Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 8/1 pp. 8-12
  • Za Ka Ci Gaba Da Yin “Tafiya Bisa Ga Ruhu”?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ka Ci Gaba Da Yin “Tafiya Bisa Ga Ruhu”?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Kusa da Allah da Kuma Kristi
  • “Mu Yi Ƙaunar Junanmu”
  • “Farinciki na Ubangiji Shi ne Ƙarfinku”
  • Ku Zauna Lafiya Kuma Ku Jimre
  • Ka Yi Alheri da Kuma Nagarta
  • “Bangaskiya Mara-Riya”
  • Ka Nuna Haƙuri da Kamewa
  • Ka Ci Gaba da Bin Ruhu
  • Kana Barin Ruhun Allah Ya Yi Maka Ja-gora Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Yi Tafiya Bisa Ga Ruhu Kuma Ka Yi Rayuwar Da Ta Jitu Da Keɓe Kanka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Me Ya Sa Ruhun Allah Zai Yi Mana Ja-gora?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 8/1 pp. 8-12

Za Ka Ci Gaba Da Yin “Tafiya Bisa Ga Ruhu”?

“Ku yi tafiya bisa ga Ruhu, ba kuwa za ku biya sha’awar jiki ba.”—GALATIYAWA 5:16.

1. Ta yaya za a iya kawar da damuwar cewa an yi wa ruhu zunubi?

AKWAI wata hanyar kawar da damuwar cewa mun yi zunubi ga ruhu mai tsarki na Jehobah. Hanyar ita ce yin abin da manzo Bulus ya ce: “Ku yi tafiya bisa ga Ruhu, ba kuwa za ku biya sha’awar jiki ba.” (Galatiyawa 5:16) Sha’awoyin jiki marar kyau ba za su sha kanmu ba idan muka bari ruhun Allah ya yi mana ja-gora.—Romawa 8:2-10.

2, 3. Idan muka ci gaba da bin ruhu, ta yaya hakan zai shafe mu?

2 Yayin da muke ci gaba da “tafiya bisa ga ruhu,” ruhun Allah zai motsa mu mu yi biyayya ga Jehobah. Za mu nuna halayen Allah a hidimarmu, a ikilisiya, a gida, da kuma sauran wurare. Yadda muke bi da wanda ko wadda muka aura, yaranmu, ’yan’uwanmu masu bi, da kuma sauran mutane zai nuna cewa ruhu yana yi mana ja-gora.

3 Yin rayuwa “ga Allah cikin ruhu” na taimaka mana mu kauce wa zunubi. (1 Bitrus 4:1-6) Idan ruhu yana yi mana ja-gora, ba za mu yi zunubin da ba a gafartawa ba. Amma a waɗanne hanyoyi masu kyau ne za mu amfana idan muka ci gaba da yin tafiya bisa ga ruhu?

Ka Yi Kusa da Allah da Kuma Kristi

4, 5. Ta yaya ne yin tafiya cikin ruhu ya shafi ra’ayinmu game da Yesu?

4 Domin muna tafiya cikin ruhu, hakan ya taimaka mana mu kasance da dangantaka na kud da kud da Allah da kuma Ɗansa. Sa’ad da ya rubuta game da kyauta ta ruhaniya, Bulus ya gaya wa ’yan’uwa a Koranti: “Ina fahimtadda ku [masu bauta wa gumaka a dā], babu mutum mai-faɗin magana cikin Ruhun Allah da za shi ce, Yesu la’ananne ne; ba kuwa mai-ikon cewa, Yesu Ubangiji ne, sai cikin Ruhu Mai-tsarki.” (1 Korinthiyawa 12:1-3) Duk wani ruhun da ya motsa mutane su la’anci Yesu, ya fito ne daga Shaiɗan Iblis. Mu Kiristoci da muke tafiya bisa ga ruhu mai tsarki, mun yarda cewa Jehobah ya ta da Yesu daga matattu kuma ya ɗaukaka shi fiye da dukan halittu. (Filibbiyawa 2:5-11) Mun ba da gaskiya ga hadayar fansa ta Kristi kuma mun yarda cewa Yesu ne Ubangijin da Allah ya naɗa bisa mu mutane.

5 Wasu da suke da’awar cewa su Kiristoci ne a ƙarni na farko A.Z., sun musanta cewa Yesu ya bayyana a jiki. (2 Yohanna 7-11) Amincewa da ra’ayin ƙarya ya sa wasu su ƙi koyarwar gaskiya game da Yesu, Almasihu. (Markus 1:9-11; Yohanna 1:1, 14) Yin tafiya bisa ga ruhu na hana mu zama ’yan ridda. Idan muka kasance a faɗake a ruhaniya ne kawai za mu iya ci gaba da morar alherin Jehobah da kuma “tafiya cikin gaskiya.” (3 Yohanna 3, 4) Saboda haka, bari mu ƙudurta mu ƙi ridda domin mu kasance da dangantaka na kud da kud da Ubanmu na sama.

6. Waɗanne halaye ne waɗanda suke bin ruhu na Allah suke nunawa?

6 Bulus ya ambata ridda da ɗariku a cikin “ayyukan jiki” kamar su fasikanci da kuma lalata. Amma ya ce: “Waɗanda ke na Kristi Yesu suna giciye jiki tare da gurinsa da sha’awoyinsa. Idan muna rayuwa bisa ga Ruhu, bisa ga Ruhu kuma mu yi tafiya.” (Galatiyawa 5:19-21, 24, 25) Waɗanne halaye ne mutanen da suke rayuwa da kuma tafiya cikin ruhu suke nunawa? “Amma ɗiyan Ruhu,” Bulus ya rubuta, “ƙauna ne, farinciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, kamewa.” (Galatiyawa 5:22, 23) Bari mu tattauna waɗannan fasaloli na ɗiyan ruhu.

“Mu Yi Ƙaunar Junanmu”

7. Mecece ƙauna, kuma menene ta ƙunsa?

7 Ƙauna, ɗaya daga cikin ɗiyan ruhu, a yawancin lokaci ta ƙunshi nuna so da kuma kula da wasu, tare da dangantaka na kud da kud da su. Nassosi sun ce “Allah ƙauna ne,” domin shi ne ya fi kowa nuna wannan halin. Allah da Ɗansa sun nuna ƙaunarsu ga ’yan adam ta wajen hadayar fansa ta Yesu Kristi. (1 Yohanna 4:8; Yohanna 3:16; 15:13; Romawa 5:8) Ana sanin mu mabiyan Yesu ne ta wajen ƙaunar da muke nuna wa juna. (Yohanna 13:34, 35) Hakika, an umurce mu “mu yi ƙaunar junanmu.” (1 Yohanna 3:23) Bulus ya ce ƙauna tana da yawan haƙuri da alheri. Ba ta kishi, ba ta yin fahariya, ba ta rashin hankali, ko ta biɗar ma kanta. Ƙauna ba ta jin cakuna, ba ta yin nukura. Ba ta yin murna cikin rashin adalci, amma tana murna da gaskiya. Ƙauna tana jimre da duka abu, gaskata abu duka, tana kafa bege ga abu duka, kuma tana daurewa da duka abu. Bugu da ƙari, ƙauna ba ta ƙarewa.—1 Korinthiyawa 13:4-8.

8. Me ya sa ya kamata mu nuna ƙauna ga ’yan’uwa masu bauta wa Jehobah?

8 Idan muka yarda ruhun Allah ya bayyana ƙauna a cikinmu, wannan halin zai bayyana a dangantakarmu da Allah da kuma maƙwabtanmu. (Matta 22:37-39) Manzo Yohanna ya rubuta: “Wanda ba ya yi ƙamna ba cikin mutuwa ya ke zamne, Dukan wanda ya ƙi ɗan’uwansa mai-kisankai ne: kun sani babu mai-kisankai wanda shi ke da rai na har abada cikinsa zaune.” (1 Yohanna 3:14, 15) Mai kisan kai zai iya samun mafaka ne kawai a birnin mafaka da ke Isra’ila idan bai ƙi jinin wanda ya kashe ba. (Kubawar Shari’a 19:4, 11-13) Idan ruhu mai tsarki na yi mana ja-gora, za mu nuna ƙauna ga Allah, ’yan’uwanmu Kiristoci, da kuma sauran mutane.

“Farinciki na Ubangiji Shi ne Ƙarfinku”

9, 10. Menene farin ciki, kuma waɗanne dalilai ne muke da su na yin farin ciki?

9 Farin ciki na sa mutum ya ji daɗi sosai. Jehobah “Allah mai farin ciki” ne. (1 Timothawus 1:11 NW; Zabura 104:31) Ɗan yana son yin nufin Ubansa. (Zabura 40:8; Ibraniyawa 10:7-9) Kuma ‘farinciki na Jehobah shi ne ƙarfinmu.’—Nehemiah 8:10.

10 Farin cikin da muke samu daga Allah yana ba mu cikakken gamsuwa sa’ad da muka yi nufin Allah har ma a lokaci mai wuya, a lokacin baƙin ciki, ko tsanantawa. “Sanin Allah” na kawo mana farin ciki! (Misalai 2:1-5) Dangantakarmu mai kyau da Allah ta dangana ne a kan cikakken saninsa, bangaskiyarmu a gare shi da kuma hadayar fansa ta Yesu. (1 Yohanna 2:1, 2) Wani abin farin ciki kuma shi ne kasancewa sashen ’yan’uwantaka na gaskiya na dukan duniya. (Zephaniah 3:9; Haggai 2:7) Begenmu na Mulki da kuma gata mai girma na yin wa’azin bishara na sa mu farin ciki. (Matta 6:9, 10; 24:14) Haka ma begen samun rai na dindindin. (Yohanna 17:3) Tun da yake muna da waɗannan bege masu ban al’ajabi, dole ne mu “cika da murna sarai.”—Kubawar Shari’a 16:15.

Ku Zauna Lafiya Kuma Ku Jimre

11, 12. (a) Mecece ma’anar salama? (b) Ta yaya ne salamar Allah take shafanmu?

11 Salama, wata sashe ce ta ɗiyar ruhu, kuma tana nufin zaman lafiya da lumana ba tare da damuwa ba. Ubanmu na sama shi ne Allahn salama, kuma an ba mu tabbaci cewa: “Ubangiji za ya albarkaci mutanensa da salama.” (Zabura 29:11; 1 Korinthiyawa 14:33) Yesu ya gaya wa almajiransa: “Salama ina bar maku; salamata ni ke ba ku.” (Yohanna 14:27) Ta yaya hakan zai taimaka wa mabiyansa?

12 Salamar da Yesu ya ba almajiransa ta ba su kwanciyar hankali kuma ta kawar da tsoronsu. Sun sami salama sa’ad da suka sami ruhu mai tsarki da aka yi masu alkawarinsa. (Yohanna 14:26) A ƙarƙashin ja-gorar ruhu da kuma addu’o’inmu da ake amsawa a yau, muna more “salama kuwa ta Allah” wadda babu kamarta, kuma hakan na ba mu kwanciyar hankali. (Filibbiyawa 4:6, 7) Bugu da ƙari, ruhun Jehobah na taimaka mana mu yi haƙuri da ’yan’uwanmu masu bi da kuma sauran mutane.—Romawa 12:18; 1 Tassalunikawa 5:13.

13, 14. Menene tsawon jimiri, kuma me ya sa ya kamata mu nuna shi?

13 Tsawon jimiri yana da dangantaka da haƙuri, domin haƙurinmu ne ke sa mu jimre sa’ad da wani ya ba mu haushi ko kuwa ya yi mana laifi, domin muna tunanin cewa yanayin zai gyaru. Allah yana da tsawon jimiri. (Romawa 9:22-24) Yesu ya nuna irin wannan halin. Mu ma muna iya amfana daga wannan halin da Yesu ya nuna, domin Bulus ya rubuta: “Na sami jinƙai dalilin wannan, domin ta wurina, ni da ke babba, Yesu Kristi shi bayana tsawon haƙurinsa duka, domin gurbi ga waɗannan da za su bada gaskiya gareshi gaban nan zuwa rai na har abada.”—1 Timothawus 1:16.

14 Tsawon jimiri na taimaka mana mu jimre sa’ad da mutane suka gaya mana maganar banza ko kuwa suka yi abin da bai dace ba. Bulus ya aririci ’yan’uwa Kiristoci: “Ku yi haƙuri da kowa.” (1 Tassalunikawa 5:14) Tun da yake dukanmu ajizai ne kuma muna yin kurakurai, babu shakka, muna son mutane su yi haƙuri da mu, kuma su nuna tsawon jimiri sa’ad da muka yi masu laifi. Bari mu ƙudurta nuna “jimrewa tare da farinciki.”—Kolossiyawa 1:9-12.

Ka Yi Alheri da Kuma Nagarta

15. Ka ba da ma’anar alheri, kuma ka ba da misalansa.

15 Muna yin alheri sa’ad da muka nuna cewa mun damu da mutane ta wajen kalamai da ayyuka. Jehobah da Ɗansa suna yin alheri. (Romawa 2:4; 2 Korinthiyawa 10:1) Duka bayin Allah da Kristi, suna bukatar su yi alheri. (Mikah 6:8; Kolossiyawa 3:12) Har ma waɗanda ba su da dangantaka da Allah sun nuna “alheri irin da ba a kan saba yi ba.” (Ayukan Manzanni 27:3; 28:2) Babu shakka, za mu iya nuna alheri idan muka ci gaba da yin “tafiya bisa ga Ruhu.”

16. Waɗanne yanayi ne ya kamata su motsa mu mu nuna alheri?

16 Muna iya nuna alheri ko da muna da dalilin yin fushi domin maganar banza da wani ya yi ko kuwa halaye marar kyau. “Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi,” in ji Bulus. “Kada rana ta faɗi kuna kan fushinku: kada kuwa ku ba Shaiɗan dama. Ku kasance da nasiha zuwa ga junanku, masu-tabshin zuciya, kuna yi ma junanku gafara, kamar yadda Allah kuma cikin Kristi ya gafarta maku.” (Afisawa 4:26, 27, 32) Ya fi dacewa a nuna alheri ga waɗanda suke fuskantar gwaji. Babu shakka, Kirista dattijo bai yi alheri ba idan ya ƙi ba da shawarar Nassi don ya guje wa fushin wani wanda yake cikin haɗarin kauce wa tafarkin “nagarta da adalci da gaskiya.”—Afisawa 5:9.

17, 18. Mecece ma’anar nagarta, kuma ta yaya ne ya kamata wannan halin ya shafi rayuwarmu?

17 Nagarta hali ne mai kyau. Allah ya fi kowa yin nagarta. (Zabura 25:8; Zechariah 9:17) Yesu yana da halaye masu kyau. Duk da haka, bai yarda da laƙabin nan “Managarci” ba sa’ad da aka kira shi “Malam managarci.” (Markus 10:17, 18) Hakan ya faru ne domin ya fahimci cewa Allah ne ya fi kowa nuna nagarta.

18 Ajizancin da muka gada na hana mu nuna nagarta. (Romawa 5:12) Duk da haka, za mu iya nuna wannan halin idan muka yi addu’a ga Allah ya ‘koya mana nagarta.’ (Zabura 119:66) Bulus ya gaya wa ’yan’uwa masu bi a ƙasar Roma: “Ni kuwa da kaina na tabbata a kanku, yan-uwa, ku da kanku cike da nagarta ku ke, cikakku ne da dukan ilimi.” (Romawa 15:14) Dole ne Kirista mai kula ya kasance “mai-son nagarta.” (Titus 1:7, 8) Idan ruhun Allah yana yi mana ja-gora, za a san mu da nagarta, kuma Jehobah zai ‘tuna da mu domin alheri da muka yi.’—Nehemiah 5:19; 13:31.

“Bangaskiya Mara-Riya”

19. Ka ba da ma’anar bangaskiya, kamar yadda take a Ibraniyawa 11:1.

19 Bangaskiya, wata sashe ce ta ɗiyar ruhu, ainihin “abin da mu ke begensa ne, tabbatawar al’amuran da ba a gani ba.” (Ibraniyawa 11:1) Idan muna da bangaskiya, za mu kasance da tabbacin cewa Jehobah zai cika dukan alkawarinsa. Tabbacin abin da ba a gani ba yana da ƙarfi sosai da har ya sa aka ce bangaskiya ta yi daidai da tabbacin. Alal misali, abubuwan da aka halitta sun tabbatar da mu cewa akwai Mahalicci. Wannan ita ce irin bangaskiyar da za mu nuna idan muka ci gaba da tafiya cikin ruhu.

20. Menene “zunubin da ke manne mamu,” kuma ta yaya za mu iya guje masa da kuma ayyukan jiki?

20 Rashin bangaskiya shi ne “zunubin da ke manne mamu.” (Ibraniyawa 12:1) Muna bukatar mu dangana da ruhun Allah domin mu kauce wa ayyuka na jiki, neman abin duniya, da kuma koyarwar ƙarya da za ta lalata bangaskiyarmu. (Kolossiyawa 2:8; 1 Timothawus 6:9, 10; 2 Timothawus 4:3-5) Ruhun Allah yana ba bayin Jehobah na zamani bangaskiya irin ta shaidu na kafin zamanin Kiristoci da kuma sauran da suke cikin Littafi Mai Tsarki. (Ibraniyawa 11:2-40) Kuma ‘bangaskiyarmu mara-riya’ za ta iya ƙarfafa bangaskiyar wasu.—1 Timothawus 1:5; Ibraniyawa 13:7.

Ka Nuna Haƙuri da Kamewa

21, 22. Menene ma’anar haƙuri, kuma me ya sa muke bukatar mu nuna shi?

21 Haƙuri na nufin guje wa yawan yin fushi. Ɗaya daga cikin halayen Allah shi ne haƙuri. Mun san haka, domin Yesu wanda mutum ne mai haƙuri, ya nuna halin Jehobah sarai. (Matta 11:28-30; Yohanna 1:18; 5:19) Saboda haka, menene ake bukata daga wurin mu bayin Allah?

22 Mu Kiristoci, muna bukatar mu ‘nuna iyakacin haƙuri ga dukan mutane.’ (Titus 3:2) Muna nuna haƙuri a hidimarmu. An shawarci waɗanda suka cancanta a ruhaniya su daidaita Kiristan da ya yi zunubi “cikin ruhun tawali’u.” (Galatiyawa 6:1) Mu duka muna iya ɗaukaka haɗin kai da salama na Kirista ta wajen nuna “tawali’u da ladabi.” (Afisawa 4:1-3) Muna iya yin haƙuri idan muka ci gaba da bin ruhu kuma muna nuna kamewa.

23, 24. Menene kamewa, kuma ta yaya yake taimaka mana?

23 Kamewa na sa mu guje wa tunani, furci, da ayyuka marar kyau. Jehobah ya ci gaba da nuna ‘dauriya’ wajen bi da Babiloniyawan da suka hallakar da Urushalima. (Ishaya 42:14) Ɗansa ya ‘bar mana gurbin’ da za mu bi ta wajen jimrewa a lokacin da yake wahala. Kuma manzo Bitrus ya shawarci ’yan’uwa Kiristoci su ƙara wa iliminsu “kamewa.”—1 Bitrus 2:21-23; 2 Bitrus 1:5-8.

24 An bukaci dattawa Kiristoci su kasance masu kamewa. (Titus 1:7, 8) Babu shakka, duka waɗanda ruhu mai tsarki yake yi wa ja-gora suna iya nuna kamewa kuma za su iya guje wa lalata, maganar banza, ko kuwa duk wani abu da zai iya kawo rashin amincewar Jehobah. Idan muka yarda ruhun Allah ya yi mana ja-gora wajen nuna kamewa, mutane za su lura da haka ta wajen furcinmu da halinmu mai kyau.

Ka Ci Gaba da Bin Ruhu

25, 26. Ta yaya ne yin tafiya cikin ruhu zai shafi dangantakarmu ta yanzu da kuma begenmu na gaba?

25 Idan muka ci gaba da bin ruhu, za mu zama masu shelar Mulki da ƙwazo. (Ayukan Manzanni 18:24-26) Za mu zama abokan kirki, musamman ’yan’uwanmu Kiristoci za su yi tarayya da mu. A matsayin mutanen da ruhu mai tsarki ke yi wa ja-gora, za mu ba da ƙarfafa ta ruhaniya ga ’yan’uwanmu masu bauta wa Jehobah. (Filibbiyawa 2:1-4) Ba abin da duka Kiristoci suke son su zama ba ke nan?

26 A wannan duniyar da take ƙarƙashin ja-gorar Shaiɗan, ba shi da sauƙi a yi tafiya bisa ga ruhu. (1 Yohanna 5:19) Duk da haka, miliyoyi suna yin haka a yau. Idan muka dogara ga Jehobah da dukan zuciyarmu, za mu more rayuwa yanzu kuma za mu ci gaba da bin hanyar aminci na Mai Tanadin ruhu mai tsarki har abada.—Zabura 128:1; Misalai 3:5, 6.

Mecece Amsarka?

• Ta yaya ne yin “tafiya bisa ga ruhu” yake shafar dangantakarmu da Allah da kuma Ɗansa?

• Ɗiyar ruhu ta ƙunshi waɗanne halaye?

• Ta waɗanne hanyoyi ne za a iya nuna ɗiyar ruhun Allah?

• Ta yaya ne yin tafiya bisa ga ruhu yake shafar rayuwarmu ta yanzu da ta gaba?

[Hoto a shafi na 10]

Ruhu mai tsarki na Jehobah yana ɗaukaka ƙauna a tsakanin ’yan’uwanmu masu bi

[Hoto a shafi na 11]

Ka nuna alheri ta wajen kalamai da ayyuka masu kyau

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba