Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 8/1 pp. 4-8
  • Ka Ƙara Wa Jimirinka Ibada

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Ƙara Wa Jimirinka Ibada
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Bukatar Jimiri
  • Abin da Ibada Take Nufi
  • Ka Gina Dangantaka da Allah
  • Ka Ci Gaba da Ƙarfafa a Ruhaniya
  • Ka Mai da Hankali ga Abubuwa Masu Lahani ga Ibada
  • Ka Bi Misalin Yesu
  • Halayen Da Ya Kamata Mu Biɗa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ibada Ta Fi Tara Dukiya
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 8/1 pp. 4-8

Ka Ƙara Wa Jimirinka Ibada

“Ku ƙara . . . cikin bangaskiyarku . . . haƙuri; cikin haƙuri kuma ibada.” —2 BITRUS 1:5, 6.

1, 2. (a) Wane irin girma ake bukata wajen yaro? (b) Yaya girma na ruhaniya yake da muhimmanci?

GIRMA na da muhimmanci ga yaro, amma ana bukatar fiye da girma na jiki. Ana bukatar girma na hankali da motsin zuciya. A kwana a tashi, yaron ko yarinyar za ta kawar da yarantaka ya ko ta zama cikakken mutum ko mutuniya. Manzo Bulus ya yi maganar wannan sa’ad da ya rubuta: “Sa’anda ina yaro, ni kan yi magana ta ƙuruciya, ni kan ji kamar mai-ƙuruciya, tunanina na ƙuruciya ne: amma yanzu da na zama namiji, na kawarda al’amuran ƙuruciya.”—1 Korinthiyawa 13:11.

2 Kalmomin Bulus sun ba da muhimmin darasi game da girma na ruhaniya. Kiristoci suna bukatar su yi girma daga zama jarirai na ruhaniya zuwa cikakkun mutane wajen “azanci.” (1 Korinthiyawa 14:20) Ya kamata su kai a ba su gata kuma su nemi su samu “misalin tsawon cikar Kristi.” Sa’annan ba za su zama “yara, waɗanda ana wofadda su suna shillo ga kowacce iskan sanarwa” ba.—Afisawa 4:13, 14.

3, 4. (a) Menene dole mu yi domin mu manyanta a ruhaniya? (b) Waɗanne halaye na ibada ya kamata mu nuna, yaya suke da muhimmanci?

3 Ta yaya za mu manyanta a ruhaniya? Yayin da ake girma na zahiri haka kawai a yanayi mai kyau, girma na ruhaniya na bukatar ƙoƙari sosai. Yana somawa ne da samun cikakken sanin Kalmar Allah da kuma aikata abin da muka koya daidai. (Ibraniyawa 5:14; 2 Bitrus 1:3) Wannan yana sa mu nuna halaye na ibada. Yadda yake da girma na jiki da fannoninsa, haka girma a halaye dabam dabam na ibada yake faruwa a lokaci ɗaya. Manzo Bitrus ya rubuta: “A wajenku, sai ku ƙara bada ƙoƙari, cikin bangaskiyarku kuma ku kawo halin kirki; cikin halin kirki kuma ilimi; cikin ilimi kuma kamewa; cikin kamewa kuma haƙuri; cikin haƙuri kuma ibada; cikin ibada kuma son ’yan’uwa; cikin son ’yan’uwa kuma ƙauna.”—2 Bitrus 1:5-7.

4 Kowanne hali da Bitrus ya lissafa yana da muhimmanci, ba za a bar ko ɗaya ba. Ya daɗa: “Idan waɗannan abu naku ne, suna kuwa yawaita, su za su hana ku zama raggaye ko kuwa marasa-amfani zuwa ga sanin Ubangijinmu Yesu Kristi.” (2 Bitrus 1:8) Bari mu mai da hankali ga bukatar mu ƙara wa jimirinmu ibada.

Bukatar Jimiri

5. Me ya sa muke bukatar jimiri?

5 Bitrus da Bulus sun haɗa ibada da jimiri. (1 Timothawus 6:11) Jimiri yana nufin fiye da jimrewa kawai a yanayin wahala da kasancewa da aniya. Ya ƙunshi haƙuri, gaba gaɗi, da dagewa ba fid da rai ba sa’ad da aka fuskanci gwaji, tangarɗa, jaraba, ko tsanantawa. Tun da muna rayuwa “mai-ibada cikin Kristi Yesu,” za a tsananta mana. (2 Timothawus 3:12) Dole ne mu jimre idan za mu tabbatar da ƙaunarmu ga Jehovah kuma mu koyi halaye da ake bukata don ceto. (Romawa 5:3-5; 2 Timothawus 4:7, 8; Yaƙub 1:3, 4, 12) Idan ba tare da jimiri ba, ba za mu samu rai madawwami ba.—Romawa 2:6, 7; Ibraniyawa 10:36.

6. Jimrewa har matuƙa yana nufin yin menene?

6 Ko idan ma mun soma da kyau, abin da ya fi muhimmanci shi ne idan muna da jimiri. Yesu ya ce: “Wanda ya jimre har matuƙa shi ne za ya tsira.” (Matta 24:13) Hakika, dole ne mu jimre har matuƙa, ko zuwa ƙarshen rayuwarmu na yanzu ko zuwa ƙarshen wannan mugun zamani. Ko yaya dai, dole ne mu riƙe amincinmu ga Allah. Idan ba tare da ƙara wa jimirinmu ibada ba, ba za mu faranta wa Jehovah rai ba kuma ba za mu samu rai madawwami ba. Mecece ibada?

Abin da Ibada Take Nufi

7. Mecece ibada, me take motsa mu mu yi?

7 Ibada ɗaukaka ce, sujjada, da kuma hidima ga Allah Jehovah cikin aminci ga ikon mallakarsa na dukan halittarsa. Domin mu yi wa Jehovah ibada, muna bukatar mu sami cikakken saninsa da hanyoyinsa. Ya kamata mu so mu san Allah sosai. Wannan zai motsa mu mu manne masa da zuciya ɗaya, wanda za mu nuna ta ayyukanmu da hanyar rayuwarmu. Ya kamata mu so mu zama kamar Jehovah yadda ya yiwu—mu yi koyi da hanyoyinsa kuma mu nuna halayensa da mutuntakarsa. (Afisawa 5:1) Hakika, ibada tana motsa mu mu faranta wa Allah rai a dukan abin da mukan yi.—1 Korinthiyawa 10:31.

8. Ta yaya ibada da cikakkiyar bauta suke da nasaba ta kusa?

8 Domin mu yi ibada ta gaskiya, dole ne mu bauta wa Jehovah shi kaɗai, kada mu bar wani abu ya ɗauki matsayinsa a zuciyarmu. Mahaliccinmu, yana da iko ya bukaci mu bauta masa shi kaɗai. (Kubawar Shari’a 4:24; Ishaya 42:8) Duk da haka, Jehovah ba ya tilasta mana mu bauta masa. Yana so mu bauta masa da yardan rai. Ƙaunarmu ce ga Allah, bisa cikakken saninsa, take motsa mu mu tsabtace rayukanmu kuma mu keɓe masa kanmu babu ragi kuma mu yi rayuwa daidai da keɓe kan.

Ka Gina Dangantaka da Allah

9, 10. Ta yaya za mu gina kuma mu riƙe dangantaka ta kusa da Allah?

9 Bayan mun nuna alamar keɓe kanmu ga Allah ta wajen baftisma, har ila muna bukatar mu gina dangantaka ta kusa da shi. Muradinmu mu yi wannan kuma mu bauta wa Jehovah cikin aminci zai motsa mu mu ci gaba da nazarin Kalmarsa da yin bimbini a kanta. Yayin da muke barin ruhun Allah ya taɓa azancinmu da zuciyarmu, ƙaunarmu ga Jehovah tana zurfafa. Dangantakarmu da shi za ta ci gaba da zama aba mafi muhimmanci a rayuwarmu. Muna ɗaukan Jehovah Amininmu kuma mu so mu faranta masa a dukan lokaci. (1 Yohanna 5:3) Farin cikinmu a dangantakarmu mai kyau da Allah yana ƙaruwa, kuma muna godiya cewa yana koyar da mu cikin ƙauna kuma ya yi mana gyara a inda muke bukatar gyara.—Kubawar Shari’a 8:5.

10 Sai mu ci gaba da ƙoƙari mu ƙarfafa dangantakarmu mai tamani da Jehovah, in ba haka ba za ta yi yaushi. Idan hakan ya faru, ba zai zama laifin Allah ba “ba shi da nisa da kowane ɗayanmu.” (Ayukan Manzanni 17:27) Muna farin ciki cewa Jehovah ba ya sa kusantarsa ta yi wuya! (1 Yohanna 5:14, 15) Hakika, dole ne mu yi ƙoƙari mu riƙe dangantaka ta kusa da Jehovah. Amma, yana taimakonmu mu matsa kusa da shi ta yi mana dukan tanadi da muke bukata mu gina kuma mu riƙe ibadarmu. (Yaƙub 4:8) Ta yaya za mu yi amfani da kyau da dukan waɗannan tanadi masu kyau?

Ka Ci Gaba da Ƙarfafa a Ruhaniya

11. Waɗanne ne wasu nuni na ibadarmu?

11 Ƙaunarmu mai zurfi ga Allah za ta motsa mu mu nuna yawan ibadarmu, cikin jituwa da gargaɗin Bulus: “Ka yi ƙoƙari ka miƙa kanka yardaje ga Allah, ma’aikaci wanda babu dalilin kunya gareshi, kana rarrabe kalmar gaskiya sosai.” (2 Timothawus 2:15) Yin haka yana bukatar mu riƙe tsari mai kyau na nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai, halartar taro, da fita hidimar fage. Za mu kasance kusa da Jehovah ta ‘yin addu’a ba fasawa.’ (1 Tassalunikawa 5:17) Waɗannan nuni ne masu kyau na ibadarmu. Ƙyale kowannensu zai kawo ciwo na ruhaniya kuma ya sa ya zama da sauƙi mu faɗa cikin dabarun Shaiɗan.—1 Bitrus 5:8.

12. Ta yaya za mu yi nasara a jimre wa gwaji?

12 Ƙarfi a ruhaniya da kuma ƙwazo na taimaka mana mu fuskanci gwaji da yawa da ke faɗa mana. Gwaji zai zo daga wurare da zai wahalar da mu sosai. Rashin so, hamayya, da tsanani zai yi wuya a jimre musu in sun fito daga iyalinmu, danginmu, ko kuma maƙwabtanmu. Matsa mana mu taka ƙa’idodin Kirista zai iya tasowa a wurin aiki ko kuma a makaranta. Karaya, ciwo, da baƙin ciki za su iya raunana mu a zahiri kuma ya sa ya yi wuya mu jimre wa gwaji na bangaskiya. Amma za mu yi nasara a jimre wa dukan gwaji idan mun nace ‘cikin tasarrufi mai-tsarki da ibada kuma. Kuna sauraron ranar Allah.’ (2 Bitrus 3:11, 12) Kuma za mu riƙe farin cikinmu a yin haka, da tabbacin cewa Allah zai yi mana albarka.—Misalai 10:22.

13. Menene dole mu yi idan za mu ci gaba da yin ibada?

13 Ko da yake Shaiɗan yana fakon waɗanda suke da ibada, ba ma bukatar mu ji tsoro. Me ya sa? Domin “Ubangiji ya san yadda za ya ceci masu-ibada daga cikin jaraba.” (2 Bitrus 2:9) Don mu jimre wa gwaji kuma mu samu irin wannan ceto, dole ne mu ‘ƙi rashin ibada da sha’awoyi na duniya . . . mu rayu da hankali da adalci da ibada cikin wannan zamani na yanzu.’ (Titus 2:12) Kiristoci, dole ne mu yi tsaro don kada kowanne kumamanci da ya ƙunshi sha’awoyi na jiki da ayyuka ya shiga cikin ibadarmu ya halaka ta. Bari yanzu mu bincika wasu cikin waɗannan abubuwa masu lahani.

Ka Mai da Hankali ga Abubuwa Masu Lahani ga Ibada

14. Me ya kamata mu tuna da shi idan tarkon son abin duniya ya jarabe mu?

14 Son abin duniya tarko ne ga mutane da yawa. Za mu iya mu ruɗi kanmu, da “aza ibada wata hanyar ribar [abin duniya] ce.” Ta haka za mu samu gaba gaɗin yin amfani da bai dace ba da amana da ’yan’uwa masu bi suka ba mu. (1 Timothawus 6:5) Za mu iya kammala da cewa daidai ne mu matsa wa Kirista mai arziki ya ba mu bashi da ba za mu iya biya ba. (Zabura 37:21) Amma, ibada ce, ba tara abin duniya ba, ke riƙe “alkawari ga rai na yanzu, da na mai-zuwa.” (1 Timothawus 4:8) Tun da “ba mu shigo da kome cikin duniya ba, ba kuwa za mu iya fita cikinta da kome ba,” bari mu ƙudiri aniyar biɗan “ibada tare da wadar zuci” mu yi ‘wadar zuci da abinci da sutura’ da muke da su.—1 Timothawus 6:6-11.

15. Menene za mu iya yi idan biɗan nishaɗi yana burgar ya kawar da ibadarmu?

15 Biɗan nishatɗi zai iya kawar da ibada. Ba zai yiwu ba cewa muna bukatar mu yi gyara nan da nan game da wannan? Hakika, ana samun wasu fa’idodi daga wasan motsa jiki da nishaɗi. Duk da haka, irin waɗannan lada kaɗan ne idan aka gwada su da rai madawwami. (1 Yohanna 2:25) A yau, mutane da yawa “ma-fiya son annashuwa da Allah; suna riƙe da surar ibada, amma sun musunci ikonta,” muna bukatar mu guji irin waɗannan mutane. (2 Timothawus 3:4, 5) Waɗanda suke mai da hankali ga ibada “suna ajiye wa kansu tushe mai-kyau domin wokaci mai-zuwa, da za su ruski rai wanda shi ke hakikanin rai.”—1 Timothawus 6:19.

16. Waɗanne sha’awoyi na zunubi ne ke hana wasu su rayu daidai da mizanan Allah na adalci, kuma ta yaya za mu ci nasara bisa waɗannan sha’awoyi?

16 Giya da shan miyagun ƙwayoyi, lalata, da sha’awoyi na zunubi za su iya halaka ibadarmu. Faɗā wa waɗannan sa hana mu rayuwa daidai da mizanan Allah na adalci. (1 Korinthiyawa 6:9, 10; 2 Korinthiyawa 7:1) Har Bulus ma ya jimre da kokawa da ta ci gaba a jiki na zunubi. (Romawa 7:21-25) Ana bukatar mataki masu ƙarfi don a kawar da munanan sha’awoyi. Abu ɗaya shi ne, dole ne mu ƙudiri aniyar kasancewa da tsabta ta ɗabi’a. Bulus ya gaya mana: “Ku matarda gaɓaɓuwanku fa waɗanda ke a duniya; fasikanci, ƙazanta, kwaɗayi, mugun guri, da sha’awa, watau bautar gumaka ke nan.” (Kolossiyawa 3:5) Kashe gaɓaɓuwar jikinmu game da irin waɗannan abubuwa na zunubi na bukatar ƙuduri don mu kawar da su. Addu’a da himma don taimakon Allah za ta taimake mu mu ƙi munanan sha’awoyi mu kuma biɗi adalci da ibada a cikin wannan mugun zamani.

17. Yaya ya kamata mu ɗauki horo?

17 Karaya za ta iya raunana jimirinmu kuma ta yi lahani ga ibadarmu. Bayin Jehovah da yawa sun fuskanci kasala. (Litafin Lissafi 11:11-15; Ezra 4:4; Yunana 4:3) Kasala musamman za ta kasance da sakamako mai halakarwa gare mu idan muna fushi don a ɓata mana rai ko an tsauta mana ko an yi mana horo. Amma, tsautawa da horo tabbaci ne cewa Allah yana son mu kuma yana damuwa da mu. (Ibraniyawa 12:5-7, 10, 11) Bai kamata a ɗauki horo cewa azabtar da mutum ne kawai ba amma hanyar koyar da adalci ne gare mu. Idan muna da tawali’u, za mu daraja kuma mu karɓi horo, domin mun fahimci cewa “tsautawar koyarwa tafarkin rai ne.” (Misalai 6:23) Wannan zai taimaka mana mu yi girma a biɗan ibada.

18. Wane hakki muke da shi game da laifofi?

18 Rashin fahimta da kuskure ga wani za su iya kasancewa ƙalubale ga ibadarmu. Za su iya kawo damuwa ko sa wasu su ɗauki mataki da ba shi da kyau na ware kansu daga ’yan’uwansu na ruhaniya maza da mata. (Misalai 18:1) Amma yana da kyau a tuna cewa ci gaba da fushi ko riƙe mutum a zuciya za su shafi dangantakarmu da Jehovah. (Leviticus 19:18) Hakika, “wanda ba ya yi ƙaunar ɗan’uwansa ba wanda ya gani, ba shi iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani ba.” (1 Yohanna 4:20) A Huɗubarsa bisa Dutse, Yesu ya nanata bukatar ɗaukan mataki nan da nan a warware matsala. Ya gaya wa masu sauraronsa: “Idan fa kana cikin miƙa baiwarka a wurin bagadi, can ka tuna ɗan’uwanka yana da wani abu game da kai, sai ka bar baiwarka can a gaban bagadi, ka yi tafiyarka, a sulhuntu da ɗan’uwanka tukuna, kāna ka zo ka miƙa baiwarka.” (Matta 5:23, 24) Roƙon gafara zai iya taimako a warkar da rauni da baƙar magana ko ayyuka da aka yi. Za a iya sulhunta kuma a maida nasaba ta salama idan mun roƙi gafara kuma mun yarda cewa mun bi da al’amura yadda bai dace ba. Yesu ya ba da wasu gargaɗi a kan warware matsaloli. (Matta 18:15-17) Muna masu farin ciki idan ƙoƙarinmu mu warware matsaloli ya yi nasara!—Romawa 12:18; Afisawa 4:26, 27.

Ka Bi Misalin Yesu

19. Me ya sa ya ke da muhimmanci sosai mu yi koyi da misalin Yesu?

19 Babu shakka za mu fuskanci gwaji, amma bai kamata su janye mu daga tseren rai madawwami ba. Ka tuna cewa Jehovah zai iya cetonmu daga gwaji. Sa’ad da muka “tuɓe kowane abin nauwaitawa” kuma muka “yi tseren da an sa gabanmu,” bari mu “zuba ido ga Yesu shugaban bangaskiyarmu da mai-cikanta.” (Ibraniyawa 12:1-3) Bincika misalin Yesu da kuma ƙoƙari mu yi koyi da shi a kalma da ayyuka zai taimaka mana mu koyi ibada kuma mu nuna ta sosai.

20. Wace lada ce take zuwa daga biɗan jimiri da ibada?

20 Jimiri da ibada suna da nasaba ta kusa wajen taimakonmu mu sa cetonmu ya kasance da tabbaci. Ta nuna wannan hali mai tamani, za mu ci gaba cikin aminci a tsarkakar hidimarmu ga Allah. Ko a lokacin da muke cikin gwaji, za mu yi farin ciki sa’ad da muka fuskanci ƙaunar Jehovah da albarka domin mun jimre kuma muna gwada ibada. (Yaƙub 5:11) Ban da haka ma, Yesu kansa ya tabbatar mana: “Ta cikin haƙurinku za ku sami rayukanku.”—Luka 21:19.

Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa jimiri yake da muhimmanci?

• Mecece ibada, kuma yaya ake nuna ta?

• Ta yaya za mu gina kuma mu riƙe dangantaka ta kusa da Allah?

• Menene wasu abubuwa da suke yi wa ibadarmu razana, kuma yaya za mu iya guje musu?

[Hotuna a shafuffuka na 6, 7]

Ana nuna ibada a hanyoyi da yawa

[Hotuna a shafi na 8]

Ka mai da hankali ga abubuwa da za su yi lahani ga ibadarka

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba