Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 7/1 p. 18-p. 20
  • Darussa Daga Littafin Zabura na Biyu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Littafin Zabura na Biyu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • JEHOBAH “MAFAKANMU NE DA ƘARFINMU”
  • (Zabura 42:1–50:23)
  • “RAINA, KA YI SAURARO GA ALLAH”
  • (Zabura 51:1–71:24)
  • “BARI DUKAN DUNIYA TA CIKA DA DARAJASSA”
  • (Zabura 72:1-20)
  • Darussa Daga Littafin Zabura na Ɗaya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Hurarrun Waƙoƙi da Suke Ƙarfafawa da Koyarwa
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
  • Darussa Daga Littafin Zabura na Biyar
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Darussa Daga Littafin Zabura na Uku da na Huɗu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 7/1 p. 18-p. 20

Maganar Jehobah Rayayya Ce

Darussa Daga Littafin Zabura na Biyu

MU BAYIN Jehobah mun sani za mu fuskanci jarabobbi da gwaji. “Dukan waɗanda su ke so su yi rai mai-ibada cikin Kristi Yesu za su sha tsanani.” (2 Timothawus 3:12) Menene zai taimake mu mu jimre wa jarabobbi da tsanantawa, ta haka kuma mu tabbatar da amincinmu ga Allah?

Sashe na biyu cikin biyar na zabura zai taimaka mana. Zabura ta 42 zuwa 72 sun nuna mana cewa idan muna so mu jimre gwaji cikin nasara, dole ne mu dogara ga Jehobah kuma mu saurari cetonsa. Wannan darassi ne mai muhimmanci a gare mu! Saƙon da yake cikin littafi na biyu na Zabura, kamar na sauran Kalmar Allah hakika, “mai-rai ce, mai-aikatawa” har a yau.—Ibraniyawa 4:12.

JEHOBAH “MAFAKANMU NE DA ƘARFINMU”

(Zabura 42:1–50:23)

Balawi yana zaman bauta. Yana baƙin ciki ba zai iya zuwa haikalin Jehobah ya bauta masa ba, ya ƙarfafa kansa, yana cewa: “Don minene ka ke tagumi, ya raina? Don minene ka ke alhini a cikina? Ka kafa bege ga Allah.” (Zabura 42:5, 11; 43:5) Wannan ayar da aka yi ta maimaita ta ta haɗa baiti uku na Zabura ta 42 da ta 43 cikin waƙa guda. Zabura ta 44 roƙo ce domin Yahuda, al’ummar da take cikin matsaloli, wataƙila sa’ad da Assuriyawa suke mata barazana a zamanin Sarki Hezekiah.

Zabura ta 45, waƙa ce game da auren sarki, annabci ne na Sarki Almasihu. Zabura uku da suka biyo baya sun kwatanta Jehobah da cewa “mafakanmu ne da ƙarfinmu,” “Babban Sarki ne bisa dukan duniya,” kuma “mafaka ne a cikin fadodinta.” (Zabura 46:1; 47:2; 48:3) Zabura ta 49 ta nuna da kyau cewa babu mutumin da zai iya “fanshi ɗan’uwansa”! (Zabura 49:7) Zabura takwas na fari a sashe na biyu an ce ’ya’yan Kora ne suka rubuta. Ta tara, wato Zabura ta 50, Asaf ne ya rubuta.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

44:19—Menene “wurin diloli”? Wataƙila mai zabura yana nufin filin daga ne, inda waɗanda aka kashe sukan zama abincin diloli.

45:13, 14a—Wacece “ɗiyar sarki” da “za a kai ta wurin sarki”? Ɗiyar “Sarkin zamanai,” ce Jehobah Allah. (Ru’ya ta Yohanna 15:3) Tana wakiltan ikilisiyar Kiristoci waɗanda aka ɗaukaka ne, su 144,000 waɗanda Jehobah ya karɓa suka zama ’ya’yansa ta wajen shafa su da ruhu. (Romawa 8:16) Wannan “ɗiya” ta Jehobah, “shiryayya kamar amarya da ado domin mijinta,” za a kawo ta wurin mijinta, Sarki Almasihu.—Ru’ya ta Yohanna 21:2.

45:14b, 15—Su wanene “budurwai” suke wakilta? Suna wakiltan “taro mai-girma” na masu bauta ta gaskiya, waɗanda suke taimaka wa raguwar shafaffu. Tun da sun fito daga “babban tsanani” da rai, za su kasance a duniya sa’ad da aka kammala aure na Sarki Almasihu a samaniya. (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 13, 14) A wannan lokaci za su cika da “murna fa farinzuciya.”

45:16—A wace hanya ce za a sami ’ya’ya a madadin kakannin sarki? Sa’ad da aka haifi Yesu a duniya, yana da kakanni da yawa. Za su zama ’ya’yansa sa’ad da ya ta da su daga matattu a lokacin sarautarsa ta Shekara Dubu. Wasu za su kasance cikin waɗanda za a “maishe su sarakuna cikin dukan duniya.”

50:2—Me ya sa aka kira Urushalima “kamilin jamali”? Ba domin kyaun birnin ba ne na zahiri. Kyaun Urushalima domin Jehobah yana amfani da ita ne da kuma kyaun da ya ba ta da ya mai da ita wurin haikalinsa da kuma babban birnin sarakuna da ya naɗa.

Darussa Dominmu:

42:1-3. Kamar yadda mariri, a ƙasar da babu ruwa yake marmarin ruwa, haka Lawiyawa suke bukatar Jehobah. Baƙin cikin mutumin yana da yawa ƙwarai domin bai iya bauta wa Jehobah ba a haikalinsa saboda haka har ‘hawayensa sun zama abincinsa dare da rana’—ya kasa cin abinci. Bai kamata mu ƙaunaci bautar Jehobah tare da ’yan’uwa masu bi ba?

42:4, 5, 11; 43:3-5. Idan domin wasu dalilai, muka yi nesa da ikilisiyar Kirista, tunanin farin cikin tarayya da muka yi a baya zai ƙarfafa mu. Ko da yake irin wannan a farko zai tsananta kewarmu, zai kuma tuna mana cewa Allah shi ne mafakarmu kuma ya kamata mu dogara a gare shi domin ceto.

46:1-3. Kowace irin matsala muke fuskanta, dole ne mu kasance da cikakken dogara ga Jehobah cewa “Allah mafakanmu ne da ƙarfinmu.”

50:16, 17. Dukan mutumin da yake yaudara da bakinsa kuma yake aikata miyagun abubuwa ba shi da dalilin wakiltan Allah.

50:20. Maimakon yaɗa kurakuran wasu, ya kamata mu yi haƙuri da su.—Kolossiyawa 3:13.

“RAINA, KA YI SAURARO GA ALLAH”

(Zabura 51:1–71:24)

Waɗannan tarin zabura sun fara ne da addu’ar Dauda bayan ya yi zina da Bath-sheba. Zabura ta 52 zuwa 57 sun nuna cewa Jehobah zai ceci waɗanda suka ɗaura masa nauyinsu kuma suka saurare shi domin ceto. Kamar yadda aka furta a Zabura na 58 zuwa 64, a dukan lokacin wahalolinsa, Jehobah ne mafakan Dauda. Ya rera waƙa: “Raina, ka yi sauraro ga Allah kaɗai; Gama daga gareshi begena ya ke.”—Zabura 62:5.

Abokantaka na kusa ya kamata ya motsa mu mu rera waƙa kuma mu “furta darajar sunansa.” (Zabura 66:2) An yabi Jehobah cewa mai tanadi ne hannu sake a Zabura ta 65, kuma Allah mai ceto a Zabura ta 67 da ta 68, kuma Allah mai yin hanyar tsira a Zabura ta 70 da ta 71.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

51:12—Da ‘ruhu na yardan ran’ waye, Dauda ya roƙa a tokara masa da shi? Wannan ba ya nufin yardan ran Allah ya taimaki Dauda ko kuma ruhu mai tsarki na Jehobah, amma yana nufin ruhun Dauda kansa, wato son ransa. Yana roƙon Allah ne ya saka masa a zuciya muradin yin abin da ke nagari.

53:1—Ta yaya mutumin da ya musanta wanzuwar Allah “wawa” ne? Wawanci a nan ba ya nufin rashin wayo ba ne. Wato irin wannan mutum wawa ne na ɗabi’a kuma haka ya bayyana a rashin ɗabi’a da aka kwatanta a Zabura 53:1-4.

58:3-5—A wace hanya ce miyagu suke kamar maciji? Ƙarya da suke yi game da wasu kamar dafin maciji ne. Suna lalata sunan mutane. “Suna kama da kāsa kurma mai-toshe kunenta,” mugu ba ya saurarar ja-gora ko gargaɗi.

58:7—Ta yaya mugu yake “narke kamar ruwan da ke gudu da sauri”? Wataƙila Dauda yana tunanin ruwan wasu ƙwari ne na Ƙasar Alkawari. A take ruwan zai ƙaru a irin wannan ƙwarin, wannan ruwan da wuri yake bushewa. Dauda yana addu’a ne domin miyagu su shuɗe da wuri.

68:13—Ta yaya “fukafukan kurciya rufe da azurfa, jawarkinta kuma da zinariya rawaya?” Wasu irin kurciyoyi masu launi shuɗi-shuɗi da ruwan toka-toka suna da wasu launi a fukafukansu. Gashinsu sai ya koma kamar ƙarfe idan suna cikin rana. Wataƙila Dauda yana kwatanta Isra’ilawa mayaƙa ne da suka ci nasara da waɗannan kurciyoyi, masu fukafukai masu ƙarfi kuma masu haske. Kuma kamar wata shawara da masana suka bayar wannan zai iya kasancewa kwatancin wani abu ne da aka kwato ganima. Ko da yaya dai, Dauda yana magana ne game da nasarori da Jehobah ya ba wa mutanensa bisa abokan gabansu.

68:18—Su waye ne “kyautai a wurin mutane”? Waɗannan mutane ne da aka kama bauta a lokacin da aka ci Ƙasar Alkawari a yaƙi. Irin waɗannan daga baya aka ba da su ga Lawiyawa su taya su aiki.—Ezra 8:20

68:30—Menene roƙon nan a “tsauta ma naman jejin nan na fadama” yake nufi? A alamance ne yake kiran abokan gaban mutanen Jehobah naman jeji, Dauda yana roƙon Allah ne ya tsauta musu, ko kuma ya rage ƙarfinsu na yin lahani.

69:23—Menene ma’anar ‘sa gadon bayan abokan gaban ya riƙa rawa kullum’? Tsoka da ke gadon baya tana da muhimmanci wurin yin ayyuka masu wuya, kamar su ɗaukan kayaki masu nauyi. Gadon baya masu nauyi na nufin rashin ƙarfi. Dauda ya yi addu’a a hana abokan gabansa ƙarfi.

Darussa Dominmu:

51:1-4, 17. Yin zunubi bai kamata ya ware mu daga Jehobah Allah ba. Idan muka tuba, za mu iya kasancewa da tabbacin jinƙansa.

51:5, 7-10. Idan mun yi zunubi, za mu iya roƙon Jehobah ya gafarta mana domin mun gaji zunubi ne. Ya kamata kuma mu yi addu’a ya tsarkake mu, ya mayar da mu, ya taimake mu mu kawar da muradin zunubi daga zuciyarmu, kuma ya ba mu ruhu mai jimrewa.

51:18. Zunuban Dauda sun yi barazana ga lafiyar dukan al’ummar. Saboda haka ya yi addu’a domin albarkar Allah ga Sihiyona. Sa’ad da muka yi zunubi mai tsanani, sau da yawa yana jawo zagi ga sunan Jehobah da kuma ikilisiya. Muna bukatar mu yi wa Allah addu’a ya gyara lahani da muka yi.

52:8. Za mu iya kasancewa kamar “ɗanyen itacen zaitun cikin gidan Allah,” muna kusa da Jehobah muna ba da ’ya’ya a hidimarsa, ta wajen yi masa biyayya da kuma karɓar horonsa da son rai.—Ibraniyawa 12:5, 6.

55:4, 5, 12-14, 16-18. Haɗin baki na ɗansa Absalom da kuma cin amanar da amintaccen mashawarcinsa Ahithophel ya yi masa, ya ta da wa Dauda hankali sosai. Duk da haka, wannan bai rage dogarar da Dauda ya yi da Jehobah ba. Kada mu ƙyale tashin hankali ya raunana dogarar da muka yi da Allah.

55:22. Ta yaya za mu zuba wahalar mu ga Jehobah? Muna yin haka ne na (1) ta wajen gaya wa Allah damuwarmu cikin addu’a, (2) ta wajen juyawa ga Kalmarsa da kuma ƙungiyarsa ga ja-gora da kuma taimako, na (3) ta wajen yin abin da za mu iya yi mu kyautata yanayin.—Misalai 3:5, 6; 11:14; 15:22; Filibbiyawa 4:6, 7.

56:8. Jehobah yana sane da yanayinmu da kuma yadda haka zai shafe mu.

62:11. Allah ba ya dogara da wani domin ƙarfi. Shi ne tushen ƙarfi. ‘Iko ga Allah ya tabbata.’

63:3. Allah “rahamarsa ta fi gaban rai” domin idan babu ita, rai ba shi da wani ma’ana. Hikima ne mu yi abota da Allah.

63:6. Dare, lokaci da kome ya yi tsit babu abu mai raba hankali, zai kasance lokaci ne mai kyau domin bimbini.

64:2-4. Tsegumi zai iya ɓata sunan mutum. Bai kamata mu saurari irin wannan tsegumi ba ko kuma mu yaɗa su.

69:4. Domin mu kasance da salama, wani lokaci zai kasance hikima ce mu “bayar” ta wajen ba da haƙuri, ko da yake mun tabbata ba mu yi laifi ba.

70:1-5. Jehobah yana saurarar roƙonmu na taimako. (1 Tassalunikawa 5:17; Yaƙub 1:13; 2 Bitrus 2:9) Allah yana iya ƙyale gwaji ya ci gaba, duk da haka zai ba mu hikima mu bi da yanayin da kuma ƙarfi domin mu jimre. Ba zai ƙyale a gwada mu fiye da yadda za mu iya jimrewa ba.—1 Korinthiyawa 10:13; Ibraniyawa 10:36; Yaƙub 1:5-8.

71:5, 17. Dauda ya koyi gaba gaɗi da zuciya ta wajen dogara ga Jehobah a ƙuruciyarsa, kafin ma ya fuskanci Goliath gwarzon Filistiyawa. (1 Samuila 17:34-37) Ya kamata matasa su yi ƙoƙari su dogara ga Jehobah a dukan abin da suke yi.

“BARI DUKAN DUNIYA TA CIKA DA DARAJASSA”

(Zabura 72:1-20)

Waƙa ta ƙarshe a sashe na biyu na Zabura game da sarautar Sulemanu ne, ya annabta irin yanayin da zai kasance a zamanin mulkin Almasihu. An kwatanta albarkatai masu ban sha’awa a nan, yalwar salama, ƙarshen mugunta da fin ƙarfi, yalwar abinci a duniya! Za mu kasance kuwa tsakanin waɗanda za su more waɗannan da kuma wasu albarkatai na mulki? Za mu more idan kamar mai zabura, muna sauraron Jehobah, muka mai da shi mafakanmu kuma ƙarfinmu.

“Addu’o’in Dauda,” sun ƙare da waɗannan kalmomi: “Albarka ga Ubangiji Allah, Allah na Isra’ila, Wanda yana aika al’ajabai shi kaɗai: Kuma albarka ga sunansa mai-daraja har abada; Bari dukan duniya ta cika da darajassa. Amin, Amin kuma.” (Zabura 72:1-20) Bari mu ma mu yi wa Jehobah albarka kuma mu yabi sunansa mai ɗaukaka.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba