Elisha Ya Ga Karusai na Wuta—Kai Kuma Fa?
Sarkin Suriya yana neman ya kama Elisha annabin Allah. Sai ya ji cewa Elisha yana Dothan, birni mai garu da ke kan tudu. Sarkin ya tura rundunarsa da dawakai da kuma karusan yaƙi zuwa Dothan. Kuma sa’ad da gari ya waye, rundunarsa sun riga sun kewaye birnin.—2 Sar. 6:13, 14.
Sa’ad da bawan Elisha ya fita waje kuma ya ga rundunan, sai tsoro ya kama shi. Sai ya yi ihu, ya ce: “Kaito ubanɗakina! yaya za mu yi?” Elisha ya ce masa: “Kada ka ji tsoro: gama waɗanda ke tare da mu sun fi waɗanda ke tare da su yawa.” Sai annabin ya yi addu’a, ya ce: “Ya Ubangiji, ina roƙonka, ka buɗe idanunsa domin ya gani.” Mene ne ya faru? “Ubangiji kuwa ya buɗe idanun saurayin; ya gani; ga shi kuwa, dutsen yana cike da dawakai, da karusai na wuta kewaye da Elisha.” (2 Sar. 6:15-17) Mene ne za mu iya koya daga wannan labarin da kuma wasu abubuwa da suka faru a rayuwar Elisha?
Elisha bai yi rawan jiki ba ko da yake rundunar Suriya sun kewaye birnin da yake ciki. Ya dogara ga Jehobah kuma ya ga yadda yake kāre shi. Bai kamata mu yi zato cewa za a yi mana mu’ujizoji a yau ba, amma a bayane yake cewa Jehobah yana kāre mutanensa a matsayin rukuni. A wani azancin kuma, dawakai da karusan wuta suna kāre mu. Idan muna da bangaskiya cewa Jehobah yana kāre mutanensa kuma muka dogara a gare shi a koyaushe, za mu kasance da kwanciyar rai kuma zai albarkace mu. (Zab. 4:8) Bari mu tattauna yadda za mu amfana daga wasu abubuwa da suka faru a rayuwar Elisha.
ELISHA YA SOMA YI WA ILIYA HIDIMA
Wata rana da Elisha yake huɗa a gona, sai annabi Iliya ya zo ya same shi kuma ya saka masa tufafinsa. Elisha ya san abin da Iliya yake nufi. Sai ya koma gida, ya yi biki, ya yi wa iyayensa ban kwana kuma ya tafi don ya yi wa Iliya hidima. (1 Sar. 19:16, 19-21) Da yake Elisha yana shirye ya yi duk abin da Jehobah ya ce ya yi, hakan ya sa Jehobah ya yi amfani da shi a hanyoyi da yawa kuma daga baya ya ɗauki matsayin annabi Iliya.
Wataƙila Elisha ya yi wa Iliya hidima na tsawon shekara shida. A wannan lokacin, Elisha ne yake “zuba ruwa a hannuwan Iliya.” (2 Sar. 3:11) A zamaninsu, mutane suna cin abinci da hannunsu, ba da cokula ba. Idan maigida ya gama cin abinci, bawa ne yake zuba masa ruwa don ya wanke hannayensa. Hakan ya nuna cewa Elisha yana wasu ayyuka da mutane ba sa ɗauka da muhimmanci. Duk da haka, gata ne a gare shi ya zama bawan Iliya.
Hakazalika, Kiristoci da yawa a yau suna saka hannu a fannoni dabam-dabam na hidima ta cikakken lokaci. Me ya sa? Domin suna da bangaskiya ga Jehobah kuma suna so su bauta masa da dukan ƙarfinsu. Alal misali, wasu suna barin gida don su yi hidima a Bethel ko kuma su yi gine-ginen wuraren bauta. Suna iya yin ayyuka da mutane da yawa suke ɗaukan ba su da muhimmanci. Amma, bai kamata mu yi hakan ba domin Jehobah yana daraja dukan ayyukan da bayinsa suke yi.—Ibran. 6:10.
ELISHA YA YI HIDIMARSA DA AMINCI
Allah ya gaya wa Iliya ya bar Gilgal ya tafi Bethel, kafin ya “kai shi sama cikin guguwa.” Iliya ya gaya wa Elisha kada ya bi shi, amma Elisha ya ce: “Ba ni barinka.” Sa’ad da suke cikin tafiya, Iliya ya ƙara gaya masa sau biyu ya koma, amma Elisha ya ƙi. (2 Sar. 2:1-6) Ya nace ya bi Iliya kamar yadda Ruth ta yi wa Naomi. (Ruth 1:8, 16, 17) Me ya sa? Yana ganin gata ne ya yi wa Iliya hidima domin aiki ne da Allah ya ce ya yi.
Elisha ya kafa mana misali mai kyau. Za mu daraja kowane aiki da aka ce mu yi a ƙungiyar Allah, idan muka tuna cewa muna bauta wa Jehobah. Babu ɗaukaka da ta fi wannan.—Zab. 65:4; 84:10.
“KA YI ROƘON ABIN DA ZAN YI MAKA”
Sa’ad da suke tafiya, sai Iliya ya gaya wa Elisha: “Ka yi roƙon abin da zan yi maka kafin in rabu da kai.” Kamar yadda Sulemanu ya ce a ba shi abin da zai taimaka masa ya bauta wa Jehobah da kyau, Elisha ya ce Iliya ya ‘bar rabo na ɗan fari na ruhunsa shi kasance a wurinsa.’ (1 Sar. 3:5, 9; 2 Sar. 2:9) Ba’isra’ile ɗan fari ne yake samun kashi biyu na gādo. (K. Sha 21:15-17) Hakan ya nuna cewa Elisha yana son ya gaji Iliya a matsayin annabi. Bugu da ƙari, Elisha yana son ya kasance da gaba gaɗi kamar Iliya wanda ya “yi kishi ƙwarai domin Ubangiji.”—1 Sar. 19:13, 14.
Mene ne Iliya ya ce game da roƙon da bawansa ya yi? Annabin ya ce: “Ka roƙi abu mai-wuya; amma duk da haka, idan ka gan ni sa’anda an fyauce ni daga wurinka, za ya zama maka; amma idan ba haka ba ba za ya zama ba.” (2 Sar. 2:10) Amsar da Iliya ya ba da yana nufin abubuwa biyu. Na farko, Allah ne zai iya tsai da ko Elisha zai sami abin da ya roƙa. Na biyu, idan Elisha yana son ya sami abin da ya roƙa, wajibi ne ya kasance tare da Iliya ko da mene ne zai faru.
MENE NE ELISHA YA GANI?
Shin Allah ya ba Elisha abin da ya roƙa kuwa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya zama fa, sa’anda suna cikin tafiya, suna zance, sai ga karusa ta wuta, da dawakan wuta, wadanda suka raba su da juna; Iliya kuwa ya hau cikin guguwa zuwa sama. Elisha ya gani.”a Ta hakan ne Jehobah ya amsa roƙon Elisha. Ya ga sa’ad da aka ɗauke Iliya, sai ya sami kashi biyu na ruhunsa kuma ya ɗauki matsayin annabin Allah.—2 Sar. 2:11-14.
Elisha ya saka tufafin da ya faɗi daga wurin Iliya. Sa’ad da mutane suka ga cewa Elisha ya saka tufafin Iliya, sai suka san cewa yanzu shi annabin Allah ne. Bayan haka, ya nuna cewa shi annabin Allah ne ta wajen raba ruwan Kogin Urdun.
Babu shakka, abin da Elisha ya gani sa’ad da aka ɗauke Iliya cikin guguwa ya ƙarfafa shi. Ba wanda ba zai yi mamakin ganin karusan yaƙi da kuma dawakan wuta ba. Waɗannan abubuwan sun nuna cewa Jehobah ya ba Elisha abin da ya roƙa. Sa’ad da Allah ya amsa addu’o’inmu, ba ma ganin wahayi na dawakai da karusan wuta, amma muna ganin tabbaci cewa Allah yana yin amfani da ikonsa don ya taimaka mana kuma ya ga an cika nufinsa. Kuma sa’ad da muka ga cewa Jehobah yana yi wa sashen ƙungiyarsa da ke duniya albarka, kamar muna ganin karusar Jehobah na samaniya na tafiya gaba-gaba.—Ezek. 10:9-13.
Elisha ya ga abubuwa da yawa da suka tabbatar masa cewa Jehobah yana da iko sosai. Ruhu mai tsarki ya taimaka wa annabin ya yi mu’ujizai 16. Wannan ya ninka mu’ujizai da Iliya ya yi sau biyu.b Elisha ya sake ganin dawakai da karusan yaƙi na wuta a Dothan, sa’ad da rundunar Suriya suka kewaye shi kamar yadda aka ambata ɗazu.
ELISHA YA DOGARA GA JEHOBAH
Ko da yake magabta sun kewaye shi a Dothan, Elisha bai ji tsoro ba. Me ya sa? Domin yana da bangaskiya sosai ga Jehobah. Mu ma muna bukatar mu yi hakan. Saboda haka, bari mu roƙi Allah ya ba mu ruhunsa don mu nuna bangaskiya da kuma wasu fannoni na ɗiyar ruhunsa.—Luk 11:13; Gal. 5:22, 23.
Abin da ya faru a Dothan ya sa Elisha ya ƙara dogara ga Jehobah da kuma rundunar mala’iku. Allah ya aika da mala’ikunsa su kewaye birnin kuma su kāre shi daga magabta. Sai Allah ya ceci Elisha da bayinsa ta wajen makantar da magabtan. (2 Sar. 6:17-23) A wannan mawuyacin lokaci da kuma wasu, Elisha ya kasance da bangaskiya kuma ya dogara ga Jehobah.
Kamar Elisha, bari mu dogara ga Jehobah Allah. (Mis. 3:5, 6) Idan muka yi hakan, ‘Allah zai yi mana jinƙai, ya albarkace mu” kuma. (Zab. 67:1) Hakika, karusai da dawakan wuta na zahiri ba sa kewaye mu a yau, amma Jehobah yana kāre mu kuma zai kāre dukan bayinsa da ke duniya a lokacin “ƙunci mai-girma.” (Mat. 24:21; R. Yoh. 7:9, 14) Kafin lokacin, bari mu riƙa tuna cewa “Allah mafaka ne a garemu.”—Zab. 62:8.
a Ba wurin da Jehobah da mala’iku suke zama ba ne aka kai Iliya. Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Oktoba, 1997, shafi na 13.
b Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Agusta, 2005, shafi na 29.