Ka Ci Gaba da ‘Mai da Hankali ga Koyarwa’
“KUNA ce da ni Malami, da Ubangiji: kuna faɗi daidai kuma; gama haka na ke.” (Yoh. 13:13) Da ya faɗi waɗannan kalaman ga almajiransa, Yesu ya nanata hakkinsa a matsayin malami. Sa’annan, kafin ya koma sama Yesu ya ba mabiyansa wannan umurnin: ‘Ku tafi fa, ku almajirtarda dukan al’ummai, . . . kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.’ (Mat. 28:19, 20) Daga baya, manzo Bulus ya kuma nanata muhimmancin zama masu koyar da Kalmar Allah. Ya gargaɗi Timotawus dattijo Kirista: “Ka maida hankali ga karatu, da gargaɗi, da koyarwa . . . Ka yi ƙwazo cikin waɗannan al’amura; ka bada kanka gare su sosai; domin cingabanka ya bayanu ga kowa.”—1 Tim. 4:13-15.
Kamar a wancan lokacin, a yau, koyarwa sashe ne na musamman na hidimarmu ta fage da kuma taronmu na Kirista. Ta yaya za mu ci gaba da ba da kanmu ga koyarwa, kuma a waɗanne hanyoyi ne hakan zai taimaka mana mu samu ci gaba, a matsayin masu koyar da Kalmar Allah?
Ka Yi Koyi da Babban Malami
Masu sauraronsa da yawa suna son yadda Yesu yake koyarwa. Ka lura da yadda kalamansa suka shafi waɗanda suka halarci taro a majami’a a Nazarat. Marubucin linjila Luka ya rubuta: “Dukansu suka shaida shi, suna mamaki da zantattukan alheri da suka fito bakinsa.” (Luk 4:22) Almajiran Yesu sun bi misalin Ubangijinsu a wa’azinsu. Hakika, manzo Bulus ya ƙarfafa ’yan’uwansa Kiristoci: “Ku zama masu-koyi da ni, kamar yadda ni kuma na Kristi ne.” (1 Kor. 11:1) Domin ya yi koyi da yadda Yesu yake koyarwa, Bulus ya zama mai koyarwa da kyau ‘a sarari da kuma gida gida.’—A. M. 20:20.
Koyarwa “a Cikin Kasuwa”
Fitaccen misalin da ya nuna cewa Bulus ya iya koyarwa a fili yana cikin Ayyukan Manzanni sura ta 17. A wajen mun karanta game da ziyararsa zuwa Atina, Hellas. Duk inda Bulus ya duba a birnin, a kan tituna, a cikin wuraren da ake samun mutane sai ya ga gumaka. Shi ya sa Bulus ya damu ƙwarai. Duk da haka, ya kame kansa. Sai ya fara “muhawara a cikin majami’a . . . a cikin kasuwa kuma kowace rana tare da waɗanda suka gamu da shi.” (A. M. 17:16, 17) Wannan misali ne mai kyau a gare mu! Ta wajen tattaunawa da dukan mutane, ban da sūka, amma da daraja, za mu iya buɗe wa wasu hanya su saurare mu kuma daga baya su samu ’yanci daga bautar addini ta ƙarya.—A. M. 10:34, 35; R. Yoh. 18:4.
Mutane da yawa da Bulus ya yi wa wa’azi a cikin kasuwar Atina sun ƙi saƙonsa. A cikin waɗanda suka saurare shi da akwai ’yan ussan ilimi waɗanda ra’ayinsu bai jitu da koyarwar da yake wa’azinsa ba. Sa’ad da masu sauraron Bulus suka soma yin gardama, ya yi la’akari da furcinsu. Wasu sun kira shi ‘mai-surutu’ (wanda a zahiri yana nufin “mai tsintar iri”). Wasu sun ce: “Yana da alama shi mai-bayanawar baƙin allohi ne.”—A. M. 17:18.
Amma, Bulus bai yi sanyin gwiwa don baƙar maganar da masu sauraronsa suka yi ba. Akasin haka, sa’ad da aka gaya masa ya bayyana koyarwarsa, Bulus ya yi amfani da wannan zarafin ya ba da jawabi mai kyau da ya nuna cewa ya iya koyarwa. (A. M. 17:19-22; 1 Bit. 3:15) Bari mu bincika jawabinsa dalla-dalla kuma mu koyi darussa da za su taimaka mana mu kyautata koyarwarmu.
Ka Tattauna Batutuwan da Masu Sauraronka Za Su So
Bulus ya ce: “Ku mutanen Atina, na gane a kowace fuska ku masu-kiyaye addini ne. Gama sa’ad . . . ina lura da abubuwan da kuke yi wa sujada, sai na iske kuma wani bagadi da wannan rubutu a kansa, ‘Ga Allahn Da Ba A San Shi Ba.’ Wannan fa da kuke yi masa sujada cikin rashin sani, shi ni ke bayyana muku.”—A. M. 17:22, 23.
Bulus ya lura da dukan abubuwan da suka kewaye shi. Daga abin da ya gani, ya koyi abubuwa da yawa game da waɗanda yake tattaunawa da su. Mu ma za mu iya koyan wani abu game da maigida idan muka zama masu lura. Alal misali, kayan wasa a wani gida ko kuma alamu a kan ƙofa za su taimaka mana mu san abubuwa da yawa. Idan muka ɗan fahimci yanayin maigidan, za mu mai da hankali mu zaɓi abin da za mu faɗa da kuma yadda za mu faɗe shi.—Kol. 4:6.
Bulus bai sūki mutane da saƙonsa ba. Amma, ya ga cewa ‘sujadar’ mutanen Atina ba daidai ba ne. Bulus ya nuna sarai yadda za su iya miƙa bautarsu ga Allah na gaskiya. (1 Kor. 14:8) Yana da muhimmanci mu yi magana a hanyar da mutane za su ji mu sosai ba tare da yin sūka ba sa’ad da muke shelar bisharar Mulki!
Ka Kasance da Basira Kuma Kada Ka Yi Son Kai
Bulus ya ci gaba da cewa: “Allah wanda ya yi duniya da abin da ke ciki duka, da ya ke Ubangijin sama da ƙasa ne, ba shi kan zauna a cikin haikalu waɗanda a ke yi da hannuwa ba; ba kuwa da hannuwan mutane a ke yi masa hidima ba, sai ka ce yana da bukatar wani abu, da ya ke shi da kansa yana ba kowa rai, da numfashi, da abu duka.”—A. M. 17:24, 25.
A nan Bulus ya jawo hankali ga Jehobah a matsayin Mai ba mu Rai, ya yi hakan da hikima ta wajen kiransa “Ubangijin sama da ƙasa.” Gata ne mu taimaka wa mutane masu zuciyar kirki daga addinai da al’adu dabam-dabam su fahimci cewa Jehobah Allah ne tushen dukan rai!—Zab. 36:9.
Bayan hakan, Bulus ya ce: “Daga tushe ɗaya kuwa ya yi dukan al’umman mutane . . . yana sanya masu wokatai waɗanda ya ayana, da iyakan mazauninsu: domin su nemi Allah, ko halama su a lallaba su same shi, ko da ya ke ba shi da nisa da kowane ɗayanmu ba.”—A. M. 17:26, 27.
Yadda muke koyarwa zai nuna wa mutane irin Allahn da muke bauta ma wa. Ban da yin wariya, Jehobah yana ƙyale mutane na dukan al’ummai “su nemi Allah, ko halama su a lallaba su same shi.” Haka nan ma, muna magana da dukan mutanen da muka sadu da su babu son kai. Muna ƙoƙarin taimaka wa mutanen da suka gaskata da Mahalicci su kusace shi, kuma hakan zai iya kai su ga samun albarka na har abada. (Yaƙ. 4:8) Amma yaya za mu taimaka wa waɗanda suke shakkar wanzuwar Allah? Za mu bi misalin Bulus. Ka lura da abin da ya ce kuma.
“Cikinsa mu ke rayuwa, mu ke motsi, mu ke zamanmu; kamar yadda waɗansu daga cikin mawaƙanku da kansu suka ce, Gama mu kuma zuriyarsa ne. Da ya ke fa mu zuriyar Allah ne, bai kamata mu zaci Allantaka tana kama da zinariya, ko azurfa, ko dutse.”—A. M. 17:28, 29.
Domin masu sauraronsa su saurare shi kuma su amince da abin da ya ce, Bulus ya yi ƙaulin mawaƙa waɗanda mutanen Atina suka sani kuma suka amince da su. Ya kamata mu ma mu faɗi abin da muka san cewa masu sauraronmu za su amince da shi. Alal misali, kwatancin da Bulus ya yi amfani da shi a wasiƙarsa zuwa ga Ibraniyawa ya dace a yau: “Kowane gida akwai mai-kafa shi; amma wanda ya kafa dukan abu Allah ne.” (Ibran. 3:4) Sa masu sauraronmu su yi tunani a kan wannan kwatanci mai sauƙi zai iya taimaka musu su amince da abin da muke faɗa. Ka lura cewa Bulus yana motsa mutane a jawabinsa, wannan wata alama ce na koyarwa da kyau.
Ka Nanata Gaggawar
Bulus ya ce: “Kwanakin jahilci fa Allah ya yi birin da su; amma yanzu yana umurtan mutane dukansu cikin kowane wuri su tuba: da ya ke ya sanya rana, inda zai yi wa duniya duka shari’a mai-adalci ta wurin mutum wanda ya ƙadara.”—A. M. 17:30, 31.
Ƙyale muguntar da Allah ya yi na ɗan lokaci ya ba dukanmu zarafin nuna masa ainihin abin da ke cikin zuciyarmu. Yana da muhimmanci mu nanata gaggawar lokacin da muke ciki kuma mu yi magana da tabbaci game da albarkar sarautar Mulki, da ya yi kusa sosai.—2 Tim. 3:1-5.
Yadda Mutane ke Ɗaukan Abu Ya Bambanta
“Sa’ad da suka ji zancen tashin matattu, waɗansu suka yi ba’a: amma waɗansu suka ce, mu sake jinka tukuna a kan wannan zance. Haka nan fa Bulus ya fita daga cikinsu. Amma waɗansu mutane suka manne masa, suka bada gaskiya.”—A. M. 17:32-34.
Wasu suna yin na’am da wa’azinmu nan da nan; wasu kuma za su bukaci ƙarin lokaci don su tabbata da koyarwarmu. Amma sa’ad da bayani mai sauƙi da muka yi ya taimaka wa mutum guda ya samu cikakken sani na Jehobah, muna yin godiya sosai cewa Allah ya yi amfani da mu ya jawo mutane ga Ɗansa!—Yoh. 6:44.
Darussa da Za Mu Iya Koya
Yayin da muke tunani a kan jawabin Bulus, muna iya koyan abubuwa da yawa game da yadda za mu bayyana wa mutane gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Idan muna da gatan ba da jawabai a cikin ikilisiya, muna iya yin ƙoƙari mu yi koyi da Bulus ta wajen yin amfani da kalamai cikin hikima da za su taimaka wa marar bi ya fahimci kuma ya amince da koyarwar Littafi Mai Tsarki. Ya kamata mu bayyana irin wannan koyarwa sosai, amma mu mai da hankali don kada mu yi baƙar magana game da imanin marar bi da ya halarci taron. Hakazalika, a aikinmu na wa’azi, za mu yi ƙoƙari mu nuna rinjaya da basira. Ta wajen yin hakan, muna bin shawarar Bulus na ‘mai da hankali ga koyarwa.’
[Hoton da ke shafi na 30]
Koyarwar Bulus tana da sauƙi, ta fita sarai kuma ya yi ta da basira
[Hoton da ke shafi na 31]
Muna yin koyi da Bulus ta wajen yin la’akari da yadda waɗanda muke yi wa wa’azi suke ji