugun halinsa ba, za a ba shi sakamako mai yawa na horo.—Misalai 11:31; 1 Bitrus 4:18.

33:6—Menene ruhu ko kuma “lumfashin” bakin Jehobah? Wannan ruhu ikon aiki ne na Allah, ko kuma ruhu mai tsarki, wanda ya yi amfani da shi wurin halittar abubuwa da ke cikin sama. (Farawa 1:1, 2) Ana ce da shi ruhun bakinsa saboda, kamar lumfashi mai ƙarfi, za a iya aikansa ya cim ma abubuwa da ke nesa.

35:19—Menene ma’anar roƙon da Dauda ya yi sa’ad da ya ce kada a bar waɗanda ke ƙinsa ba dalili su runtsi ido? Idan maƙiyan Dauda suka runtsa idanunsu, zai nuna cewa suna jin daɗin nasarar da suke samu daga mugun shiri da suke yi a kansa. Dauda ya yi roƙon cewa kada hakan ya kasance.

Darussa Dominmu:

26:4. Abin hikima ne mu guji yin abokantaka da waɗanda suke ɓoye kamaninsu a wurin hira na intane, waɗanda suke son su zama abokanmu ta hanyar zamba a makaranta ko a wurin aiki, ko ’yan ridda da suke yi kamar su sahihan mutane ne, da kuma waɗanda suke yin rayuwa iri biyu.

26:7,12; 35:18; 40:9. Dole ne mu yabi Jehobah a taron jama’a ta Kirista.

26:8; 27:4. Muna son halartan taron Kirista?

26:11. Sa’ad da yake furta ƙudurinsa don ya ci gaba da amincinsa, Dauda ya yi roƙo domin fansa. Hakika, za mu iya daidaita amincinmu ko da yake mu ajizai ne.

29:10. Jehobah yana zaune a bisa “rigyawa,” wannan ya nuna cewa yana da iko.

30:5. Halin Jehobah na musamman shi ne ƙauna ba fushi ba.

32:9. Jehobah ba ya son mu zama kamar alfadari ko kuma jaki da sai da linzami ko bulala yake biyayya. Maimakon haka, ya shawarce mu, mu yi masa biyayya domin mun fahimci manufarsa.

33:17-19. Babu wani mutum da zai iya kawo salama komin ƙarfinsa. Dole ne mu dogara ga Jehobah da tsarin Mulkinsa.

34:10. Wannan tabbaci ne ga waɗanda suka sa Mulkin Allah a gaba!

39:1,2. Idan mugayen mutane suka nemi wani bayani don su cuci ’yan’uwanmu masu bi, zai yi kyau idan muka ‘rufe bakinmu da takunkumi’ muka yi shiru.

40:1, 2. Sa’ad da muke cikin baƙin ciki, Jehobah zai taimake mu mu jimre kuma mu fita “daga cikin rami mai-halakarwa, daga cikin laka mai-kafo” idan muka dogara gare shi.

40:5,12. Kome yawan bala’i ko kuma kasawar da muke fuskanta, ba za su sha kanmu idan ba mu manta cewa albarkarmu “sun fi gaban lissafi” ba.

“Albarka ga Ubangiji”

Zabura 41 na littafi na ɗaya suna ta’azantarwa kuma suna ƙarfafamu! Idan muna fuskantar wahala, jarabobbi ko damuwa game da wani laifi, za mu sami ƙarfafa daga cikin wannan kalmar Allah. (Ibraniyawa 4:12) Littafin Zabura na cike da bayani da ke ba da tabbatacciyar shawara a harkar rayuwa. Muna da tabbaci cewa ko da wace irin wahala ce muke fuskanta, Jehobah ba zai yashe mu ba.

Sashe na farko na Zabura ya ƙare da waɗannan kalmomi: “Albarka ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, tun daga farko har abada. Amin, kuma Amin.” (Zabura 41:13) Bayan mun gama yin la’akari da su, za su motsa mu, mu yabi Jehobah.

[Hasiya]

a Zabura ta 2 ta samu cikanta ta farko a zamanin Dauda.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba