Halayen Da Ya Kamata Mu Biɗa
“Ka bi adalci, ibada, bangaskiya, ƙauna, haƙuri, [da kuma] tawali’u.”—1 TIM. 6:11.
1. Ka kwatanta manufar kalmar nan “bi.”
MENENE ka ke tunawa sa’ad da ka ji kalmar nan “bi”? Wataƙila za ka tuna da zamanin Musa sa’ad da sojojin Masar “suka bi” Isra’ilawa, amma suka halaka a Jan Teku. (Fit. 14:23) Ko kuma za ka tuna da haɗarin da wanda ya yi kisan kai ba da son ransa ba yake fuskanta a Isra’ila ta dā. Dole ne ya gudu ya shiga ɗaya daga cikin biranen mafaka guda shida. Idan ba haka ba, “mai-jan jini zai bi mai-kisan, tun zuciyassa tana ƙuna, ya kuwa tarshe shi, . . . ya kashe shi.”—K. Sha 19:6.
2. (a) Wace kyauta ce Allah ya ce wasu Kiristoci su biɗa? (b) Wane bege ne Jehobah ya ba Kiristoci da yawa a yau?
2 Akasin wannan misalin da ke cikin Littafi Mai Tsarki da aka ambata a baya, ka yi la’akari da ra’ayi mai kyau da manzo Bulus yake da shi: “Ina nace bi har zuwa ga goal, in kai ga ladan nasara na maɗaukakiyar kira ta Allah cikin Kristi Yesu.” (Filib. 3:14) Kamar yadda Bulus ya kammala, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa shafaffun Kiristoci guda 144,000 tare da Bulus ne suka sami wannan kyauta ta yin rayuwa a samaniya. Za su yi sarauta da Yesu Kristi ta shekara dubu bisa duniya. Wannan bege ne mai kyau da Allah ya ce su biɗa. A yau yawancin Kiristoci na gaskiya suna da bege ko makasudi da ta bambanta. Jehobah ya ba su abin da Adamu da Hauwa’u suka yi hasararsa, wato, begen yin rayuwa ta har abada da cikakkiyar lafiya a aljanna a duniya.—R. Yoh. 7:4, 9; 21:1-4.
3. Ta yaya za mu nuna godiyarmu ga alherin Allah?
3 Mutane masu zunubi ba za su iya samun rayuwa ta har abada ba ta wajen yin ƙoƙarin su yi abu mai kyau. (Isha. 64:6) Samun rayuwa ta har abada zai yiwu idan muka ba da gaskiya ga hanyar ceto da Allah ya yi tanadinsa ta wurin Yesu Kristi. Me za mu yi don mu nuna godiya ga wannan alheri da Allah ya yi mana? Wani abin da za mu iya yi shi ne, mu bi wannan umurnin: “Ka bi adalci, ibada, bangaskiya, ƙauna, haƙuri, tawali’u.” (1 Tim. 6:11) Yin la’akari da waɗannan halayen za su iya taimakon kowannenmu mu ƙudiri aniyar bin su “ƙwarai da gaske.”—1 Tas. 4:1; LMT.
Ka Biɗi “Adalci”
4. Me ya sa ya kamata mu tabbata cewa biɗan “adalci” yana da muhimmanci, kuma wane mataki ne mutum yake bukatar ya ɗauka?
4 A wasiƙunsa ga Timothawus, manzo Bulus ya lissafa halayen da za a biɗa, a kowannensu ya ambata “adalci” da farko. (1 Tim. 6:11; 2 Tim. 2:22) Amma, a wasu ayoyin, Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu a kai a kai mu biɗi adalci. (Mis. 15:9; 21:21; Isha. 51:1) Za mu fara yin haka ta wurin ‘sanin Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda [ya] aiko, Yesu Kristi.’ (Yoh. 17:3) Biɗan adalci zai motsa mutum ya tuba kuma ya “juyo” don ya yi nufin Allah.—A. M. 3:19.
5. Me ya kamata mu yi don mu samu kuma mu kasance da adalci a gaban Allah?
5 Mutane da yawa da suke biɗan adalci da gaske sun keɓe kansu ga Jehobah kuma sun yi baftisma. Idan kai Kirista ne da ya yi baftisma, ka taɓa tunanin cewa yadda kake rayuwa zai nuna ko kana biɗan adalci ne? Abu na farko shi ne, ka fahimci abu mai “nagarta da mugunta” daga cikin Littafi Mai Tsarki sa’ad da ka ke son ka tsai da shawara mai muhimmanci game da rayuwarka. (Ka karanta Ibraniyawa 5:14.) Alal misali, idan kai Kirista ne da ya isa yin aure, ka ƙudiri aniyar guje wa soma soyayya da wadda ba Kirista ba ce da ba ta yi baftisma ba? Za ka yi hakan idan kana biɗan adalci.—1 Kor. 7:39.
6. Menene biɗan adalci ya ƙunsa?
6 Kasancewa da adalci ya bambanta da adalcin kai ko kuma “cika yin adalci.” (M. Wa. 7:16) Yesu ya yi gargaɗi game da nuna irin wannan adalci don a nuna an fi wasu. (Mat. 6:1) Hakika biɗan adalci ya ƙunshi zuciya wato, gyara tunani, halaye, muradi, da kuma sha’awoyi marar kyau. Idan muka ci gaba da yin hakan, da kyar mu yi zunubi mai tsanani. (Ka karanta Misalai 4:23; ka gwada Yaƙub 1:14, 15.) Bugu da ƙari, Jehobah zai albarkace mu kuma ya taimake mu a biɗan halayen Kiristoci masu muhimmanci.
Ka Biɗi “Ibada”
7. Mecece “ibada”?
7 Ibada ta ƙunshi keɓe kai da kuma kasancewa da aminci. Wani ƙamus na Littafi Mai Tsarki ya ce kalmar Hellenanci da aka fassara “ibada” tana nufin “kasancewa da hali mai kyau don kada mu bar kome ya hana mu tsoron Allah.” Sau da yawa Isra’ilawa sun kasa nuna irin wannan ibada, kamar yadda suka aikata bayan da Allah ya cece su daga Masar.
8. (a) Wace tambaya ce zunubin Adamu ya jawo? (b) Ta yaya ne aka bayyana amsar wannan “asirin”?
8 Shekaru dubbai bayan da Adamu kamiltacce ya yi zunubi, ba a amsa wannan tambayar ba, “Akwai mutumin da zai iya yin cikakkiyar ibada kuwa?” A cikin wannan zamanin, babu wani mutum mai zunubi da ya yi rayuwa ta cikakkiyar ibada. Amma a daidai lokacinsa, Jehobah ya bayyana amsar wannan “asirin.” Ya mai da ran Ɗansa makaɗaici cikin mahaifar Maryamu don ta haife shi kamili. A dukan rayuwarsa a duniya da kuma mutuwar wulakancin da ya yi, Yesu ya nuna ma’anar keɓe kai da kuma kasancewa da aminci sosai ga Allah na gaskiya. Addu’arsa ta nuna yadda ya ɗauki bautar Ubansa na samaniya. (Mat. 11:25; Yoh. 12:27, 28) Saboda haka, Jehobah ya huri Bulus ya yi magana game da “ibada” ta wajen kwatanta rayuwa mai kyau da Yesu ya yi.—Ka karanta 1 Timothawus 3:16.
9. Ta yaya za mu iya biɗar ibada?
9 Da yake mu ajizai ne, ba za mu iya bauta wa Allah a kamiltacciyar hanya ba. Amma za mu iya yin ƙoƙari mu bauta masa. Hakan yana bukatar mu bi gurbin Kristi kud da kud. (1 Bit. 2:21) Da haka, ba za mu zama kamar munafukai da suke “riƙe da surar ibada, amma sun musunci ikonta” ba. (2 Tim. 3:5) Hakan yana nufin cewa ibada ta gaskiya ta shafi yadda muke ado. Alal misali, sa’ad da muke zaɓan kayan da za mu sa a ranar aurenmu ko kuma kayan da za mu sa mu je kasuwa, ya kamata adonmu a kowane lokaci ya jitu da “shaidan ibada [ta Allah]” da muke yi. (1 Tim. 2:9, 10) Hakika, ibada tana bukatar mu mai da hankali ga mizanan Allah masu adalci a rayuwarmu ta yau da kullum.
Ka Biɗi “Bangaskiya”
10. Menene ya kamata mu yi don bangaskiyarmu ta ci gaba da kasancewa mai ƙarfi?
10 Ka karanta Romawa 10:17. Don ya samu kuma ya ci gaba da kasancewa da bangaskiya mai ƙarfi, dole ne Kirista ya ci gaba da yin bimbini a kan gaskiya mai tamani da ke cikin Kalmar Allah. “Bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya yi mana tanadin littattafai masu kyau da yawa. Littattafai uku fitattu su ne The Greatest Man Who Ever Lived, Ka Koya Daga Babban Malami, da kuma Come Be My Follower,” an tsara waɗannan littattafai don su taimake mu mu san Kristi sosai kuma mu bi gurbinsa. (Mat. 24:45-47) Rukunin bawan nan yana kuma shirya taro, manyan taro, da kuma taron gunduma, waɗanda yawancin su suna nanata “maganar Kristi.” Ka ga hanyoyin da za ka iya amfana sosai daga waɗannan tanadodin sa’ad da ka “ƙara mai da hankali” ga abubuwan da Allah yake tanadinsu?—Ibran. 2:1.
11. Menene muhimmancin addu’a da biyayya a bangaskiyar da muke biɗa?
11 Addu’a wata hanya ce da za a ƙarfafa bangaskiya. Mabiyan Yesu sun taɓa roƙonsa: “Ka ƙara mana bangaskiya.” Za mu iya roƙon Allah ya ba mu bangaskiya. (Luka 17:5) Don haka, dole ne mu yi addu’a don samun taimakon ruhu mai tsarki na Allah; bangaskiya tana ɗaya daga cikin fannonin “ɗiyan Ruhu.” (Gal. 5:22) Bugu da ƙari, yin biyayya ga dokokin Allah yana ƙarfafa bangaskiyarmu. Alal misali, za mu iya ƙara sa hannu a aikin wa’azi. Hakan zai sa mu kasance da farin ciki sosai. Sa’ad da muka yi tunanin albarkar da ake samu a “biɗan mulkin [Allah], da adalcinsa,” bangaskiyarmu za ta ƙaru.—Mat. 6:33.
Ka Biɗi “Ƙauna”
12, 13. (a) Mecece sabuwar dokar Yesu? (b) Waɗanne hanyoyi ne na musamman ya kamata mu biɗi ƙauna irin ta Yesu?
12 Ka karanta 1 Timothawus 5:1, 2. Bulus ya ba da shawara mai kyau a kan yadda Kiristoci za su nuna wa juna ƙauna. Dole ne ibadarmu ta ƙunshi biyayya ga sabuwar dokar Yesu da ta ce a nuna ‘ƙauna ga juna’ kamar yadda ya ƙaunace mu. (Yoh. 13:34) Manzo Yohanna ya ce: “Amma wanda shi ke da dukiyar duniya, yana kuwa ganin ɗan’uwansa da tsiya, ya hana masa tausayi, ƙaƙa ƙaunar Allah tana zaune a cikinsa?” (1 Yoh. 3:17) Za ka taɓa tuna lokacin da ka nuna ƙauna kuwa?
13 Wata hanya kuma da muke biɗar ƙauna ita ce ta wajen gafartawa, ban da riƙe ’yan’uwanmu a zuciya. (Ka karanta 1 Yohanna 4:20.) Maimakon haka, za mu so mu bi wannan hurarriyar shawara: “Kuna haƙuri da juna, kuna gafarta ma juna, idan kowanne mutum yana da maganar ƙara game da wani; kamar yadda Ubangiji ya gafarta muku, hakanan kuma sai ku yi.” (Kol. 3:13) Akwai wanda za ka iya yin amfani da wannan shawara a kansa a cikin ikilisiya? Za ka gafarta masa ko mata?
Ka Biɗi “Haƙuri”
14. Menene za mu koya daga ikilisiyar da ke Filadalfiya?
14 Yana da sauƙi mu yi iya ƙoƙarinmu mu cim ma makasudi da ba zai ɗauki lokaci sosai ba, amma ba shi da sauƙi mu cim ma makasudin da zai ɗauki lokaci fiye da yadda muke tsammani. Babu shakka, biɗar makasudi na rai har abada yana bukatar jimiri. Ubangiji Yesu ya gaya wa ikilisiyar da ke Filadalfiya cewa: “Tun da ka kiyaye maganar haƙurina, ni ma zan kiyaye ka daga sa’ar jaraba.” (R. Yoh. 3:10) Hakika, Yesu ya koyar da muhimmancin yin jimiri, wato, halin da zai hana mu yin sanyin gwiwa sa’ad da muke fuskantar jarraba. ’Yan’uwa da suke ikilisiyar Filadalfiya a ƙarni na farko sun nuna fitaccen jimiri a dukan jarrabawar da suka fuskanta domin bangaskiyarsu. Saboda haka, Yesu ya ba su tabbaci cewa zai yi musu ƙarin taimako a lokacin jarrabawa mafi girma da ke zuwa.—Luka 16:10.
15. Menene Yesu ya koyar game da jimiri?
15 Yesu ya san cewa mabiyansa za su fuskanci ƙiyayya daga hannun ’yan’uwansu marasa bi da kuma duniya gabaki ɗaya, saboda haka, ya ƙarfafa su sau biyu da waɗannan kalaman: “Wanda ya jimre har matuƙa, shi ne za ya tsira.” (Mat. 10:22; 24:13) A wannan lokacin Yesu ya nuna yadda almajiransa za su sami ƙarfin da suke bukata don su jimre. A wani kwatanci, Yesu ya kwatanta ƙasa mai duwatsu da mutanen da suka “karɓi magana da farinciki” suka yi sanyin gwiwa sa’ad da aka jarraba bangaskiyarsu. Amma, ya kwatanta mabiyansa masu aminci da ƙasa mai kyau domin sun “riƙe” Kalmar Allah “da haƙuri kuma suna bada amfani.”—Luka 8:13, 15.
16. Menene ya taimaki mutane da yawa su jimre?
16 Ka fahimci asirin jimiri kuwa? Dole ne mu “riƙe” Kalmar Allah a zuciyarmu. Samun New World Translation of the Holy Scriptures, wato, tabbatacciyar fassara mai sauƙin karantawa da ke harsuna da yawa ya sa ya kasance da sauƙi. Yin bimbini bisa Kalmar Allah kowace rana zai taimake mu mu sami ƙarfin ci gaba da ba da amfani da “haƙuri.”—Zab. 1:1, 2.
Ka Biɗi “Tawali’u” da Salama
17. (a) Me ya sa “tawali’u” yake da muhimmanci? (b) Ta yaya Yesu ya nuna cewa yana da tawali’u?
17 Babu wanda yake farin cikin idan aka zarge shi da abin da bai faɗa ba ko bai yi ba. Ba abin mamaki ba ne mutane su fusata idan aka zargi su kuma su rama zagin da aka yi musu. Amma yana da kyau a nuna “tawali’u”! (Ka karanta Misalai 15:1.) Ba shi da sauƙi a nuna tawali’u idan aka zarge mutum. Yesu Kristi ya kafa misali mai kyau a wannan batu. “Sa’anda aka zage shi, ba ya mayarda zagi ba; sa’anda ya sha azaba, ba ya yi kashedi ba; amma ya damƙa maganatasa ga wanda ke yin shari’a mai-adalci.” (1 Bit. 2:23) Ba a bukatar mu yi daidai yadda Yesu ya yi a wannan batu, amma za mu iya yin ƙoƙari don mu nuna tawali’u.
18. (a) Wane abu mai kyau ne tawali’u yake cim ma? (b) Wane hali ne aka aririce mu mu biɗa?
18 Don yin koyi da Yesu, bari ‘kullum [mu kasance] a shirye mu ba da amsa,’ don imaninmu, da tawali’u “da ladabi.” (1 Bit. 3:15) Hakika, kasancewa da tawali’u zai iya hana bambancin ra’ayi da zai iya sa mu yin fushi da mutane da muka haɗu da su a hidimarmu da kuma ’yan’uwanmu. (2 Tim. 2:24, 25) Tawali’u zai taimake mu mu sami salama. Wataƙila shi ya sa a wasiƙarsa ta biyu ga Timothawus Bulus ya lissafa “salama” a cikin halayen da ya kamata mu biɗa. (2 Tim. 2:22; ka gwada 1 Timothawus 6:11.) Hakika, “salama” tana cikin halayen da Nassosi ya ƙarfafamu mu biɗa.—Zab. 34:14; Ibran. 12:14.
19. Bayan da muka tattauna halayen Kiristoci guda bakwai, menene ka ƙudurta cewa za ka biɗa, kuma me ya sa?
19 Mun tattauna halaye bakwai da aka aririce mu mu biɗa wato, adalci, ibada, bangaskiya, ƙauna, jimiri, tawali’u da kuma salama. Abin farin cikin ne ’yan’uwa maza da mata a kowace ikilisiya su yi ƙoƙari su kasance da waɗannan halayen masu kyau. Hakan zai girmama Jehobah kuma ya sa dukanmu mu yabe shi.
Domin Bimbini
• Menene biɗar adalci da ibada ya ƙunsa?
• Menene zai taimake mu mu biɗi bangaskiya da jimiri?
• Ta yaya ƙauna za ta shafi dangantakarmu da juna?
• Me ya sa muke bukatar mu biɗi tawali’u da salama?
[Hoto a shafi na 12]
Yesu ya yi gargaɗi game da nuna adalci don a burge mutane
[Hoto a shafi na 13]
Za mu iya biɗar bangaskiya ta wajen yin bimbini a kan gaskiyar Kalmar Allah
[Hoto a shafi na 15]
Za mu iya biɗar ƙauna da tawali’u