Abin Da Ranar Jehobah Za Ta Bayyana
“Ranar Jehobah za ta zo kamar ɓarawo . . . kuma za a gano duniya da ayyukan da ke cikinta.”—2 BIT. 3:10, NW.
1, 2. (a) Yaya wannan mugun zamani zai zo ƙarshensa? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?
AN KAFA wannan mugun zamani bisa ƙaryar cewa mutum zai yi sarautar duniya kuma ya yi nasara ba tare da taimakon Jehobah ba. (Zab. 2:2, 3) Duk wani abin da aka kafa bisa ƙarya zai kasance har abada ne? A’a! Duk da haka, ba ma bukatan mu jira duniyar Shaiɗan ta halaka kanta. Maimakon haka, Allah ne zai halaka ta a lokacinsa da kuma yadda ya ga dama. Matakin da Allah zai ɗauka a kan wannan muguwar duniya zai nuna cikakken adalcinsa da kuma ƙaunarsa.—Zab. 92:7; Mis. 2:21, 22.
2 “Ranar Jehobah,” in ji manzo Bitrus, “za ta zo kamar ɓarawo; sa’an nan sammai za su shuɗe tare da ƙara mai girma, amma abubuwa da ke cikinsa da ƙuna mai zafi za su narke, kuma za a gano duniya da ayyukan da ke cikinta.” (2 Bit. 3:10) Menene “sammai” da “duniya” da aka ambata a nan? Waɗanne “abubuwa” ne za su narke? Kuma menene Bitrus yake nufi da cewa “za a gano duniya da ayyukan da ke cikinta”? Sanin amsoshin waɗannan tambayoyi zai taimaka mana mu kasance a shirye domin abubuwa masu ban tsoro da za su auku nan gaba.
Sammai da Duniya da Za Su Shuɗe
3. Menene “sammai” da aka ambata a 2 Bitrus 3:10, kuma yaya za su shuɗe?
3 Sa’ad da aka yi amfani da ita a alamance a cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “sammai” sau da yawa tana nuni ne ga masu sarauta waɗanda ake ɗaukakawa fiye da talakawansu. (Isha. 14:13, 14; R. Yoh. 21:1, 2) “Sammai [da] za su shuɗe” suna wakiltar sarautar ’yan Adam bisa al’umma marar ibada. Shuɗewarsu da “ƙara mai girma” wataƙila yana nufin halaka waɗannan sammai da sauri.
4. Menene “duniya” kuma yaya za a halaka ta?
4 “Duniya” tana wakiltar duniyar ’yan adam da take a bare daga Allah. Irin wannan duniya ta kasance a zamanin Nuhu kuma da umurnin Allah aka halaka ta da Rigyawa. “Amma sammai da suke yanzu, da duniya kuma, bisa ga wannan magana kanta an tanaje su domin wuta, ajiyayyu zuwa ranar shari’a da halakar mutane masu-fajirci.” (2 Bit. 3:7) Ko da yake Rigyawa ta halaka dukan miyagu a lokaci ɗaya, halaka mai zuwa zai faru a daki-daki a lokacin “babban tsananin.” (R. Yoh. 7:14) A sashe na farko na wannan tsananin, Allah zai sa ’yan siyasa da suke mulki a wannan duniya su halaka “Babila Babba,” hakan zai nuna fushinsa ga wannan karuwa na addini. (R. Yoh. 17:5, 16; 18:8) Sa’an nan, a yaƙin Armageddon, sashe na ƙarshe na babban tsananin, Jehobah da kansa zai kawar da sauran duniyar Shaiɗan.—R. Yoh. 16:14, 16; 19:19-21.
“Abubuwa . . . Za Su Narke”
5. Abubuwa na alama sun ƙunshi menene?
5 Waɗanne “abubuwa” ne “za su narke”? “Abubuwan” da Bitrus ya ambata suna nuni ga muhimman abubuwan da suka sa duniya ta kasance da mummunan halayenta, hanyoyinta, da makasudinta. “Abubuwan” sun haɗa da “ruhun duniya,” wanda “ke aiki yanzu a cikin ’ya’yan kangara.” (1 Kor. 2:12; karanta Afisawa 2:1-3.) Wannan ruhun ko iska yana ko’ina a duniyar Shaiɗan. Yana motsa mutane su yi tunani, su yi shiri, su yi magana, kuma su yi abubuwa a hanyoyin da ke nuna tunanin Shaiɗan, “sarkin ikon sararin sama” mai fahariya da kuma taurin kai.
6. Yaya ruhun duniya yake nuna kansa?
6 Saboda haka, da saninsu ko ba da saninsu ba, waɗanda ruhun duniya ya shafa suna ƙyale Shaiɗan ya rinjayi zuciyarsu, don su nuna tunaninsa da halinsa. A sakamakon hakan, suna yin abin da suke so, ba tare da damuwa da nufin Allah ba. Suna yin abubuwa ne bisa fahariya ko son kai, suna nuna taurin kai ga masu mulki, kuma suna faɗawa dumu-dumu ga “kwaɗayin jiki, da sha’awar idanu.”—Karanta 1 Yohanna 2:15-17.a
7. Me ya sa ya kamata mu ‘kiyaye zuciyarmu’?
7 Saboda haka, yana da muhimmanci mu ‘kiyaye zuciyarmu’ ta wajen yin zaɓi mai kyau bisa abin da muka koya daga Allah game da zaɓan abokai, abin da muke karantawa, nishaɗi, da kuma dandalin Duniyar Gizo da muke kallo a Intane! (Mis. 4:23) Manzo Bulus ya rubuta: “Ku yi hankali kada kowa ya cuceku ta wurin iliminsa da ruɗinsa na banza, bisa ga ta’adar mutane, bisa ga ruknai na duniya, ba bisa ga Kristi ba.” (Kol. 2:8) Wannan umurnin ya fi kasancewa da gaggawa yayin da ranar Jehobah take kusatowa, domin ‘zafi’ da ba a taɓa irinsa ba zai narkar da dukan “abubuwa” na zamanin Shaiɗan, kuma hakan zai tabbatar da cewa ba za su iya jimre zafin fushin Allah ba. Wannan ya tuna mana kalaman Malakai 4:1: “Rana tana zuwa, tana ƙuna kamar tanderu; dukan masu-girman kai, da dukan waɗanda ke aikin mugunta, za su zama tattaka; ranan da ke zuwa kuma za ta ƙoƙone su.”
“Za a Gano Duniya da Ayyukan da ke Cikinta”
8. Ta yaya aka “gano” duniya da ayyukanta?
8 Menene Bitrus yake nufi sa’ad da ya rubuta cewa “za a gano duniya da ayyukan da ke cikinta”? Bitrus yana nufin cewa a lokacin babban tsanani, Jehobah zai tona asirin duniyar Shaiɗan, zai fallasa ta cewa tana gaba da shi da kuma Mulkinsa don hakan ta cancanci a halaka ta. Sa’ad da yake yin annabci game da wannan lokacin, Ishaya 26:21 ta ce: “Ubangiji yana fitowa daga wurinsa domin shi yi wa mazaunan duniya hukunci saboda muguntarsu: ƙasa kuma za ta buɗe asirin jininta, ba kuwa za ta ƙara rufe kisassunta ba.”
9. (a) Menene ya kamata mu ƙi, kuma me ya sa? (b) Menene ya kamata mu koya, kuma me ya sa?
9 A ranar Jehobah, waɗanda duniya da mugun ruhunta take rinjayarsu za su nuna ainihin halayensu, har ma su kashe juna. Hakika, wataƙila mugun nishaɗi dabam-dabam da ke ko’ina a yau suna shirya zuciyar mutane da yawa ne ga lokacin da hannun kowane mutum zai “tasam wa hannun maƙwabcinsa.” (Zech. 14:13) Saboda haka, yana da muhimmanci mu ƙi duk wani abu, wato, silima, littattafai, wasannin bidiyo, da sauran su da za su sa mu koyi halayen da Allah ba ya so, kamar su fahariya da kuma son mugunta! (2 Sam. 22:28; Zab. 11:5) Maimakon haka, bari mu nuna ’yar ruhu mai tsarki na Allah, don irin waɗannan halaye za su iya jimre da zafi na alama na ranar Jehobah.—Gal. 5:22, 23.
“Sababbin Sammai da Sabuwar Duniya”
10, 11. Menene “sababbin sammai” da “sabuwar duniya”?
10 Karanta 2 Bitrus 3:13. “Sababbin sammai” shi ne Mulkin sama na Allah, wanda aka kafa a shekara ta 1914 sa’ad da “zamanan Al’ummai” suka cika. (Luk 21:24) Yesu Kristi da abokan sarautarsa 144,000 da yawancinsu sun samu ladarsu na sama ne suke cikin wannan gwamnatin. A cikin littafin Ru’ya ta Yohanna, an kwatanta waɗannan da aka zaɓa da “birni mai-tsarki, sabuwar Urushalima, [da take] saukowa daga sama daga wurin Allah, shiryayya kamar amarya da ado domin mijinta.” (R. Yoh. 21:1, 2, 22-24) Kamar yadda Urushalima ta duniya ita ce cibiyar gwamnati a Isra’ila ta dā, Sabuwar Urushalima da Angonta ne gwamnatin sabon zamani. Wannan birni na samaniya zai ‘sauko daga sama’ ta wajen mai da hankalinsa ga duniya.
11 “Sabuwar duniya” tana nuni ga sabuwar al’ummar ’yan adam a duniya da suka miƙa kansu da son rai ga Mulkin Allah. A ƙarshe, aljanna na ruhaniya da mutanen Allah suke morewa a yanzu za ta kasance a yanayinta da ya dace a wannan kyakkyawar “duniya mai-zuwa.” (Ibran. 2:5) Ta yaya za mu iya kasancewa sashen wannan sabon zamanin?
Ka Yi Shiri Don Babbar Ranar Jehobah
12. Me ya sa ranar Jehobah za ta zama abin mamaki ga duniya?
12 Bulus da Bitrus sun annabta cewa ranar Jehobah za ta zo kwatsam, kamar “ɓarawo” a ɓoye. (Karanta 1 Tasalonikawa 5:1, 2.) Har Kiristoci na gaskiya, da suke jiran wannan rana, za su yi mamakin yadda za ta zo farat ɗaya. (Mat. 24:44) Amma, duniya za ta fi shan mamaki. Bulus ya rubuta: “Bayan [waɗanda suke bare daga Jehobah] suna cikin faɗin, kwanciyar rai da lafiya, sai halaka farat ta auko musu, kamar yadda nakuda ta kan auko ma mace mai-ciki; ba kuwa za su tsira ba ko kaɗan.”—1 Tas. 5:3.
13. Ta yaya za mu guji ƙyale faɗin “kwanciyar rai da lafiya” ya ruɗe mu?
13 Faɗin “kwanciyar rai da lafiya” zai zama wata ƙarya da aljanu suka hura, duk da haka ba zai ruɗi bayin Jehobah ba. “Ba cikin duhu ku ke ba” in ji Bulus, “da ranan nan za ta tarshe ku kamar ɓarawo: gama ku duka ’ya’yan haske ne, ’ya’yan rana kuwa.” (1 Tas. 5:4, 5) Saboda haka, bari mu kasance cikin haske, mu yi nisa daga duhu na duniyar Shaiɗan. Bitrus ya rubuta: “Ƙaunatattu, domin kun rigaya kun sani, ku yi hankali kada ya zama a janye ku bisa ga kuskure na masu-mugunta, [wato, malaman ƙarya cikin ikilisiyar Kirista,] har ku fāɗi daga cikin tsayawarku.”—2 Bit. 3:17.
14, 15. (a) Ta yaya Jehobah yake daraja mu? (b) Waɗanne hurarrun kalamai ya kamata mu riƙa tunawa?
14 Ka lura cewa Jehobah bai ce “ku yi hankali” kawai ba. Maimakon haka, ya daraja mu ta wajen ‘sa mu sani’ tun da wuri abin da zai faru nan gaba.
15 Amma abin baƙin ciki, wasu ba su damu ba ko kuma suna ba’a game da tunasarwa na kasancewa a faɗake. Suna iya faɗin cewa, ‘Mun yi shekaru aru-aru muna jin wannan tunasarwar.’ Amma, ya kamata irin waɗannan mutanen su tuna cewa ta wajen yin irin waɗannan kalaman, suna shakkar Jehobah da Ɗansa, ba kawai rukunin bawan nan mai aminci ba. “Ka kira shi,” in ji Jehobah. (Hab. 2:3, Littafi Mai Tsarki) Hakazalika, Yesu ya ce: “Ku yi tsaro . . . gama ba ku sani ba cikin kowace rana Ubangijinku ke zuwa.” (Mat. 24:42) Ƙari ga haka, Bitrus ya rubuta: “Waɗanne irin mutane ya kamata ku zama cikin tasarrufi mai-tsarki da ibada kuma? kuna sauraron ranar Allah, kuna kuwa marmarin zuwanta ƙwarai.” (2 Bit. 3:11, 12) Rukunin bawan nan mai aminci da Hukumarsa ta Mulki ba za su taɓa ɗaukan waɗannan kalmomin da wasa ba!
16. Wane hali ne za mu guje wa, kuma me ya sa?
16 Hakika, “mugun bawan nan” ne ya kammala cewa Ubangijin yana jinkiri. (Mat. 24:48) Wannan mugun bawan yana cikin rukunin da aka kwatanta a 2 Bitrus 3:3, 4. “Cikin kwanaki na ƙarshe” in ji Bitrus, “masu-ba’a za su zo” waɗanda bisa “nasu sha’awoyi,” suke ba’a ga waɗanda suke tunawa da ranar Jehobah cikin biyayya. Hakika, maimakon su mai da hankali ga al’amura na Mulki, irin waɗannan masu ba’a suna tunani ne kawai game da kansu da nasu sha’awoyi na son kai. Kada mu taɓa koyan irin wannan rashin biyayya da mugun hali! Maimakon haka, bari mu “maida jimrewar Ubangijinmu ceto” ta wajen shagala a aikin wa’azin Mulki da almajirantarwa kuma kada mu damu ainun game da lokacin abubuwa da suke hannun Jehobah Allah.—2 Bit. 3:15; karanta Ayyukan Manzanni 1:6, 7.
Ka Dogara ga Allah Mai Ceto
17. Yaya Kiristoci masu aminci suka aikata ga gargaɗin da Yesu ya yi musu na guduwa daga Urushalima, kuma me ya sa?
17 Bayan sojojin Roma sun kai wa Yahudiya hari a shekara ta 66 A.Z., Kiristoci masu aminci sun bi gargaɗin da Yesu ya yi musu na guduwa daga Urushalima a zarafi na farko. (Luk 21:20-23) Me ya sa suka aikata nan da nan? Babu shakka, sun riƙe gargaɗin da Yesu ya yi musu a zuciya. Hakika, sun san cewa shawarar da suka tsai da za ta sa su sha wahala, kamar yadda Yesu ya gaya musu. Duk da haka, sun san cewa Jehobah ba zai taɓa yasar da amintattunsa ba.—Zab. 55:22.
18. Ta yaya kalaman Yesu da ke rubuce cikin Luka 21:25-28 suka shafi ra’ayinka game da ƙunci mai girma da ke zuwa?
18 Ya kamata mu ma mu dogara sarai ga Jehobah don shi kaɗai ne zai cece mu sa’ad da wannan zamani ta fuskanci ƙunci mafi girma a dukan tarihin ’yan Adam. A wani lokaci bayan somawar babban tsanani kafin Jehobah ya zartar da hukunci a kan duniya, mutane za su “suma don tsoro, domin tsammanin al’amuran da ke auko wa duniya.” Amma, yayin da magabtan Allah suke rawan jiki don tsoro, bayin Jehobah masu aminci ba za su ji tsoro ba. Akasin haka, za su yi farin ciki domin sun san cewa cetonsu ya kusa—Karanta Luka 21:25-28.
19. Menene za a tattauna a talifi na gaba?
19 Hakika, rayuwa mai ban sha’awa a nan gaba tana jiran waɗanda suka ware kansu daga wannan duniya da “abubuwa” da ke cikinta. Kamar yadda talifi na gaba ya bayyana, idan muna son mu samu rai, ba za mu guji yin abin da ba shi da kyau kawai ba. Muna bukatan mu koyi halayen da ke faranta wa Jehobah rai kuma mu yi ayyukan da ya amince da su.—2 Bit. 3:11.
[Hasiya]
a Don cikakken bayani a kan halaye da ruhun duniya yake ɗaukaka, ka duba littafin nan Reasoning From the Scriptures, shafuffuka na 389-393.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Menene . . .
‘sammai da duniya’ na yanzu?
“abubuwa”?
‘sababbin sammai da sabuwar duniya’?
• Me ya sa muka dogara sosai ga Allah?
[Hoton da ke shafi na 5]
Ta yaya za ka “kiyaye zuciyarka” kuma ka ci gaba da ware kanka daga duniya?
[Hoton da ke shafi na 6]
Ta yaya muke nuna cewa muna ɗaukan “jimrewar Ubangijinmu ceto”?