Ka Kusaci Allah
Ki “Ɗauki Ɗanki”
2 SARAKUNA 4:8-37
MUTUWAR ɗa yana cikin hasara mafi ban ciwo da ’yan Adam za su iya fuskanta. Jehobah Allah yana da ikon kawar da irin wannan rashin. Mun san cewa wannan gaskiya ne domin ya ba maza kalilan a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki ƙarfi su ta da matattu. Misali ɗaya, da ke rubuce a 2 Sarakuna 4:8-37, shi ne na wani yaro da annabi Elisha ya ta da daga matattu.
Labarin ya faru ne a birnin Shunem. Wata bakarariya da kuma mijinta sun yi wa Elisha abin kirki, sun ba shi abinci da wurin kwana a kai a kai. Wata rana, annabin mai godiya ya ce wa matan: ‘Baɗi war haka, za ki rungumi ɗa.’ An kai ranar da take tsammani cewa ba zai taɓa zuwa ba, kuma kamar yadda Elisha ya faɗa, ta rungumi ɗanta. Abin baƙin ciki, farin cikin da take yi bai daɗe ba. ’Yan shekaru bayan lokacin, yaron ya yi ciwon kai mai tsanani sa’ad da yake gona sai aka komar da shi gida, inda ya mutu a ‘guwawun mamarsa.’ (Ayoyi ta 16, 19, 20) Matar mai baƙin ciki ta ɗauki gawar sai ta ɗaura shi a kan gadon da annabin ya saba kwana a kai.
Ba tare da ɓata lokaci ba kuma da amincewar mai gidanta, ta yi tafiyar mil ashirin zuwa Tudun Karmel don ta ga Elisha. Sa’ad da ta sadu da shi, ba ta yi kuka ba kuma ba ta nuna baƙin ciki ba. Shin ta ƙi yin kuka ne don ta samu labari cewa Iliya, magajin Elisha, ya ta da ɗan gwauruwa daga mutuwa ne? (1 Sarakuna 17:17-23) Shin wannan Ba-shunammiyar tana da imani cewa Elisha zai iya ta da ɗanta ma? Ko yaya ya faru, ta ƙi ta koma gida sai Elisha ya yarda ya je tare da ita.
Sa’ad da suka koma Shunem, Elisha kaɗai ya shiga cikin ɗakin da ya sani sosai sai ya ga gawar “bisa gadonsa.” (Aya ta 32) Annabin ya yi addu’a ga Jehobah sosai da kalaman da za a iya kwatanta kamar roƙo mai zurfi. Sai Elisha ya miƙe a kan yaron, sannan “naman yaron ya yi ɗumi.” Yaron ya soma numfashi kuma! Elisha ya kira mamar yaron kuma ya furta kalaman da za su mai da baƙin cikinta zuwa farin ciki sosai: Ki “ɗauki ɗanki.”—Ayoyi ta 34, 36.
Labarin tayar da ɗan Ba-shunammiyar daga matattu abin bege da ƙarfafa ne sosai. Jehobah ya fahimci baƙin cikin iyayen da ɗansu ya mutu. Ƙari ga hakan, yana ɗokin ya cire wannan matsalar. (Ayuba 14:14, 15) Ta da matattu da Jehobah zai yi a sabuwar duniyarsa da ke zuwa zai fi wanda Elisha ya yi da kuma waɗansu da aka yi a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki girma.a
Alkawarin Littafi Mai Tsarki game da tashin matattu bai kawar da baƙin cikin da muke ji ba sa’ad da wanda muke ƙauna ya mutu. Wani Kirista mai aminci wanda ɗansa tilo ya mutu ya ce: “Ba zan taɓa daina baƙin ciki gabaki ɗaya ba sai lokacin da zan sake riƙe ɗana kuma.” Ka yi tunani game da gatar sake kasancewa tare da waɗanda kake ƙauna da suka mutu. Yin tunani cewa za ka sake iya riƙe su kuma zai iya sa ka samu ƙarfin jimre wa baƙin cikinka. Shin kana son ka daɗa koyo game da Allahn da ke ba mu wannan bege mai tamani kuwa?
[Hasiya]
a Don ƙarin bayani game da alkawarin Littafi Mai Tsarki game da tashin matattu, ka duba babi na 7 na littafi nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.