Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w20 Yuni p. 17
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Makamantan Littattafai
  • Za Ka Ci Gaba Da Yin “Tafiya Bisa Ga Ruhu”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Kana Barin Ruhun Allah Ya Yi Maka Ja-gora Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ku Ci-gaba da Saka ‘Sabon Hali’ Bayan Kun Yi Baftisma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Halayen Da Ya Kamata Mu Biɗa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
w20 Yuni p. 17

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Halayen da aka ambata a Galatiyawa 5:​22, 23 su ne kaɗai halayen da ruhun Allah yake sa mu kasance da su?

  • ƘAUNA

  • FARIN CIKI

  • SALAMA

  • HAƘURI

  • NASIHA

  • NAGARTA

  • AMINCI

  • TAWALI’U

  • KAMEWA

Ayoyin sun lissafta halaye guda tara: ‘Ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki [nasiha], nagarta, aminci, tawali’u, da kuma shan ƙarfin sha’awar jiki,’ wato kamewa. Amma bai kamata mu yi tunanin cewa waɗannan ne kaɗai halaye masu kyau da ruhun Allah zai sa mu kasance da su ba.

Ka yi la’akari da abin da manzo Bulus ya rubuta kafin waɗannan ayoyin. Ya ce: ‘Ayyukan halin mutuntaka . . . su ne iskanci, da halin lalata, da halin neman jin daɗi na rashin kunya, da bautar gumaka, da maitanci, da ƙin juna, da faɗa, da kishin juna, da fushi, da sonkai, da rabuwa, da yin tawaye, da kishi, da buguwa, da bukukuwan shaye-shaye, da kuma sauran irin abubuwa kamar haka.’ (Gal. 5:​19-21) Ba kome Bulus ya ambata a ayar ba, shi ya sa ya faɗa a Kolosiyawa 3:5 cewa, “da kuma sauran irin abubuwa kamar haka.” Hakazalika, bayan ya lissafta halaye guda tara masu kyau, ya ce: ‘Babu dokar da ta hana waɗannan abubuwa.’ Don haka, Bulus bai lissafta dukan halayen da ruhun Allah zai iya taimaka mana mu kasance da su ba.

Hakazalika, Bulus ya ƙarfafa Timoti cewa ya kasance da halayen nan shida masu muhimmanci, wato “adalci, da kasancewa da hali irin na Allah, da bangaskiya, da ƙauna, da jimrewa, da kuma tawali’u.” (1 Tim. 6:11) Guda uku ne kaɗai daga cikin waɗannan halayen, wato bangaskiya da ƙauna da kuma tawali’u aka ambata cikin halayen da ruhun Allah ke haifarwa. Duk da haka, Timoti yana bukatar taimakon ruhu mai tsarki don ya zama mai adalci, ya kasance da hali irin na Allah, da kuma jimrewa.​—Ka gwada Kolosiyawa 3:12 da 2 Bitrus 1:​5-7.

Saboda haka, ba a lissafta dukan halaye da ya kamata Kirista ya kasance da su a littafin Galatiyawa 5:​22, 23 ba. Ruhun Allah zai taimaka mana mu kasance da halaye tara da ruhu mai tsarki yake haifar da su. Kuma da akwai wasu halaye ma da muke bukatar mu kasance da su yayin da muke manyanta kuma muka “ɗauki sabon halin nan da Allah ya halitta bisa ga kamannin kansa. Halin nan kuwa, ya bayyana cikin adalci da zaman tsarki.”​—Afis. 4:24.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba