Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 7/15 pp. 7-11
  • “Ku Yi La’akari Da Irin Mutane Da Ya Kamata Ku Zama!”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ku Yi La’akari Da Irin Mutane Da Ya Kamata Ku Zama!”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Koyi Halaye na Ibada
  • Ka Kasance ‘Marar-Aibi Marar-Laifi’
  • Bari Jarrabobi Su Ƙarfafa Ka
  • Ka Kasance da Ƙwazo a Hidimar Jehobah
  • Kana Da Halin “Jira”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ka Ƙara Wa Jimirinka Ibada
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Darussa Daga Wasiƙun Yaƙub da Bitrus
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Darussan da Wasiku Biyu da Bitrus Ya Rubuta Suka Koya Mana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 7/15 pp. 7-11

“Ku Yi La’akari Da Irin Mutane Da Ya Kamata Ku Zama!”

“Tun da yake duk waɗannan abubuwa za su narke haka nan, ku yi la’akari da irin mutane da ya kamata ku zama cikin ayyuka masu tsarki da ibada kuma!” —2 BIT. 3:11, NW.

1. Me ya sa wasiƙar Bitrus ta biyu ƙarfafawa ce na kan kari ga Kiristoci a zamaninsa?

SA’AD da manzo Bitrus ya rubuta hurarriyar wasiƙarsa ta biyu, ikilisiyar Kirista ta riga ta jimre wa tsanani mai yawa, amma wannan bai rage himmarta ba ko ƙaruwarta. Saboda haka, Iblis ya yi amfani da wata dabara, wadda ta yi nasara sau da yawa a dā. Kamar yadda Bitrus ya bayyana, Shaiɗan ya yi ƙoƙarin ya ɓata mutanen Allah ta hanyar malaman ƙarya waɗanda “idanunsu cike da zina suke” da “zuciya forarriya zuwa kwaɗai.” (2 Bit. 2:1-3, 14; Yahu. 4) Saboda haka, wasiƙar Bitrus ta biyu ƙarfafawa ce na kasancewa da aminci ga Allah.

2. A kan menene Bitrus ta 2 sura ta 3 ta mai da hankali, waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu?

2 Bitrus ya rubuta: “Ga ganina daidai ne, muddar ina cikin wannan tent, in dama hankalinku ta wurin tuna maku; domin na sani dole zan ajiye wannan tenti nawa da sauri . . . Zan ba da anniya domin kowane loto bayan rasuwata ku iya tuna da waɗannan al’amura.” (2 Bit. 1:13-15) Hakika, Bitrus ya san cewa mutuwarsa ta kusa, amma yana son a ci gaba da tuna koyarwarsa na kan kari. Hakika, an rubuta su cikin Littafi Mai Tsarki kuma mu duka za mu iya karanta su a yau. Sura ta 3 ta wasiƙar Bitrus ta biyu tana da muhimmanci sosai a gare mu, domin ta mai da hankali ne a kan “kwanaki na ƙarshe” na zamani da kuma halakar sammai da duniya na alama. (2 Bit. 3:3, 7, 10) Wace shawara ce Bitrus ya ba mu? Ta yaya bin wannan shawarar zai taimaka mana mu samu amincewar Jehobah?

3, 4. (a) Wane furci ne na motsin rai Bitrus ya yi, kuma wane gargaɗi ya ba da? (b) Waɗanne darussa uku ne za mu bincika?

3 Bayan ya ambata cewa za a kawar da duniyar Shaiɗan, Bitrus ya ce: “Ku yi la’akari da irin mutane da ya kamata ku zama cikin ayyuka masu tsarki da ibada kuma!” (2 Bit. 3:11, 12) Bitrus ya san cewa waɗanda suka yi nufin Jehobah kuma suka nuna halaye da suka faranta masa rai ne kaɗai za su sami ceto a “ranar sakaiya” da ke zuwa. (Isha. 61:2) Saboda haka, manzon ya daɗa: “Ku fa, ƙaunatattu, domin kun rigaya kun sani, ku yi hankali kada ya zama a janye ku [tare da malaman ƙarya] bisa ga kuskure na masu-mugunta, har ku fāɗi daga cikin tsayawarku.”—2 Bit. 3:17.

4 Tun da yake yana cikin waɗanda sun ‘rigaya sun san’ abin da zai faru nan gaba, Bitrus ya sani cewa a kwanaki na ƙarshe ya kamata Kiristoci su mai da hankali sosai domin su riƙe amincinsu. Daga baya, manzo Yohanna ya bayyana sarai dalilin da ya sa za su yi hakan. Ya hangi cewa an jefar da Shaiɗan daga sama kuma zai yi “hasala mai-girma” ga “waɗanda suke kiyaye dokokin Allah, suna riƙe da shaidar Yesu.” (R. Yoh. 12:9, 12, 17) Bayin Allah shafaffu masu aminci tare da abokansu “waɗansu tumaki” masu aminci za su yi nasara. (Yoh. 10:16) Mu kuma fa ɗaɗɗaya? Za mu riƙe amincinmu kuwa? Za a taimaka mana mu yi hakan idan muka yi ƙoƙari muka (1) koyi halaye na ibada, (2) muka kasance marasa aibi, marasa laifi a ɗabi’a da ruhaniya, kuma (3) muka kasance da ra’ayin da ya dace game da gwaji. Bari mu tattauna waɗannan batutuwan.

Ka Koyi Halaye na Ibada

5, 6. Waɗanne halaye ya kamata mu yi ƙoƙari mu koya, kuma me ya sa hakan yake bukatan “ba da ƙoƙari” sosai?

5 Daga farko-farkon wasiƙarsa ta biyu, Bitrus ya rubuta: “Ku ƙara ba da ƙoƙari, cikin bangaskiyarku kuma ku kawo halin kirki; cikin halin kirki kuma ilimi; cikin ilimi kuma kamewa; cikin kamewa kuma haƙuri; cikin haƙuri kuma ibada; cikin ibada kuma son ’yan’uwa; cikin son ’yan’uwa kuma ƙauna. Gama idan waɗannan abu naku ne, suna kuwa yawaita, su za su hana ku zama raggaye ko kuwa marasa-amfani zuwa ga sanin Ubangijinmu Yesu Kristi.”—2 Bit. 1:5-8.

6 Hakika, muna bukatan yin “ƙoƙari” sosai don mu yi ayyukan da za su taimaka mana mu nuna halaye na ibada. Alal misali, muna bukatan ƙoƙari don mu halarci dukan taron Kirista, mu karanta Littafi Mai Tsarki kullum, kuma mu kasance da tsari mai kyau na nazari na kanmu. Kuma muna bukatan yin aiki tuƙuru tare da shiri da kyau don mu riƙa yin Bauta ta Iyali da yamma a kai a kai, mu sa ya yi daɗi kuma ya kasance mai ma’ana. Amma muddin muka samu tsari mai kyau, zai kasance da sauƙi mu koyi waɗannan halaye, musamman sa’ad da muka shaida fa’idodin.

7, 8. (a) Menene wasu suka ce game da Bauta ta Iyali da yamma? (b) Yaya kake amfana daga bauta ta iyalinku?

7 Game da tsarin bauta ta iyali, wata ’yar’uwa ta rubuta: “Yana sa mu koyi darussa masu yawa.” Wata ta ce: “A gaskiya, ban so yadda aka daina rukunin nazari ba. Shi ne taron da na fi so. Amma yanzu da muke da yamma na Bauta ta Iyali, na fahimci cewa Jehobah ya san abin da muke bukata da kuma lokacin da muke bukatarsa.” Wani shugaban iyali ya ce: “Bauta ta iyali tana taimaka mana sosai. Yin taro da ya dace da ainihin bukatunmu a matsayin ma’aurata yana da amfani sosai! Mun ga cewa muna kyautata yadda muke nuna ’yar ruhu mai tsarki, kuma muna farin ciki sosai a hidimarmu fiye da dā.” Wani shugaban iyali ya ce: “Yarana suna yin nasu bincike suna koyan abubuwa da yawa kuma suna jin daɗinsa. Shirin ya sa mun ƙara kasancewa da tabbaci cewa Jehobah ya san bukatunmu kuma yana amsa addu’o’inmu.” Kai ma kana jin hakan game da wannan tanadi mai ban al’ajabi daga Allah?

8 Kada ku ƙyale abubuwa da ba su da muhimmanci su hana ku bauta ta iyali. Wata mata da mijinta sun ce, “Kowane Alhamis da yamma cikin makonni huɗu da suka shige, wani abu yana faruwa a cikin iyalinmu da ya kusan hana mu yin nazari, amma ba mu yarda ba.” Hakika, a wani lokaci kuna iya canja tsarinku. Duk da haka, ku ƙudurta cewa ba za ku bar yin Bauta ta Iyalinku da yamma ba, ko da mako guda!

9. Ta yaya Jehobah ya kiyaye Irmiya, kuma menene za mu iya koya daga misalinsa?

9 Annabi Irmiya ya kafa mana misali mai kyau. Yana bukatan abinci na ruhaniya da yake samu daga Jehobah kuma yana jin daɗin hakan. Wannan abincin ya taimaka masa ya yi wa’azi da jimiri ga mutanen da suka ƙi yin na’am ga saƙon. “Maganar Ubangiji . . . kamar wuta mai-ƙonewa a kulle cikin ƙasusuwana” in ji shi. (Irm. 20:8, 9) Ya kuma taimaka masa ya jimre lokaci mai wuya da ya ƙare da halakar Urushalima. A yau, muna da cikakkiyar rubutacciyar Kalmar Allah. Sa’ad da muka yi nazarinta sosai kuma muka san ra’ayin Allah a kan al’amura, kamar Irmiya, cike da farin ciki, za mu iya jimrewa a hidima, mu kasance da aminci a lokacin gwaji, kuma mu kasance da tsabta na ɗabi’a da na ruhaniya.—Yaƙ. 5:10.

Ka Kasance ‘Marar-Aibi Marar-Laifi’

10, 11. Me ya sa za mu yi iya ƙoƙarinmu mu kasance “marasa-aibi marasa-laifi,” kuma menene wannan yake bukata a gare mu?

10 Mu Kiristoci, mun san cewa muna rayuwa ne a kwanaki na ƙarshe. Saboda haka, ba ma mamakin cewa duniya ta shaƙu da abubuwan da Jehobah ba ya so, kamar haɗama, lalata, da mugunta. Ana iya taƙaita dabarar Shaiɗan haka: ‘Idan ba za a iya tsorata bayin Allah ba, wataƙila za a iya ɓata su.’ (R. Yoh. 2:13, 14) Saboda haka, dole ne mu bi umurnin Bitrus: ‘Ku ba da anniya a tarar da ku cikin salama, marasa-aibi marasa-laifi a gaban [Allah].’—2 Bit. 3:14.

11 Furcin nan ku “ba da anniya” ya yi kama da shawarar da Bitrus ya ba da da farko cewa a “ba da ƙoƙari.” A bayyane yake cewa, Jehobah wanda ya hure Bitrus ya furta waɗannan kalaman ya san muna bukatan mu yi iya ƙoƙarinmu don mu kasance “marasa-aibi marasa-laifi” daga dattin duniyar Shaiɗan. Yin iya ƙoƙarinmu ya ƙunshi kāre zuciyarmu don kada munanan sha’awoyi su shafe ta. (Karanta Misalai 4:23; Yaƙub 1:14, 15.) Ya kuma ƙunshi yin tsayin daka da waɗanda suke mamaki game da tafarkin rayuwarmu ta Kirista da kuma waɗanda suke ‘aibatanmu.’—1 Bit. 4:4.

12. Wane tabbaci muka samu a Luka 11:13?

12 Domin ajizancinmu, muna yin gwagwarmaya don mu yi abin da ya dace. (Rom. 7:21-25) Za mu iya yin nasara ne kawai idan muka juya ga Jehobah, wanda yake ba da ruhu mai tsarki a sake ga waɗanda suke roƙonsa. (Luk 11:13) Wannan ruhun yana sa mu koyi halayen da Allah ya amince da su kuma yana taimaka mana mu jimre da jarraba da kuma gwaji na rayuwa, waɗanda za su iya ƙaruwa yayin da ranar Jehobah take kusatowa.

Bari Jarrabobi Su Ƙarfafa Ka

13. Sa’ad da muke fuskantar jarrabobi a rayuwarmu, menene zai taimaka mana mu jimre?

13 Muddin muna cikin wannan tsohon zamani, dole ne mu fuskanci jarrabobi iri-iri. Amma maimakon ka yi sanyin gwiwa, ka ɗauki jarrabobin a matsayin zarafi na tabbatar da ƙaunarka ga Allah kuma ka ƙarfafa bangaskiyarka a gare shi da Kalmarsa. Almajiri Yaƙub ya rubuta: “’Yan’uwana, kadan jarabobi masu-yawa sun same ku, ku maishe shi abin farinciki sarai; kun sani gwadawar bangaskiyarku tana jawo haƙuri.” (Yaƙ. 1:2-4) Ka tuna kuma cewa “Ubangiji ya san yadda za ya ceci masu-ibada daga cikin jaraba.”—2 Bit. 2:9.

14. Ta yaya misalin Yusufu ya ƙarfafa ka?

14 Ka yi la’akari da misalin Yusufu, ɗan Yakubu, wanda ’yan’uwansa suka sayar zuwa bauta. (Far. 37:23-28; 42:21) Yusufu ya yi rashin bangaskiyarsa ne domin mugun zaluncin da ya fuskanta? Ya yi fushi ne da Allah don ya ƙyale mugunta ta faɗa masa? Kalmar Allah ta ce a’a! Ƙari ga haka, ba wannan ba ne jarraba na ƙarshe da Yusufu ya fuskanta ba. Bayan haka, an yi masa zargin ƙarya na son yin fyaɗe kuma aka jefa shi kurkuku. Duk da haka, ya sake kasancewa da amincinsa ga Allah. (Far. 39:9-21) Ya ƙyale jarrabobin su ƙarfafa shi, kuma an albarkace shi sosai don wannan.

15. Menene za mu koya daga misalin Naomi?

15 Hakika, jarrabobi suna iya sa mu baƙin ciki. Wataƙila Yusufu ya ji hakan a wasu lokatai. Wasu bayin Allah masu aminci sun ji hakan. Ka yi la’akari da Naomi, wadda mijinta da yaranta biyu suka mutu. “Kada ku ce da ni Naomi,” in ji ta. “Mara za ku ce da ni, [yana nufin “Baƙin ciki”], gama Mai-iko duka ya yi mini aiki mai-zafi ƙwarai.” (Ruth 1:20, 21) Abin da Naomi ta yi ba laifi ba ne kuma an fahimci abin da ya sa ta yi hakan. Amma, kamar Yusufu, ba ta ƙyale hakan ya shafi bangaskiyarta ba ko kuma dangantakarta da Jehobah. Jehobah kuma ya albarkaci wannan matar mai tamani. (Ruth 4:13-17, 22) Ƙari ga haka, a cikin Aljanna ta duniya mai zuwa, zai daidaita dukan ɓarnar da Shaiɗan da muguwar duniyarsa suka yi. “Ba za a tuna da al’amura na dā ba, ba kuwa za su shiga zuciya ba.”—Isha. 65:17.

16. Menene ya kamata ya zama halinmu game da addu’a, kuma me ya sa?

16 Ko da wace jarraba ce muke fuskanta, sanin cewa Allah a koyaushe yana ƙaunarmu zai taimaka mana mu jimre. (Karanta Romawa 8:35-39.) Ko da yake Shaiɗan ba zai daina ƙoƙarin da yake yi na sa mu sanyin gwiwa ba, ba zai yi nasara ba idan muka “yi natsuwa cikin hankalin[mu]” kuma muka “lura ƙwarai da gaskiye a cikin addu’a.” (1 Bit. 4:7) Yesu ya ce: “Amma a kowane loto sai ku yi tsaro, kuna yin roƙo ku sami ikon da za ku tsere wa dukan waɗannan al’amuran da za su faru, ku tsaya kuma a gaban Ɗan mutum.” (Luk 21:36) Ka lura cewa Yesu ya yi amfani da kalmar nan “roƙo,” wadda take nufin yin addu’a sosai. Ta wajen ƙarfafa mu mu yi roƙo, Yesu ya nanata cewa wannan lokaci ne na ɗaukan matsayinmu da muhimmanci a gabansa da kuma Ubansa. Waɗanda suke da amincewarsa ne kaɗai za su samu begen tsira a ranar Jehobah.

Ka Kasance da Ƙwazo a Hidimar Jehobah

17. Idan wurin da kake wa’azi yana da wuya, yaya za ka amfana daga misali mai kyau na annabawa na dā?

17 Yin ayyuka na ruhaniya yana wartsakar da mu. Wannan yana tuna mana kalaman Bitrus: “Ku yi la’akari da irin mutane da ya kamata ku zama cikin ayyuka masu tsarki da ibada kuma!” (2 Bit. 3:11) Wanda ya fi muhimmanci a cikin waɗannan ayyuka shi ne shelar bishara. (Mat. 24:14) Hakika, aikin wa’azi yana iya kasance da wuya a wasu yankuna, wataƙila domin wariya ko kuma hamayya ko kuma domin mutane sun shagala da rayuwarsu na yau da kullum. Bayin Jehobah na dā su ma sun jimre da irin waɗannan halayen. Duk da haka, ba su yi sanyin gwiwa ba amma sun “yi ta aika musu” saƙon da Allah ya ba su. (Karanta 2 Labarbaru 36:15, 16; Irm. 7:24-26; Littafi Mai Tsarki) Menene ya taimaka musu su jimre? Sun ɗauki aikinsu bisa ra’ayin Jehobah, ba daga ra’ayin duniya ba. Kuma sun ɗauki kiransu da sunan Allah a matsayin gata mafi girma.—Irm. 15:16.

18. Yaya aikin wa’azin Mulki zai shafi ɗaukaka sunan Allah a nan gaba?

18 Mu ma muna da gatan yin shelar sunan Jehobah da nufe-nufensa. Ka yi tunanin wannan: Saboda aikin wa’azin da muke yi, magabtan Allah ba za su iya cewa ba a taɓa gaya musu game da shi da nufe-nufensa ba sa’ad da babban ranarsa ta zo. Hakika, kamar Fir’auna na dā, za su san cewa Jehobah yana gāba da su. (Fit. 8:1, 20; 14:25) A wannan lokacin, Jehobah zai ɗaukaka bayinsa masu aminci ta wajen sa ya bayyana a fili cewa sune wakilansa.—Karanta Ezekiel 2:5; 33:33.

19. Ta yaya za mu nuna cewa muna son mu yi amfani da kyau da haƙurin Jehobah?

19 A kusan ƙarshen wasiƙarsa ta biyu, Bitrus ya rubuta zuwa ga ’yan’uwansa masu bi: “Ku maida jimrewar Ubangijinmu ceto ne.” (2 Bit. 3:15) Hakika, bari mu ci gaba da yin amfani sosai da haƙurin Jehobah. Ta yaya? Ta wajen nuna halayen da ke faranta masa rai, ta wajen kasancewa “marasa-aibi marasa-laifi,” da kuma kasancewa da hali mai kyau game da jarrabobi, da kuma shagalawa a hidimar Mulki. Ta yin hakan, za mu samu albarka marar iyaka da ke haɗe da “sababbin sammai da sabuwar duniya.”—2 Bit. 3:13.

Ka Tuna?

• Ta yaya za mu koyi halaye na ibada?

• Ta yaya za mu kasance “marasa-aibi marasa-laifi”?

• Menene za mu iya koya daga Yusufu da Naomi?

• Me ya sa yin aikin wa’azi gata ne mai girma?

[Hoton da ke shafi na 9]

Menene zai taimaka muku magidanta da iyalanku ku koyi halaye na ibada?

[Hotuna da ke shafi na 10]

Menene za mu koya daga yadda Yusufu ya bi da jarrabobi?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba