Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 4/15 pp. 23-27
  • Kana Barin Ruhun Allah Ya Yi Maka Ja-gora Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Barin Ruhun Allah Ya Yi Maka Ja-gora Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Tawali’u da Tsawon Jimrewa Suna Kawo Salama a Cikin Ikilisiya
  • Ka Wartsake Iyalinka da Nasiha da Nagarta
  • Ka Nuna Bangaskiya Sa’ad da Ka Kaɗaita
  • Ka Kar̄e Zuciyarka ta Wajen Nuna Kamewa
  • Za Ka Ci Gaba Da Yin “Tafiya Bisa Ga Ruhu”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Me Ya Sa Ruhun Allah Zai Yi Mana Ja-gora?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Yi Tafiya Bisa Ga Ruhu Kuma Ka Yi Rayuwar Da Ta Jitu Da Keɓe Kanka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 4/15 pp. 23-27

Kana Barin Ruhun Allah Ya Yi Maka Ja-gora Kuwa?

“Ruhunka mai-nagarta ne; ka bishe ni cikin ƙasar adalci.”—ZAB. 143:10.

1, 2. (a) Ka faɗa wasu lokatai da Jehobah ya yi amfani da ruhu mai tsarki a madadin bayinsa. (b) Ruhu mai tsarki yana aiki ne a lokatai na musamman kawai? Ka bayyana.

MENE ne kake tunawa idan ka yi tunanin aikin ruhu mai tsarki? Shin kana tunanin ayyuka masu girma da Gideon da Samson suka yi? (Alƙa. 6:33, 34; 15:14, 15) Wataƙila ka yi tunanin gaba gaɗin Kiristoci na farko ko kuma halin lumana na Istifanus yayin da ya tsaya a gaban Majalisa. (A. M. 4:31; 6:15) Me kuma za a faɗa game da farin cikin da ake yi a taronmu na ƙasashe, da amincin ’yan’uwanmu da aka saka a kurkuku don tsakatsakinsu da kuma ƙaruwa mai ban mamaki da ake samu a aikin wa’azi? Waɗannan misalan sun nuna cewa ruhu mai tsarki yana aiki.

2 Shin ruhu mai tsarki yana aiki ne a lokatai ko kuma a yanayi na musamman? A’a. Kalmar Allah ta ce Kiristoci suna “tafiya bisa ga Ruhu,” ‘ruhu ya bishe su’ kuma suna “rayuwa bisa ga Ruhu.” (Gal. 5:16, 18, 25) Waɗannan kalamai sun nuna cewa ruhu mai tsarki zai iya ci gaba da rinjayarmu a rayuwa. A kowace rana ya kamata mu roƙi Jehobah ya ja-goranci tunaninmu, da furcinmu da kuma ayyukanmu ta wurin ruhunsa. (Karanta Zabura 143:10.) Idan mun ƙyale ruhun ya yi aiki a rayuwarmu zai sa mu nuna ’yar ruhu da za ta wartsake mutane da kuma sa a yabi Allah.

3. (a) Me ya sa muke bukatar ja-gorar ruhu mai tsarki? (b) Waɗanne tambayoyi za mu tattauna?

3 Me ya sa yake da muhimmanci ruhu mai tsarki ya yi mana ja-gora? Domin da akwai wani ruhu da yake nema ya rinjaye mu, wani abu da yake hana ruhu mai tsarki ya yi aiki. Nassosi sun kira wancan ruhu “jiki,” wanda yake nuni ga halaye na zunubi na ajizancinmu, wato, ajizancin da muka gada a matsayin ’ya’yan Adamu. (Karanta Galatiyawa 5:17.) Mene ne ƙyale ruhun Allah ya yi mana ja-gora ya ƙunsa? Shin da akwai matakai masu kyau da za mu iya ɗauka don mu hana jikinmu na ajizanci ya rinjaye mu? Bari mu yi la’akari da waɗannan tambayoyi yayin da muke tattauna sauran fannoni shida na ‘’yar ruhu’ wato, “tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, kamewa.”—Gal. 5:22, 23.

Tawali’u da Tsawon Jimrewa Suna Kawo Salama a Cikin Ikilisiya

4. Ta yaya tawali’u da tsawon jimrewa suke kawo salama a cikin ikilisiya?

4 Karanta Kolosiyawa 3:12, 13. Tawali’u da tsawon jimrewa suna aiki tare don ikilisiya ta kasance da salama. Waɗannan fannoni na ’yar ruhu suna taimaka mana mu bi da mutane da kyau, mu natsu idan aka ɓata mana rai kuma mu ƙi ramawa idan mutane suka yi mana laifi ko kuma baƙar magana. Idan muka samu matsala da wani ɗan’uwa Kirista, tsawon jimrewa ko kuma haƙuri zai taimaka mana kada mu yasar da ɗan’uwanmu ko ’yar’uwarmu amma mu yi iya ƙoƙarinmu don mu kasance da salama. Shin ana bukatar tawali’u da tsawon jimrewa a cikin ikilisiya da gaske? Hakika, domin dukanmu ajizai ne.

5. Mene ne ya faru tsakanin Bulus da Barnaba, kuma mene ne wannan ya nuna?

5 Ka yi la’akari da abin da ya faru tsakanin Bulus da Barnaba. Sun yi hidima shekaru da yawa tare suna yaɗa wa’azin bishara. Kowannensu yana da halaye masu kyau. Duk da haka a wani lokaci, “matsanancin saɓanin ra’ayi ya auku, har ya kai su ga rabuwa.” (A. M. 15:36-39, Littafi Mai Tsarki) Wannan ya nuna cewa amintattun bayin Allah za su iya samun saɓani a wasu lokatai. Idan akwai saɓani tsakani ’yan’uwa biyu, mene ne za su iya yi don kada maganar fushi ta sa dangantakarsu ta ɓace a dindindin?

6, 7. (a) Wane gargaɗi na Nassi ne za mu iya bi don kada tattaunawa da ɗan’uwa mai bi ya zama na fushi? (b) Me ya sa ‘hanzarin ji, jinkirin yin magana, da jinkirin yin fushi’ suke da amfani?

6 Wasu fassarar Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa matsalar da ta taso tsakanin Bulus da Barnaba ta faru ne farat ɗaya. Idan Kirista ya ga cewa ya fara yin fushi sa’ad da yake tattauna wani batu da ɗan’uwa mai bi, yana da kyau ya bi gargaɗin da ke cikin Yaƙub 1:19, 20: “Kowane mutum ya yi hanzarin ji, ya yi jinkirin yin magana, ya yi jinkirin yin fushi: gama fushin mutum ba ya aikata adalcin Allah ba.” Bisa ga yanayin, yana iya canja batun, ya bar zancen zuwa wani lokaci, ko kuma ya bar wurin kafin tattaunawar ta zama ta fushi.—Mis. 12:16; 17:14; 29:11.

7 Mene ne amfanin bin wannan gargaɗin? Kirista yana barin ruhun Allah ya yi masa ja-gora ta wurin sa hankalinsa ya kwanta, ya yi addu’a game da batun, kuma ya yi tunanin yadda zai fi kyau ya ba da amsa. (Mis. 15:1, 28) Zai iya nuna tawali’u da tsawon jimrewa idan ruhun ya yi masa ja-gora. Ta hakan yana shirye ya yi biyayya ga gargaɗin da ke Afisawa 4:26, 29: “Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi . . . Kada kowane ruɓaɓen zance shi fita daga cikin bakinku, sai irin abin da ke mai-kyau garin ginawa yayinda ake bukata, domin shi ba da alheri ga waɗanda suke ji.” Hakika, sa’ad da muka yafa tawali’u da tsawon jimrewa, muna sa ikilisiyar ta kasance da salama da haɗin kai.

Ka Wartsake Iyalinka da Nasiha da Nagarta

8, 9. Mene ne alheri da nagarta, kuma yaya suke sa yanayin gida ya kasance?

8 Karanta Afisawa 4:31, 32; 5:8, 9. Alheri da nagarta suna wartsake mutum kamar iska mai daɗi da shan ruwan sanyi a inda ana rana mai zafi. Suna kawo yanayi mai kyau a cikin iyali. Alheri hali ne mai kyau da muke nunawa don mun damu da mutane, ana yin sa ta ayyukan taimako da kuma kalmomi na sanin ya kamata. Kamar alheri, nagarta hali ne mai kyau da ake nunawa ta ayyuka da suke amfanar mutane. Ana yinsa ta yin karimci. (A. M. 9:36, 39; 16:14, 15) Amma nagarta tana nufin abubuwa da yawa fiye da wannan.

9 Nagarta ɗabi’a mai kyau ce. Ta ƙunshi abin da muke yi da kuma musamman irin mutum da muke. Tana kamar ’yar itace da ke da zaƙi kuma cikin da bayan ba ta lalace ba. Hakazalika, nagartar da ruhu mai tsarki ke haifarwa ana bayyana a yadda Kirista yake rayuwarsa gabaki ɗaya.

10. Mene ne za a iya yi don a taimaki waɗanda suke cikin iyali su nuna ’yar ruhu?

10 Mene ne zai iya taimaki iyalan Kirista su bi da juna cikin nagarta da alheri? Sanin Kalmar Allah sosai yana da matsayi mai muhimmanci. (Kol. 3:9, 10) Wasu magidanta suna haɗa nazarin ’yar ruhu a Bautarsu ta Iyali da yamma na kowanne mako. Yin nazarin wannan ’yar ruhu yana da sauƙi. Ta yin amfani da kayan bincike da kuke da su a yarenku, ku zaɓa littattafai da suka yi magana a kan kowanne fanni na ’yar ruhu. Za ku iya tattauna sakin layi kaɗan kowanne mako, kuna tattauna kowanne fanni makonni da yawa. Yayin da kuke yin nazarin littafin, ku karanta kuma ku tattauna nassosin da aka yi ƙaulinsu. Ku nemi hanyoyin da za ku yi amfani da abubuwan da kuka koya, kuma ku yi addu’a ga Jehobah don ya albarkace ƙoƙarce-ƙoƙarcenku. (1 Tim. 4:15; 1 Yoh. 5:14, 15) Shin irin wannan nazarin zai iya shafan yadda waɗanda suke cikin iyali suke bi da juna?

11, 12. Ta yaya ma’aurata biyu Kiristoci suka amfana daga yin nazari a kan alheri?

11 Wasu ma’aurata da suke son su yi nasara a aurensu sun tsai da shawara su yi nazarin ’yar ruhu sosai. Ta yaya suka amfana? Matar ta bayyana: “Koyan cewa alheri ya haɗa da riƙe amana da kuma aminci ya shafi yadda muke bi da juna har yau. Ya koya mana kasancewa da sauƙin hali da kuma yafewa. Kuma ya koya mana mu riƙa ce, ‘na gode’ da ‘yi haƙuri’ sa’ad da yin hakan ya dace.”

12 Wani ma’aurata Kirista kuma da suke fuskantar matsaloli a aurensu, sun fahimci cewa ba sa nuna alheri a aurensu. Sai suka tsai da shawarar yin nazarin wannan halin tare. Mene ne sakamakon hakan? Mijin ya tuna: “Yin nazari game da alheri ya taimake mu mu amince da juna maimakon mu riƙa cusa wa juna laifuffuka, mu riƙa duba halaye masu kyau na juna. Mun soma kula da bukatun juna sosai. Yin alheri ya haɗa da gayyatar matata ta furta ra’ayinta ba tare da yin fushi a kan abin da ta faɗa ba. Yana nufin na daina yin girman kai. Sa’ad da muka soma nuna alheri a aurenmu, saɓani da muke samu ya fara raguwa a hankali. Ya sa mun samu wartsakewa sosai.” Shin iyalinka za su iya amfana kuwa daga yin nazarin ’yar ruhu?

Ka Nuna Bangaskiya Sa’ad da Ka Kaɗaita

13. Wane haɗari ga ruhaniyarmu ya kamata mu guje wa?

13 Kiristoci suna bukatar su ƙyale ruhun Allah ya yi musu ja-gora sa’ad da suke tare da mutane da kuma sa’ad da suka kaɗaita. Hotunan batsa da kuma mugun nishaɗi sun yaɗu sosai a duniyar Shaiɗan. Wannan zai iya ɓata dangantakarmu da Jehobah. Mene ne ya kamata Kirista ya yi? Kalmar Allah ta gargaɗe mu: “Ku kawarda dukan ƙazanta da yaɗuwar mugunta, da tawali’u kuma ku karɓi dasashiyar magana, wanda ta ke da iko ta ceci rayukanku.” (Yaƙ. 1:21) Bari mu yi la’akari da yadda bangaskiya wadda wata fanni na ’yar ruhu za ta taimake mu mu kasance da tsabta a gaban Jehobah.

14. Ta yaya rashin bangaskiya zai kai ga mugun hali?

14 Idan muna da bangaskiya na ƙwarai, za mu yi tunanin Jehobah a matsayin mutum na ƙwarai. Idan Allah bai kasance mutum na ƙwarai a gare mu ba, muna iya faɗa wa mugun hali da sauƙi. Ka yi la’akari da abin da ya faru tsakanin mutanen Allah a zamanin dā. Jehobah ya bayyana wa annabi Ezekiel cewa ana yin abin ban ƙyama a ɓoye, ya ce: “Ya ɗan mutum, ko ka ga abin da dattiɓan gidan Isra’ila su ke yi a cikin duhu? Kowane mutum a cikin ɗakin sifofinsa? Gama suna cewa, Ubangiji ba ya gan mu ba: Ubangiji ya rabu da ƙasan.” (Ezek. 8:12) Ka lura da abin da ya jawo matsalar? Ba su gaskata ba cewa Jehobah ya san abin da suke yi. Ba su ɗauki Jehobah a matsayin mutum na ƙwarai a gare su ba.

15. Ta yaya kasancewa da bangaskiya sosai ga Jehobah yake kāre mu?

15 Akasin haka, ka yi la’akari da misalin Yusufu. Ko da yake ba ya tare da iyalinsa da mutanensa, Yusufu ya ƙi ya yi zina da matar Fotifar. Me ya sa? Ya ce: “Ƙaƙa fa zan yi wannan mugunta mai-girma, in yi zunubi ga Allah kuma?” (Far. 39:7-9) Hakika, Jehobah ya kasance mutum na ƙwarai a gare shi. Idan Allah ya kasance mutum na ƙwarai a gare mu, ba za mu so mugun nishaɗi ba ko kuma mu yi kome a ɓoye da muka sani zai ɓata wa Allah rai. Za mu ƙuduri aniya kamar marubucin wannnan zabura wanda ya rera waƙa: “Cikin kamalar zuciya zan yi tafiya a cikin gidana. Ba zan sa wani mummunan al’amari a gaban idanuna ba.”—Zab. 101:2, 3.

Ka Kar̄e Zuciyarka ta Wajen Nuna Kamewa

16, 17. (a) Kamar yadda aka kwatanta a cikin littafin Misalai, ta yaya “wani saurayi marar fahimi” ya faɗa cikin zunubi? (b) Kamar yadda aka nuna a shafi na 26, ta yaya irin wannan abin zai iya faru wa mutum a yau ko da shekarunsa nawa ne?

16 Kamewa wanda fanni ne na ƙarshe na ’yar ruhu yana taimaka mana mu ƙi yin abubuwa da Allah ba ya so. Zai iya taimaka mana mu tsare zuciyarmu. (Mis. 4:23) Ka yi la’akari da yanayi da ke Misalai 7:6-23, wanda ya kwatanta yadda “wani saurayi marar-fahimi” ya faɗa wa ruɗun wata karuwa. Ya faɗa cikin tarkonta bayan ya “ratsa karabka ta kusa da saƙonta.” Wataƙila ya shiga unguwarta don son sani. Nan da nan, bai gane ba cewa ana rinjayarsa ya bi mugun tafarki da zai sa “ransa” cikin haɗari ba.

17 Ta yaya saurayin zai guji wannan mugun kuskure? Ta wajen bin wannan gargaɗin: “Kada ka ratse zuwa cikin hanyoyinta.” (Mis. 7:25) Da akwai darassi da za mu koya a nan: Idan muna son ruhun Allah ya yi mana ja-gora, muna bukatar mu guji saka kanmu cikin yanayi da zai sa mu cikin jarraba. Hanya ɗaya da mutum zai iya ratse zuwa cikin mugun tafarki na “saurayi marar fahimi” ita ce ta wurin canja zuwa tashar talabijin dabam dabam ba tare da sanin ainihin wanda muke son mu kalla ba ko kuma kallon Intane. Da saninsa ko ban da saninsa, yana iya ganin wuraren da ake lalata. A hankali yana iya koyan mummunar halin kallon hotunan batsa, da zai ɓata lamirinsa da kuma dangantakarsa da Allah. Yana iya sa ransa cikin haɗari.—Karanta Romawa 8:5-8.

18. Waɗanne matakai ne Kirista zai iya ɗauka don ya kāre zuciyarsa, kuma ta yaya yin hakan yake bukatar nuna kamewa?

18 Hakika, muna iya kame kanmu ta wajen aikatawa nan da nan idan muka ga hotuna masu ta da sha’awar lalata. Amma zai fi kyau mu guji yanayin! (Mis. 22:3) Don mu yi kāriya da ta dace kuma mu manne mata muna bukatar nuna kamewa. Alal misali, za mu kāre kanmu ta wurin saka kwamfuta a wurin da kowa zai riƙa gani. Wasu sun ga ya fi musu kyau su yi amfani da kwamfuta ko kuma su kalli talabijin a lokacin da mutane suke gida. Wasu sun ƙi samun hanyar shiga Intane. (Karanta Matta 5:27-30.) Bari mu ɗauki ko waɗanne matakai da suka dace don mu kāre kanmu da kuma iyalinmu domin mu bauta wa Jehobah da “zuciya mai-tsabta da lamiri mai-nagarta da bangaskiya mara-riya.”—1 Tim. 1:5.

19. Mene ne fa’idodin barin ruhun Allah ya yi mana ja-gora?

19 ’Yar da ruhu mai tsarki yake haifarwa tana kawo fa’idodi masu yawa. Tawali’u da tsawon jimrewa suna sa ikilisiya ta kasance da salama. Alheri da nagarta suna sa iyali ta kasance da salama. Bangaskiya da kamewa suna sa mu ci gaba da kasancewa kusa da Jehobah kuma mu zama da tsabta a gabansa. Bugu da ƙari, Galatiyawa 6:8 ya tabbatar mana: “Amma wanda ya shuka ga Ruhu, daga wurin Ruhu za ya girbe rai na har abada.” Hakika, ta wurin fansar Kristi, Jehobah zai yi amfani da ruhu mai tsarki don ya ba da rai na har abada ga waɗanda suka ƙyale ruhun ya yi masu ja-gora.

Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya tawali’u da tsawon jimrewa suke kawo salama a cikin ikilisiya?

• Mene ne zai taimaki Kirista ya nuna alheri da nagarta a cikin iyali?

• Ta yaya bangaskiya da kamewa za su taimaki Kirista ya kāre zuciyarsa?

[Hoton da ke shari na 24]

Ta yaya za ka guji sa tattaunawa ta zama na fushi?

[Hoton da ke shari na 25]

Yin nazarin ’yar ruhu zai amfane iyalinka

[Hoton da ke shari na 26]

Waɗanne haɗarurruka ne za mu guji ta wurin nuna bangaskiya da kuma kamewa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba