Sashe 11
Hurarrun Waƙoƙi da Suke Ƙarfafawa da Koyarwa
Dauda da wasu sun haɗa waƙoƙi don bauta. Littafin Zabura yana ƙunshe da guda 150
LITTAFI mafi girma a cikin Littafi Mai Tsarki shi ne na waƙoƙi masu tsarki. An rubuta dukan littafin ne a misalin shekaru 1,000. Littafin Zabura yana ɗauke da wasu daga cikin furcin bangaskiya masu girma kuma masu motsawa da aka taɓa rubutawa. An kwatanta motsin rai na mutane dabam-dabam a cikin waɗannan waƙoƙi na yabo, an kwatanta farin ciki, godiya, baƙin ciki, da kuma tuba. A bayyane yake cewa waɗanda suka rubuta zaburar suna da dangantaka na kud da kud da Allah. Yi la’akari da wasu batutuwan da aka tattauna a cikin waɗannan waƙoƙin.
Jehobah ne Mai Ikon Mallaka, kuma ya cancanci bauta da yabo. Mun karanta a Zabura 83:18 cewa, “Kai, wanda sunanka Jehovah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.” Zabura masu yawa sun yi yabon Jehobah domin ayyukansa na halitta, kamarsu taurari a sama, rayuwa mai ban al’ajabi a duniya, da kuma jikin mutum mai ban mamaki. (Zabura 8, 19, 139, 148) Wasu kuma sun ɗaukaka Jehobah a matsayin Allahn da ya ɗauki matakai don ya ceci waɗanda suke bauta masa da aminci kuma ya kāre su. (Zabura 18, 97, 138) Wasu sun ɗaukaka shi a matsayin Allah mai adalci, wanda yake kawo sauƙi ga waɗanda ake zalunta kuma ya hukunta mugaye.—Zabura 11, 68; 146.
Jehobah yana taimaka wa waɗanda suke ƙaunarsa kuma yana ƙarfafa su. Wataƙila zaburar da aka fi sani ita ce ta 23, inda Dauda ya kwatanta Jehobah a matsayin Makiyayi mai ƙauna, wanda ke yi wa tumakinsa ja-gora, yana kāre su, kuma yana kula da su. Zabura 65:2 ta tuna wa masu bauta wa Allah cewa Jehobah “Mai-jin addu’a” ne. Mutane da yawa da suka yi mugun zunubi sun sami ƙarfafa daga Zabura ta 39 da 51, inda Dauda ya kwatanta tubansa da kalaman gaskiya kuma ya furta bangaskiyarsa a gafarar Jehobah. Zabura 55:22 tana ɗauke ƙarfafawa ta dogara ga Jehobah da kuma ɗaura dukan damuwa a kansa.
Jehobah zai canja duniya ta hanyar Mulkin Almasihu. Surori da yawa a cikin Zabura suna nuni ne ga Almasihu, Sarkin da aka annabta. Zabura ta 2 ta annabta cewa wannan Sarkin zai halaka mugayen al’ummai, da suke hamayya da shi. Zabura ta 72 ta bayyana cewa wannan Sarkin zai kawar da yunwa, rashin adalci, da zalunci. In ji Zabura 46:9, ta hanyar Mulkin Almasihu, Allah zai kawar da yaƙi kuma ya halaka dukan makaman yaƙi. A Zabura ta 37, mun karanta cewa za a halaka miyagu, kuma masu adalci za su rayu a duniya har abada, suna more salama da kuma haɗin kai a dukan duniya.
—An ɗauko daga littafin Zabura.
◼ Ta yaya ne Zabura ya tallafa wa ikon da Jehobah yake da shi na yin sarauta?
◼ Waɗanne zabura ne suka nuna yadda yake taimako da kuma ƙarfafa waɗanda suke ƙaunarsa?
◼ In ji littafin Zabura, ta yaya ne Allah zai canja duniya?
[Akwati a shafi na 14]
WAƘAR WAƘOƘI
A cikin Waƙar Sulemanu, sarkin ya bayyana cewa yawan arziki ba ya nufin cewa zai sami duk abin da yake so a batutuwan soyayya. Ya rubuta labarin ƙoƙarin da ya yi don wata budurwa ta ƙaunace shi wadda ta riga ta soma soyayya da wani yaro makiyayi. Wannan hurarriyar waƙar ta nuna cewa sa’ad da mutane suka so juna, suna bukatan su guje wa yin abin da bai dace ba. Waɗannan masoyan sun nuna kamun kai, ɗabi’a mai kyau, da kuma aminci.
[Taswira a shafi na 14]
Farawa
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
1 Sama’ila
2 Sama’ila
1 Sarakuna
2 Sarakuna
1 Labarbaru
2 Labarbaru
Ezra
Nehemiya
Esther
Ayuba
● Zabura
Misalai
Mai-Wa’azi
● Waƙar Waƙoƙi
Ishaya
Irmiya
Makoki
Ezekiel
Daniyel
Hosiya
Joel
Amos
Obadiya
Yunana
Mikah
Nahum
Habakkuk
Zafaniya
Haggai
Zakariya
Malakai
Matta
Markus
Luka
Yohanna
Ayyukan Manzanni
Romawa
1 Korintiyawa
2 Korintiyawa
Galatiyawa
Afisawa
Filibiyawa
Kolosiyawa
1 Tasalonikawa
2 Tasalonikawa
1 Timotawus
2 Timotawus
Titus
Filimon
Ibraniyawa
Yaƙub
1 Bitrus
2 Bitrus
1 Yohanna
2 Yohanna
3 Yohanna
Wasiƙa ta Yahuda
Ru’ya ta Yohanna