Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 3/15 pp. 19-23
  • Jehobah Ne Mazauninmu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Ne Mazauninmu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • JEHOBAH NE AINIHIN ‘MAZAUNIN’ BAYINSA NA DĀ
  • JEHOBAH NE AINIHIN “MAZAUNINMU” A YAU
  • JEHOBAH ZAI CI GABA DA ZAMA “MAZAUNINMU”
  • Jehobah Ne “Allah Mai Ba Da Salama”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Shi “Allah na . . . Masu Rai” Ne
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Yakubu da Isuwa Sun Shirya
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Tagwaye Da Suka Bambanta
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 3/15 pp. 19-23

Jehobah Ne Mazauninmu

“Ya Ubangiji kai ne mazauninmu tun cikin dukan tsararaki.”—ZAB. 90:1.

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya Jehobah ya zama ainihin ‘mazaunin’ Ibrahim da Ishaƙu da kuma Yaƙubu?

  • Mene ne za mu koya daga misalin Ibrahim?

  • Ta yaya za mu nuna cewa Jehobah ne ainihin “mazauninmu”?

1, 2. Yaya bayin Allah suke ji game da wannan duniya, kuma wane gida ne suke da shi?

KANA da kwanciyar hankali a cikin wannan muguwar duniya? Idan amsarka a’a ce, ba kai kaɗai ba ne. Tun zamanin dā, dukan waɗanda suke ƙaunar Jehobah suna ji kamar su baƙi ne a wannan duniya. Alal misali, waɗanda suka bauta wa Allah da aminci da suka ƙaura zuwa wurare dabam-dabam a ƙasar Kan’anan, sun ‘shaida su baƙi ne, alhazai cikin duniya.’—Ibran. 11:13.

2 Hakazalika, shafaffu mabiyan Kristi, waɗanda suke “yangaranci cikin sama” suna ɗaukan kansu a matsayin “saukakku, baƙi masu-tafiya” a cikin wannan duniyar. (Filib. 3:20; 1 Bit. 2:11) “Waɗansu tumaki” ma na Kristi “ba na duniya su ke ba, kamar yadda [Yesu] ba na duniya ba ne.” (Yoh. 10:16; 17:16) Amma, mutanen Allah suna da gida. Wannan ba gida ba ne da muke gani da idanunmu, gida ne inda kowa ke ƙaunar juna kuma aka fi samun kwanciyar hankali. Musa ya rubuta: ‘Ya Ubangiji kai ne mazauninmu tun cikin dukan tsararaki.’a (Zab. 90:1) Ta yaya Jehobah ya zama ‘mazauni’ ga bayinsa masu aminci a dā? Yaya ya zama ‘mazauni’ ga mutane masu ɗauke da sunansa a yau? Kuma yaya zai zama mazaunin bayinsa a nan gaba?

JEHOBAH NE AINIHIN ‘MAZAUNIN’ BAYINSA NA DĀ

3. Da mene ne aka kwatanta Jehobah a littafin Zabura 90:1, kuma me ya sa?

3 A wasu lokatai, Littafi Mai Tsarki yana kwatanta Jehobah da abubuwan da muke gani don mu fahimci halinsa da kyau. Alal misali, Zabura 90:1 ta kwatanta Jehobah da ‘mazauni’ ko kuma gida. Idan aka ce gida, yana nufin wurin da ake da salama da kāriya kuma ake nuna ƙauna. Me ya sa aka kwatanta Jehobah da gida? Domin Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah ƙauna ne. (1 Yoh. 4:8) Shi kuma Allah na salama ne da ke sa bayinsa su kasance “cikin natsuwa.” (Zab. 4:8) Alal misali, bari mu tattauna yadda Jehobah ya zama kamar gida ga bayinsa Ibrahim da Ishaƙu da kuma Yaƙubu.

4, 5. Ta yaya Allah ya albarkaci Ibrahim da kuma kāre shi?

4 Wataƙila, Ibrahim ya yi mamakin abin da ya sa Jehobah ya ce masa: “Ka fita daga ƙasarka, daga danginka kuma, . . . zuwa ƙasa da zan nuna maka.” Babu shakka, kalamin Jehobah na gaba ya ƙarfafa shi sosai: “Daga wurinka zan yi al’umma mai-girma, zan albarkace ka kuma, in sa ka yi suna . . . waɗanda sun albarkace ka zan albarkace su, in la’antar da wanda ya la’antar da kai.”—Far. 12:1-3.

5 Jehobah ya yi alkawari zai albarkaci Ibrahim da zuriyarsa kuma ya kāre su, kuma ya yi hakan. (Far. 26:1-6) Alal misali, ya hana Fir’auna na ƙasar Masar da Sarki Abimelek na ƙasar Gerar su kashe Ibrahim kuma su ƙwace matarsa, Saratu. Ya kāre Ishaƙu da Rifkatu, kamar yadda ya kāre Ibrahim da Saratu. (Far. 12:14-20; 20:1-14; 26:6-11) Littafi Mai Tsarki ya ce: “[Jehobah] ba ya bar wani mutum shi zalumce su ba; I, ya tsauta wa sarakuna sabili da su; Ya ce, Kada ku taɓa shafaffuna, Kada ku cuci annabawana.”—Zab. 105:14, 15.

6. Mene ne Ishaƙu ya gaya wa Yaƙubu ya yi, kuma yaya Yaƙubu ya ji?

6 Jehobah ya kuma kula da Yaƙubu, jikan Ibrahim. A lokacin da Yaƙubu yake son ya yi aure, babansa Ishaƙu ya gaya masa: “Ba za ka yi aure daga cikin yan matan Kan’ana ba. Ka tashi, ka tafi Paddan-aram, zuwa gidan Bethuel uban uwarka; ka yi aure daga cikin ’ya’yan Laban wan uwarka.” (Far. 28:1, 2) Yaƙubu ya yi abin da ya faɗa. Ya bar iyalinsa a Kan’ana kuma ya yi tafiya mai nisa zuwa Haran, wataƙila shi kaɗai ne ya yi tafiyar. (Far. 28:10) Mai yiwuwa ya yi tunani: ‘Yaushe zan dawo? Shin kawuna zai marabce ni kuma ya ba ni mata mai ƙaunar Jehobah kuwa?’ Wani abu da ya faru a garin Luz, mai nisan mil 60 kafin a kai birnin Beer-sheba, ya taimaka wa Yaƙubu ya daina damuwa. Mene ne ya faru?

7. Ta yaya Allah ya ƙarfafa Yaƙubu?

7 Jehobah ya bayyana wa Yaƙubu a mafarki a garin Luz, kuma ya gaya masa: ‘Ina tare da kai, zan kiyaye ka inda ka tafi duka, in komadda kai cikin wannan ƙasa kuma; gama ba ni barinka, sai na gama dukan abin da na ambata gareka.’ (Far. 28:15) Babu shakka cewa wannan kalamin ya ƙarfafa Yaƙubu sosai. Bayan haka, ƙila Yaƙubu ya yi ɗokin ganin yadda Allah zai cika alkawarinsa. Wataƙila, ka damu kamar Yaƙubu don ka bar gida kuma kana hidima a wata ƙasa. Babu shakka, ka ga tabbaci cewa Jehobah yana kula da kai.

8, 9. Ta yaya Jehobah ya zama ‘mazauni’ ga Yaƙubu, kuma mene ne za mu iya koya daga wannan misalin?

8 Sa’ad da Yaƙubu ya isa Haran, kawunsa Laban ya marabce shi sosai, kuma daga baya ya aurar masa Lai’atu da Rahila. Amma, da shigewar lokaci, Laban ya so ya cuci Yaƙubu kuma ya sauya ladarsa sau goma. (Far. 31:41, 42) Yaƙubu ya jimre da dukan waɗannan abubuwa domin ya gaskata cewa Jehobah zai kula da shi. A lokacin da Allah ya gaya wa Yaƙubu ya koma ƙasar Kan’ana, ya riga ya samu “manyan garkuna, da kuyangi, da bayi maza, da raƙuma da jākai.” (Far. 30:43) Yaƙubu ya yi godiya sosai ga Jehobah, kuma ya yi addu’a: “Ni ban isa mafi ƙaramta a cikin dukan jiyejiyanƙanka, da dukan gaskiya, waɗanda ka nuna wa bawanka ba; gama da sandata na haye wannan Urdun; yanzu kuwa na zama jama’a biyu.”—Far. 32:10.

9 Waɗannan misalan sun nuna cewa kalamin Musa gaskiya ne: “Ya Ubangiji kai ne mazauninmu tun cikin dukan tsararaki.” (Zab. 90:1) Hakan wannan kalamin yake a yau, domin “sakewa ba ta yiwuwa gareshi [Jehobah], ba kuwa inuwa ta juyawa.” Har ila, yana ƙauna da kāre da kuma kula da bayinsa masu aminci. (Yaƙ. 1:17) Bari mu ga yadda yake yin hakan.

JEHOBAH NE AINIHIN “MAZAUNINMU” A YAU

10. Me ya sa za mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ci gaba da zama mazaunin bayinsa?

10 Ka yi tunanin wannan yanayin, a ce kana ba da shaida a kotu game da wani mutum mai basira da kuma iko sosai. Shi maƙaryaci ne da mai kisan kai, kuma yana da masu yi masa aiki a dukan duniya. Yaya za ka ji sa’ad da ka fito daga cikin kotun idan an gama shari’ar? Za ka kasance da kwanciyar hankali ne? Ko kaɗan! Za ka nemi wanda zai kāre ka. Hakan nan ma, a matsayin bayin Jehobah, muna tona asirin Shaiɗan, magabcin Jehobah. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 12:17.) Shaiɗan yana ƙoƙari ya sa mutanen Allah su yi sanyin gwiwa. Shin ya yi nasara ne? A’a! Mun ci gaba da yi wa mutane da yawa wa’azi a faɗin duniya. Ta yaya hakan ya yiwu? Domin Jehobah ne ainihin “mazauninmu.” Yana kāre mutanensa da kuma yi musu albarka, musamman ma a wannan kwanaki na ƙarshe. (Karanta Ishaya 54:14, 17.) Jehobah zai ci gaba da zama “mazauninmu” idan ba mu ƙyale Shaiɗan ya yaudare mu ba.

11. Wane darasi ne muka koya daga Ibrahim da Ishaƙu da kuma Yaƙubu?

11 Ga wani darasi da za mu koya daga Ibrahim da Ishaƙu da kuma Yaƙubu. Ko da yake suna zama a ƙasar Kan’ana, sun ware kansu daga mutanen ƙasar kuma sun tsani mugayen abubuwan da suke yi. (Far. 27:46) Ba sa bukatar jerin dokoki don su san abin da ya dace ko kuma abin ba daidai ba. Sun san abin da Jehobah yake so da abin da ya tsana. Saboda haka, sun yi iya ƙoƙarinsu don kada su zama sashen wannan duniyar. Sun kafa mana misali mai kyau! Kana ƙoƙari ka yi koyi da waɗannan bayin Jehobah masu aminci ta wajen zaɓan abokan kirki da kuma mai da hankali ga irin nishaɗin da kake yi? Abin baƙin ciki, wasu a cikin ikilisiya suna samun kwanciyar hankali a duniyar Shaiɗan. Idan kana jin hakan, ka nemi taimakon Jehobah. Ka tuna cewa wannan duniya ta Shaiɗan ne, kuma shi mai son kai ne da ba ya kula da mu.—2 Kor. 4:4; Afis. 2:1, 2.

12. (a) Ta yaya Jehobah yake taimakon bayinsa? (b) Yaya kake ji game da wannan taimakon?

12 Idan ba ma son Shaiɗan ya ruɗe mu, dole ne mu yi amfani da taimakon da Jehobah yake ba bayinsa. Alal misali, yana taimaka mana ta wurin taron Kirista da bauta ta iyali da kuma dattawa da suke ƙarfafa mu da tallafa mana don mu jimre da matsalolin rayuwa. (Afis. 4:8-12) Ɗan’uwa George Gangas, ya ɗebi shekaru yana hidima a matsayin ɗaya cikin Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah kafin ya rasu. Ya rubuta yadda yake ji sa’ad da yake tarayya da mutanen Allah cewa: “Sa’ad da nake tsakaninsu ina ji kamar ina tare da iyalina.” Shin kana jin hakan?

13. Wane darasi ne mai muhimmanci za mu iya koya daga Ibraniyawa 11:13?

13 Wani darasi mai muhimmanci da muka koya daga waɗannan ubanni shi ne, bai kamata mu ji tsoron kasancewa dabam da mutanen da suke tare da mu ba. Kamar yadda muka karanta a sakin layi na ɗaya, waɗannan mutane masu aminci sun “shaida haka nan su baƙi ne, alhazai ne cikin duniya.” (Ibran. 11:13) Shin kana nuna cewa ka yi dabam da mutanen wannan duniya? Hakika, yin hakan ba shi da sauƙi. Amma, za ka yi nasara da taimakon Allah da kuma ’yan’uwanka. Ka tuna cewa ba kai kaɗai ba ne. Dukan waɗanda suke son su bauta wa Jehobah suna kokawa da Shaiɗan da kuma wannan duniya. (Afis. 6:12) Amma, za mu yi nasara idan muka dogara ga Jehobah kuma muka sa ya zama mazauninmu.

14. Wane ‘birni’ ne Ibrahim ya jira?

14 Ya kamata mu yi koyi da Ibrahim kuma mu ci gaba da jiran samun ladar. (2 Kor. 4:18) Manzo Bulus ya rubuta cewa Ibrahim “yana tsumayen birnin da ke da tussa, wanda mai-sifansa da mai-aikinsa Allah ne.” (Ibran. 11:10) Mulkin Allah ne wannan “birnin” kuma Ibrahim ya jira “birnin” ya zo. Mu ba ma jiran Mulkin, domin ya riga ya soma sarauta a sama. Kuma annabci da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ba da daɗewa ba, zai yi sarauta bisa dukan duniya. Shin salon rayuwarka ya nuna cewa ka gaskata da Mulkin? Kana saka Mulkin farko a rayuwarka kuma kana ware kanka daga wannan duniyar?—Karanta 2 Bitrus 3:11, 12.

JEHOBAH ZAI CI GABA DA ZAMA “MAZAUNINMU”

15. Mene ne zai faru da waɗanda suka dogara ga duniyar nan?

15 Kafin ƙarshen ya zo, matsaloli za su ci gaba da ƙaruwa a wannan duniyar. (Mat. 24:7, 8) Kuma za a fuskanci matsaloli sosai a rayuwa sa’ad da aka soma ƙunci mai girma. A dukan duniya, za a halaka abubuwa da dama, kuma mutane da yawa za su firgita su rikice. (Hab. 3:16, 17) Littafi Mai Tsarki ya ce mutane za su damu har ma su fara neman su “ɓuya cikin ramummuka da fannun duwatsu.” (R. Yoh. 6:15-17) Amma, babu rami ko ƙungiyoyin kasuwanci ko kuma na siyasa da zai kāre su.

16. Yaya ya kamata mu ɗauki ikilisiya, kuma me ya sa?

16 Jehobah zai kāre mu a lokacin ƙunci mai girma. Kamar annabi Habakkuk, za mu “yi murna cikin Ubangiji” kuma mu ‘yi murna a cikin Allah mai-cetonmu.’ (Hab. 3:18) Ta yaya Jehobah zai zama ainihin “mazauninmu” a lokacin damuwa? Za mu jira mu ga abin da zai faru. Amma, muna da tabbaci cewa za a tsara mutanen Jehobah da kyau kuma a riƙa ba su umurni kamar Isra’ilawa da suka bar ƙasar Masar a dā. (R. Yoh. 7:9; karanta Fitowa 13:18.) Ta yaya Jehobah zai ba da wannan umurnin? Zai yi amfani da ikilisiya don ya gaya mana abin da za mu yi. An kwatanta ikilisiyoyi da ‘ɗakunan’ da Ishaya 26:20 ya annabta. (Karanta.) Kana ɗaukan taron ikilisiya da muhimmanci kuwa? Shin kana yin duk abin da Jehobah ya gaya maka ta hanyar ikilisiya?—Ibran. 13:17.

17. A wace hanya ce Jehobah ya zama ‘mazaunin’ bayinsa masu aminci da suka mutu?

17 Jehobah zai ci gaba da zama ‘mazaunin’ masu aminci da suka mutu kafin ƙunci mai girma. Ta yaya? Zai ta da su daga matattu. Da daɗewa bayan Ibrahim da Ishaƙu da kuma Yaƙubu suka mutu, Jehobah ya gaya wa Musa cewa: “Ni ne Allah . . . na Ibrahim, Allah na Ishaƙu, Allah na Yaƙub.” (Fit. 3:6) Yesu ya ƙara maimaita wannan kalamin sa’ad da ya ce: “Shi dai ba Allah na matattu ba ne, amma na masu-rai: gama duka suna rayuwa gareshi.” (Luk 20:38) A gaban Jehobah, bayinsa masu aminci da suka mutu suna nan kamar masu rai, domin zai ta da su daga matattu.—M. Wa. 7:1.

18. Ta yaya Jehobah zai zama ainihin ‘mazaunin’ mutanensa a sabuwar duniya?

18 A cikin sabuwar duniya, Jehobah zai zama ainihin ‘mazaunin’ mutanensa a wata hanya dabam. Ru’ya ta Yohana 21:3 ta ce: “Duba, mazaunin Allah yana wurin mutane, za ya zauna tare da su.” Jehobah zai sa Yesu Kristi ya yi sarauta bisa duniya na tsawon shekaru dubu. A ƙarshen shekaru dubu, Yesu zai mayar wa Ubansa Mulkin, da yake ya cim ma nufin Jehobah ga duniya. (1 Kor. 15:28) Sa’an nan, Jehobah da kansa zai yi sarauta bisa ’yan Adam. Babu shakka, za mu ji daɗin rayuwa a nan gaba a duniya. Kafin wannan lokacin, bari mu yi koyi da bayinsa na dā masu aminci ta wurin sa Jehobah ya zama “mazauninmu” a yau.

a Juyin Contemporary English Version ya fassara Zabura 90:1 cewa: “Ubangijinmu, ka zama gidanmu a dukan tsararraki.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba